Showing 51001 words to 54000 words out of 69834 words

Chapter 18 - ABIN CIKIN RUHINA BY MISS BB.txt

Miss Bb   

10 Jul 2024

8273

bb
Mom muhseen.


Wattpad name
Humaira7531.


DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.


46.


Wani kullutune ya tsaya man ga mak'oshi,daker nake had'iye miyau,banma lura ba ga hanci na keta gwagwad'a mata nono,saida ummi ta kaimin duka ga baya"don ubanki kasheta zakiyi ki kalli gabanki."
Sai sannan naja numfashi sannan na maida hankalina kan Airah,amman badan ina cikin natsuwata ba. gaishe da mutanen wajen tayi,tana gaida su ummi cike da kunya.
Annie saijanta take wai amarya bata yawo,kartayi bak'i,basusan wadannan kalaman jinsu nake kamar wuta.mimi ce ta kawo mata lemu da snacks,suna ta janta da hira harda salma,kmar na kamasu da duka haka nakeji.


Kusadani yazo ya zauna yana danna waya,dama tuni su ummi sun koma ciki,Airah baci tayi ysa na maida nono na ina rik'e da ita ga hannun.
"Oum Airah ga zulfa,a tazo ganin baby baku gaisaba,saida nayi daker na fizgo murmushin da iyakarshi kan lab'b'ana,nace.
"Sannu da zuwa."


Tana murmushi itama tace"barka khairat Allah ya raya Airah."
Daker nake magana "ngd sosai ga tanan,na mik'ama shi ita yabata sai kokarin ganin yasaka idonsa anau yake nak'iya,.ansarta tayi tana yabawa da kyanta don Airah abun biyu ya hade mata,don dr kyakkyawane sosai haka nima badon yaban kaiba,nasan im beautiful more.
Hirar su suke kamar sun saba da ita,salma damar gwanar surutu.
Husna ta fito daga ciki tayo sallar laasar suka gaisa ta zauna gefena tana mun rad'a.
"Waccen ce kishiyar taki."
Tureta nai ina banka mata harara nace"banson iskanci,karki sake mun haka don't like."
Dari ya tayi tana rufe baki duk yana kallonmu yace mata,
"Husna gulma ko,mekuke cewa."
Sanin danai husna ba karamin aikinta bane ta fadi abunda tace yasa na tashi zanbar wajen,naji bakuwar nacewa"ansheta khairat wucewa ma zanyi wlh inason zuwa saloon,saimun dawo suna."
Cikin rashin walwala nace"bawa mimi ta goyata zanje na kwanta inajin bacci,kigaida gida mungode."


Nayi wucewa ta shiya tashi ya rakata tayiwa su ummi sallama,sannan suka fita ya maidata.
Gaba d'aya hankalinsa yana kanta sauri kawai yake ya dawo yaje gareta,duk da baisan me zaice mata ba,amman yanada bukatar magana da ita yayi tsananin missing ganinta kwana biyar,sadda yashigo get di n anata kiran sallar isha,i dole tafito yadauki buta wajen maigdi yayi Alwallah yashige masallaci.


Yau wankan magaruba mukai,don fitowa ta kenan ba adora ruwan da wuri bane shiyasa.
Ina daure da towel ina goge jikina da wani,ummi kuma nayiwa Airah wanka sai kuka take,ummi na mata tsiya wai raguwa.....dariya nake masu na zauna ina shafa mai harta gama mata sannan ta mik'omun ita.
"Anshinan kinji ko mijina nacan najirana kina iya shiryata."
Shagwabe fuska nai nace"wayyo ummi wlh ni ban iyaba kar nakarya mata hannu,plss ki idasa ladarki shima dadyn ai bazai ce komi ba inkikace Amaryarsa kika yiwa shiri."
Hararar wasa tayi man tace"zan makeki wlh nikadaice ga mijina har abadan,don haka inma baki iyaba ki koya,kinjama daga yau kece mai shiryata,nan gaba ma wankan ke zaki ringa mata."ficewa tayi tabarmu murmushi nai ina daukota inajin wata irin kaunarta cikin raina,
"Kinji wai sweetie,ummi kishi take da ke karki anshe mata miji,kyaleta haushi takeji kinfita kyau."
Na sunbaci goshinta ina dariya kamar almara itama tayi dariyar,nanfa naita dariya ina biye mata kamar zararrah.
Riga na dauko ta bacci na zira sannan na dawo ina shafa mata mai,kamar ina tsoranta haka nake shafa mata shi.


Bayan dawowar sa masallaci ya zube falo duk hira ake,ana kallo dan zauna wa yayi ya lumshe idonsa yana sauraren bugun xuciyarsa,yunwa yakeji amman son ganinsu itada baby ya danne yunwar.........Annie tace "kana lafiya kuwa Areef."
Idona ya danyi ja yace "ba komi kaina ke ciwo."
"Ayya sannu kaci abinci kasha magani."
Tashi yayi nufi cikin gidan karo sukai da salma tace"sorry yah ban ganiba,"
"Ba komi ina khairat."
"Suna daki tana shirya baby Airah."
Wucewa yai itama ta wuce sadda ya tsaya bakin kofar jiyai numfashinsa yana d'agawa,runtse ido yayi ya bude sannan ya shiga da sallama.


Tun d'azu nake son saka mata kayan na kasa,daker nasa mata pant.
Waigowa nai jin motsi wajen kofa.........wani irin dokawa gabana yayi dandanan nad'an sha mur kadan,na ansa ciki ciki.
Isowa yayi ya tsaya bayana yana kallon mu sai jagwalgwala ta nake,me zatai ba kuka ba ni duk na rikice tunda yashigo,nama rasa me zanmata.
Jinai kurun ya sunkuyo ta bayana ya anshi rigar,sannan ya dawo gabanmu ya zauna daukarta yayi yana cewa"sorry my angel,ur mom she do not know yadda zata saka maki kaya gashinan duk ta karairaya maki hannuwa badole kiyi kuka ba."
Kirjina ya bada rass jin yace na karyata,cikin rudewa nace"dagaske najimata ciwo,wlh ban saniba ummi ce tace dole saina saka mata,wlh kuma ban iyaba."sai hawaye sharrrrr "donAllah mukaita asibiti,aduba karta mutu itama."
Ina kukana ina kallon yadda take shashsheka.
Murmushi yayi yace"ruwa ruwa to wasa nake,saiki goge hawayen."
Wata ajiyar xuciya nayi nace"ina sonta banson ta mutune kamar dayar."


Rigar yasaka mata yana cewa"dont worry insha Allah keda ita ever and ever." Maganarsa tamun dadi rirrigata yake yana kallon fuskarta yacigaba da cewa.
"Inama zaki ban ita idan anyi bikina ta zauna wajena,zulfa,a zata kula da ita fiyeda tunaninki because she love her so much,kamar yadda nakeson Airah itama tana sonta,pls inason Airah inaji kamar cikin jinina take,zaki ban ita oum Airah.?


Tunda yafara maganar naji zuciyata tana amsawa saboda dukan da take,kalamansa jinake kamar ni yake fad'a masu,saidai jin cewar inbashi ita zulfa,a zata kula da ita duk ya wargaza man mood dina........bansani ba bansan yadda zan fasalta yadda nakejin kishin wannan matar ba,banson ko sunanta ana kira man.taya ma yake tunanin zan iya bashi y'ata ta zauna karkashin ikon wata,watarma wadda nakejinta tafita daban daga cikin mutanen da suke haska farincikina.......jinaima kwallah tacika idona,ban bari tafitoba tunda daman kaina k'asa yake......jinai ya sunbaci kuncinta yace"kinji inason Airah zakiban ita."
Still kaina kasa nace cikin sanyin murya ina control din mood dina "kayi hkr bazan iya mallakawa kowa sweetie ba saboda nafi kowa bukatarta,kayi hkr sadda akai auren naku Allah zai baku taku kuma."


Shiru yayi yana rik'e da ita har tayi bacci kafin ya mik'e ya isa ga gadonmu ya sakata cikin net dinta,bayan yasake sunbatar ta yace"sleep tight my angel."
K'ofa ya nufa baice komi ba har ya b'ude kofar nace batare dana daagoba"tnx for helping me during labour."
Idasa ficewa yayi bayan yagama jin abunda zance.


Kwata kwata ranar ban iya samun bacci mai dadiba,kawai ina imagining ne yadda yakeji lokacin dazanyi aure,daman haka yakeji haka kishin yake wannan zafin duk na kishinne,da ker da taimakon kaina nayi bacci.


Areef wannan daren yasha kuka,don duk sadda ya kusanci inda take kamar karamai wutar sonta ake,shiyazayyi da wannan auren bazai iya yin rayuwar aure mai dadi ba alhalin zuciyarsa daruhinsa gabaki daya suna gawata,bazai iyayimata adalciba zai tauyeta zai cutar da ita,taya zai ganar da ummi cewa bason zulfa,a khairat yakeso.
Taya zai fahimtar dasu cewar itace farincikinsa,itace burinsa tsawon shekara aru aru.ina zai saka ransa soyayyar da yake mata shikanshi tana bashi tsoro,Amman sanin halin ummi shike tada mashi hankali,don ko duniyar zata tsaya bayanshi akan bazai auren nan ba babu wanda ya isa ya canza mata ra,ayi saidai idan itace taga dama.
Jahid najinsa yana sabbatu yayi kamar baijiba,don yayi alkawarin bazai ce mashi uffan ba,ai kukama yanzu kafara Areef indai akan khairat ne badai ka wulakanta ta ba abaya tukunna ma dai.


*********


Anyi sunan baby Airah taro yayi kyau,maijego da yarta sunsha kyaututtuka kamar hauka,don kudi masu sunan kudi khairat bazata iya lissafa yawansu ba,daga mai dubu biyar sai abunda yakai sama.
Sunsha kyau kamar kasace su karuga,masha Allah Airah tasha gayu kowa sai saka Albarka yake,gidan yacika sosai yan uwa nanesa dana kisa kowanyazo sai daidaiku da basu samu zuwa ba.
Haka dangin dr sun zo kuma sunyi bajinta sosai,ranar ma nasha kukan rashin dr don yadda yaci burin sunan lokacinan komi yace ai za,ai sunan da babu irinsa duk abuja.Ashe baida rabon gani Allah kakai rahma kabarinsa,itace adduata akodayaushe.


Taro ya watse saidai muce Allah ya raya maryam (Airah).


Bayan suna da sati biyu Areef ya shirya zai koma spain,saboda bai idasa aikin sa ba zaiyo wata guda,ga biki nata gaba towa baifi wata biyu ba,Abbu yaita fad'a cewar ba zaije ba ya tura yaronsa na office yatattaro mashi duk wasu ayyukan,amman taya zai tafi ga hidima anayi.


Haka dadynsa ma yace dadynsu yah meenah kurun yabashi goyon baya,yace ayi hkr yaje har yadawo abunda duk ya kamata ayi za,ai mashi sadda ya dawo saiyaji da sauran.
Kana dole suka hkr suka barshi ummi kiwa sai fada take,


"To wlh bazaka tai ba saika bada kudin da za,a idasa hada lefe,aibani zan maka lefenba."


Muna falo take fadarhaka nidai ina gefe inashayar da Airah,maah tace"haba yaya,don Allah kibarshi haka mana tun safe kike mashi fad'a ko abincin kirki baici gidan nan ba,kin tasoshi gaba sai bambami kike,kwana nawane idan Allah yakaimu,indai donta lefe ki kwantar da hankalinki wlh ni nagama hada komi."


Duk kallon mamaki sukwa maah,Annie xtace yaushe duk kikai bau sani ba,Amma gaskiya kin shaacemu."
Dariya tayi tace"kallonku kurin nake nariga nagama da wannan babin wlh,nabar maku nasu mujahid da Shahid."
Ummi tace"ai haka abun yake kinso danki ko zamugani dana shin danasu nawa zaifi kyau."
Nan sukabhau hirar kayan,already ni nagansu nasan kuma daman nashine.


Kallona yayi nai saurin kauda kai,don tun wannan maganar bamu sake maganaba illa gaisuwa,
Miko hannu yayi yadauki baby Airah data gama shan nono,bance komi ba ya shige ciki da ita.
Nasan meyake nufi idan na matsu inbishi in ansota, ya samu damar yimun magana,buris nai dashi banma motsaba nake ma Su maa maganar makaranta tata,don su yah meena final exams suke yanzu.
Tace na bari Abbu ya dawo inmai magana tasan shima cewai zai inbari Airah tayi kwari.


Tashi nai nazuba abinci naci har karfe goma bai dawo da itaba,babu kuma wanda ya lura balle yace ina take.gajiya nai nanufi daki nayi shirin kwanciya wauata dake gefena naji tayi kara alamar tex massege,dubawa nai naga yace _Come and take Angel_ tsaki naja najefawayar can gefe inacewa"wlh banzuwa inka gaji kakawota d'an rainin wayau,baka ga komi ba wlh saika gane baka da wayau."

Mimi ta shigo ta zauna gefena tace"oum Airah shawara nazo muyi."
Tashi nai ina kallonta nace"inajinki mekefaruwa."


Murmushi tayi tace"babu batun b'oye b'oye,kinason yah hargobe,shima kuma bama sainace maki yana sonki ba,kinsani.........enough mimi bansani ba,bansan komi yake ciki ba."........Aa oum Airah karkiyo saurin katseni,wlh duk wanda ke gidannan yasan halin dakuke ciki,kuma nayi imanin anyi shiru ne don aga iyakar gudun ruwanku,bawai ba asan halin da kuke cikiba."
Cikin fushi nace"mimi pls kibari banson in nuna maki fushina shin waima meye naki ciki nacemaki ni zan sake aurene,nida aure saina gidan aljannah insha Allah.,and pls idan wannan maganar ta kawoki workout."
Babu alamar fushi ko jin haushi kan fuskatar ta tace"shikenan,zaki gane menake nufi ni mai son farincikin kuce wlh i wish inganku kun mallaki juna..........oh may God,wai mimi nace maki knason mallakarsa ne..........kofar da aka bude yasa nai shiru,amman naso injuye haushina tsaye yake sab'e da Airah da alamar tayi bacci.
Mikewa tayi tace"saida safe"banza nai na kyaleta tazo zata wuce yawurga mata wani kallo,tab'e fuska tayi tace"wlh nifa banyi komiba........common get out yaceda ita."


Fita tayi sanna ya tura k'ofar da kafarsa,jallabiyace maroom da wani zanen kwalliya gaban ta,tayi masifar fiddo kyansa,haskensa ya sake bayhan cikin rigar,kauna kai nayi ina zaune fefn gadon ya k'araso yasaka Airah cikin net ya rufe sannan ya tsaya gabana idonsa akaina,aijinai kamar na kurma ihu azo afita dashi.
Tsaye yai rungume da hannunsa perfume dinsa sai bugarmun hanci yake,duk yayiman gigirin bisa kai.


"Nakiraki kin nunaman ban isa ba ko."


Sai lokacin nad'ago kaina na kallai,saidai nai nadamar kallon don jinai zuciyata tana man wata irin rawa,sadda kai nayi nace.


"I'm sorry banji kiranba shiyasa."
Stool yajawo ya zauna gabana sosai kamar zai shige cikina,yace"ban kirakiba text nai maki."
Banyarda nasake kallon saba nace"Ayya ban ma san inda wayar take ba banganiba,sorry again."


Numfashi yafesar har kan fuskata runtse ido nai na wani lokaci na bude yace,
"What mimi said."
Jinaigabana ya tsinke yafad'i,nashiga uku mezance mashi.


"She telling about me and u."
Nabani karfa ace yaji.


"What she tell."
"Nifa babu komi kawai tana maganar.........karkiyi karya naji komi,don haka kikwantar da hankalinki indai nine kinsamu,inhar dai zaki iya zama da kishiya ba damuwa zan hada dake."
Wani irin haushi da bakinciki suka cikaman zuciya cikin fushi da masifa nace,
"Ni bance komi akanka ba,hasalima ni babu wanda ke gabana inbanda Airah,bazan sake aure ba balle nayi ma mijina butulci,ni bazan iya mashi reable ba,don allah karka bata man mood dina nimezan dakai plstkatai dakinka kwanciya zan.............fizgo hannuna yayi idonsa cikin nau dasuka cika da kwallah yace,
"karya kike,u are lie kina sona kifito fili kifurta man tunkan lokaci yankure maki,karki damu zan soki ayadda kike i will manage u..............wata irin fizga naima hannuna na kwce n tureshi daga gabana,hawaye tuni sun wanke fuskata cikin fushi da kuka nace.


*"bansonka! I hate u too."*


"Ko maza sun kare bazan aure kaba,duk wanda yace maka ina sonka ya yaudareka,yes before bikina am sure Ilove u love u too,amman after and now Am sure 100% sure I HATE U I HATE U YAH AREEF,NA TSANEKA BANSONKA kadaina tunanin akwai tsarin sake yin aure cikin rayuwata,zaka yaudari makaryaciyar zucoyarka ne abanza don wlh bazan aurekaba ko duniya zata tashi ahalin yanzu ................idonsa kamar anzuba garwashi fuskarsa tayi jajawur,ya fizgoni ya rike kafaduna yana girgizani,cikin daga murya yace,


"Karya kike khairat,u still love me ever and ever,kuma sai in aureni nine nan mijinki babu wani duk fadin duniyar nan saini.........kofar dakin aka turo nafizge daga gareshi ina koma wa gefe ina cigaba da kukana.
Ummi ce da Annie sai su yah jahid da anty shida sai salma da yah meenah,shigowa sukai annie ketambayar lafiya.
Dagani harshi babu mai iya bada ansa,kukan danake yasa ummi ta sake tunzura ta daka mashi tsawa tace,
"Karkasake in sake tambayarka ,mekayiwa khairat kukan me take hayaniyar mekuke,dakai nake don ubanka.............mahana zaiyi ta daga hannu cicin karfinta ta kwasa mashi zazzafan mari......har cikin kokon raina naji marin,har saida na dago ina kallonta.
Kaina tayo tana masifa,
"daki ka dago rama mashi zakiyi don ubaki,nace rama mashi zakiyi ana tambayarku kin maida mu shashashu,........."
Kukana naciga dayi Annie tace"kiyi hkr inajin can tsakaninsu ne,ki kyalesu."


Ummi tankamana harara sannan tafita kowa yafita,Annie ce kirin bata fitaba tura kofar tayi taiso inda nake tana bubbuga bayana.
Tsawkn lokaci tana lallashina har nayi shiru.


"Wannan kad'ai ya isa ya nuna mana cewar abunda muke tunani haka yake,kowanenku yana son d'an uwansa.........saurin katseta nai nace"Aa Annie banson sa,ban kaunarsa pls kice yafita rayuwata,bazan iya wa dr kishiyaba......"shima cikin fushin yace"kinjiko Annie abunda take cewa,taya kunnena zai juri sauraren wadannan kalaman nata masu d'aci."


Annie tace"ya isa haka ban son sakejin maganar kowa,yarage naku ku sasanta kanku,yarage naku karku sasanta kunaji kuna gani zaku sake rasa junama wannan karon,don haka bawanda zan hana duk abunda yaga dama,don haka shawara tarage gamai shiga rijiya,don ingaya maku iyayaenku maza babu wnda baisan wainar dakuke toyawa ba,hakan kuma bai hana aurenka kai Areef,don haka kunga tafiyata."


Tafita tabarsu nan shima daga baya yajuya yafita cikin tsananin fushi.........zan iya cewa wannan darw babu wanda ya rintsa cikinsu,gashi gobe zai wuce spain early morning.




Share it pls.


Mrs bb ce
Mom muhseen.
[7/6, 7:25 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕
🌹
*ABIN CIKIN RUHINA*


Writing by mrs bb
Mom muhseen.


Wattpad name
Humaira7531.


DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.


47.


Washe gari tun asuba da mukai wanka nida Airah bamu tashiba sai eleven,sadda na fito ina sab'e da ita zanyi break naji gidan ya rage hayaniya.
Lami mai aiki na tambaya ina mutan gidan tace"maah dai tana ciki itada su shahida,salma da mimi sunje rakiyar Areef,.........tundaga sannan naji jina gaba daya ya dauke bansan me take sake cewa ba.
Zamanai da Airah ga hannu kamar kwai ya fashe man ga ciki.


Kamar marar lafiya haka na koma,kukan airah ya dawo dani daga duniyar tunanina.har cikin raina banso tafiyar ba,duk da haushinsa dana kwana dashi,hakan bai hana ni jin kewarsa ba.
Dayanzu ya dauki baby bai maido man ita sai tafara kuka kokuma tayi bacci,hawaye naji sun cika idona nai saurin sharewa saboda mutsin danaji bayana.
Maah ce da anty shida suka shigo falo,ina kan dining nayi tagumi ga Airah sai kuka take bam jin kukan,saboda halin da zuciyata take ciki.


Jinai kurun Anty ta dauketa tana rirrigata,maah ta banka man harara.
"Wahalalla,kicigaba da yi kar Allah yasa kidaina,."
Idona cike da kwallah nace"maah menayi menamaki kuma."
Tsaki taja ba wuce warta ta cigaba da huddodinta,kuka na rushe dashi saboda banson abunda kuma nayi ba,meyasa maah keyin haka duk dan sabida ita nake treating yah Areef haka,Amma Ku ma still ban yi daidaiba............Anty shida tace"ansheta kibata tasha sai kicigaba."
Ansarta nai natashi na koma dakina abincin da banci ba kenan,yini nai daki duk mai son ganina can yake samuna.
Babu wanda yadamu da damuwata,abun ya hademan biyu koma ince uku.
Ga soyayyar wanda nasan har abadan bazan samesa ba,ga canjin hali daga maah sai hantara ta take,.........ga kewa da tsananin begen Dr sai tunaninsa ya dawo man sabo.
Ganin abun ya isan naje na samu Abbu da safe kafin yafita.
Duk nayi zuru zuru cikin kwana biyu ita kanta airah,don Annie na shigowa tana ansarta da wuyar da xata sha tana da yawa,don ma tafara wayau yanxu.
Break yakeyi keyi na samu Maah tana saving dinsa,harara ta watsa man naji kwallah sun cika idona.
"Ta alkairin abbu iso mana."
Shiga nai ina rakub'ewa jikin kunera nesa dashi,ina goge kwallata,
"Zomu Karya nasan baki kaiga yin nakiba,"
Girgiza kai nai cikin sanyin murya nace"Aa kaci naka Abbu idan nafita zanyi nawa,dama nazo ne kan batun makaranta anshiga sabon session."


Kunun gyadarsa ya kurb'a ya saka tsokar nama baki sannan yace"nasan da haka,zan tura jahid sai yayi maki duk abunda yadace.,sai mekuma."


Sadda kai nayi nace "bakomi"


Na zo tashi yace "zauna ban sallameki ba."
Zama nai ina wasa da yatsuna........duk gudan yafita kaina ummi kanta duk ta canza to wai menayi masu haka.


"Meke damunki kwana biyu,bakida walwala kina yini dki bki shiga cikin y'an uwanki...........meke damunta daya wuce wahala,yarinya tana son kunyatani tadauki son duniya ta dorawa mashi,kamar shikadaine autan maza........"duk maah ke wannan maganar.


Tuni hawaye sun wanke fuskata shashshekar kuka nake kasa kasa,saboda jin abunda maah tace,ni yaushe nayi wani abu har da zai nuna masu cewar har yanzu inason sa,to banyi karya ba inasonsa har gobe amman me wlh yadda ta nuna bata sona dashi nima shiyasa nake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login