Showing 12001 words to 15000 words out of 69834 words
haske da manyan idanu wanda idan ina magana suke kunshewa,ga zara zaran eyelashes har wani kwanciya suke, sai tsawonsa don Maah bazadai Kace mata guntuwa ba, kuma ba gajeraba.
Amman am sure ni doguwace kuma tsayina ma daidaici, komina mai tsarine,amman cikar fuskata da cikar halittar jikina duk na Maah ne,da kyawawan hakoranta,da wushirya,masha Allah dai kawai za,ace komi yaji.
Sweetheart kuwa komi na Abbu ne har rashin kib'arta, Idan tayi dariya sak Abbu.
sweetheart kamar kwalin omo take ba nauyi,ga kuma fara,a ko bacci take.
Shiyasa tafini qawaye dayawa don ni k'awayena basu wuce biyar bah, itako lodi lodi haka zaka gansu,in fita mukai kan na had'u da Wanda na sani ta had'u da mutun goma........ Kai sweetheart akwai kwashe kwashe wallahi.
yah meenah ma ba laifi don Itama tubarkallah, Allah yayi mata halitta maikyau, komi yaji kenan don tun yanzu har samari sun fara mata yawa,saida na bata shawarar korarsu don inhar tace yanzu zatai soyayya ba makawa Dady aure zai mata, duk ta firgice don tana son boko kamarni.
An tambayeni me zan karanta nace I like medicine Shima kuma b'angaren hakori,da farko Abbu da maah sunce Ina karatun yayi tsawo,kuma zansha wuya, saida nayi masu kuka sannan suka barni, Shima saida sweetheart taga dagaske baza su barni ba,yasa ta kira Yah Areef tana kukan shagwaba take sanar mashi, dafari cewa yai tabani wayar ya lallasheni, Amman nace tace nafita.
Shi yayi magana aka barmun cause d'ina, Yah meenah kuma, nursing.
kuma nace bazan je wata k'asa ba anan gida Nigeria zanyi.
Yanzu har mun cike komi an bamu admission anan Abuja zamuyi karatun, kuma day zamuyi, sweetheart kasancewar karatun bai wani d'a d'ata da k'asa ba bata wani d'auki cause mai wuya ba, don education ta d'auka fanin intergrated science.
Yanzu registration za muyi mu fara zuwa,b'an gare guda kuma cikin satin nan su Yah mujahid zasu dawo,sweetheart kamar tayi hauka don dad'i nikuwa da naji Ana maganar ma gabana fad'uwa yake sosai.
*wannan kenan.*
Mu had'u next page.
Mom muhsen ce
Mrs bb.
[5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: ππππππππ
*_ABIN CIKIN RUHINA_*
Written by [Mrs bb]
Mom muhsen ce
*NI AISHA ABUBAKAR (MRS BB) INAYIWA D'AUKACIN MASOYANA BARKA DA SALLAH FATAN MUNSHA RUWA LAFIYA UBANGIJI YASA MUNA DAGA CIKIN Y'AN TATTATUN BAYI, ALLAH YANUNA MANA WATA SHEKRAR LAFIYA.*
*____________________________________*
*ππ°AINUWA πΌRITER'SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
10&11.
Har na isa b'angaren Anni tunani ya cushe Mani k'walwa, ni banga abun fushi anan ba, to mema nayi masa har haka koko don na tafi wani waje bayan nasan zai dawo, to in nasan zai dawo goyashi zanyi, koko mezan masa.
Tsaki naja sanda nake ajiye mayafi na, kallona yah meenah tayi tace.
"Lafiya dai, ya kuka k'are dashi."
Raina 6ace na wurgar da jikkata nace,
"Wai yah meenah ni za,a dizga kiga fa yadda yake ta shan k'amshi, kodai ubana in yaje unguwa ya dawo iyakar abunda zan mar kenan, to d'aukarsa zanyi don murna shine zai banza dani, to gidan ya tarar bazan lamunci wulakanci ba, idan wancan karon anyi nashanye yarinta Ce yanzu kuwa da girmana bazan jura ba wallahi."
Mai yah meenah take shafawa tace mun,
"Ban son wanan zafin ran naki khairat, ki ringa bin komi ahankali."
"Haba yah meenah kina ganin yadda yayi Mani halin ko in kula, ita kuma salma kowa yana magana Amman ita uffan ta kasa cewa."
"Nadai ce maki kiyi hakuri ki sama kowa ido, karki nuna b'acin ranki afili, ki share inkikai hakan wallahi zakisha mamaki, oya shiga kiyi wanka kizo kiyi sallah ko mangaruba bakiyi ba ga isha,i anata kira."
Haka na d'auki maganar yah meenah saboda koba komi ita kad'ai ke kulawa da lamarina.
Yadda tace nayi haka nayi, sai gashi cikin ikon Allah nasamu yar natsuwa, wanka nayi nazo nashirya cikin kayan baccina masu shegen kyau, ummin Dubai ta aiko mana dasu kala uku uku mu uku, ba k'arya ummi naji damu, more exspicialy ni bama yini guda bata kirani bah, haka d'anta yah imran jininmu y had'u da juna, don sosai yake ji dani don duk dare idan bana komi, shima yagama duk abunda zai zaikirani video call, nan zamu d'au lokaci muna hira har wani zubin yah meenah ta zo ayi da ita, har sun saba dashi itama.
Sallah nayi na gama na jawo system dina ina cireta daga caji, yah meenah tashigo.
"Khairat kifito muci Abinci inji yah mujahid."
"Wallahi da kwanciya zan, inyaso inci abincin anan d'aki, Amman tunda yah mujahid ne muje."
Abaya doguwa har k'asa nasa mukafito, ina cigaba da danna system din, muna hira har cikin falon maah.
Salma ta tusa shi gaba yana cin abinci, ga uban juice da ta had'a mashi, itace keta zuba mashi surutu kamar kanyar da babu dadi.
Bama tasan mun shigo ba, mu kad'aine falon maah na wajen Abbu nasani, don baka ganinta irin wannan lokacin, idan ba tazo duba muba, don duk dare zata zo taduba idan munyi baci, in bamuyi ba tace komi muke a ajiye akwanta.
Zama nayi kusada yah mujahid k'asa nida yah meenah.
Murmushi yayi mana yace,
"Kun zama y'anmata khairat, nan bada jima wa ba zamu badaku ko."
Dariya nayi ina danna laptop dina nace,
"Haba yah janmu kake kaima, duka nawa muke ai mun samu muma muyi yar bokon nan da ake mana yanga kanta.
Har ga Allah ni ban fad'a da wata manufa ba Amman Ashe na jawo ma kaina fitina, jinai ya ajiye spoon dinsa yace mun,
" ke!"
Cikin wata tsawa da ta firgitani bama ni kadai ba, har yah meenah ta tsorata.
Juyawa nayi ina kallonsa gabana kamar zai fito waje.
Cikin kakkausar murya yace Mani,
"Da ubanwa kike wannan maganar, watau kinga na kyaleki shiyasa zaki gaya mun magana ko."
Yah mujahid yace,
"Look Areef, ya daga dawowarka zaka fara halinka don Allah Ka daina, ba dakai take ba, karka tada mata hankali."
" jahid kafita cikin maganarnan kana so kace man na kyaleta, bacin maganar da tafad'a d'azu bai isheta ba shine yanzu ma tasake yin wata, shin ni abokin kine khairat, koko kakanki ne ni to zangyara maki zama, ko inuwata kika hango zaki ruga."
Idona ya cika da kwallah nace cikin karyewar murya,
"Yah........wata tsawar ya dakan data saka na zabura zan ruga, saida yah meenah ta rik'eni........rawa jikina keyi hawaye nata zarya akan fuskata.
" tashi bar nan falon, idan na sake ganinki inda nake sai na b'ab'b'alla k'afafunki stupid girl kawai, kenan don ubanki har kin girma ko, to daga yau karna sake ganinki inda kikasan ma zan zauna, aguje nafice ina jin wani irin kuka yana kuccemun, Wanda har numfashina jinake yamun kad'an...........kafin na idasa d'aki ban san sanda najini yashe k'asa ba, saboda wani kullutun bak'in ciki ne ya tokaremun mak'oshi, numfashin ya d'auke.................fitowar maah daga d'akin Abbu kenan saboda tsawar da takejin Areef na kwatsawa, taga fad'uwar khairat.........aguje ta rugo tana kwalaman kira da mugun k'arfi, Amman ina numfashin ya tafi, aguje ta koma suka taho da Abbu.....kankace me gidan kowa ya taru tuni Abbu ya ruga dani asibiti, donjin duk wasu hanyoyin sadarwa na sun daina aiki, kuka riris maah keyi Wanda ya ba kowa mamaki don Abu bai tab'a samun khairat tayi kuka ba, don wani lokacin ma tafi nuna damuwarta kan salma.
Amman kuma abun mamakin salma ko gezau batayi ba, don kowa yashiga halin damuwa Amman danna wayarta kawai take, yah meenah kuka take.
Tuni yah jahid da anty shidah sun tafi asibitin.
Abbu da yah jahid gaban likitan da ya gama duba ni, fad'a yake yi kamar zai ari baki, hakuri suketa bashi daker ya yi masu bayani.
"Kasan yarka na daf da kamuwa da ciwon zuciya kuwa, tun sadda na duba ta lokacin baya nasanar dakai,na kuma cema adaina fusata ta da yawa, to gashinan zuciyar ta na mataki na second to the last, muddin irin haka ta cigaba da faruwa, to bazan iya kareta daga abunda zai biyo baya ba.
Don haka ruwanka ne kasama mata farinciki, ruwanka ne kabarta damuwa ta kasheta."
Maguguna ya rubuta tare da sallama, idan tatashi baccin wuyar da tashiga.
Suduka jikinsu yayi masifar yin sanyi,koda suka fito kowa da irin abunda yake sak'awa.
Mutan gidan duk sunzo Anni kad'ai suka baro, meenah idonta yayi jawur, Areef kuwa karkaso hada ido dashi, don kamar jangauta haka yakoma, babu wanda yabi ta kanshi tsakanin Abbu da jahid.
Ban farka ba sai wajen shabiyu na dare, dole saida nakai washe gari sannan muka koma gida.
Kowa sai nan nan yake dani maah kuwa inakan cinyarta, abinci kanshi da kanta take bani, har yanzu Abbu baice komi ba, yah jahid baya yin cikakkar one hr baizo ya duba niba wata sa,in ina bacci wata sa,in ina danna waya komuna fira da maah.
Gogan naku kuwa har yanzu banga keyarsa ba, haka zalika nima kuma ko inuwarsa bana kaunar gani, don yanzu wata irin tsanarsa nakeji har kasan zuciyata.
Salma kuwa yanzu duk ta canza Mani, bama niba kowa na gidan ta canza mar fuska, maah kuwa ta yi iskar kare da ita, ban sa mekefaruwa ba abun yana cimun tuwo a kwarya, shiyasa nace zan mata magana yau.
Yah meenah ta gama mana registration dinmu, tun kwana uku da suka wuce.
Ranar Monday zamu fara zuwa makarantar, dadi ya kamani ko banza nashafe babin wanan gayen mai bakin hali.
B'angaren Abbu na nufa don kiran maah tazo muci abinci, insamu damar tambayarta.
Saidai ina shiga nafara jiyo sautin magana da d'an karfi yana tashi, saika kasa kunne sosai zakaji maganar kamar ana fad'a.........gabana ya yanke ya fad'i abunda ban tab'aji ba iyakar tsawon rayuwata.
Ahakali da najuya zanfita, saidai ambaton sunana danaji anyi yasa dole matsawa jikin k'ofar bedroom dinsa na kanga kunnena.
"Saudah baki tab'a neman wani Abu arayuwata nace bazan iya maki shiba, duk kanin abunda kike buk'ata ko ina dashi kobani dashi saina nemo na kawo maki don inga farinciki cikin akan fuskarki, ban tab'a zuwa maki da wata bukata ba tunda mukai aure, tsawon shekara talatin yanzu sai yau, Amman kirufe idonki ki watsa mani k'asa ga ido.
Ban boye maki halin da y'arki keciki ba, na sanar maki don musamu mafita, mufitar da ita daga halin da take ciki shekara goma sha, Ashe ke kina can kin saka takunkumi mai tsananin girma tsakaninsu, kinjefa yarki cikin halin damuwa, kin jefata cikin masifar da zata iya rasa ranta abisa wannan dalilin, shin idan Areef ya Auri Khairat yana nufin ya tashi daga d'anki kenan, ko yana mufin kin rabu dashi kenan."
Kuka take tana cewa Abbun khairat shin wai kamance alkawarin mu da anty hafsat, agabanka tayi magana aranar da ta bani Areef, cewa tabani halak malak, kuma bata yafe ba idan na banbantashi da yarana, sannan gudun son juna ya kama guda, yasa tace na haramta masu juna, idan ba haka ba babu ta yadda za,ai areef ya cigaba da zama matsayin d'an dana haifa, inhar yasan wannan babu makawa duk girman da yayi wajena zata anshi abunta, don tana son Areef ya d'auka nice uwarsa har iyakar karshen rayuwarmu nidashi, ina son Areef Abbun khairat, wallahi ko shahid da shahida, da ita khairat din banajin kaunarsu irin yadda nakejin sa, saboda shine mutumin daya samomin kima da mutunci waje mutanen da suka gasa mun aya ga hannu, akanshi suka fara yimun kallon rahama, taya kuma yanzu saboda yar cikina in fallasa wanan abun, yaka keson suringa kallona bazan iya barin wannan abun ya fito bah, khairat tayi hakuri Allah zai yaye mata, ko salma ba zata aurai ba ta gama haukan nata. "
"Na gode maki saudah, akan wannan kikeson y'ata ta mutu ko, saboda kar Yayarki tace zata anshi yaronta ko, to shikenan ni zan Sanar da wanna sirrin ga kowa, zan kuma yiwa Areef tayin Auren khairat, saidai idan shine yace baya sonta bazai aureta ba, zan hakura kuma zan yiwa khairat Addua Allah ya bata Wanda yafishi Alkhairi, inhar khairat bata samai ba babu Wanda zai auresa daga salma har shahida da meenah, nagode."
Jin alamun zai fito yasa nafice aguje, kewaye na shige nayi kuka kamar idona zaifita, nayi kukan da ban taba irin saba, Wanda har saida nayita amai akewayen.......
Mom muhsen ce
Mrs bb[5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: ππππππππ
*_ABIN CIKIN RUHINA_*
Written by [Mrs bb]
Mom muhsen ce
*____________________________________*
*ππ°AINUWA πΌRITER'SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
12&13
Ganin halin dana shiga zai iya saka aganoni, shiyasa nayi iyakar kokarina wajen ganin na dawo cikin natsuwata, ina nan kwance salma tashigo tana wani taunar cingam cikin yatsina fusma, mamaki nake yadda salma ta canza sosai daga dawowar su yah Aree zuwa yanzu, kokadan yanzu salma bata damu da damuwata ba, sai gari ya waye har rana ta koma ga ubangiji, salma ko kallon banza ban isheta ba, idan ma ni nayi mata magana baza ta kallan ba zata ban ansa, tabbas ina hasashen wani Abu dangane da ita, salma ba haka take ba inson sanin dalilin canzawarta.
Wayarta ta ajiye ta shiga wanka ta fito tahau shirin bacci, Amman sai ka d'auka miji gareta sai kwalliya take yi, tana ta feshe jikinta da turaruka, kallon ta nake ina mamakinta.
Har ta gama bata cemun uffan ba, saida zata fita har takai kofa ta juyo cikin rainin hankali tace,
"Oh na manta fah kifito can babban falon Abbu ana nemanki."
Ta juya bin bayanta nayi da kallo kafin na yuk'ura na tashi, sake wanke fuskata nayi nafito, tabbas nasan wannan maganarce za,ai gaba na yana fad'uwa na isa kowa nanan har dadyn yah meenah, dasu Anni da yah jahid kowa dai yana nan banda yah shahid da sai karshen wata zaizo hutun karshen shekara.
Zama nayi can gefe bakin kofa, saboda irin kallon k'ask'ancin da yayi min muna had'a ido, bacin tsoronsa da yacika zuciyata ai dana rama.
Yah jahid ne ya bude mana taro da addua,kafin kowa ya shafa muka maida hankalinmu kan Abbu, gyaran murya yayi ya fara da cewa.
"Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata,ala da yanuna mana wannan rana, ya kuma nuna mana girmanku, Wanda da ba haka kuke ba, an wayi gari kowa ya mallaki hankalin kanshi, zuwa wannan lokacin nasan wasu daga cikinku kanku yatoshe, abisa wasu al, amurrah watau abunda kefaruwa shine, azahirin gaskiya Yayanku areef ba mune muka haifeshi ba, bamune mukashayar dashiba, saidai kuma mune iyayen rikonsa, konace ahalin yanzu dai Areef namune, watau Abunda ya kawo wanan magana shine babu batun b'oye b'oye, Areef kanwarka khairat tataso tun bata san kanta ba, take kaunarka Wanda data kara girma ta fahimci cewar babu aure tsakaninku, tayi kuka tashiga damuwa Wanda wannan damuwar itace ta ja har aka mata ripeting makaranta, karshe ta kasa rikewa ta sanar da Annin Ku, ganin wannan ba abunda za, a kyale bane yasa ta sanar dani, bata gaya ma mahaifiyarku ba saboda taji irin furucin da tayi wa yarinya k'arama, cewar inhar ta sake jin wani yanayi na soyayyarka aranta bata yafe mata ba, alokacin ta nuna cewar akwai alakar aura tayya tsakaninku, Amman ta haramta mata kai, saboda wani dalili.
Ban tab'a d'aukar hakan zai kawo ma khairat matsala ba, sai gashi lokacin da ta kwanta asibiti likita ya sanar dani tana da damuwa, idan da hali a San yadda akai akayi mata maganinta, saboda zuciyarta ba zata iya d'auka ba, ban d'auki wani mataki ba, saboda ina ganin abari zuwa sadda zaka kammala karatuka sannan itama tafara hada hadar shiga jamia,sai na sameka da maganar in ka amunce na aura maka ita."
Shiru falon yayi sai shashshekar kukana dake tashi cikin falon, duk na jike hijabita da majina da hawaye.
Cigaba yayi da cewa,
"Sanda kuka dawo nayi farinciki saboda ganin kamar abunda nake tunani zai tabbata,saidai kuma naga kamar ba haka ba, saboda kulawarka kaf akan salma kake yinta, sai kwatsa da kyara da kakewa khairat, har dalilin haka yaja zuciyarta hau hauwa, Wanda likita ya tabbatar mun da cewar wanan matakin shine na karshe data sake ta wuce shi babu makawa zata kamu da ciwon zuciya, shiyasa hankalina ya tashi na kasa natsuwa, gani nake duk sakacina ne, Amman sai naga wannan damar ce kawai zata warware komi."
"Na samu saudah da maganar hadaku aure Amman Kalmar farko data furta mun itace cewa ta haramta maku juna kaida ita,saboda alkawarin da tayiwa ummin Dubai cewa cikin yaranta babu mai auren wani, ma,ana khairat ko shahida bazasu aureka ba, kai matsayin wansu kake uwa daya uba daya, alakar aure bazata tab'a shiga tsakanin kuba, don haka khairat saidai tayi hakuri Allah ya bata wani Amman ba kaiba."
"Nikuma nace muddin ka amunce da tayin da nayi maka akan khairat, to kuwa wanan auren babu fashi saidai idan mahaifiyarka ta Dubai ce tace aa ko mahaifinka, kokuma kai da bakinka kace bazaka aureta bah."
Shiru ya k'ara yawaita cikin falon zuwa yanzu kukana ya karu, don sonjin ansar da zai bayar, har ga Allah duk irin abunda yah Areef yake mun banji zan iya hakura dashi ba ina jinsa shine ABIN CIKIN RUHINA Amman ya na iya da hukuncin ubangiji, muddin yace zai auran, inkuma har naji sab'anin haka nayi alkawarin yafeshi har iyakar karshen rayuwata, haka zalika bazan sake tada hankalina akanshi ba zan d'auke shi matsayin yayana uwa d'aya uba d'aya.
Tsawon lokaci baice komi ba Wanda kowa sonjin ta bakinsa yake, har saida dady yace masa.
"Areef dakai ake kayi shiru."
Ajiyar xuciya yayi yace,
"Abbu meye dalilin da yasa maah ta furta hakan."
Baidamu da tambayar da yayi ba yashiga bashi ansa.
"Watau Areef bari nayi maku dalla dallah."
Shekarun baya tun da mukai aure da sauda saida muka shekara goma ko b'ari bayi ba, nan yashiga sanar dasu halin da suka shiga, da irin takurawar da dangin Abbun suka mata, har sadda suka bar kasar..........
"Ranar da muka sauka kasar gidan ummin Dubai muka sauka, Wanda aranar aka haifeka Areef, tun da aka sallamoku asibiti nida saudah muka nuna sha,awar abamu kai, to sanin cewar suma kaikad'ai garesu yasa bamu rok'aba, to Ashe da saudah suka kebe da hafsat, ta sanar da ita halin da take ciki na rashin haihuwa, har gashi ance na k'ara aure saboda bata haihuwa.
Saboda son juna da tausayin halin da saudah keciki yasa umminku ta nemi iznin mahaifinka, akan zata barma saudah kai, koda yaji halin da muke ciki baiyyi jaa ba, yace har duniya