Showing 30001 words to 33000 words out of 69834 words
yace"yes come in"
Girgiza kaina nayi ina murmushi"Aa nagode da tayinka bismillah kazauna."
B'ata fuska yayi yana zama saman hannun kujerar danake"bakison welcoming dina ko princess."
"Aa ba haka bane kabari irin wannan welcoming din sai munje can sainayi maka amman pls not now."
Gyara zaman shi yayi yana dubana cike da so,
"Dagaske."
D'aga kai nai murmushin yasake yi yace"karkisa inje in samu Abbu ince pls Abbu amaido daurin auren nan gobe ta alkairinka tayi man alkawarin something sweet nikuma bazan iya jira har sai nan da 3week ba."
Dariya yaban ganin yadda yake maganar cikin karya murya kamar mai shirin kuka.,
Dariyar yake taya ni yace"wallahi kin iya dariya rannan nace ki koya man kika kiya ko."
Yah meenah ce tashigo hakan baisa ya tashi daga inda yake ba,saima murmushi yake yana yimata sannu.
Tana fara,a tace"yah muhd sannu da zuwa."
Cikin sakin fuska yace"yawwa Anty Meemah sannunki da kokari,kina ji dani kullum bakya gajiya."
"Wallahi babu komi ai kai nagida ne."
Nan fa ya samu yar tayin surutu,don dr akwai zafin surutu saida tayi daker ya barta tatafi.
Jiyo wa yai kaina cikin salon kauna lemu ya zuba ga cup yanufo bakina,dole na bude na kurba har shatin jan bakina ya fito........saida yalashe shi tas sannan ya aza bakinsa wajen dana sha,kunya ta rufeni duk da bayau yafara irin wannan abunba.
Nayi serving dinsa komi yadda yadace sannan nasauko kusa dashi k'asan don yace yafi jin dadin zaman kasan,yadanci yana jana dafira yaudai duk karatu yafi yawa.
Ya jima sosai don nan yayi sallar mangaruba,har suka gaisa da dady da Abbu.najashi cikin gida suka gaisa da maah,har ya ajiye mata rafar yan dubu guda gabanta.
Sanda na rakoshi salma tadawo daga rakiyar Ameer don yau yazo,ko kallon inda muke batai ba ni kunya ma naji don saida yace"kamar salma ko."
Yake nayi nace "itace"
Bai sake cewa komiba
Har bakin mota na rakashi yabude baya ya miko man wata leda,
"Turarenki yana burgeni ummlkhair,kamshin sa yana sakani shauki matsananci,pls matso na sake jinsa."
Matsoni yayi sosai har numfashin mu yana haduwa,dandanan naji tsikar jikina tatashi,sunkuyo da kanshi yayi gefen wuyana ya sauke numfashi mai zafi,saida na runtse ido, nai saurin ja baya.
Rungume hannuwa yayi yana kallona da idonsa daya canza yanayi,wani abu nakejin yana shigata bansan komeye ba,kauda idona nayi.
Yace"pls just a kiss."
Ba arziki na Ruga nabarshi, don wallahi idan natsaya dr yau saiya tsotse man baki,har mamakin sa nake soyayyarsa dandanan take shigar mutun,ya iya tafiyar da ita yadda yadacesaidai idan kabiye zuciya taufa tuni zaku canza ma soyayya mazauni.
Mrs bb ce👌🏻😉💕
[6/11, 12:28 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕💕 🌹
*ABIN CIKIN RUHINA*
Writing by mrs bb
Mom muhseen.
Wattpad name
Humaira7531.
DEDUCATED BY ZAUREN MRS BB
_SABODA KAUNAR DA KUKE MAN YASA ZANYI UPDATE YAU,DON DA SAI GOBE INA ALFAHARI DA KAUNARKU DA ADDUOIN KU ALLAH YABAR KAUNA_ 💕💕😘
Not edited.
29.
Washe gari mukai shirin koma wa school,nasa rigima dole yah shahid zai kaimu don inada wani plan..........saida yabiya damu mukai shopping sosai saboda semister mai tsawoce,duk da dai Auren yakusa inso samuna nane abarshi nagama aji ukuna,sai ayi lokacin mana cikin hutu,zan ma dr magana yayi wa su Abbu magana abarmu mukarasa wannan semister.
Hira muke tayi yana taya mu,ahaka har na sako batun husna inacewa.
"Wallahi yah meenah ban tab'ayi kawa irin Husna ba,tana da kirki ga kokari,kisan idan akai abu class tasan ban ganeba muna dawowa hostel mungama duk abunda zamuyi zata ce inxo muyi bita.....bata barina har saina gane,ina sonta sosai gashi akwai natsuwa."
Ina maganar ina satar kallon fuskarshi murmushi yake amma baice komi ba,nace"yah kaima ai ka lura da haka ko rannan daka sameta gida."
Shan mur yayi yace"don ubanki zama zanyi inta kallonta har naga wani abu tattare da ita."
Shiru nai ina kunshe dariyata yah meenah na tayani,
Sai kuma yace"kawai dai tana da tarbiyya akwai girmama nagaba."
Dadi naji ya kamani nace"sosai kuwa wallahi husna tayi,shiyasa cousin dinta dake sonta yake bala,in jida ita bayason kowa yana rab'arta kishinta yake sosai."
Kallon fuskarsa nayi naga dandanan ta canza yah meenah banda dariya babu abunda take,ni kuwa na sha mur irin dagaske haka maganar take,bacin karya ce kurun na shatata don ingane yana ciki ko haukana nake.
Bai sake ce mana komi ba amman yanayin sa gaba daya ya canza,magana zan ciga gaba dayi ya dakan tsawa dole naja bakina naguntse,banji haushiba nasan kishine yake damunsa dadi yakamani na kaga mu isa in fesa mata albishi.
Har bakin get din hostel ya kaimu muka tsaya fiddo kaya,don suna da yawa saboda kayan yah meenah.
Kin tafiya yayi yana ta danna waya,zuwacan yace "kikirata ta taya ku daukar kayan mana."
Wayyo dadi haka naji aikuwa nai maza na shiga contact dinta na danna mata kira.
"Besty nah gamu bakin get pls kizo ki taya mu kwasar kaya tare muke da yah meenah."
"Besty ina hangenku ganin bayanku yanzu nadawo daga cefane bari in karaso."
Dadi kamar yayi yaya dani don inson wannan kaunar ta jone,
Kamar wasa sai gata sai fara,a take tunma kafin ta san waye amotar,
"Yah meenah oyoyo,wallahi naji dadin zuwanku zaman nika dai ya isan,kewa tayi mun yawa."
Rungume juna mukai ina mata oyoyo.
A kunne nayi mata rad'a nace"kalli gefenki pls."
Juyawa tayi ta ganshi zaune cikin mota,kirjinta yabada rassss duk ta diririce daker tace tana yar fara,"yah shahid ur welcome."
Dagowa yai ya kawata fuskarsa da murmushinsa mai kyau yace"Asma,u ykk ya makarantar."
Tana wasa da hannunta tace"dasauki makaranta yah angode Allah."
Jinjina kai yayi yace"Allah ya bada sa,a ga friend dinki nan na maido maki na fita ko."
Dariya tayi kadan ta kalleni na kashe mata ido guda tace"ka kuwa kyauta wallahi thank you."
Murmushin yayi mata yana tada motar,
"Ga wannan akara kudin siyen garin rogo."
Dariya tayi ta ansa tana godiya tace"ai mu bama cin irin wadannan yah mu fa inkaga dish din damuke ci zakaso kazauna dakinmu."
Yana dariya yace "ok zan gani wataran zan maku shigar bazata."
Matsowa mukai muka mashi sallama yayi mana jan hankali kan karatu sannan yafita.
Ihun murna nake harda taka rawa,bada dariya babu abunda suke man har mukaje daki............nan fa na sata gaba da tsokana badai tace komiba wai kunyar yah meenah take,
"Nace bur wallahi lallai kin ma daina wallahi,wai besty ya kuka kare rannan."
Mikewa tayi zatabar dakin nai saurin rikota,
Yah meenah tana dariya tace"husna ya haka mun zama daya fa ki bar jin kunyata ni banajin taku,inkuwa haka ne daki zan canza."
Dole ta dawo na matsa mata saita gaya man yadda sukai.
"Wallahi besty kinfi ciwon ciki katsawa,bafa wani abu ya faruba kawai ya na ta jana da firar school ne tare da cewa kardai na biye samarin makaranta su hanani karatu,shikenan fah."
Murmushi nayi nace"soon zakiji ya kiraki yana cewa Asma,u in bakeba sai rijiya mai kwalabe."
Gaba daya muka saka dariya,tun tana nokewa taki sakin jiki da yah meenah har ta sake,ranar munsha fira don babu mai lectures cikinmu sai tomorrow morning.
💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕
A hankali rayuwar take gurgurawa har gashi fara shirin exams,saboda nayiwa dr magana yayiwa Abbu magana yabarni na gama aji uku na,ya kuma yi mashi yayarda ga shirye shiryen biki ga na exams,dole dr ya hakura da takura man kan kira da kuma zuwa,don ma ba sosai muke haduwa ba ko acikin schol din.
Saidai koran weekend yazo ya dauke mu muje yawo da shopping.
Duk abunda nakeyi ba wai na mance da *ABIN CIKIN RUHINA* ba ne Aa babu second ko awa da zuciyata bata bugawa dashi,daidai darana guda bai tab'a barin zuciyata da *ruhina* huta wa ba,banda wani abun tunawa dashi,illa kalaman sa na karshe nidashi airport.
_ina maki fatan Alkairi matar muhammad kaseem,sai wata rana bazaki sake ganina ba,kiyi hkr dani mun haramta ga juna har abadan,domin bazan iya karya wa maah Alkawarin taba,zanje nayi jinyar zuciyata kikula da kanki And plsss forget About Areef farouk,good by ummulkhair._
Wadannan kalaman sun zamar mani kamar fatiha cikin sallar farillah,duk daren duniya sune suke amsa kuwwa cikin kunnena,juriyace da karfin hali kawai suke rike dani,don nayiwa Abbu Alkawarin hakuri da kaddarata,yace man na tai makeshi karya rasani,in nabiye shiga damuwa komi zai iya faruwa dani,don ciwon zuciyata zai iya tashi kuma likita ya sanar da su cewa inhar nasa ke irin wannan kwanciyar,komi zai iya faruwa dani don haka inyi hakuri kowa da kalar jarabawarsa ke kuma taki haka tazo,don haka ki yi wa Allah godiya tare da kokarin ganin kin cinye jarabawar.
Kalaman Abby kenan ranar dazan dawo makarnta,naji nasihar sa sosai don inason Abbu na ba zanso ya shiga wani hali ba saboda ni.
Zuciyata ta azalzaleni akansa har nakusan shiga wani yanayi,kalamnasa da ya gaya man ranar kafin mufita mota sune suke tunzura bacin raina,har ma inji to miye na kwallafa raina dashi tunda koda babu dr nasan yadda ya fadi kalaman hakan nanufin nai mashi kadan.
_k'wailaye daku berori da bakusan kanku ba._
Wadannan kalaman sunfi komi kona man rai,har nakan kalli kirjina dake cike masha Allah,wanda nasan idan za,a tara mata goma cinkinsu da wuya asamu biyu masu irin breast dina,shine yake ceman k'waila,to nayarda dai salma k'walarce Amman ni wallahi ba ita bace.
Haka dai nake ta abuna abu wanda yasan halin nake ciki,illah yah meenah da besty husna.
Suma ba suda abun yi man face lallashi da ban baki,insuka na yini daki ko lecteres ban jeba nakicin abinci sosai sun san abunne ya tukoni,zasuyita lallashina suna gaya man kalamai masu kwatar da hankali,sai inji nasamu natsuwa.
Rannan dai nazauna nayi wa kaina karatun ta natsu,nace shifa wanda nake wannan haukan donshi yana can yana rayuwarsa cikin kwanciyar hankali,wata kila man ya shafe babina ya bude wani sabon shafin,kilama yayi budurwa ko ince yayi yanmata don nasa shi gwanin farin jinine akansu.
Tunda natuna haka nacire ma raina yah Areef,ganin gamai sona kamar yayi mani sujada saboda tsananin kaunar da yake mani,to akan me zan dorama kaina damuwar wanican da ko kirana mu gaisa baiyi,saidai najishi suna waya da yah meenah amman ko agaidani baicewa,to kan wane dalili wata jotter ta sabuwa da ban fara komi cikin taba nayi rubuta kamar haka.
*_NI UMMULKHAIR FAROUK,NAYI ALKAWARIN SHAFE BABIN SA CIKIN RAYUWATA,NAYI ALKAWARIN MAN TASHI CIKIN RAYUWATA,NAYI ALKAWARIN DAINA YIN CIWO SABODA SHI,BAZAN SAKE SAKA YAN UWANA DA IYAYENA CIKIN HALIN DAMUWA BA SABODA SHI,ZAN FARA SABUWAR RAYUWA DA MASOYINA KUMA MIJINA INSHA ALLAH._*
na jefata cikin tarkacena ban sake bai takan taba,don promise ne bazan karya ba zanba marad kunya inaha Allah.
Cikin yardar Allah muka gama exams,kuma muduka muna fatan samun sakamako mai ktau,daga wannan hutunne zamutai pratical sai munyi six months sannan mudawo makaranta.
Shirye shiryen bikinmu ake babu kama hannun yaro,duk kullum husna nagidan mu sai dare yah shahid yamaida ta,kasancewar yanzu babu laifi sun saki jiki dajuna amman ban tunanin yafurat mata yana sonta,suduka dai idan kagan su tare kasan akwai soyayya mai karfi,amman kowa jinkai dajan class ya hanashi,amman inanan ina hada masu tarko sai yah shahid yafurta da tsiya ma bada arzikiba.
Mrs bb ce😉👌🏻
[6/12, 6:28 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕
🌹
*ABIN CIKIN RUHINA*
Writing by mrs bb
Mom muhseen.
Wattpad name
Humaira753.
DEDUCATED BY ZAUREN MRS BB.
NOT EDITED.
30
Komi aka sama rana sai yazo,cikin ikon lillahi gashi dai bikinmu yarage saura kwana uku,yau mutanen dubai suka sauka,da iyalanta yah imaran da kanensa saifudden,sai yar auta mimi taci sunan mahaifiyarsu maah watau zahra,u shine ake kiranta da mimi.
Ummi kamar ta goyani don tsananin murnan ganina,nima haka nakeji don yinin ranar muna tare da ita,sai jana take wai ina surukinta yazo ya kawo gaisuwa.
Nace metake ci nabaka na zuba zaizo,har sata gaji dashi.
Wasu irin kayan kitcheen tazo man dasu new moden,kai daka gansu kasan an narkar da kudi waken,kuma abun jin dadin bani kadai ba harda sweetheart dina salma.
Naji dadin kayan sosai naita mata godiya, dun gureman kai tayi wai ai miye na godiya bacin hakkinta ne matsayinta na uwa,kuma haka batunta yake saboda ummi na sonmu tana kaunar maah batajin tsadar abu inhar mune zata yiwa alkairinsa.
Mimi tsararmuce amman mun dan girmeta da shekara guda,amman inka ganta zakace itace ta girmimu.
Don girman jikine da ita sosai,banyi mamakin rashin ganin *ABIN CIKIN RUHINA* ba don daman naji ajikina bazai halarci daurin aurena ba,ganin kamar zanji babu dadi yasa nai saurin kawar da tunanin hakan cikin raina,
Dadaddare Dr yazo gaida ummi sai nokewa yake tana masa dariy,don ummi babu ruwanta da jin kunya,maah cema kejin nauyinsa sosai Annie ma batajin kunyarsa sosai.
Gida ya dauki harami don yan gidansu Annie sunzo hada hajiyarsu,da kanwarta da yayarta sai hidima ke dasu,dangin maman salma kuwa basu zo nan gidaba sunacan wajen Inna,hakan yafi don sai anyi rigima yadda nasansu basuda hakuri kona kwabo.
Gyaran jiki muke zuwa tunda yarage saura sati biyu,shiyasa gamunan ko ince ganinan nayi wata irin canzawa,don salma bansan wace take cikiba,taki shigowa cikinmu ko kadan,itada kawayenta su raihana kurun suke hidimarsu,har kararta nakai wajen Abbu yace in kyaleta tunda ta janye daga gareni nima injanye mata,idan nacigaba da cusa kaina wajenta zata yi kokarin ganin ranki ya baci,nikuma bazanso abunda zai taba rankiba har agama bikinku ta Alkairi.
Rungume Abbu nai ina fashewa da kuka,don tun yanzu nafara jin kewarsa inajin sa har cikin kokon raina,yadda yake tattalina yake gudun duk abunda zai shigar dani cikin damuwa,lallashina yake sosai daker nayi shiru.
Kallona yake yana murmushi yace"Kinyi kyau ta Alkairin Abbu,Allah ya kawo ranar da ta alkairina tazama babba zata tai gidan miji itama."
Sadda kaina nayi inajin kunyarsa.
Dagoni yayi yana dariya yace"kiyi man alkawarin kulawa da mijinki da danginsa da yan uwansa abu mai muhimmanci ma ace mahaifansa,don hakan zai kara maki daraja da kima ga idon su da idon duniya,hakan yasaka mahaifiyarki kullum Allah yake daukaka darajarta akan sauran mutane,saboda tsaye take kan dangina da mahaifiyata,sujjada ce kurin bata yi masu,don haka kizama jaruma mai jajircewa acikin gidanta,hakuri shine babban jigo ga rayuwar Aure idan kika rikeshi kingama dacewa,sannan kizama mai rike sirrin gidanki,sirrin mijinki bakomi akeji da bakin matar gidaba,nasihata kenan wajenki ta Alkairi,ubangiji yasaka Albarka acikin rayuwar aurenku,Allah ya kareku daga sharin masu sheri,kiyi riko da Addininki kirike ibada,duk Abunda ya dameki ki gayawa Allah shi zai jibanci ramurranki."
Kuka nake don hakika nasihar shi tashigeni,naji duk wata natsuwa tashigan,naji hankalina ya natsu da auren saboda kalaman abbu,yayi man addua ya sakaman Albarka wannan ma kadai ya isheni,don kowace amarya konace budurwa zataso ta rabu da yayenta lafiya yayinda zata gidan miji,su rabu suna samata Albarka.
Haka na fito ina share hawayena.
Yah imran tunda ya kyella ido yaga yah meenah shikenan ya zama kamar bindinta,saita boye idan zamu fita yo wani abun,don duk ya hanata samun sukuni,ga yah imran badai iya love ba duk yarudar man da yah meenata.
Yaune akagama man gyaran jiki,gobene daurin aure,don nidai nace banason kowane irin event,sai angama daura Aure sai ayi dinner gidan iyayen dr.
Mun shigo gidan kenan mukai karo da yah shahid,duk ya fita natsuwarsa murmushi nai don duk yau banbari sun hadu da mutuniyarba,kallonmu yai yasha mur.
"Ina Asma,u."
Da yake sunsan kanun zancen sainai saurin cewa,
"Au nafa manta,yah shahid wannan wanda nace maka yana sonta din nan, yah kamal cousin dinta.
ya samemu wajen gyara,ana gama mata ya dauketa inajin sai anjima kadan zaka ga tashigo."
Gani kawai nai yadafe kai cikin masifa yake ceman,
"Donme zaki bari wani yatai da ita wani waje,bayan kinsan amana mominsu tabaki,ehye maza kirata yanzun nan ta dawo."
Mimi da yah meenah sabewa sukai suna dariya kasa kasa,don sun san idan ya kama su suna mashi dariya ran sune zai baci.
Sake shan mur nai nadanne dariyata nasake tun zurashi da cewa,
"Yah nace maka cousin dinsu ne,ansanshi gidansu,ko ita momin nasan bazatai fad'a ba don antsayar da ranar aurensu bayan sallah babba."
Wayyo kuzo kuga tashin hankali karara kan fuskar yah shahid,
Cikin tsawa yace.
"Sa ranar banza da wofi, aure akai masu dazai bita wani waje ya dauke ta ehy,laifin kine da kikajata.
maza maza nace kikirata yanzun nan tabaro duk inda take ta dawo,inba haka ba daga ke har itan sai rayukanku sun b'aci."
Ya bar wajen kamar zararre.
Saboda dariya har duke wa nake lallai yah ya kamu over,haka nakeso daman,dole ya sauke girman kanshi yafurta tunda shine namiji,wayata na fiddo ina cigaba da dariyata nakirata,
"Plan dinmu yayi Husna maza kishigo kafin yah shahid yasama gidan nan bom yatashi.....ina dariya."
Itama dariyar takeyi tace,
"Ganinan tahowa ina cikin taxi,dama nasan za,ai haka saina iso kiban insha."
Kashe wayar nai ina dariya sakon dr ya shigo man.
_AMARYAR GOBE YAUDAI D'AYA ABARNI NAZO NAGA KWALLIYARNAN DA AKETAYI KUSAN WATA GUDA._
Murmushi nai inatura mashi sakonsa cewa saikazo.
Dakin yah meenah nanne madaddalarmu,can nanufa,.
Ina shiga kofar falon Annie naji munyi mugun karo da wani abu,har wayana tana faduwa.......duka wanai na daukota ina murza kaina,saidai sadda zan d'ago banga kowaba........kirjina naji yace dammm saboda wani k'amshi da ko mutuwa nai nadawo bazan iya mance shiba,..........bin hanyar nayi da kallo jikina yana wata irin rawa.............
Taufah.🤔
Wani irin sanyi jikina yayi kamar ansakani cikin frig,ina waigen hanyar na karasa cikin daki,hayaniyar suce kurin ketashi,daki suna kyalkyala dariya suna maida yadda kai.
Kamar wadda akazarewa kuzari da lakkar jiki haka naji,ina sando na shiga dakin ina bin bango.
Silalewa nai kasa bakin kofar shiga bayi,wani irin kerma jikina yake...........wayata na ajiye kan madubi babu wanda ma ya lura dani saboda daroyarsu suke suna ta hirarsu.
Rungume kafafuna nayi ina dora kaina saman guiyawuna,ina sauraren bugun zuciyata.
Bazan iya cewa ga halin da zuciyata take cikiba,runtse idona nayi ina dauke numfashina na wucinngadi kozan daina jin wannan mayataccen kamshin,amman ina kamar ma hade yake da numfashina,duk sanda zan shakesa tare nake jinsu.
Husna ce tashigo tana sauke numfashi,duk suka juyo suna kallonta,mimi ce tai saurin jawota
"Ya kuka kare husna na matsu inji wannan dramer."
Harararta tayi tana dariya yah meenah tace"Ai da kin jima baki dawo ba kilan yah shahid bulala zaisa ya zanemu tas har amaryar."
Cu dariyar suke husna tace,
"Ina Amaryar take.......shiru tayi ganina zaune bakin toilet na kudundune kafafu,duk wajen suka kalla.
Husna ta ajiye jikarta ta iso wajena.
"Khairat,meye haka lafiya kike,yanzu fa muka rabu dake awaya lafiya lau,meya faru daga baya."
Duk sun shiga damuwa kowa so yake yaji abunda ya saman,taya zan iya yi masu bayani mezance masu,karo nai da wani mai kama dashi,koko kamshin sa naji,wane daga ciki zan fada.
Nashiga ukuna miye haka zuciyata ya ina cikin farin ciki zaki yiman haka,gobene fa daurin aurena inkikamun haka kin zalinceni