Showing 45001 words to 48000 words out of 93195 words

Chapter 16 - Tsaka Mai Wuya Complete Hausa Novel By Janafty .txt

Janafty   

10 Jul 2024

11461

Sauran littafai kuma yana cikin malaman MSS na makaranta yana kuma limanci a masallacin makaranta, Sannan duk karattukan da ake yi da Sadiq a ke shi Yazo karatun boko ammh kuma ya samu har da karin na addini kuma in ya koma gida Hutu ya rika Daukan Wajen Mallam Taju.
Sadiq ba bu abunda ya taba nema ya rasa a makaranta sai dai ma ya kyautar shine siyama marasa karfi Handout sannan ya dinga Rabon kayan abincinsa ga duk wanda yasan yana Bukata. Sadiq tausayinsa ga Mutane mai yawa ne.
Duk da Abba da mako da son abun duniya ammh Sanadin Sadiq yasa ya ke alheri a chan Shinkafi sai kiga Mutum na da lambar Sadiq ammh kuma ba shi ta Abba. Saboda abunda Sadiq zai yi maka Abba bazai iya yi maka ba shiyasa shi ba iya magajin gida ya ke ba, shi magajin kowa ne.
Shi kuma yasa Abba ya jawo yan'uwansa ajiki ya kuma ba da Kofar kowa na zuwa gidan Abba ayi zumumci.
Shi kuma ya saka Tsarin zuwa Shinkafi zumunci da kuma in sha'ani ya tashi Duk bala'in Innani bata iya ma Magajin gida shi ma kuma ya Fahimci har da Jahilci ke damun Innani shiyasa ya ke kokarin Gyara mata in tayi kuskure.
Maganar auran sa da Sultana kuma Umarnin Umma ce, Sannan Innani ta Dora Burinta shi kuma Umma da Innani suna da Daraja a wajensa shiyasa batare da Tunanin watarana zai iya shiga tsaka mai wuya ba ya amince.


Sultana ta taso ne da mganar Sadiq shine mijinta a bakin kowa. Yarinya ce shiyasa ba zata daura mizanin komai a yanzu ba ammh Abu daya ta sani Sadiq shine mijin da kowa yasan zata aura hatta iyayenta sun sani da Yan'uwanta, ta na zuwa Hutu ganin su ammh fa In innani ta yi ra'ayi har a yanzu Innani Tsine ma Shitu ta ke yi tace bakincikinsa da na matansa ya yi Sanadiyar Rasuwar Hauwa kulu.
Sadiq ya zabi ya yi karatu a zariya saboda Dalilinsa na zama in da Mutane ke harkokinsa ya yi kuma rayuwarsa kamar yadda daidai da yanayin da ya ke so Rayuwarsa ta kasance sannan ya zabi zama a Hostel saboda halinsa na son Mutame da mu'amala in da Mutane suka fi yawan zama.


Bai cika son zama gidan su ba saboda anguwa ce da ba ta cika Hayaniya ba. Allah ma yasa yana da yayye mata kadaici bai cika Damunsa ba in dai yana gida to kowa Burinsa ya faranta masa.
Suna kaunarshi kamar yadda ya ke kaunarsu. Duk da Mama na taba kishi da Umma ganin Innani ta fi sonta sannan ita ce uwar Magajin gida ammh bata isa ta raba kan ya'yan gidan ba. Ba bambamci Tsakaninsu duk Daya suka Dauki junansu musamman Sadiq ko da ya ke karami a acikinsu yana da kyakyawan Tunani mai kyau tunda ya karanta kuma ya gani.
Bayan Sadiq Mama ta kara Haihuwan Salima da Siyama wacce itace karama daga ita aka rufe haihuwa agidan Siyama ta zama autan Gidan. Sadiq kuma ya kasance Autan Umma Shalelen Abba da Innani.
Dukkansu matan sun yi aure a garin Gusai, Suba'atu ke aure a kano sai Saddiqa da ke kebbi.
A dakin Mama kuwa Sa'ima da Sakeena suma suna Gusai ne suna aure. Sahida na aure a katsina ita kuma Saliha na auran yaron yayar Mama ce suna garin Ibadan da zama in da ya ke aiki a kamfanin Dangote.
Kuma kowacce ta na jin dadi agidan da mijinta sun kuma hayayyafa da ya'yen su turbarkallah masha Allah.
Lokacin da Sadiq ya kamallah makaranta cikin yan'uwan sa ba wacce ta so ya yi bautar kasa a zariya ammh kuma Tunda yace chan zai yi ba su da tacewa barin ma Surayya da suke kira Big sis taso yaje kasar waje ya yi karatun liktanci tare da kanin Mijinta Sadiq yace baya ra'ayin haka.
Da farko Har Abba da Umma sun Amince Innani ma ta samu ta shawo kanta ammh A'a din Sadiq kad'ai ya isa da ya Rusa komai.
Dole a kabarshi ya tafi zariya again Bautar kasa. A wannan karon ma Abba yaso ya siya masa gida yace shima baya Ra'ayi sai haya ya kama da Farko a Daura Tahir ya so ya yi nasa Hidimar kasar ammh Ganin Sadiq ya koma zariya shima ya nema ya koma Saboda Abotan da ke tsakaninsu ta yi nisan da har Ahalin juna sun sani.
Sadiq yadda ake son shi yasa ko Kashi ya kai gida ya ke da Daraja. Shiyasa Tahir ya ke kamar dan gida a gidan su Sadiq duk kuma abunda Sadiq yace ayi masa Abba ba gaddama ya ke yi masa. Ranar farko da Tahir yazo yaga irin gatan da Sadiq ke ciki bayan sun koma Zariya ya kallesa yace"kai ko wani irin abu ka ke samu a garin nan da ka zabi irin wannan Rayuwar Alhalin kai dan gata ne?
Sadiq mirmishi kawai ya yi masa bai ce komai ba, Sadiq ya je ya sauke Farali kafin su gama makaranta shi da Innani Umra kam ya sha zuwa tun yana matashinsa.
Shekaran da suka dawo ne Innani ta fara fama da matsalan idon da yasa aka kaita asibitin ido Makka na larabawa da ke kano. Aka yanka mata gilashi Tunda ganin nata ya koma sai hankali sannan ga tsufa ammh bazata bar Halinta ba.
A rayuwar Abba in da ace yau ba Sadiq da Tuni lamarinsa ya wuce Tunanin mai karatu abunda ya zama Dole kawai ya ke yi. Ko zakka baya Fitarwa sai tasowan Sadiq yasa duk Shekara sai an fitar da Zakka sannan kuma yasa yana taimaka ma su Baba Sammani da kudi duk Damina suna yin Noma domin ci da iyalansa sannan in zasu tafi sai an cika booth da kayan abinci.
Gidan Innani da ta gada Tun iyayenta Abba ya gyara nan suke sauka in sun zo garin ,Sadaka ko akai akai Sadiq kan saka Abba na yi, ko a masallaci yaji ana neman taimako zai ce Abba zamu ba da namu taimakon Abba bashi da mgana sai dai yace zamu taimaka musu magajin gida.
Shiyasa yadda Mutane ke ganin kima da Girman Magajin gida wlh Alhaji Sulaiman ba shi da wannan kimar.
Kannenshi Mata su Hassu dalilin Sadiq su kan sazo gidan su da iyalansa su yi kwanaki sai dai zasu sha Mgana da Habaici bakin Innani ta yi ta fadin Sulaimanu ba mai kudi ba ne Rufin asirin Allah ne.


Wayar Sadiq ko da yaushe cikin kiransa yan'uwa suke yi, Alhaji Sulaiman kuwa wani sai ya jima bai kirashi ba Ammh Sadiq sha yanzu ne kuma mganin yanzu.
Da ka kira shi ka gayamasa matsalan ka shikenan.
Ko'ina ka je addu'a ce da Fatan alheri ga Alhaji da iyalansa Sanadin Sadiq Magajin gida.


*Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.*
*Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.*
*SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode*










*Janafty*
*TSAKA MAI WUYA.*


*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*


*11*


*Zariya*
Laraba.


Abubuwa biyu ne suka min tsaye a kahon raina a kwanaki nan.
Na farko yau kwanaki biyar cur mutumin da ke siyan Danwaken Sannan kuma ya kuma bar min chanjin naira na gugan naira har Dari biyu ya daina zuwa.
ina lissafe tun Alhamis da ya aiko aka siya masa bai kara dawowa ba har ga shi yau talata. Tun safe na ke duban hanya ammh shuru har su datti na kira na tambaye su sukace suma sun daina ganinsa yana zuwa. Acikin raina na ke ta faman wasi wasin to lafiya?
Wata zuciyar kuma ta kwab'eni da cewa"Hasiya kada zak'ewar ki ta cika yawa fa."
Nima sai daga baya naga na zak'en gaskiya mutumin da ban taba sani ba me yasa zan damu kaina Saboda shi? Sai wata zuciyar tace min ko ban san shi ba Cinikayar ya had'amu kuma sanin Mu'malace ka yi cigiyar abokin Cinikaryar ka.
Tun Safe da na zauna kujeran saka Danwake a tsakar gida na ke ta faman duba kofar gida da naga yaro ya shigo sai na Dauka shine, ammh kuma rashin ganin yar kular da ya saba aikowa ke sakarmin da gwiwa.
Maganar gaskiya ina cikin zullumi Ajiyar rai na sauke lokacin da Goma ta gota na gama Saka Danwake gabadaya har ya kare iya wanda zan ci kad'ai na rage.


Shi kuma abu na biyun da ke damuna Salisu ne! Ya na yawan Fad'omin a rai a kwanaki nan jiya har mafarkin sa nayi. Wai mun had'u na gaishe shi ya ki amsawa naga Musabahu a wajen da ya ce masa"Salisu Hasiya ce fa ke gaisheka ka yi kamar baka ji ba."
Kai tsaye naji muryan Salisu na Fad'in"Bazan amsa mata ba Musbahu koma miye faru. Bai kamata na kwanta Jiya Hasiya taki gaisheni ba."
Daganan na farka ina ta faman zufa. Tun daga lokacin zullumi na ya karu akan na baya. A bakin Mamam boy nake jin sun koma asibiti an kara Dubashi an ce sai karfen jikinsa ya shekara za'a cire masa.
Maman boy Idon gari ce ka rasa ina take samun wasu labaran, ko da ya ke Gantali ce da ita ba inda kafarta baya shiga da mijinta ya fita itama ta ke saka kafa ta fita kusfa kusfa a samaru nan anguwar Tsamiya Da'i da'i kun gidaje ne Maman boy ba ta shiga ba. shiyasa akwai labaran gidajen mutane da dama abakinta.
Nasan ko giyan wake na sha ban isa na dauki Siraran kafafuwana zuwa gidan Salisu da sunan gaishe shi ba. na tabbata Sahura sai ta kasheni kamar yadda ta kudurta in kuma ban mutu ba to tabbas zan samu manyan Rauninka da zan jima cikin Doguwar suma. tuna haka kad'ai kan kwabar da Niyyata ko Amma na kasa gayamata zuciyata duk da ta ganni suku suku da ta tambayeni sai na ce mata ban jin dad'i da Safen ne.
Amma na da wani irin hali ko ya ya na ke cikin damuwa ta sani sai da ta kalleni cikin Nazarina kafin ta kad'a kai tana fadin"Ko ulcer d'in ki ce zata tashi?
Kai tsaye nace mata"In ma itace ina da Sauran magunguna na ruwa da na kwayar sai na sha."
Kai tsaye itama tace min"In bazaki Jefa Danwaken nan ba a hakura yau Hasiya."
Ban bari ma na ja mganar da ita ba. Taga na mike na fara had'a kayan yin Danwaken sai ba ta kara mgana ba Ammh ta jima ta na kallona ta kuma san tabbas wani abu na Damuna to ta ina ma zatayi Tunanin bazan damu ba. Damuwa a gareni ta zama Tilas ko domin yadda na zama abun gudu da kyama wajen jama'a.
Ramatu na ke son gani ko zan gayamata cikina ta ba ni shawara, Shiyasa ina gama wanke wanken kayan da na bata, bayan na kai Daki na zo na saka ruwan zafi a rushin da na rage na leka Dakin Maman Boy nace ta aramin wayarta zan kira Ramatu.
Kai tsaye tace min"Gaskiya ba kudi acikin wayar"
Cikin mamaki nace mata"Ba kud'i? Ba shekaranjiya na saka Dari da zan kira Adda Fati ba? Kuma ba mu jima mu na mgana ba. Na dai san ban isa cinye wannan Darin ba."
Cikin tabe baki tace"To ni dai bansani ba, ban kira kowa da shi ba."
Ban kara mgana ba Na karb'i wayar na juya ban ko tsaya duba kudin wayar ba na leka kofar gida na kira Salihi na Dauki Naira dari da goma cikin cinikin Danwake na ce ya ruga ya siyomin Katin Mtn ya yi Sauri.
Sanin Halin Salihi da aikensa da sai ka mamta da shi ya ke dawowa yasa na koma Daki na fara kanta shi zan gyara Amma na saman gadonta barci ya kwasheta itama duk sai a hankali kwanaki nan da zazzabi ta ke kwana.
Har sai da na gama na share daki na wanke bayi saboda bazan iya shigarsa haka batare da na wanke ba. Na juye ruwa na yi wanka na fito na sauya kaya sannan Salihi ya dawo, Allah ya taimakeni ma ya kawomin katin lafiya.
Ina gama Loda katin na kira Ramatu daman na Haddace lambarta bayan ta Dauka mun gaisa da tambayan su Amma da Noor nace"Ke ina son ganinki kina gida gobe..?
Da zumud'i tace"To ni kuma ai goben nake shirin zuwa miki Yini ni da Noor. Gidan Inna zan kwana da Sassafe tahowa kawai zan yi"
Cikin jin dad'i nace"To shikenan ma sai kin zo d'in. Ki gaida inna Talatu"
Kai tsaye tace"Zata ji nima ki gaidamin da Amma da Habi auta."
Daganan muka yi sallama. Jin tace zata zo sai naji dadi a raina.
Ban koma na zauna ba sai da na Mayar ma Maman boy wayarta sannan na dawo na saka Danwake da manja da maggi naci.


Ganin Amma nata barci yasa na kwashe yan kayanta da suka yi datti na Daureye mata da nawa na aikin Danwake. Kayan ba su da yawa tunda wanchan Sati Habi ita tayi mana wankin kayan duka ranar Sati tunda ba makaranta.
Su datti na bama goma goma suka Debemin ruwa a waje. Ina mamakin yadda matan gidanmu ba su damu da sanya yaransu a makaranta ba sai dai su bar su su yi ta gararamba a gari ba arabi ba boko. Na taba yin musu mgana Maman Salihi tace min da na abinci za su ji ko da na kudin makarantarsu daganan sai na Rufe bakina. Duk da sai ayi abu Dari ban saka bakina ba yanzu sai kiji gori na tashi ni da ke da ababen gori gasusan kaca kaca.
Kwanakin nan ma da na ga Kaltume na jin Haushina daga ni har Amma bata kulamu kawai saboda mijinta na son Danwake na,ya kan siya ya ci kafin ya fita sai ta fara adawa da ni kai Tsaye kuma ta same ni ta min mgana cewa bata son na kara saida ma Mijinta Danwaken mu in tace bata so kawai a barshi kada rayuka su baci.
Amma na jin haka tace a barshi kawai saboda Kaltume ba ta tsoron Tijara Tundaga ranar ban kara saida masa ba ko ya aiko zan ce gabadaya an siye shi ba bu. Daganan na samu lafiya,ammh har alokacin bata daina min gani gani ba ita a tunaninta kada Mijinta yace ya na sona na saka ta uku ni kam a raina nace ta ya ya zai ce ya na sona? Shi kan shi ai baya so ya shiga cikin ukun ba.


*****


Washegari saboda zuwan Ramatu sai ban kwab'a danwake da yawa ba. Tunda tace min sabon gari ta kwana kenan zata iso nan da wuri, shiyasa tun safe na tashi na fara aikin Habiba ta taimakamin da wura gawayi ni har ta sakamin tukunyar Farko.
Daga baya na amsheta ta shiga wanka Saboda tafiya makaranta.
Cikin ikon Allah yau sai ga Mutumin ya aiko Datti da gudunsa ya zo min da kular ya na washe baki ya ce"Adda Hasiya ga Mutumin nan ya zo"
Bansan dalili ba sai da naji wani sanyi a raina na karbi kular da Sauri tare da dubu d'ayan da ya ke ba ni.
Ga mutane na layi ammh sai da na saka masa sannaan na mika ma Datti ina Fad'in"Ka ce masa mai Danwake tace lafiya kwana biyu bai zo ba?
Sai Faman mirmishi na ke yi ni kadai Har sai da Datti ya Dawo yana cemin"Yace tafiya ya yi shiyasa."
Kad'a kaina na yi a fili nace"Haba shiyasa naji sa shuru ashe.."
Har Datti ya juya na sake kwalamasa kira ya dawo na kallesa kafin nace"Tambayarka zan yi. Mutumin nan da ke aiko ka yaro ne ko babba?
Da Sauri Datti yace"Kai Babba ne fa."
Ya fad'a cikin nuna yarintarsa.
Da gudu kuma ya fita ya barni ina mamakin kaina na miye nawa na son sanin yaro ne ko Babba?.
Yau cikin Nishad'i na cigaba da Saka Danwake na zuwa tara na gama komai na share wajen, sannan na wanke kwanukan da na taba girki zan yi saboda zuwan Ramatu. Ammh sai nace bari sai tazo kada na Dafa ya yi sanyi.
Amma na fara saka ma ruwan wanka na juye mata ta yi tunda jiya bata samu yi ba, kokon da na Dama mata na sha nima tunda ba shi da Tsami sai waken da na saka masa manja kadan naci saboda kumburin ciki.
Kafin ta fito wanka na gyara dakin na Share ta na fitowa nima na shiga na yi, koda na fito na isketa ta shirya ta na zaune ta na shafama kafafuwanta man zafi.
Cikin yanayin mganarta tace"Hasiya nace ki siya ko karamar waya ce. Ta na da amfani tunda ga shi ina ta son na kira Adda mu gaisa ba wayar da zan kirata."
Ina shafa ma jikina Vaselin nace"Amma zan siya. Ki bari riban ya kara taruwa ba na so na taba ne kuma mu shiga har uwar kudin"
Amma ta yi mirmishi kafin tace"Hasiya ina zaki kai wannan tattalin naki?
Dariya na kyalkyalce da shi kafin nace"Amma rayuwar nan sai mutum ya iya tattali ballatana yadda Tsadar rayuwa ya kara Hauhawa."
Amma ta jinjina kai kafin tace"Hakane ina miki Fatan watarana mijinki ya Mori wannan Tattalin naki da hangen nesan da Ubangiji ya mallaka miki su Hasiya."
Na ji add'aunta acikin raina na amsa da Ameen batare da na ji acikin raina hakan zai iya kasancewa ba.
Na riga na Sadakar na gama aure a Duniya baxan kara yarda na auri wani ba. Ballatana nazo na zame masa matsala a rayuwarsa. Iya bakin Fentin da shafa ma kaina Dalilin Aure ya isheni ba na kuma Bukatar karin wani Tozarcin.
Amma itama ta Fahimceni sai ta sauya Hirar zuwa ta Adda Fati ta na Fadin"Oh Fati shuru kwana biyu bata zo ta dubamu ba."
Ina Zura Doguwar riga a jikina nace"kinsan ta yi ta fama da Zazzabi ita da yara. Ta na samun Sarari zaki ganta, Adda Rukayyace ma naga kwana biyu yan ganin Damanta ba su turo ta zo ba."
Amma tace"Itama sai da nayi mganarta a raina. Allah yasa suna lafiya su da iyalansu"
Ina Daura Dankwali nace"Amma lafiya ke shuru fa. Suna nan lafiya da wani abu ya faru da mun sani."
Amma na shirin mgana mukaji sallamar Adda Fati suna gaisawa da su Maman Boy.
Na kalli Ammi ta kalleni kafin nace"Amma Muryan Adda Fati ce fa."
Amma tace"Baiwar Allah ina ta zencen ta sai ga ta"
Ta na ko dago labule ta shigo nace"Kinsan yanzu Amma ke mganar ta ji ku shuru ke da Adda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login