Showing 1 words to 3000 words out of 69834 words

Chapter 1 - ABIN CIKIN RUHINA BY MISS BB.txt

Miss Bb   

10 Jul 2024

8259

ο»ΏMom Muhseen: πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’• πŸ’•
*_ABIN CIKIN RUHINA_*


Written by [Mrs bb]


Mom muhsen
*____________________________________*


*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*




*Allah ka bani ikon rubuta Abunda zai anfani Al,ummarka,Allah ka kiyaye mani harshe na ka bani ikon rubuta alkairi Ameen summa Ameen.*


1.


*1998*


Wani yaro ne da ba zai ga za shekara tara zuwa goma bah, ya tusa mahaifiyarsa ga ba kuka kawai ya ke saboda irin yadda ya ga halin da take ciki na tsananin labour...........murk'ususu take duk ta fice da ga hayyacinta, fita ya yi karo na babu iya ka tsakar gidan,wani d'aki Ya shiga Ya na kuka.


"Antu lantana ki yi hakuri ki zo ki taimaki Maah kar ta mutu......ga ta can ta na yin irin abun nan kamar na mutuwa.........Cikin Wata irin tsawa da tun da ya zo duniya bai tab'a jin irin ta bah....... Tace,


"Idan na sake ganin bak'ar fuskar ka Cikin d'akin nan wallahi sai na yi maka dukan da za, a kasa ganeka.......fita anan shegen yaro Mai shegen naci, nima halin da nake ciki kenan fita."


Haka ya juya ya na kuka bai koma d'akin ba waje ya fita ya shiga wani gida da ke kallon na Su da kukan sa......tun kafin ya fad'i abunda ya ke so matar ta tare shi cikin kulawa.........


"ya a Kai *Areef*?lafiya kuwa? me ya faru gidan naku?maman ka tana lafiya kuwa?."
Duk lokaci d'aya ta jera masa wad'annan tambayoyi kamar tana yiwa wani babba.


Yana shashshekar kuka muryar ta kasa fita sosai yace,


"Maah.......maah.......za ta mutu...... Ki taho karta mutu....."


Cikin tashin hankali ta jashi suka fice ko gidan bata tsaya rufewa ba.
Sadda Su ka je har faya ta fashe tana nishin wuya d'an na son fitowa........waje ta kora shi ta shiga tai makonta Cikin yar dar Allah sai ga jaririya ta fad'o wani wahalallen nishi ta sauke........dan danan jaririyar ta fara tsanyara kuka asan dai ta iso duniya.... Cikin lokaci k'an k'ane aka gyare su sannan aka d'ora sanwar wanka..........Areef sai tsallen murna ya ke kamar ya anshe ta hannun maah da ke bata nono, d'akin da Areef ya fara shiga ne Wata mata ta fito Cikin tashin hankali tayi waje.........duk kiran da Anni ke kwala mata ba ta saurare ta bah, zuwa can ta dawo nan ma Anni sai tambayarta take ta yi mata banza.........ita sai ma ta k'yaleta.... Lantana aka fiddo aka Kai Asibiti.


Alhaji farouk haifeffen garin Katsina ne,ne man Arzik'i ya kawo sa gari Abuja. Alhamdulillah an same shi kuwa don yanzu ya na zuwa Dubai da Sudan sarin kaya,matansa biyu Saudah ita ce mace ta farko da Allah ya bashi wacce A kullum ya ke Alfahari da ita, saboda aurenta shine Abun da ya d'aukaka shi har ya samu rufin asirin Allah,ya na masifar son matar sa sai dai matsalar farko da suka fara fuskanta, ita ce matsawar danginsa akan rashin haihuwarta da wuri, don alokacin sai da suka shekara goma da Aure Saudah ba ta yi ko b'atan Wata ba.......tsegumi dacece kuce ya ringa tashi akan wannan lamarin Idan ta shiga mutane an ringa harararta kenan, gashi Saudah ba mafad'aciya bace za ka jima ka na mata abu ba za ta tab'a tan ka ma ba,sai dai ta sha kukanta idan ya na kusa ya lallasheta ya ba ta hakuri, don idan ba shi ya bata ba bai San me zai ce mata ba, ana Cikin hakan tafiya ta same shi, bai saurari kowa bah ya d'auki matarsa suka cana Dubai............wannan tafiyar ta tun zura mahaifiyarsa.
"tace Don nayi ma ka Maganar k'arin aure shine ka gudu kaida matarka ko, to kaje ko inane ka dawo Ina nan Ina jiranka."


Basu dawo ba sai da suka shekara biyu.


Abun mamakin shine ganin Saudah da su Kai da yaro, Areef Kenan.
nan ma wata maganarce tai ta tashi, matar farouk ta haihu saboda bai d'auke mu bakin komi ba shine babu Wanda ya sanar ma.
...........hakan bai hana wannan auren ba Saudah tayi kuka kamar idon ta zai fita saboda bak'in Cikin halin da ta ke ciki, me ta yi masu su ke mata irin wannan k'iyayyar haka mai zafi.


Haka saudah ta ci ga ba da zaman hakuri da dangin mijinta, ta na ci gaba da kulawa da yaronta Areef wanda ta ke ma wata kalar soyayya, Wanda idan so samunta ne ko k'uda karya ta b'a mata shi.............wata biyu da da wowarsu akai bikin Alhaji farouk da d'iyar k'awar mahaifiyarsa........ko kad'an ba ya son lantana, ba ma lantana kad'ai ba shi duk wata mace kallon na miji ya ke mata idan ba saudar sa ba, jinta ya ke har Cikin *RUHINSA* kuma ya yi alkawarin har abadan ita ce *ABIN CIKIN RUHINSA* bai tab'a cewa ba ya son lantana ba,Ya barwa ransa don Annabi Muhammad [S A W ] Ya yi hani akan furta k'iyaya ga wanda baka so.


Zaman lantana da Saudah kamar zaman doya da manja,ko misk'ala zarratin lantana ba ta Kaunar ta,haka ko ya Areef ya rab'eta sai dai duka shi yasa Saudah ke kaffa kaffa da Yaronta.......Areef na da shekararsa hud'u Saudah ta sake samun wani Cikin, y'an uwanta sun ta ya ta murna da mijinta, mace da namiji ta haifa aka sa ma macen *SHAHIDA* namijin kuma *SHAHID* zan iya cewa wannan haihuwar ta janyo ma sauda wata irin kauna wajen dangin mijinta,
Aka fara juya ma lantana baya, yayin da su ka ta so ta gaba kan cewar bata iya komi ba sai dai taci ta yi kashi.
wasa wasa sai da lantana ta shekara biyar ko b'ari ba ta yi ba, nan fah kuma tsanar da ake ma Saudah ta dawo ga lantana,saboda daman ko kad'an ba ta ganin girman innah mahaifiyar Alhaji farouk,sai ta yi wata uku ba ta je ta gaida ta bah, idan gidan ta zo a wulak'ance ta ke kallon ta..........su ma sauran dangi duk haka take masu....... Kan Ka ce me sun dawo da kulawarsu A kan Saudah wadda Su ke ganin da can zalintar ta Suke.
......yanzu kuwa kamar su goye ta su ke ji...........haka lantana ta ko ma saniyar ware saboda bak'in halin ta,wanda hakan da ta ga su na mata bai sa ka ta canza hali bah..........haka rayuwar ta ci gaba da tafiya Areef ya na ji da y'an uwansa nan mak'otansu akwai matar abokin Alhaji farouk........lawisa yaran ta biyu, namijin sa,an Areef ne Macen kuma sa,ar Su SHAHIDA,tun da aka auri Saudah su ka kulla k'awance,don Mazajen su ma aminnan juna ne shiyasa su ma su ka had'a kansu abun gwanin sha,awa.........wanda takai har dangin Saudah sun san da lawisa,ita ma lawisa danginta sun san Saudah,
Akwana A tashi ba wuya wajen Allah, lantana su ka samu Ciki kusan lokaci d'aya da Saudah............wanda shine yanzu sauda ta sauka, ita kuma ta na kan hanya da sauran Aiki tukun..........Alhaji farouk ba yanan ya je Dubai akan wani kasuwanci da yake Fatan ya tabbata, Wanda idan hakan ta samu ba karamar nasara ya yi bah,don arzikin sa zai linka na da fintinkau..........da zai tafi twins suka matsa akai Su wajen ummin Dubai [yayar saudah ce d same father d same mother]
Dole ya tai da su don ganin halin da Saudah ke ciki na haihuwa yau ko gobe, koda akai ma Areef tayin zuwa yace Aa shidai ya na tare da Maah d'insa.............


*wannan kenan*


[Mrs bb]ce kuma
Mom muhsen
[5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•
*_ABIN CIKIN RUHINA_*


Written by [Mrs bb]


Mom muhsen ce


*____________________________________*


*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*




2.


Sai dare Saudah ta San cewar lantana tana Asibiti labour ta ke, lawisa ke sanar da ita Abun da ya faru da yamma.


Sai da suka natsu sannan Saudah tace,
"Annin Muhajid ya kama ta akira Abun Areef a gaya masa."


"tun d'azu na so inyi masa albishir to na duba wayar taki babu Kati, hankalina ya ya d'auku ga wannan tsaleliyar babyn,wallahi ba batun son kai bah Saudah baki tab'a haihuwar k'yak'k'yawar baby irin wannan ba, tun yanzu ma angane kyanta inaga ta girma."


Murmushi tayi tana gyara ma babyn kwanciyar ta.
tace,
"Anni kenan ai kuwa duk wanda zan haifa to saidai ya biyo bayan Areef A komai ma,don yaro na kin san indai ta nan ne to sai dai Ashafa fatiha."


"Ai nasan da shi nace haka nufina Cikin wad'anda kika hai...............innalillahi lawisa! Don Allah kiyi shiru Meyasa zakiyi maganar nan please na rok'eki karki k'ara irin haka,yanzu Idan Areef idonsa biyu kikai wannan maganar wallahi akwai damuwa, kin san shi da kaifin basira Abun zai zauna masa karshen ya titsiyeni akan maganar."


"yi hakuri Qawata wallahi na shafa,a Amman bazan sake wannan maganar ba nai maki alkawarin hakan."


Ajiyar zuciya ta sauke tace,
"Qawatah,wallahi son da nake ma Areef shahid da shahida bana masu irin sa,duk da kuwa haihuwar su nayi da cikina Amman ba na jin Su irin yadda na keji da Areef, saboda shine silar kawar mun da duk wani k'unci da nake ciki na rashin haihuwa,ta dalilin sa dangin mijina da surukata Su ka fara martaba ni, Ya fitar dani halin kuka da damuwar da na fuskanta don haka ko zan haifi singa da sabon gari wallahi bayan Areef suke,kuma insha Allah Cikin yara na babu maijin wannan sirrin,ke ma don na yarda da ke ki taya ni b'oyon sa don Allah."


"insha Allah Qawata daga bakina dai babu maijin wannan sirrin."


πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•


Sai washe gari aka sanar da y'an uwa da abokan arzik'i wannan haihuwar, Wanda Alhaji farouk ya kejin kamar an masa albishir d'in gidan Aljannah.
Saboda ana gama sanar da shi wannan labarin, abokin kasuwancinsu yayi masa albishir d'in burinsa ya cika, nan take ya yi sujjadar shukru, yana mai tsananin godiya ga Allah Lallai Saudah alkhairi ce garesa,haka zalika wannan Yarinya tazo da arzik'i,nan take yake sanar da Amininsa mijin lawisa cewar asaka ma yarinyar *UMMULβ€” KHAIRI*.


Saida lantana tayi kwana hud'u tana labour baiwar Allah,duk ta fice daga hayyacinta Akwana na biyar likita yace saidai aimata aiki, ranar Alhaji farouk ya dawo duk yadda lantanar take k'unziga mashi hakan bai hana yaji tausayinta ba, nan yasa hannu aka shiga da ita theater room y'an uwanta kuka kawai Suke da iyayenta.


Saudah Kanta taji tausayin halin da take ciki saboda duk taurin zuciyarka idan kaganta sai ka tausaya, har kuka tayi Areef kansa yaji babu dad'i.
Ba,a fito da ita ba sai bayan awanni biyar, ansamu nasarar fiddo jaririyar wadda ke kama da babanta kamar Alhaji farouk yayi kaki,anyi murnar sosai kafin ashiga nemo ran uwar saidai tun abun suna ganin baida wuya har hankalin Su ya fara tashi, don duk wata kafa ta sadarwar jikinta sun duba Amman babu alamun tana da rai.............sun kwashe awa biyu akanta Amman babu wani alamun zata tashi..........dole suka fito jikinsu yayi sanyi k'alau,da gudu y'an uwanta suka tare shi yaya lantanar.


Girgiza Kai likitan yayi yace kuyi hakuri Allah ya amshi Abunsa.............inna lillahi wa Inna ilaihir taju,un hazbunallahu wani imal wakil...........abunda Alhaji farouk ke ta Nana tawa kenan babu ji babu gani sauran kuwa banda ihu da kururuwa babu abun da suke, daga mai suma sai mai fad'uwa haka wannan rana ta zo babu dad'i,duk wani wanda keda alak'a da lantana yayi kuka kamar idonsa zai fita, na yarda da maganar hausawa da akace ko naman jikinka mutun yake yanka kullum,duk randa babu shi za kaji babu dad'i balle ace ma ya rasu.....hazbunallahu wani imal wakil Allah ya jikan lantana Allah ya yafe mata tayi shahada Allah ya haska kabarinta.


Abunda Saudah ke ta fad'a kenan,
Areef ganin halin da maah d'in sa take ciki Shima sai ya kama kuka, Duk yinin ranar ummul kairi tana wajensa sai idan tayi kuka ya kaita ta sha mama.


Haka akai sadakar uku Saudah ta anshi yarinyar tace zata shayar dasu tare, Allah ya bata ladar shayarwar, babanta yayi mata hud'uba da *ummu salma*


Haka aka share zaman makoki kowa rai babu dad'i, yayin da Saudah kejin gidan yayi mata girma, daga ita sai yaranta guda biyar ikon Allah kenan, kamar ba itace ke kukan rashin haihuwa bah shekarun baya, sai gashi yau Allah ya azurtata da yara biyar Cikin shekaran da basu Gaza bakwai bah.


Babu wani taron suna da akai, Alhaji farouk yadai yanka ma yaransa ragunan suna daga nan suka cigaba da kalawa da Yaransu.


Rayuwar taci gaba da gara wa yayin da Areef yake primary 5 zai zana common interest yaje js one, shahid kuma shida shahida suna primary 2 sai twince Dake da y'an watannin,kulawa Suke samu sosai shiyasa suke Wata irin kib'a tajin dad'i, Abunda Saudah ta lura shine Areef yafi nuna kulawarsa ga UMMU SALMA saboda acewarsa UMMUL KHAIRI ta cika kuka da fitina,da ya dawo daga makaranta ita zai fara d'auka yana mata wak'a, yana mata rawa duk kuwa ba wai yana k'in d'aukar UMMUL KHAIRI ba Aa yana d'aukarta Amman da ta fara kuka zaice,
"Maah wallahi *khairy* nine bata son na d'auketa kowa yana mata wasa lafiya lau Amman ni da nazo zan mata sai ta yi tayin kuka."


Sai tace,
"haba babban yaya ai shi yaya babba hakuri aka sanshi dashi, dukansu k'annenka ne kowa ce kuma tana buk'atar kulawar yayanta."


Tun daga nan komi zai ma guda to zaima d'ayar,har takai yanzu khairy ta daina masa kuka, har bata yarda da kowa saishi haka Itama SALMA.


Alhaji farouk likafa tayi gaba don yanzu ya bud'e sabon kamfanin sa na sarrafa yadiddika materials, boyels ne Gasunan wasu ma bazan ce ga sunan Su ba,ya zuba ma akata da yawa hada amininsa jafar mijin lawisa.


Hakan ya ka'ra karfafa zumuncinsu sosai har iyalinsu, don wata sa,in idan su shahida basu nan to tabbas suna gidan Dadyn Muhajid da Meenah,mujahid abokine ga Areef don babu Nisa tsakaninsu ashekaru,Areef zai bashi shekara biyu Meenah kuma kanwar Su shahid ce zasu bata shekara uku........don yanzu duka shekarar ta uku.


Gida Alhaji farouk ya fara ginawa na nuna ma sa,a yayin da zai gyara ma mahaifiyarsa wannan da suke ciki.


*shekara kwana inji y'an k'arin magana har gashi y'an yaran Maah sun girma, don yanzu kowace nada 12 years*


Mrs bb ce kuma
mom muhsen.


πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•
[5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•
*_ABIN CIKIN RUHINA_*


Written by [Mrs bb]


Mom muhsen ce


*____________________________________*


*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*




4.


Duk yinin yau Khairat bata fito ba,saidai salma ta ringa kawo mata abinci har d'aki,tunda ta dawo daga makarantar ko salma bata nuna ma result d'inta na,yah Meenah kawai ta gani Itama don tasan bazata fad'ama kowa bah, duk yadda shahida tayi akan ta bata ta gani cewa tai wai nata yab'ace idan ankoma hutu za,a sake dubawa.


Shahida bata yarda bah haka ta rabu da ita saboda sanin Khairat badai taurin kaiba.


Kwance take ta gama sallar isha,i tana saman abun sallar salma ta shigo jikinta yayi mugun sanyi, ta samu gefen gadonsu ta zauna kallon Khairat kawai take,zuwa can tace.


"sweetheart wai kina lafiya kuwa?."


Tana daga kwance bata ko d'ago ba tace,
"lafiyar kenan mekika gani."


Isowa tayi wajenta ta na tadata zaune,
"wallahi sweetheart baki da lafiya, bafa tun yau kike wannan Abunba I think tun fad'an................


"bana son tada abunda ya wuce kinarni na huta pls sweetheart."


"Shikenan kiyi hakuri, daman Abbu ne yake neman mu mu duka,ke kawai akejira."


Runtse idonta tayi tanajin Wata matsananciyar fad'uwar gaba,tabbas maganar result d'inta za,ai kuma tasan Yah Aree ya binciko repiting d'in da akai mata...........yau ita tashiga uku idan ya kamata, babu abunda ya tsana sama da kafad'i exams,ko Su yah shahid idan yaga sun fad'i suna gane kurensu, zai kawar da komi ya baka punishment.


"sweetheart karfa yah Areef ya biyo mu,naga yau cike yake damu bama mu ba wallahi har su Anty ma haka."


Tashi tayi tana jin wata masassara mai zafi na ratsa dukan jikinta,
Ko hijab d'in dake jikinta har k'asa bata cire bah tace,


"muje"


Haka suka jera suka tafi,yayinda Khairat duk taku d'aya gabanta yake tsananta fad'uwa, ji take kamar tayi fuffuke ta tashi ko kuma tayi Samara anemeta arasa.


Koda suka zo bakin k'ofar babban falon Abbu sai ta tokare ta k'ishiga, salma tayi tayi ta shigo ta k'iya dole ta kyaleta ita tashiga.


Zama tayi Maah tace,
"Ina Khairat d'in yo."


Cikin karyewar murya tace,
"Maah don Allah Kice kar yah Aree karya doki sweetheart,wallahi kingan ta can ta kasa shigowa tsoro take ji."


Dariya kawai Maah tayi don yau zata ga yadda za,a kaya Areef zai iya hukunta kannen nashi.


Abbu Ya kwala mata kira,
" *ta Alkairi* shigo kinjiko yayanki bazai maki komi bah."
Dayake haka yake ce mata tun da aka haifeta.


kasa shigowa tayi ganin tak'i shigowa yasa ya bud'e deep voice d'insa yace mata.


"wallahi Idan na iso wajen nan jikinkine zaiyyi tsami,dani kike bayani yau Allah kuwa."


shahid yace yana dariya,
"oga sweetheart ce fah."


Harararsa yayi yace" to ina ruwanka y'an saka ido."


Anty shahida da Yah meenah Su mujahid duk dariya suke mashi,
Kamar wadda k'wai ya fashe wa aciki haka ta fara bin bango kamar gizo gizo, sosai ta bashi tausayi, Amman baijin zai rangwanta akan wannan saken da tayi,tunda yasha fad'a masu cewar karsu had'a karatunsu da komi, karsu yarda damuwa ko wani Abu ya d'auke masu hankali akan karatunsu.


Kusada Anni ta zauna idonta ya cika tab da kwallah, k'iris take jira ta fashe kuka.


Abbu ne yace yah shahid ya bud'e taron da Addua
Yakaranto muka shafa.


Kasa Kallonsa tai don tasan had'a idonsu Wata masifar ce wajenta, Jitai Abbu yace.
"Kai shahid muga naka."


Ba musu ya mik'ama Abbun yayi ba tare da wata damuwa ba, don yasan baida matsalar komi.


Yaba mashi yayi sosai tare da mashi kyauta ta musanman, key aka bashi na sabuwar mota y'ar yayi, nan Yashiga murna kowa yana taya shi,ita kuwa ta kasa cewa Uffan.......Anty shahida ma kusan duk iri d'aya ne sakamakon, don naga Itama anbata kyautar motar saidai yah Aree ya ansa ya ba Anni yace,


"gashinan Anni ki ajiye wajenki har sai ta natsu sannan ki bata, wallahi ko bayan bani nan naji labarin kin hau mota batare da izinina ba kingama hawan mota saidai Idan tukaki za,ai understand."


Cikin rashin jin dad'i tace,
"yes."


Iri d'aya ce ita da Yah shahid,yah meenah Abbu yace ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login