Showing 9001 words to 12000 words out of 69834 words

Chapter 4 - ABIN CIKIN RUHINA BY MISS BB.txt

Miss Bb   

10 Jul 2024

8262

karatunku karkuga ban nan kuce zakuyi abunda kakeso, wallahi Ina biye da duk motsinku don haka amaida hankali a ajiye mun k'yak'k'yawan results,ke kuma da akama repiting sai ki maida hankali agaba kuna iya tafiya........salma ta fara mik'ewa sannan ni bazan Iya kwatanta yadda zuciyata ta keba, nasan dai ina cikin kunan zuciya da wani irin yanayi marar misltuwa,daker nakai k'ofar har salma ta wuce jinai yace,


"zonan"


Tsaye nayi na kasa juyowa kuma na kasa tafiya,saida ya dakan tsawa sannan jiki na rawa na isa gabansa na sadda kaina..........shiru tsawon lokaci baice komi ba, nima ban motsa ba, na sadda kaina kurun kwalla na zuba suna d'iga ga hijabina.


Jinai dai kawai ya d'ago fuskata nayi hanzarin rufe idona yayin da wasu kwallan suke zuba, handcif ya saka mai fitinennen k'amshi ya na goge mun kwallar.............amman wasu na sake silalowa bai daina gogewar ba har saida suka k'afe, sannan ya saki fuskar.


Yace Cikin muryarsa da tayi matukar sanyi,
"idan kika sake kukan nan ko bayan kin tafi d'aki nida kene swe.....Khairat."


Fita nayi inajin k'afafuna kamar ba zasu iya d'aukata ba,


wannan ranar yadda naga rana haka naga dare, tun asuba akafara shirin tafiyarsu, inajin sadda salma tatashi nayi kamar bansan me take bah.......sai tara na tashi nafito wanka kenan Ina tsane jikina naji muryarsa yana tambayar meenah Ina nake, tace ina d'aki.........yana bud'e k'ofar ina shigewa toilet na da tse k'ofar...................


Mom muhsen ce
Mrs bb 👌🏻
love u wujiga wujiga fan's d'ina ❤❤❤❤❤
[5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕 *_ABIN CIKIN RUHINA_*


Written by [Mrs bb]


Mom muhsen ce


*____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*




7.


Jingina nayi da k'ofar toilet d'in Ina sauke numfashi k'asa k'asa, jikin k'ofar yazo ya Jingina bayan sa Shima, murya can k'asa k'asa yake magana, tayi rauni sosai sai kayi tunanin kuka yake.


"zamu tafi *sweetheart* saidai abun haushin zamu rabu kina fushi da Ni,pls kiyi hakuri ki fito ko dukana kiyi Wanda zan ringa tunawa da shi."


Kuka ya kucce mun mai tab'a zuciya,kamar numfashina zai fice runtse idonsa yayi yana jin babu dad'i, duk yadda yaso yasake ganinta k'iyawa nayi, haka yafita jiki babu kwari........daman shikad'ai akejira gab'a d'aya gidan aka tafi masu rakiya banda Maah da Khairat.


Ina bayin nan har suka tai saida nasha kukana kamar ba gobe sannan nafito daga bayin,daidai shigowar Maah d'akin.


Zama tayi bakin gadon mu tana kallona bata dai ce komi ba har na gama shiryawa, nazo nayi walha da nake yi na gama sannan na kalleta nace.


"Maah ko wani abun zanyi naga tunda kika shigo baki ce komi ba."


Wani kallon banza tayi mun kafin tace mun, in biyota d'akinta.


Jikina yayi sanyi Allah yasa ba laifi nayi mata ba, Ina tsoran fad'an ta Maah babu sauk'i indai wajen fada ne,duk na tsure tsoro nake kar ta dokeni gashi mai cetona bainan,don wata sa,in idan na mata taurin kai jibgata take kamar jaka, sai shine zai kwaceni.


Zama nayi k'asa wajen k'afafunta, na sadda kaina kamar munafuka.


Sunana ta kira.


" *UMMUL KHAIRI*"
D'agowa nai na kalleta nace,


"Na,am Maah."


"Miye matsayina wajenki."


"Maah ke mahaifiya tace."


"idan ance mahaifi me ake nufi kenan."


"ana nufin wanda ya yi silar kawoka duniya, kuma wanda nauyin kulawarka ci da sha da sutura suka rataya akansu, idan baka lafiya akaika Asibiti tarbiyyarka tana kansu."


Wani dad'i ya kama maah lallai duk cikin yaranta babu kamar Khairat wajen komi, Amman sai ta sake Shan mur tace.


"sab'amasu yana nufin mekenan."


"yana nufin ka sab'ama Allah [S W A] kuma duk mai ja dasu bazai tab'a ganin daidai bah."


Jinjina Kai ta sake yi sannan tace.


"madallah da malamin islamiyyarku,tunda har duk kinsan wad'annan bazan sha wahalar yi maki bayani bah, kallani nan Khairat."


Banyi musuba na d'ago Ina Kallonta ina ganin wasu maganganu masu tsananin nauyi cikin idonta, jinai taciga da cewa.


_*"matsayina na mahaifiyarki, na umurceki da cire duk wani Abu dake ranki akan yayanku AREEF,sannan na haramta Aure tsakaninki dashi har gaba da abadan, duk Yarinya ce ke nasan kinsan me ake nufi da haramci,to na haramta maku junan ku, kuma muddin kika take doka ta wallahi ummul khairi BAN YAFE MAKIBA."*_


Iya dauriya nayi bansan ni d'in jaruma ce ba sai yau, ilahirin jikina rawa yake amman nadanne na k'i bari Maah ta gane, idona k'em akanta nace.


"insha Allah nayi maki wannan alkawarin,saidai tambayar da nake da ita itace..........."


"Bana sonjin tambayar,duk motsinki na sani Khairat karkiga ina nuna halin ko in kula akan lamarin ku, wallahi kar nake kallonku, don haka idan na sakejin kun samu sab'ani da juna keda salma billahil azim zanar tsiya zan maku,kiyi k'ok'ari idan ta dawo ku sasanta kanku,sannan kan karatunki, wallahi Khairat idan kika sake barin damuwa tayi gala ba kanki nida kene."


"don haka idan kunne yaji..........


Kaina k'asa Nace,
"jiki ya tsira."


Tace,
"good girl,sannan kidawo da walwalarki, bana son wannan d'ari_d'arin da kike bance kuma kidaina yi masa magana ba,ko kuyi fira, Aa zakuyi duk wannan amman muddin kika sakejin wani yana yi kanshi.........basai na ida ba kinsan sauran tashi Kibani waje."


Jiri ke neman kada ni na dafa bango zan fita,sai kuma na juyo Nace,
"Maah."


kallona tayi alamun tana jina.


Cikin karyewar murya kad'an ya hana kuka na bayyana nace,


"Maah, don Allah kiyi mun hakuri bazan iya cigaba da magana mai tsawo dashi ba,idan nayi hakan bazan iya hana zuciya ta jin wani abuba, kibarshi murinka gaisawar ya isa,sannan kiman afuwar yau bazan iya warware wa lokaci guda ba,amman namiki alkawarin bazan Kai lokacin da salma zata dawo ahaka bah.......plss Maah."


Wani marayan Tausayin y'ar tata ya rufeta,jawoni tayi ta rungume,wanda ba zance ga tsawon lokacin da Maah ta d'auka rabon da ta rungumeni.


Cikin muryar lallashi tace,
"nayi maki wannan uzirin Khairat,badan na cuta maki nai hakan ba, gata ne nayi maki, ko ince nayi maku keda yayyenki, na kausasa kalamaina ne don na tsorata ki akan abunda kikeji kan AREEF,amman bazan iya hana Allah ikonsa akanku ba, kiyi k'ok'arin kiyayewa kinjiko ta alkhairin Abbunta.


Wannan kalamin yasa nasamu natsuwa, nasake mata alkawarin kiyayewa,k'arshe ajikinta nayi bacci, ta kwantar dani ta fita................


Mom muhsen ce
Mrs bb 👌🏻
[5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕💕
*_ABIN CIKIN RUHINA_*


Written by [Mrs bb]


Mom muhsen ce


*____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*




9.


Shirye shiryen dawowar Su kawai ake babu ji babu gani,b'angarensu angyaare an cire komi ansa sabo, har kaya sawa saida Abbu Ya siya masu, Manya da k'anana.


Abun har mamaki yake bani, saikace shugaban k'asar mu ne zaizo,amman sai ban nuna ba nayi kamar ban san me Akeba,ban shiga mamaki ba saida naga ana sake fentin gidan, nace Eh gaskiya lamarin azimun ne.


Sweetheart kuwa duk tafi kowa zak'alk'alewa, banga wanda yayi mata magana ba,saidai suyi ta yi mata dariya.


Ranar da ta kama jirginsu zai sauka,washe garin muka tai registration,sweetheart cewa tayi zatayo daga baya, Amman bazata iya fita gida ba har sai sun iso.


Haka muka tai nida meenah wadda abun ya isheta har tace,


"rawan kan sweetheart d'inki tayi yawa Khairat,ba zaki ringa kwab'arta bah."


Murmushi nayi Ina danna wayata, kasancewar itace ke driving d'inmu ni ina gefenta.


"Uhm yah meenah kenan, ni asuwa ince ma sweetheart ta rage rawar Kai, wai kokin San yadda take ji dashi kuwa!uhmmm muddin nayi mata Wata magana fad'a zamuyi, kibarta tayi tunda yanzu babu haramcin hakan,duk da har yanzu basan ainahin abunda ya faru ba."


"Shikenan,Allah yasa mudace amman hakan babu kamun Kai gaskiya, koshi yana sonta yadda take masa zai ji tana sire mashi."


"can su gane banda Wata matsala dasu, ni yanzu fata nake Mu gama registration d'in nan lafiya,so nake muje Dubai."


"murmushi tayi mun tace, Kedai kawai Kice wajen heartbeat d'inki zaki."


Dariyar da ban shirya mata ba nayi,
"kina da ban dariya,wai kin mance cause d'ina ne haba yah meenah wallahi ni ban shirya ma soyayya yanzu ba, saboda ita tana da zak'in da zata shagaltar dake daga komi ma,haka zalika tana da rad'ad'in da zata hana ki dukan wasu abubuwa masu muhimmanci,cikinsu kuwa harda karatunki, tsaf zata k'arar da farincikinki Arudun Allah."


Dariya meenah taringa yi harda dukan Sikiyarin motar, haka suka cigaba da hirarsu har sukaje.


Kasancewar ranar farko ce shiyasa suka tadda wajen acike,kamar ana rabon kud'i shiyasa basu samu kansu ba sai anata salar magruba, wai ahakan ma basu gama ba sai sun sake dawowa gobe........a matukar gajiye suka iso don yanzu Khairat kejansu,kamar tayi kuka don gajiya tana shigowa harabar gidan gabanta ya yanke ya fad'i........ras ras kallon juna mukai nida yah meenah.


"yah meenah Bazan iya shiga gidan nan bah."


Idona ya canza Kala kuka nake so nayi Amman Ina danne halin da nakejin zuciyata.


Dafa kafad'ata tayi cikin kwantar da hankali tace,
"come down Khairat,babu abunda zai faru, kiyi ta karanta duk adduar da tazo bakinki,Allah yana sane dake."


Kwallah sun cika idona nace,
"yah meenah,inajin tsoran tashin wani miki acikin zuciyata,maah tace mun Idan nasake jin wani feelings Akansa bata yafe bah,yazanyi Idan zuciyata ta k'i saurarena hakan yana nufin na sab'a umurnin Maah, kuma Allah zai tsine mun."


Na fad'a ina goge kwallah.


Ajiyar zuciya meenah tayi ta anshi key din ta kashe motar,sannan ta zagayo Inda nake na bud'emun,kallonta nayi ta jinjina mani Kai sannan nafito.


"Allah bazai kama ki da laifin da bakida tsumi ko dubara Akansa, shi ai yasan abunda yake zuka tanmu,bazai yanke mana hukuncin da yasan bamuda laifin saba, saboda bake kika sama kanki bah Khairat,don haka kiyi iyakar k'ok'arin ki kiyi wa Maah biyayya,sauran kuma kibarwa Allah,idan mun shiga ki saki ranki kamar babu wani Abu,kiyi mashi irin na y'an boko ke kanki zaki samu natsuwa,ok."


Murmushi nayi inajin Wata natsuwa na Shigata,ina k'arajin Yah meenah cikin raina itace mai kwantar mun da hankali koda Yaushe sai fah Anni, don sweetheart bama ta natsuwa balle har tasan damuwata ta lallasheni.


Cikin kwarin guiwa muka nufi cikin gidan..........
[Wayyo tsoro nakeji😟 anya kuwa Khairat,🤔 Amman duk da haka kin bani tausai😢]


Tunda da kan Yah Areef d'in har kawo kan salma babu Wanda babu falon,kirjina kamar zai fito wajen daker nake yak'e, har muka k'arasa Cikin falon tsundum.


"Aaaaah kaga mutanen turai,iyyen bah wai kun ganku kuwah yah Areef,yah Muhajid kaine kuwa anya ba musanya mana ku akai ba."
Duk ni nake fad'ar haka inajin dukan kirjina yana yawaita,amman duk da haka murmushi mai kyau akan fuskata.


Harara ya wurgomun cikin sigar wasa ya d'auke kai yana ma Yah meenah magana.


Murmushin na sake k'awata wa na isa ga Yah mujahid,zama nayi gefensa Ina lank'washe k'afafuna Nace ina rik'e ha6ata.


"wallahi yah mujahid idan a Wajene naganku zagaye ku zanyi in wuce saboda ko k'an wanda yasanku shekarun baya, yanzu bazai iya gane ku bah."


Duk dariya aka saka mana,
Salma ce ta shigo d'auke da tiren dinner d'insu.


"sweetheart Kinga yah Aree, Kinga yadda ya koma wallahi nayi zaton irin turawan nan ne da ya shigo, ban zaci shine bah."


nan ma dariyar ake na kalleshi Shima ni ya kallah, muna had'a ido ya sake harara ta,dariya nayi kafin na shagwa6e fuska na Kalli Anni nace,


"Kinga Anni tunda na shigo yake ta harara ta, kofa ansa sannu da zuwar da nayi masa baiba."


Annin tace.
"Haba babban yaya laifin me yar gidana tayi."


Wata murya naji tana magana kamar Ana busa sarewa, cike da tsananin taushi,laushi Kai harda wani sino take fitarwa,saurin Kallonsa nayi Ina sake baza kunnena donjinta da kyau.


"Anni,karkice komi wallahi don tunda kika ga nayi shiru kibari kawai, don Kinga Abbu baice komi ba don yasan ta Alkhairin tashi tayi mun laifi."


Lumshe idona nayi na kalli maah cikin langa6ar da fuska.
"Maah, ba zaki ce komi bah."


Murmushi tayi mun tace,
"ba ruwana Khairat,kema fa kinsan bakiyi daidai bah."


Maida kallona nayi wajen Abbu nace,
"Abbuna Kace yayi hakuri."


Tashi yayi yana ceman,
"ta Alkhairi Kinga nayi nan zanje wani waje sai ten zan dawo, ai da nayi maku sharia."


Duk wanda na nufa sai ya zare kanshi, daga mai yimun dariya sai mai tashi ya fice.


Yah meenah tace,
"yah taci albarka cina ayi mata hakuri, wallahi registration mukaje, munso dawowa kan lokaci kodan mu tarbeku,Amman wallahi wajen a cike daker muka samu aka fara mana, kuma ba agama ba dole sai mun koma gobe."


"Shikenan Aminatu jeki abunki."


Kallona tayi tace,
"saikin taho Khairat bari naje nayi wanka yunwa ma nakeji."


Ta fice daga ni sai shi da yah mujahid sai sweetheart,dake ta wani narkewa.


Yana biyewa shirmenta,tab'e baki nayi ganin ita tak'i ce masa komi, yah mujahid nayi ma magana,ganin shi ya shareni.


"yah mujahid bari naje na dawo kabani labarin UK."


Murmushi yayi mai kyau don yah mujahid badai kyau bah,shida Yah Aree saidai suzo tangal.


Har na fice banji Yace mun komi ba, sai hirarsu suke da salma ita ce ma tafi bani mamaki, ganin tak'i saka baki ya kulani.
[5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕💕
*_ABIN CIKIN RUHINA_*


Written by [Mrs bb]


Mom muhsen ce


*____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*




8.


Rayuwa mai cike da k'alubale, wannan haka yake dukan nin wanda kake gani, to fah kowa da irin yadda rayuwar take zuwa mashi,don babu Wanda zaice tana yimashi 100%,babu shi wallahi dole akwai ta Inda Allah zai jarabceka.


Haka yake ga Khairat Allah ya jarabeta da matsanancin son yayanta, Wanda ita kanta bata san lokacin da hakan ta faru da ita ba,gashi bata da masaniyar wace irin ak'akace tsakaninsu, shin ita dashi Waye bare kuma Waye d'angida,idan ta fahimci Maah yadda tayi mata magana ya nuna akwai aure tsakaninsu, Amman to Miye dalilin yi mata shamaki da shi.


bata da mai bata wannan ansar, zata bita yadda tace tayi alkawarin bazata sab'ama umurnin taba, zata yi iyakar iyawarta don ganin duk wasu feelings da takeji nashi ta yi yak'i dasu.


Tsakanin ta da salma yanzu zakayi mamaki, sun koma y'an biyunsu sak,kaya kansu Iri d'aya suke saka wa,duk wani Abu na shawara zasuyi da juna, kowace nayin iyakar k'ok'arinta wajen ganin ta guje b'acin ran y'ar uwarta.
B'angaren karatunsu yanzu komi successful duk da ba class d'aya suke bah,suna tsananin taimakon juna wajen karatu, shahid da shahida Suke guarding d'insu sosai Idan suka dawo gidan, koda salma zasuyi jsce Khairat ce tayi mata time table tana sake fahimtar da ita wasu abubuwan da bata gane bah,hakan ba k'aramin dad'i yayiwa su Maah da Abbu ba, ganin haka yasa yace zai saka asa sunan ta cikin masuyin jsce d'in.


Amman tace Aa yabarta ita ba tajin komi, hakan ma yana mata dad'i don tana koyar da y'an class d'in su, dole suka k'yaleta haka salma tazo tayi jsce d'inta cikin sa,a.


B'angaren yayansu kuwa babu ranar banza da baya bugo waya, kuma kowa Ana gaisawa dashi banda Khairat,duk yadda Abbu zai yi ta ansa su gaisa saidai tace Aa Abbu Kace dai ina gaidashi.


Salma kuwa saboda Shak'uwar su da Areef yasa Abbu Ya siya mata waya 7+ da tayi jss d'inta, tun mutanen gida na mamakin shak'uwarsu har suka daina, don idan suna Waya kamar wata zararra dariya da shagwaba,idan kuwa sukai fad'a Khairat ce ke gaya mata yadda zasu shirya.


Yawan sanar da ubangiji damuwarta da take, yasa cikin ikon Allah duk wani zafi da kunan zuciya da takeji idan taga yadda salma Suke waya dashi yanzu ta samu sauk'i sosai, don wata sa,in ma dariya take musu.


Cikin k'ank'anen lokaci salma ta rufta tarkon kaunarsa,wanda ita kanta bata sani ba Amman Khairat ta Ganota,mamaki take tana jiran taji Maah tayi ma salmar gargadin hakan amman taji ko Uffan batace mata ba, tambayoyi ne cike cikin cikinta,amman baiyuwa tayi ma Maah su don bazata fad'a mata bah.


Ta tattara duk wasu abubuwa ta watsar da su gefe guda, ta d'auki karatunta da muhimmanci,indai ka ganni Zaune to ko dai karatu nake ko kuma ina duba wasu words ga dictionary,na saka Kaina busy da ko hirarshi da salma kemun some times bana ma zaman d'akin balle tayi mun, Ina falo cikin mutane Ina d'an saka baki cikin hirarsu Anni.


Su Anty shidah da Yah shahid Sunyi candy,yanzu su Yah kusan shekararsu d'aya da rabi da tafiya, Yah meenah yanzu mate d'in juna muke,shiyasa k'awancen mu yazo d'aya,komi tazo wajena Khairat kaza Khairat kaza, har karatu meke tare.


*shekara kwana inji y'an hausa.*
Har y'an matan uku sun kammala secondary school d'insu, don har Dadyn meenah ya fara hidimar samar masu admission xuwa jamia,yah shahid yana spain yana karantar engineering,Anty shahida tana katsina tana karantar business administration,ta dad'e tana masifar son harkar kasuwanci,maah taita fad'a akan me zata ce shi zatai, saida Anni ta fahimtar da ita cewa, yaro idan yace zai iya had'iye gatari sai asakar masa k'ota,saboda idan aka matsa mata kan wanda ba taso baza tayi karatun bah, wannan maganar ta anni ce yasa su Abbu suka barta tatafi, y'ar aduwa takeyi amman wajen kanwar Abbu take zaune, don dama goggo baraka tana son Anty shidah.


Manyan k'asa su Yah mujahid da Yah Areef suna can UK an rik'esu tunda suka gama, wai sai Sunyi masu aikin shekara uku,yanzu cikin ta biyu Suke next year suna gida war haka.
Salma kamar tayi tsuntsuwa taje inda suke,zuwa yanzu Anni tayi mun bayanin yadda muke da yah Areef, sai hankalina ya kwanta, ganin yadda sweetheart d'ina ke masifar kaunarsa Idan aka rabasu inajin tsoron halin da zata shiga,don ba zata iya jure abunda nake jurewa bah, yanzu kam zance Alhamdulillah duk wasu feelings da nakeji nashi narasa, saboda na farko bana ganinsa, ko waya ba muyi, don cikin shekarun nan da basu nan sau d'aya mukai waya Shima ina kwance kan cinyar Maah, naji suna Waya yake tambayata da yi mata k'orafin bana gaidashi,tunda nai waya shine ta bani Shima kuma bai wuce y'an seconds ba.


"yah ina wuni."


muryarsa ta sake zama ta y'an Gayu yace,


"ai da fushi nake dake Khairat,amman dai na huce ya kike ya karatunku."


Nace,
"Alhamdulillah karatu ka gaida yah mujahid."


Na mik'a mata wayar, ita kanta tayi mamakin yadda Nayi, bata ce komi ba, suka cigaba da wayarsu har nayi bacci.


Nida salma kowa ji yake da kyansa,bawai batun son kai bah, zan iya cewa nata b'angare d'aya ne, ni kuwa duka b'angaren biyu na d'auko, don Maah fulanin yola ne na usil, Abbu kuma buzune Amman kuma k'ar yake kamar Jini zaifito jikinsa, yayinda Maah take ruwan tarwad'a amman hutu dajin dad'i yanzu yasaka takoma jawur,
Na biyo Abbu ta wajen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login