Showing 24001 words to 27000 words out of 69834 words

Chapter 9 - ABIN CIKIN RUHINA BY MISS BB.txt

Miss Bb   

10 Jul 2024

8280

karfi alkalamina.
Tun daga bakin get d'in wajen nake baza idon ina zan ganshi,don baka shiga saida get fast,wanda duk zaishiga saiyabada kid'i sannan subashi get fast din,idan kuma kagama zaka barmasu abunsu nan.
Tsaye nayi ina kallon masu shige da fice,wani daga cikin masu kula da waje ne ya iso inda nake yace"madam bismillah,ga yallaban can yace ayi maki iso."
Bin bayanshi nayi abayace jikina har k'asa saboda fakistan ne jikina riga da wando...........wajen babu yawaitar jama,a don inajin akwai ranakun da zakazo kasamu mutane fiye da haka.
Wani waje muka nufa naji zuciyata tana bugawa fast,runface maitsananin kyau wajen grass capet yakara fiddo kyan wajen,saidai zuwa yanzu bn ganin kyan wajen,saboda abun nani da firgtni,kocikin miliyoyi mutane naganshi dole shaida shi.....duk tuku guda danake jinake kirjina zaifad'o saboda tsabar fargaba da firgici........bayashi kurun nagani Ammn zuciyata kakarwa take,meya kawosji wajen nan nashiga ukkua ni khairat.


Wlh ngaji pls sorry mu hadu gobe.


Mrs bb ce.πŸ‘ŒπŸ»
[6/5, 11:43 AM] Mom Muhseen: πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•
πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•
*ABIN CIKIN RUHINA*


WRITTEN BY (MRS BB)
MOM MUHSEEN.


*GODIYA TA BATA DA IYA KA AKAN KU MASOYANA,HAKIKA KUNE JIGON LITTAFINAN,INA MATUKAR ALFAHARI DAKU AKODA YAUSHE,ALLAH KUMA YASAKA MAKU DA MAFIFICIN ALKAIRINSA,INASONKU KAMAR YADDA KUKE SONA.*


*JINA GAREKI UWARIDAN SARDAUNA FATIMA,MARUBUCIYAR SOORAJ ALLAH YABAR KUNA KEDA MAIGIDANKI*πŸ˜‚πŸ˜‰


*not editing*
Idan kunga mistake kuyi hkrπŸ‘ŒπŸ»


24.


Wani irin tuntub'e ne nayi daya yi silar fad'uwar pos dina,dama d'an rakiyar tunda yashigo dani wajen yajuya tunda naga inda zanje,duk'awa nai na d'auka inajin d'an yatsana yana jinga babban,d'agowar da zanyi naga wayam inda yake zaune su biyun saura Dr amman shi banganshi ba,murje idona nayi sosai amman ban ganshiba ko iskar da ta d'eboshi ban ganiba,waige waige nake amman ko b'urbushinsa ban ganiba.......jikina yayi wani irin sanyi nabani uku wai k'alau nake kuwa kodai tsoron sa ne yasa naga kamar shine awajen da farko,k'arfafa zuciyata nayi na karasa wajen ina ajiyar zuciya k'asa k'asa.
Tun kafin na zauna yake kallona yana zaune kan kura ga table gabansa an k'awata shi da yan kayan ci kadan,yad'ora kafarsa kan d'aya yarik'e hab'arsa da hannunsa,fesincap ce kansa wadda ba sosai nake kallon cikin idonsa ba,tabbas Dr ya hadu hadedden guy ne,wanda ya iya daidaita wankanshi,jeans ne dark blue sai light blue d'in shirt tabi jikinshi ta kwanta,agogoce d'aure ga hannunsa na hagu sai daukar ido take,kamshi ketashi mai tsananin shiga rai da kwantar da hankali,har lokacin kallona yake nikuma ina tsaye,da hannunsa ya yi man nuni da na zauna,kujerar dake kallonsa jikina yayi wani lakwab haka na jaye hijab dina na zauna ina wasa da yatsuna,nakasa kallonshi,don bazan iya had'a ido dashi yana mun irin wannan kallonba.
Cap din naga ya ajiye gabanshi ya tashi zaune sabanin da dayake kwance cikin kujerar.
"Ina wuni."
Wayyo kamar zan nitse haka nakeji,kunya ta kamani mema yasa tunda nazo ban gaidashi ba,kasa ansawa nayi inata matsar yatsuna kamar zan tsinkasu,kozafi banaji wanda da kalau nake bazan iya sarrafasu irin haka ba.
"Karkijima kanki ciwo,yana zuba lemo cikin cup fuskarshi da murmushi wanda kokad'an baya yinsa cikin class.


Mik'omun yayi "bismillah,ance in kayi bako first abunda zaka taryeshi dashi shine abunsha,kafin komi yabiyo baya."


Duk na kasa sakewa gashi sai kallona yake ni kallonne bansaba dashiba,yana ban kunya kuma idaniyata bazata zureba.
Cikin low voice dina da bansan dalilin sanyinta ba nace"sorry sir good evening."
Sautin murmushin sa naji yana rik'e da cup din ruwa saida ya kurba sannan yace"bazan ansa ba tunda nima baki ansa tauba."
D'agowa nai nad'an kallai kafin nasadda kai nace"sorry sir bazan it ansa gaisuwarka ba,bacin ni yadace nafara gaidaka kuma banyiba,I'm sorry na shafa,a ne."
Ajiye cup d'in yayi yana tattara duk hankalinsa kaina,
"Me ya shagaltar dake,nagadai ko kallona ma bakiyiba balle nasaran ko *Muhammad kamees* ne ya d'aukar maki hankali."
Innalillahi wayyo Allahna wannan guy din ya iya bada kunya,jinai kamar inzura aguje.
(πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚basaban ba khairat)


Shiru nai inata murzar hannuna nakasa cewa komi,to mekuwa zance mai jinai yace"kinyi shiru,kisaki jikinki bafa sace ki zanba wallahi ban iya satar mutane."
Dariya yaban bashiri murmushi ya kubcemun mai had'e da dariya,rufa bakina nayi nakara sadda kaina inayin abuna.
Inajinsa yana tayani amman nashi babu sauti sosai.
Saida nagaji nadaidaita kaina yace,
"Haka kika iya dariya,
Aikuwa zaki koya man nima naringa yiwa budurwata."
Kallonsa nai bance komiba murmushi dai nake yi.
"Meya hanaki zuwa class 2days,anyi abubuwa dayawa bakyanan."
Nad'an saki jikina nace masa
"Wallahi bana da lfy kwana biyu amman nasamu sauk'i,husna tana mun bayani idan ta dawo."
"Kin tabbata tana yi maki,"
D'aga kai nayi murmushi yayi yace "to bari mugani idan bayanan sunzauna kanki."
Tambayoyi yashiga yiman ina bashi ansa tare da bayani sosai.
Tab'i yashiga yimun yana cewa "good,very nice gaskiya husna ta cancanci kyauta kibata wannan inkin koma."
Wata envelop ce ya mik'omun.
Kallosa nai nace"sir kabarshi ai basai kabata wani abuba."
Gabana ya ajiye yana kallon cikin idona yace"don me basai anbata ba,bayan tayi abunda ya farata man,kefa ta yiwa taya bazanji dadiba."
Sadda kaina nayi nama rasa mezance masa wlh
Dole na k'akaro smile nace"to tagode."


Shiru muka sake yi na tsayin lokaci,kuma har yanzu idonsa akaina wlh jinake kmar in bace sabod wannan kallon nashi.
Ga magaruba tataho dandanan hankalina ya tashi,saboda ganin bakwai saura minty talatin.


"Da alamun dai kin k'osa kibar nan ko,ban tunanin wajen bazai burgekiba aida munje *kalam guiden*."
Yak'e nayi nace"Aa wlh yayi kyau,sosai wajen akwai nishad'i."
Mik'ewa yayi yana cewa"musanman idan akwai wanda ya sace mka zuciya awajen ba."
Ban tashiba nabishi da kallo,shima ni yake kallo wanda bazan iya jure shiba,inda nake ya iso yad'an sunkuyo ta gefen fuskata kamar zai sunbaci kuncina,dandanan jikina ya kama kerma runtse idona nai injin kashin turarensa yana huda gashin jikina,i wonder nakejin something akanshi,mekenan nashiga ukkuna.
Cikin wata murya da tayi masifar tada tsikar jikina yace" *ummulkhair,why kika mun irin wannan satar plsss ko kinsan kin kassarani akanta,na zama zero tundaga lokacin da kika yimun wannan satar,plsss ki maido man kayata in samu relief.*"


Tunda yafara magnar kirjina ke bugawa babu k'ak'k'autawa,na k'an kame jikina da nakejin kamar yana zarar raina kamar yana fiddamun duk wani kuzari dayayi saura cikin jikin. Wata ajiyar zuciya nasauke mai mugun sanyi jin yatashi daga inda yake,bud'e idona nai ina jin kamar na fasa ihu akan yanayin danaji.
Pos din ya d'aukarmu namik'e shikuma ya jaye kujerar nafito,tare muke tafiya zuwa inda yayi parking.
"Bakice komi ba."
Fuskata kamar zanyi kuka na kallai nace'pls wlh bansan abunda na satar makaba kayi hkr."
Dariya yashigayi yana shafa kanshi,hannunsa yana rik'e da cap dinsa,
"Gaskiya ba zanyi hkr ba sai kin biyani,idan kuma baki biyaniba zan rama idan na tashi ramawa naki sai yafi zafi,don ko har kuka saina saki."


Shiru nai banda ansar bashi,a matsayina na yar jamia wacce ta waye tasan kuma me ake kira da so,to dole nasan me dr yake nufi da kalamansa akaina,nagane komi yke nufi dani nagane kenan yadda na sace mashi zuciya shima yna nufin zai sace tawa.
Hakika zan iyacewa zuciyata babu kowa aciki,empty set take amman kuma inajin can k'asan raina wani gurbi da wajen yake yawan bugawa,muddin naji wani feelings akan DR hakan meyake nufi,basan me hakan yake nufiba nabarwa Allahn daya halittamun wannan zuciyar.


Bud'emun gaba yayi nashiga yazagayo yashiga,fita mukai mukai mukanufi school,jana yake da fira anman nakasa sakin jikina nabiyeshi,saboda maganarmu dashi ta karshe itace kemun yawo akai,wani gefen zuciyata inajin tsoron Kamuwa da sonsa,wani shashen yana nuna man idan nakamu da son nashi menene,wanda kikemawar dai akwai babban ginshik'i tsakaninku,duk yadda kikakai ga son kasancewa dashi yariga ya zama haramiyarki.
Rutse idona nayi inajinsa yana ta gayaman wsu kalamai wanda babu tantama dr zai iya yin nasarar sacemun zuciya cikin d'an karamin lokaci,kamar yadda yafad'a man.
Bakin get d'in hostel ya saukeni saida nayi dagaske sannan yabarni nashige..........Allah Allah nake na isa d'aki,don inji shin an aiko nemana,inhar an aiko to tabbas yah yazo,inkuma bai aikoba hakan nanufin baizoba.
Don yanzu takwas harda minty ashirin.


Husna na tadda tana bud'e wata katuwar ledar shooping,kayane gasunan birjik kamar ba,asan zafin kudiba aka siyosu,tsayenai ina kallon kayan,nidai nasan Dr bai ban komiba ,haka bai aiko kowaba to waye zai kawo,kodai husna aka kawomawa.


Jinai tace"sai yanzu kenan,da alama Dr yasamu karb'uwa."
Banbi takan kalaminta ba nace"bak'o kikai husna."
Mik'ewa tayi tana jingina d bango tace"aa,ke aka kawowa yayanki ya zo bazan iya lissafa adadin mutanen daya turo nemankiba,inacewa baki fito lecture ba,karshe hardai nace bakidawo d'akiba.
Baiyi minty goma da tafiya ba ga kaya nan ya aiko dasu abaki,hada wasu cards idan kin duba duk zaki gani."
Silalewa nayi k'asa wata zufa na karyomun zuciyata da sauri take bugawa............


Mrs bb ceπŸ‘ŒπŸ»
Mom muhseen


09034722970.
[6/6, 12:48 PM] Mom Muhseen: πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•
*_ABIN CIKIN RUHINA_*


Written by (mrs bb)
Mom muhseen.


*Dedicated by ZAUREN MRS BB* πŸ˜‰πŸ’•


*watt pad*
*HUMAIRA 7531*


*GODIYA MARAR IDADI GAREKU MARANTA LITTAFINA,INA MAKU FATAN ALKAIRI.*


*not edited*


25.


Duk nayi zufa hijab din tajik'e sharkaf,wallahi inajin tsoran yah inajin tsoron yasan wani abu tsakanina da dr,shin idan ya tambayan inda naje inazance mashi,bayan nidakaina nace ya saman school at 7:00 pm gashi kuma yazo ni bandawo ba,damuwata wannan karyar danayi cewar naje lecture bayan kuma tabbas yah ne nagani tareda dr wajen sahad guiden,nabani nalalace yazanyi.


Hus na ce tatako har gabana,ta durkusa tana cireman hijab dina da gyalen fakistam dina.
Cikin kulawa da nuna damuwa tace taso saga nan zauna nan,ta kamani muka zauna kan katifar mu.
"Meye faru,duk wannan tashin hankalin nameye,shin mala,ikane yayan naku da har kika tsorata dashi haka,haba khairat ki dawo natsuwarki mana,kefa yar jamia ce babbar budurwa mai daukar overaller na department dinmu,kyakkyawa maiji da wayewa da kudi da kokari,taya zaki ringa jin tsoron namiji irin haka duk da bansan dalilin tsoron nakiba amman yayi yawa,kozan iya sanin alakarku dashi."


Jingina nayi jikin bangon dake bayana,ina dunkule kafafuna nasauke ajiyar zuciya maikarfi sannan na kalleta,
Cikin karyewar murya da low voice dina nace"husna,idan nace maki yah badan gidan mu bane hakan ba gaskiya bane,saidai zan iya cewa shid'in ba uwarmu daba haka ba ubanmu dayaba,shid'in dane ga yayar mahaifiyata maah.
Nabata labarin abunda nasani da wanda naji bakin su Abbu,da yadda nakamu da sonsa shekarun baya harda ciwon zuciyata,komi nasanar da husna har kan abunda kefaruwa yanzu da abunda salma keman.


Jinjina kai kurun take tana kallona,kafin ta nisa tace"tabd'ijam,yanzu ya kenan kina ganin cewa yanzu zai iya dawowa yanuna yana sonki,kokuma mekike tunanin ya kawoshi wajenki.
Ban bude komiba cikin ayancan akawai ina fiddo kayan ne,akwai cards ciki idan kika duba muna iya samun ansar abunda mukenema,kuma yanzu ke yakikeji cikin ranki akanshi."
Zamewa nai na kwanfa ina kallon sama nace"banajin komi kanshi banajinsa irin yadda najisa shekarun baya,bana jin feelings akanshi irin shekarun dasuka wuce,husna saidai abu guda inajin tsananin tsoronsa wanda nikaina bansan daliliba,daidai da second idan muka keb'e ko nake kusada shi in takaice maki har suma ina iyayi.
Basan why ba inson daidaita alak'ata dashi kamar sauran yan uwana,amman nakasa wallahi bazan iya cemaki da reason guda dayaba dayasa nake mashi wannan tsoron,..............


"Lallai na maganar maah,datace maki something behind,tunda ada kince ba haka kuke ba dole akwai dalili kece baki saniba,amman nasan maah tasani bazadai ta sanar dakeba."
Kallon husna nayi nace"kin tabbatar da haka kuwa."
Murmushi tayi mun"na tabbatar saboda tace maki tana ankare da duk abunda kowa keyi,kuma zata san abunyi.
Kishirya kije gida kuyi magana zaki tabbatar da maganata,ance zato zunubine koda ya kasance gaskiya,ina zargin yar uwarki da yin wani abu duba da yadda kika gayaman soyayyar da takewa yah Arref din."


Tashi nai zaune ina kallonta kamar yau nafara ganinta,
"Husna mekike cewa,wace yar uwar tawa karkice salma salma duk son da takema yah bazata cutar daniba,tana sona bazata so abunda zai tab'aniba."
Murmushin tayi mun"ada kenan khairat,kibude idonki kifahimci reality,ki auna abubuwa da yawa ada da kuma yanzu d'aya suke,son da kikace tana maki da yanzu tana makishi? Yaushe rabon da ta zauna kuyi hira,tunda kikazo school konace tunda kika dawo hostel ta tab'a kiranki awaya?ta zo inda kike common text wannan tayo maki?,ki bud'e kwalwarki dakyau kifuskanci gabanki makashinka na tare dakai salma bata sonki,zatayi komi don raba wannan kaunar.
Karkiyi mamakin idan nace maki yah Areef he love u he love everything for u,amman akwai abubuwa dasukai discouraging power nashi,kiyi mai uziri kisama ranki cewar yayanki bai tsanekiba,bai kikiba hasali kece wacce yabinne cikin zuciyarsa,bance kiyardaba amman wannan shine gaskiyar magana.
Wannan dalilin zaisaka salma taga tayi komi don ganin ta sameshi,don ba ita yakeso baba itace dreaming d'insaba thats why."


Kamar Tv haka nake kallon husna,kamar almara haka nakejin kalamanta cikin kunnena,jinake ban tabajin magana data d'aure dukkan tunani ba irin wannan,zuciyata tanason yarda da kalan Husna,yayinda wata takeson karyata hakan shin da wace zan yarda.
(YAN ZAUREN MRS BB KHAIRAT NA BUKAYAR ZABINKU.πŸ˜‰πŸ‘ŒπŸ»)


Tashi husna tayi tashiga tayo Alwallah tafara sallah,don har tara tayi gashi ko magruba bataiba,khairat daman ba sallar takeba.


Tunani yayi man sallama nayi zurfi cikinsa,narasa inda zan kama dole zanje gida dole maah ta tabbatar mun da maganar husna.


Ranar haka nai bacci da tarin tunanika,kasancewar yau lecture dare garemu dukda weekend ne. shiyasa tun safe dana tashi nai wanka,banma jira cin komiba muka fito da husna tace itama gida zata,saida nashiga muka gaisa da mama sannan mai taxi d'in yawuce dani gidan.


Duk motocin kowa nanan,harabar gidan
Alamun dai babu Wanda yafita.


sosai muka gaisa da maigadinmu,sannan na isa cikin gidan falon mai aikinmuce keta mopping cikin mutunci ina fara,a muka gaisa da ita,nace"basu tashiba ko."


"Tace aa suna wajen yin karin kumallo,ai dayake yau ranar hutuce da shad'aya tayi suke tashi."
Jinjina kai nayi na wuce dinning room din,fun Karin na isa najiyo uryar Abbu yana fad'a.
Cikin sauri na idasa shiga tare da sallama.
Annie,dady,maah,Abbu,yah Areef,yahjahid,Anty shida,Yah shahid,sai Yah meena da salma dake durk'ushe kasa gaban Abbu,duk ta kare itce yakewa fadan..........Annie ta tareni tare da rungumeni,sannan na gaidata tana ta murnan ganina,najega yah menah rungume juna mukai inajin kewarta sosai tare dani,duk daina gaida kowa Anty shida tace"ta alkairi kinga yadda kika kara girma,kinyi hankali sosafah."
Yah shahid yace"ba,a yabon d'an kuttru sai ya shekara goma da yatsa."
Tab'e baki nai ina kallon Abbu,
"Kagansu KO yanzu kenan Abbu ni banyi hankaliba gaskiya kaja masu kunne."


Dariya yayi yace sudaina jana,salma na kalla sai share kwallah take nace"Lafiya salma kuka kuma."
Maad dai dauke kai tayi itama salmar bata ban ansa ba,yah meenah dai tace"itada Abbune."
Yah Areef ne ya mik'e yana goge bakinsa da tushu,fuskarsa babu alamun faraa ko kadan,don daman tunda na gaiashi bai ansani ba.


Sorry WLh nagaji ajima zanamuku wani.


Mrs bb ce πŸ‘ŒπŸ»
[6/6, 7:44 PM] Mom Muhseen: πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•
🌹
*_ABIN CIKIN RUHINA_*


Written by mrs bb.
Mom muhseen.


*Dedicated to ZAUREN MRS BB* πŸ˜˜πŸ’•πŸ’‹


*watt pad*
*HUMAIRA7531*


26.


Muryarsa adake yace ma Abbu,
"Zan wuce Abbu."
Kallonsa yayi yace"sai yaushe kenan."
Agogonsa ya kallah yace"wallahi bansan lokacin ba anma ina kyautata zaton zamuyi aikin 2month a paris,kafin nan mu wuce japan muyo 2 month da ko sati biyune,banda tabbacin zamu dawo kan lokaci gaskiya."
Shiru duk akai anan na fahimci tafiyace zaiyyi,kuma bazai dawo nan kusaba.


Dady yace"maganar salmar fah."
Fuskarsa na kalla yasake d'aureta tam,yace"Dady munyi maganar daga baya,jahid muje kasaukeni time na tafiya."
Duk tashi akai don yi mashi rakiya zuwa mota,da alama akwai abunda yafaru kowa naga fuskarshi babu dad'i.ina tsaye yaketa sallama da kowa ina gefe guda na rungume hannu.
Maah rungumeshi tayi harda kwallanta,wai zatai kewarshi murmushi nai ina jinjina kaunarta tsakaninta dashi,kamar bazai bar jikintaba haka yaisa ga Annie itama ya rungumeta,su Anty shida da su yah jahid namai dariya wai kuka zai,ina ganin sadda ya hararesu sannan ya mikama yah shahid hannu sukai musaba ha,ya kalli yah meenah yakama kunnenta yace"karatu tukuru."
Duk dariya akai masu salma ya mik'ama hannu,isowa tayi yajata gefe bansan me yace mata ba,naga dai tana d'aga kai sannan ya shiga mota.
Abbu ne yace mashi"Areef ka gaisa da kowa banda ta alkairi,laifin me tayi maka haka."
Shafa kanshi yayi yana murmushi baice komiba,Abbu ya juyo ya yafitoni da hannu.
Jikina asanyaye na nufi inda yake,i wonder banji tsoron da nake jiba idan na tunkareshi,isa nai gani nai yabud'e bayan motar yace"shiga."
Kallon Abbun nake nama rasa mezance mashi daga man kai naiyayi,dole nashiga Anty shida ma tataho "Abbu inazuwa."
Bai musuba tashiga tana dariya,yah jahid na satar kallonta ta mirrow jan motar yayi muka fita,yah jahid da Anty shida kurun suke firarsu anman ni bakina ma yayi nauyi,waimeke faruwane yau gani ga dodona amman narasa inda tsoran ya tafi,yanayin dana shekara uku ko nace hudu banjiba shine nakeji,duk wani yanayi da da nake tsintar kaina cikinsa idan ina tare dashi yadawo,mekenan mamaki da al,ajabi sun rufeni.


Har mukaje filin jirgin bance komiba,yah jahid da anty shida suka fita can wajen zama suka samu suka cigaba da firarsu,shiru motar tayi na kasa yin magna gashi lokaci yana ta tafiya,don nasan karfe d'aya zasu tashi,gashi shabiyu da rabi.


Ganin yak'i tankaman don yadda duk yabi yasha mur natabbata in nabiyeshi har yatai bzai ceman komi ba,cikin sanyin muryata nace"yah kayi hkr kazo baka saman ba wallahi............"shot up."
Ba shiri naja bakina nayi shiru.
Cikin muryarsa dakakka yace batare da yajuyoba "Aure dai kikeso dai ko,to ki kwantar da hankalinki nasanar da Abbu kafin nadawo ya aurar dake,idan yaga dama shi masoyin naki sai yabarki ki k'arasa."
Atsorace nake kallonsa daga inda nake zaune,zuciyata bugawa take babu kakkautawa,
"Yah dongirman Allah kayi..........."karki sake kiyi man magiya,kenan don uabanki har kinyi girman kiyimum karya don kije ki had'u da saurayi,to gara da Allah ya nuna man,insha Allah end of this month keda salma duk zaku idashi gidajen mijinku,tunda har taurin kanku yakai haka ga yayarku nan tunda tafara karatunta ba,asameta da wata matsalaba harta gama saiku *kwalaye daku berori da bakusan kankuba.* zakugane bakuda wayau badai aure kukeso ba.
Ai bansan sadda kuka ya kubcemun ba ina kukan ina cewa"yah kai mun rai.......inkika sake magana makeki zanyi fita anan sakara kawai."
Dana zoyin mgana sai ya kwatsa man tsawa duk yadda naso yasaurareni abun yaci tura,,.
Gashi bakina yakishiru inacewa"wallahi ni banda saurayi Allah yagani ni banyi komiba karatuna nake yadda akasani,shine zakace aimun aure wallahi banso inkuma akayishi saina gudu wallahi........jinai kurun ya faskeni da mari.
"Nikike ma musu ni zakiyiwa gardama,khairat duka nawa kike atafin hannuna fa kika girma,karya zan maki kina nufin kocikin biliyoyin mutane kimashiga bazan shaidakiba,balle wajen da babu kowa.
Uhmmm yayi kiyi duk abunda zakiyi intakama kikashe kanki amman tabbas Aurenki da............kasa anbatar sunan yayi yanajin kirjinsa yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login