Showing 15001 words to 18000 words out of 69834 words

Chapter 6 - ABIN CIKIN RUHINA BY MISS BB.txt

Miss Bb   

10 Jul 2024

8267

tatashi Arref na mune halak makal, wannan yasa bamu dawo ba saida aka gama shayar dakai, ta dalilinka komi ya canza
Duk da saida kaddarar haihuwar salma tasa na sake wani auren, da marigayiya lantana uwa gareki salma, ranar da aka haifeki ranar mahaifiyarki ta koma ga Allah, saudah ta had'aki da khairat ta shayar daku batare da banbanci ba, kaji tushe mafari komi yanzu INA son ji daga gareka, shin zaka auri kanwar ka khairat kokuwa."


Idona akansa hawaye kawai kefita, yayinda kirjina yake wata irin duka, gyara zamanshi yayi yace.


*"Abbu kamar yadda maah tace nima ina ganin hakan din ne, kayi hakuri ni nadauki khairat kanwata ta jini ban tab'a jin sonta ba, koda na minty gudane idan nace zan amunce da auren zan iya kwararta, saboda bana son ta, gaskiyar magana ma SALMA NAKE SO BA KHAIRAT BA."*


INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJU, UN HAZBUNALLAHU WANI IMAL WAKIL.............kala man da nake ta nanata wa kenan cikin zuciya da kan bakina, duk iyayen AC din dake cikin d'akin sunkai shidda Amman zuface nakeyi ta fitar sharia, jikina har karkarwa yake gaba d'ayan falon yayi tsit bakajin motsin komi.


Abbu ne yayi karfin hali yace,
"Salma kina son yayanku."


Kallonta nayi naga ta sadda kai tana wasa da yatsun hannunta, kafin Anni tace,
"Ansarta kenan Abbun khairat alamun ta amunce kenan."


Jinjina kai yayi duk yana yinsa ya canza sosai, daka kalli fuskarshi zaka gane ranshi ab'ace yake.


"Kowa na iya tashi zan nemeku idan bukatar hakan tatashi."


Daya bayan daya haka kowa kefita jiki babu kwari, maah duk jikinta yayi mugun sanyi, ta kasa yiwa Abbun magana.


Tashi nayi zan fita don har wata juwa ke kwasata, jinai Abbun yace,


"Yaki nan ta alkairi, kisameni da safe kafin nafita aiki, kinjiko."


Ban iya bashi ansa ba kawai jinjina kai nayi nafita................






Mom muhsen ce
Mrs bb
[5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•
*_ABIN CIKIN RUHINA_*


Written by [Mrs bb]


Mom muhsen ce


*____________________________________*


*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition isV to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*




14&15


Basai na kwatan ta muku yadda daren ya kasancewa khairat ba,domin kuwa bacci duk yadda ya kware wajen sata to fah wannan ranar ya gagara satar khairat,yadda taga rana haka taga dare,don kasa kwana tayi dakin su itada salmar,kuka tun tanayi da hawaye har ya dawo idon ya bushe,wani irin zafi takejin kirjinta nayi kanta kamar zai rabe gida biyu,haka meenah tayi lallashin tagaji tayi bacci ta barta.


Duk wani tashin hankali da na kejin zuciyata aciki, nayi iyakar yina nayi control din kaina kafin gari ya waye,don nayi wa kaina rantsuwa da alkawarin idaniyata ta gama kukan *SO* kuma insha Allah zanba marad'a kunya.


Shirin bacci jahid keyi yana yi yana kallon Areef da ya kwanta kasa saman kafet din dake malale tsakiyar dakinsu,ko combus din dake kafarsa bai cireba balle ya samu damar fara canza kaya,girgiza kai kawai Jahid keyi don lamarin Areef abun yana kaishi Bango,tsaki yaja wanda Areef baisan ma yana yi bah..........


"Dallah malam tashi anan,kawani sheme kasa kamar Wanda aka aikowa sakon mutuwa."


Kallon jahid din yayi yana sauke ajiyar zuciya,lumshe kyawawan idanunsa yayi yana sake yin filo da hannayenshi,baice ma jahid komi ba.


Haushi ne ya sake turnik'e jahid,don ganin yaki kulashi wani tsakin ya sake ja yana hayewa gadonsu wayarsa yafiddo yana danne danne........tsayin mitina babu wanda ya sake kula kowa har jahid ya gama abunda yake yayi addua ya kwanta.
Sai lokacin yyi magana.


"Jahid baka ga kamar Abbu ransa ya baci sosai ba."


Cikin kuluwa yajuyo yana cemashi,
"Au sai yanzu kagane haka ashe,ai babu anfanin hakan wallahi kabani mamaki Areef,yadda ka bashi kunya ka nuna cewar kana bayan maah,kasan me hakan kenufi kuwa.?to bari ni na gaya maka,kanuna cewar bai isa dakai ba,kuma shi ba matsayin mahaifi yake wajenka ba."


Sai lokacin yayi saurin tashi zaune idonsa ya canza kala saboda damuwa yace,
"Karka fassarani haka jahid,taya zan dauki mutumen da ya haskaka rayuwata irin haka,kasan matsayin da naba Abbu ciki zuciyata kuwa."


Wani tsakin yaja yace mashi,
"Duk irin matsayin da kabashi baida wani anfani,tunda har ka wulakanta bukatarshi gaban kowa,kadaina cewa yana da babban matsayi wurinka."


Rutse idonsa yayi da karfi yana jin kamar ya kama jahid da mugun bugu,don jin irin kalaman da yake anbata mashi.


Cikin muryarsa data canza sauti saboda bacin rai yace,
"Karka sake anbata mani irin haka,na fadi iyakar gaskiyata ne saboda banson ya dauki amanar ta yabani inakasa rikewa,because i don't love her salma nakeso itace wadda na zabarwa kaina matsayin abokiyar rayuwata,akanme zanyi karyar yin abunda nasan ba zan yiba,idan kadamu ne saboda nace bason pls and pls jahid marry her."


Murmushin takaici yayi yana kallonsa kafin ya gyara jinginarsa jikin gadon yace,
"Areef kenan wallahi tallahi kaji rantsuwar dan musulmi ko,da ace babu wata acikin raina ban riga na furta inasonta ba,jiya dana baka mamaki gabankowa zan ce ni yabani aurenta,saboda khairat matan dake ma maza wuyar suce,kuma kaima nan gaba am sorry 2 say wallahi u will regretting."


Wani wawan tsaki yaja ya mike yashige toilet yana cewa,
"U are not in ur sense wlh,nidin zanyi regretting akan wannan yarinyar marar hankali,mtsss amman babu wanda ya kasheni irinka Allah ya isana wallahi."
.......yashige warshi.


Jinjina kai kawai jahid yayi yana hango yada lamarin zaikaya.


*************


Tun da na tashi da asuba nayi sallah nake karatun qur,ani saboda in kara samun kwarin guiwa,saida naji zuciyata tayi sanyi sannan na tashi yah meenah har ta koma bacci,fita nayi don har lokacin banajin bacci sosai saidai kaina da yayi nauyi saboda rashin baccin,kitchen nasamu anni tana had'a break dinsu Dady don dashi suke tafiya,itada maah idan yau wanan yyi gobe wannan yyi,tsarinsu gwanin burgewa.


"Annie ina kwana,ai ina cewa sadaqallahul azim nayo nan,saboda k'amshin girkinki d a ya hana hancina sak'at."


Murmushi a kan fuskarta tana motsa fruit salad da ta gama had'awa tace,
"Lafiya lau yar gidan Annie,Amman dai kinsan ko lashe bazan y'an maki ba ko."


Ansa nayi ina zubawa cikin mazubin da take niyar zubawa nace,
"Ba komi k'amshin ma da naji is okay for me,zai cika mun cikina."


Kallona tayi ina cigaba da idasa hada basket din break din nasu,cikin tausaya wa tace mun.
"Y'ar gidan Annie kallanni."


Banyi musuba na d'ago ina kallonta.


Hannuna ta rik'o dana gama saka komi tace,
"Bakiyi bacci ba khairat,karkice mani abunda yafaru jiya shine ya hana idonki runtsawa,idan kuwa haka ne to banji dadi ba,khairat shin ko kin manta da cewar yarda da k'addara mai kyau ko marar kyau imani ne,ladace mai tarin yawa karki soma yin halin irin na marasa ilimi,ke yarinyace mai ilimin addini dana zamani,zanso aduk sanda kika tsinci kanki acikin wannan halin kiyi anfani da iliminki,don haka kiyi mani alkawarin wannan shine karon farko kuma na karshe."


Kaina yana k'asa nace,
"Annie nayi maki alkawarin haka insha Allah."


"Yawwa diyar albarka naji dadin haka,nasan kuma tunda kikayi man alkawari bazaki karya ba,Allah yayi maki albarka ya kuma cigaba da karfafa maki akan komi,dauki break din kikai falon Abbunku shizai wuce dashi,dadynku sabko yayi don suna da bak'i."


Dauka nayi na nufi cikin fat dinmu,
Kowa bacci yake don lokacin karfe bakwai da rabi,falon na sameshi yana karanta jarida,maah na zaune gefenshi, yana yin dana gansu ya nuna akwai damuwa.
Sallama nayi na ajiye ina gaida maah,ta ansa cikin kulawa shima na gaidashi.


Nai zaune ina jiran ya fadan abunda yasa yace in sameshi da safe,jinai yace mum.
"Ta alkairi kije zuwa dare mun hadu,amman ki tabbatar kiyi baci isashe don idonki ya nuna jiya bakiyi bacci ba."


Ina wasa da hannuna nace,
"Insha Allah Abbu,saika dawo Allah ya kiyaye."


Cikin kulawa yace,
"Amen Allah yayi maki albarka."


Nace"ameen"na baro falon


Mom muhseen ce.
Mrs bb.
[5/27, 8:12 AM] Mom Muhseen: πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•
*_ABIN CIKIN RUHINA_*


Written by [Mrs bb]


Mom muhsen ce


*____________________________________*


*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*




16.


Daki na koma nayi dakin yah meenah na sameta tashin ta kenan,tana mik'a da salati.
Murmushi nayi mata ina hayewa gadon nace,


"Morning my dear."


Hararata tayi kafin ta sauka daga gadon tana cewa,


"Mai kukan banza kawai,wallahi saboda kuka wataran sai kin makance rab'o kawai."


Dariya nayi don yadda ta dage sai hararata take tana fad'a,
"Kinyi dariya mana ni kinga shigata wanka,kinsandai yau muke fara attending lectures ko."


Kwanciya nayi ina jan bargo tare da cewa,
"Wallahi yah meenah ko bature bazai nuna maki biting time ba,kiga fa kwata 2 eight muda keda lectures ten thirty."


Ta na daga cikin barth room din tagama wankeshi tana hada ruwan wanka tace,
"Kanki akeji don wallahi bazan ringa let ba,dana gama inhar baki tashiba saidai kisaman can,don na lura nawarki is too much wlh."


Dariya nayi nashige bargo don sanyi akeyi kwanan kamar kamarme.
Dandanan bacci yayi gaba dani don dama idon sai lumshewa yake saboda tsabar baccin dake cina.


**********


Areef ne da jahid suna wajen exercise dinsu,don wajene keb'entacce wanda aka k'awatashi da abubuwan more rayuwa,babuce babu awajen Abbune yafito zaiwuce ya hangi k'ofar wajen abude,yafasa shiga ya cewa driver yasaka mashi jikarshi baya yana dawowa.


Shiga yayi ya samesu duk sunyi gumi,jahid na kan machine din gudu Areef na gefe yana kan na keke......hira suke jefi jefi saida yagama kallesu sannan yayi gyaran murya,duk juyowa sukai suka kallo wajen...........da sauri areef ya sauko daga inda yake ya iso inda Abbun yake,ya dan rugumeshi yana cewa.
"Good morning Abbu."


D'agoshi yayi yace,
"Morning."
Jahid ma yazo ya rungumeshi ya gaidashi,don wannan salon tun suna yara sukeyinshi kuma Abbun ne ya koyar dasu hakan,don yanajin dadin jin yaransa ga jiki,Allah kadai yasan irin son da yake masu.


Duk suna zaune kasa shi yana tsaye,
"Ya kamata dai kamar yanzu kunfara zuwa office,ai kun huta haka nan ko."


Areef ya langab'ar dakai zaiyyi shagwabar da ya saba,Abbu yace.
"Karkace komi,sarkin son jiki kaikuwa wata macen ma tafika jarumta,don haka banason korafi idan na dawo am talking about that issue OK."


Duk suka ce yes Abbu tare suka fito suka rakoshi har mota,Areef ya bude mashi baya yashiga sannan yarufe,daga mashi hannu sukai har yafita...........
Komawa sukai suka cigaba d aikinsu,Jahid yace.


"Don Allah bakaji kunya ba."


Kallon haushi yayi mashi yace,
"Kunya! For what."


Jinjina kai yayi yaci gaba da abunda yake,saida yadauki lokaci sannan yace,
"Ka wulakanta bukatarsa jiya sannan yanxu ko kunyar had'a ido dashi bakayi,meyasa akullum baka damuwa da damuwar wani sai taka,wallahi Areef ur Always selfishness gay ka gyara wannan ba rayuwa bane."


Ran Areef yayi masifar b'aci ko kallon da yake ma jahid kad'ai zai tabbatar maka da hakan,cikin muryarsa data zama so deef yace,
"Duk Akan wannan yarinyar kake gaya mun magana yadda ranka yaso ko jahid,to bari kaji wani abu wallahi kalma guda da kake fadan marar dadi akan wannan vellege girl din karajin tsanarta nake cikin zuciyata,don haka ba zance ka daina ba plss continue."




Shi ma cikin tsananin bacin ran yace,
"Uhmmmmm Areef kenan i know u hate her very much,kawai don baka da rabone Allah yajuyar da lamarin,domin kuwa khairat ta fi karfinka don class dinta bana irinku bane,Amma kasani wallahi ba ayin shishshigi cikin lamarin ubangiji,ni bansan gaibuba shiyasa bazan yanke maka hukunciba,Amman insha Allah very soon sai khairat tazamema *dan hakin daka raina* sai khairat ta saka idaniyarka kuka,sai khairat ta saka ka jinyar da tunda kazo duniya baka tab'a yin ir......... *stop jahid.......* stop stop Areff ya fada cikin tsananin tsawa da b'acin rai.........takowa yyi har gabanshi ya daki kafad'arsa yace,


"Stop said that,because har abadan hakan bazai faruba,khairat k'anwata ce kadauka ciki daya muka fito,aure ya haramta agaremu,plss don't said that again banson b'acin raina yasa nayi ma yarinyar abunda har ta mutu zata tsaneni akanshi,don haka daga yau karka sake mun maganar that girl."


Janyewa jahid yayi yafice Areef ya silale kasa jikin bango dafe da zuciyarsa,ya lumshe idonsa shikad'ai yasan feeling din da yakeji ahalin yanzu,ya dauki almost thirty minutes awajen kafin yatashi ya fito.


Meenah ce tafito sauri kawai take don ganin goma saura minty goma, kad'an ya hana basuyi karo da Areef din ba,tayi saurin jaa baya cikin tsoro tace,


"Am sorry yah ban gankaba ne ina sauri,ina kwana."


Saida ya gama kalleta duk da har lokacin fuskarnan turb'une,sannan yace.




"Lafiya,Ina zaki kike sauri."


Kallon agogon hannunta tayi tace,
"Wlh yau muke fara attending lectures shine nake sauri."


"OK u can go."


Har ta juya tayi taku uku ya juyo cikin dakakkar voice nashi yace,


"Meenah"


Saurin dawowa tayi ta tsaya,
"Ke kadai zaki school dinne ina sweetheart."


Jin abunda yace ne yasa tasan bada khairat yake ba yasa tace,
"Ita sai offer monday suke farawa nida khairat ne muke starting."


Shiru yayi kafin yajuyo yace.
"Ta na Ina."


"Bata idasa shiryawa ba shine zanyi gaba,gudun yin let."


Jinjina kai yyi ya shige gidan ciki tafiyarsa ta takama,tasan tasota gaba zai shiyasa ta d'an jira A little bit.


Wanka na fito inata sauri tsane jikina nashiga yi kafin nafara mulke jikina da cream,idan kuka ganta sai ku rantse yanga take,Amman nan iyakar iyawarta take sauri,farar powder na saka da lipstick sai kwalli daya fito da ainahin kyawun idona,sunyi k'ar k'ar kamar farar takada kaya na fara kokowar cirowa,don aron kayan yah meenah zanyi,kasacewar size dinmu daya har shoes,kayan sunyi mun nisa yasa na jawo stool na taka,Ina cikin jawo kayan aka banko k'ofar dak'arfi wanda tsoro yasani fasa k'ara............stool din ta jurgud'e muka taho tare k'asa...............na sadak'ar karairayewa zanyi kawai.........amman sainajini nafado jikin mutun,jinai yace washhh..........wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke nafara bud'e idona surprise fuskarshi nayi tozali da ita..........idona cikin nashi ga towel dina ya gama tattarewa cinya waje,har d'an pant dina ana gani........babu alamun sakin fuska tare dashi,ganin kallon yaki karewa yasa ya sakeni k'asa timm.......wata kara na saki ta azaba,don k'uguna har saida ya ansa........kuka nafara ina murza bayana katseni yayi da tsawa.......


"Tashi anan ko in makeki ubanwa kikeyi har yanzu baki fitaba,ok tun yanzu kin fara wasa da karatu ko,to wallahi kika sake naga spill over ga result dinki kinshiga uku gidan nan,zaki tashi ki shirya ko saina tattakaki."


Kukana nake silently ina mik'ewa da k'er kayan nake kokarin komawa in dauko,don bankai ga jawosuba ya kallan yaja tsaki,hannu ya mik'a kurun ya fiddosu ya watso mani ga fuska.........ya fita yana cewa kisake na sake dawowa."


Haka nasaka na dauko log hijab dina nasaka da takalmi,matching color nayi na pink anda red........babu wanda nayiwa bankwana nafita......amman kafin na isa compound din gida na gyare fuskata,kamar komi bai faruba.
Koda muka shiga mota tace me yayi mani cewa kawai nayi fada yayi mun infito.........munje kan lokaci kowa ya nufi department dinsu,Alhamdulillah lectures din sunyi mani dadi nesa ba kusaba,don yawancin abubuwan duk i knowing them,Amman fa da alama zamusha lectures harsai munce masha Allah,ga azumi tafe kuma cikinshi zamu fara test,natsinci kaina cikin farincikin dana jima banjiba,nayi friend guda husna ladan........d'an zaman da mukai da ita na lura tanada natsuwa sosai,zanji dadin friending da ita,koda muka samu hutun thirty minutes mukaje capteria na nemi yah meenah ban ganta ba,na tambayi ko yan department dinsu sun fito akace sai four,wanda lokacin mu zamu koma sai six zamu tashi.


Husna ta siya mana lemo nikuma na siya mana pizzer da shawarma.......sannan muka koma muka cigaba da attending,na lura itama hazik'ace wajen karatun,shiyasa zan zage bazan yarda tafiniba.don inda kishi kan hakan,bazan yarda kafiniba saidai muzo tangal..


Muna class naga miss call din yah meenah,alamun sun tashi,saidai namata text cewar mu sai six tatafi da motar zanhau taxi.


Husna hostel take sai naji inama nima Abbu zai barni na zauna hostel din da nafi samun natsuwar karatun.......amman yau zan mashi magana Allah yasa ya yarda.


Koda muka tashi nayi wata irin gajiya,har wata juwa nake gani yasa nazauna na fiddo phone dina nayi dialing number yah jahid...........muna zaune da husna ta rakoni bakin get.


"Plsss yah don Allah kazo kad'aukeni wallahi bazan iya kawo kaina gidaba,wallahi nagaji."


Dariya yakeyi yana daidai fitowa daga gida yayi wani matsiyacin wankan yamma,dama fita zaiyyi takira daidai lokacin.


"OK my dear am coming now."


Godiya nayi ina kallon husna tana murmushi,
"Kincika rangwanta kinga mu mun d'an saba tunda tun satin akafara."


"Uhm tunda nake wallahi ban tab'a shan irin wannan wuyarba,lectures fah akwai dadi amman akwai gajiya wallahi."


Hira muke ahankali tana k'ara nuna man sauran abunda akai ban nan.....har sanda yah yashigo da motarshi da tasha wanki sabuwar prado dinsu shida yah Areef,don itace gift dinsu sanda suka dawo daga UK.......sun gaisa da husna tayi mun bankwana tatafi.


Har mukaje gida ina bashi labarin karatun mu yana kara karfafamu guiwa,anata sallah muka iso gidan yah Areef yana Alwallah bakin get da gani unguwa yaje yau,kafin motar tayi parking yah jahid yake cemun.


"Dear matsayin yayanki zan baki shawara kinjiko."


Na maida duk hankalina kanshi,


"Karki kullaci Areef akan abunda ya faru kinjiko,ki d'auka hakan damace Allah ya baki kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali,kicire shi daga cikin ranki kidaina kallonshi irin kallon dakike masa baya,ki kalleshi irin kallon da kikeman kikewa shahid,zaki samu kwanciyar hankali da natsuwar zuciya kin fahimceni."


Ina wasa DA azurfar hannuna nace,
"Nagode yah Kuma nayi maka alkawrin hakan,daman wallahi yah Jahid tun ajiyan banyi bacciba saida nayi ma kaina karatun ta natsu,nasan cewa samu da rashi duk na Allah ne,haka zalika wani baya auren matar wani,nasan cewa wata kila daman badanni akayishiba rabon yar uwatane,har abadan zancigaba da yi mashi kallon da yakeman matsayin k'anwarsa ciki guda,nima matsayin yaya shahid zan cigaba damai namaka alkawarin cire wannan feeling din."


Murmushi yayi mani yace,
"That my dear khairat"
ya bani hannu muka tab'a sannan muka fito angama sallah lokacin,har yah Arref yafito daga masallacin cikin gidanmu....kallonmu yayi yana ma yah jahid alamar baiyyi sallaba,yace"sorry oga yanzu zanyi ai,dear jeki gida ayi sallah da wanka ahuta ko."


Nace to tare da bin bayan yah Areef har na cinmmashi naji yace mun"ba gaisuwa ta Alkairi."


Mamakinsa ya kasheni amman sai ban nuna bah nayi murmushi nace masa"sorry yah ina wuni."
Gaba yayi yana cewa"lafiy ya school din".
Answa nayi nima na shige d'akinmi don duk yau banga salma ba,da maah.


Mrs bb ce


09034722970
[5/28, 2:22 PM] Mom Muhseen: πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•
*_ABIN CIKIN RUHINA_*


Written by [Mrs bb]


Mom muhsen ce


*____________________________________*


*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*




17.


Salma ce da k'awarta raihana suketa kwasar dariya cikin d'akin,har basujin sallamar da nake.......abayar na cire ina cewa,
"Sai Ihu kuke har ba ma kujin sallama ko."


Wani kallo naga raiha nayi mun kafin ta sake kwashewa da dariya,salma na taya ta binsu nayi da kallo tsayin lokaci kafin na shige toilet,don na lura wanan dariyar dani suke kuma babu tantama salma labarin abunda yake faruwa ta bata,nasan kuma wannan labarin kaf k'awayenta ta basu shi........wani takaici ya kamani har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login