Showing 27001 words to 30000 words out of 69834 words

Chapter 10 - ABIN CIKIN RUHINA BY MISS BB.txt

Miss Bb   

10 Jul 2024

8264

duka,zuciyarsa tana zafi,idan kakalli idonsa zakasan zafin da yakeji ga ranshi.
"Fitarmun anan karkija nayi kasa kasa dake awajen anan."


Kuka nake wanda bazan iya tuna lokacin da nayi shiba,haka nafito jikina yana kerma kafafuna sun kasa d'aukata,can gefe nasamu na durkushe ina cigaba da kukana mai cin xuciya.........jinake kamar zan sike ni za,ama aure saboda nayi me kawai don na ansa gayyatar malamina,banyi iskanciba banyi fasikanciba babu abunda aka kamani dashi na haramci shine zasu tsigeni daga karatun da nake so fiye dakomi...............kiransu aka farayi na minty biyar har akafara sanarawar rufe jirgi......inanan durkushe kuka kurun nakeyi.
Taku naji abayana ahankali kamshin sa yna sake nufoni,har sanda ya tsaya gabana,durkusawa yayi ya d'agoni tsaye kokrin cire hannuna yake ina bige hannun nashi dake tab'ani,don wani irin haushin sa nakeji,hakan bai hanashi son ganin na bude fuskataba,karshe dole nasaue hannun ina shashshekar kuka idona rufe,duka hannayena ya rik'e da hannu guda dayan kuma yadago hab'ata,kada kaina nayi yasake juyo da fuskar tawa gabanshi,uffan baice ba illa iyaka sakin hnnuna yyi yasaka handchif yana tsane mun hawayena,amman still wasuna biyo baya.
Jinai wani irin feelings ya taso mun form some where,wanda bazan mance iri a ba ranar daya daukan yakai har daki.........tun daga yatsan kafata nakejin wani yanayi har cikin jinin jikina,numfashi nake saukewa zuwa yanzu kukan ya tsaya,saidai ajiyar zuciya kuma har lokacin banbude idonaba,kallon fuskata kawai yake jinai anata neman shi jirgi zai tashi amman shinko ajikinsa,sai lokacin na bude idona ahankali idonsa ya sauya launi yakada yayi ja,amman hakan bai hana wani abu fitowa ba yana shiga cikin nawa idon.
Jinai kafafuna bazasu iya daukata ba,silalewa zanyi kasa yayi azamar rikeni,saidai najini yayi mun wata kyakkyawar runguma.
Fashewa nai da kuka wanda yafi nafarko,bubbuga bayana yake yakasa magana,injiyo yadda zuciyar sa ke duka dagoni yayi yasunbaci goshina,kuncina da tafin hannuna.
Saida na rutse idona kafin ya yimun rad'a ga kunne *INA MAKI FATAN ALKAIRI MATAR MUHAMMAD KASEEM,SAI WATARANA BAZAKI SAKE GANINA BA,KIYI HKRI DANI MUN HARAMTA GA JUNA HAR ABADAN,BAZAN IYA KARYAWA MAAH ALKAWARINTA BA.ZANJE NAYI JINYAR XUCIYATA KIKULA DA KANKI AND PLSSSS FORGET ABOUT AREEF FAROUK,GOOD BY UMMULKHAIR.*


(Wayyo nasan YAN ZAUREN MRS BB ZASUYI MISSING AREEF.)
MUHADU GOBE LOVE U ALL MY MASOYA πŸ˜‚πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ’•πŸ’•πŸ’•


MRS BB CE πŸ‘ŒπŸ»
09034722970
[6/8, 1:14 PM] Mom Muhseen: πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•
πŸ’•πŸ’•
*_ABIN CIKIN RUHINA_*


Written by mrs bb
Mom muhseen.


Wattpad
Humaira7531.


DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.


NOT EDITED:INKUNGA MISTEK BE SORRYπŸ˜‰


27.
Missing pageπŸ’•


Silalewa nazoyi zan zube sabo yadda jikina gaba ki dayanshi babu kuzari,babu karfi tare dani jinai anyi azamar rikoni,bazan iya gane ma kowaye ba nadaiji muryar yah jahid yan cewa abude mota,kilan shine yatareni.
Motar aka sakani sannan nafara gawowa natsuwata,ina hango jirgin ya lula cikin sararin samaniya,wani kuka ne ya kubceman mai rikitarwa,na dunkule waje guda inayin abuna.........Anty ce tarungumoni jikinta tana lallashina,
"Kiyi hkr mana ance makine yatafi kenan,duka wata nawane in Allah yakaimu."
Jinai yah jahid yace"nima cikin satin nan zantafi ai."
Cikin rudewa tace"rufaman asiri kabari idan anyi auren saimutai duk inda kakeso,amman wlh banda yanzu azan iya jurewa ba."


Murmushi yayi yace"to taya kike tunanin ita zata iya jurewa,kinsan irin d'acin da takeji cikin zuciyarta kuwa."
Daina kukan nai don inason tabbatar wa shin dagaske auren za,aimun don maganganunsu sun nunaman cewa ansan da kaunarsu agida.


"Anty,wai dagaske aure Abbu zaiman."
Kallona tayi tace"ina kiji maganan nan,bacin anhana kowa yi maku ita."
Jinai wani kullutu yazo man wuya ya tokare,shiru nai ban sake tankawaba.
Don wani abun yafi gaban kuka sonake naje naji shin dalilin dazaisa atsigeman karatu ayiman aure,bayan ni nace baso banasoshi yanzu abarni nayi karatuna mana,wallahi duk wanda yayi dalilin wannan maganar Allah ya isarmu.


Muna isa gida afusace nafito na wuce bangaren maah,bata nan na zube kan gadonta ina sharar kwallah jinake kamar nayi tsutsuwa na bishi,wani irin yanayi nake ciki rashisa yafi mun ciwo matuka akan auren da akece za,aimana,jinake banda wani sauran farinciki ko annashuwa akan tafiyarsa,duk wani feeling's dinsa danakeji ada can baya,na yanzu yalinkashi goma kirjina nakejin yana mun nauyi,jinake bazan iya kaiwa har wannan lokacinba,wata hudu koma fiye dahaka wannan abun danake ciki zaibarni kuwa.
Maah ce tafito daga bandaki tayo wanka,kallona take yi batace komiba.
Ina ganinta natashi na fada jikinta narushe dawani irin kuka mai tsananin cin rai.............bata kokarin lallashina ba kuma tabace mun komiba yinake yi har inajin kamar numfashina zai dauke,cikin kukan nake cemata"maah Meysa zaki yarda aiman aure nan,maah kinfi kowa sanin banso ni banso karatuna nakeso ayazu nakeson aurenba,maah wallahi in akayishi zanshiga wani hali kitai amakeni,kiyiman rai............rungumeni tayitsam jikinta muka kara sa saman gado da ita sai lokacin tashiga lallashina,
"Ya isa haka kidaina kuka,inkinason nayi maki bayani idan kuma bakyaso to kiyita kukan."
Dole nayi shiru ina sauke ajiyar zuciya sai shan majina nake,shiru duk mukai ina sauraronta.
Cikin taushin murya da lallami tafara man bayani.


"Bayan tafiyarki makaranta kinkoma hostel,zuwan inna gidannan yafi biyar tana zuwa wajen mahaifinku bai dawo ba,bayan yadawo tasake zuwa muna tare lokacin ko ansa gaisuwata bataiba,take yiwa Abbunku magana akan tana bashi umurnin cikin wata uku ya aurar da duk yaran dake gidannan,don salma taje tasameta akan cewa itafa batason karatu,aure takeso kuma wanda takeson ni nahana shi ya amunce da ita,ina son dole sai nabashi aurenki."


Anan tasan cewar Areef banau bane,tayi fada tatashi hankalin kowa agidannan,har takecewa sai yabar gidan tunda bana uban shi bane,wallahi idan baibar gidanba saita tsinema mahaifinku.
Ananfa shima yanuna mata nashi b'acin ran,yace Areef bazai tafi ko inaba shine ubanshi har duniya tatashi.
Tace to kuwa wallahi zaiga bacin ranta kuma muddin bai aurar dakuba tasan matakin da zata dauka akai,kuma wallahi muddin tana raye cikin ku jikokinta babu wacce zata auri Arref,.
Anan nace ta kwantar da hankalin duk cikin yarana baida mata,domin Areed dana nacikina nake kallonsa,yayansune shi tsayyae kan lamuransu,nan tace naimata rashin kunya ke tashin hankali babu kakkautawa,saida ker Annie tafiddata gidannan.


Ranar salma bata kwana gidanba don wallahi nai alkawarin tashigo hannuna sai na lahira yafita jin dadina,bayan wannan yawuce Abbunku yazaunar dani mukai magana kan issue din,cewa salma fa ta dge akan muddin bata samu Arref ba to kuwa babu wadda zata zauna dashi,kuma Khairat bazata zauna lafiya dashiba,don wannan tsoron dakikemai salma ce takai sunanku wajen malamin zaure,akan ya shiga tsakaninku yamaki tsoronshi,yafidda maki duk wani yanayi da soyayyarshi cikin ranki,kinji dalilin jin tsorsnki.
Abbunku yaje yayi bincike sosai yagano hakan daman ni tun tana nan gidan nalura da ita,bandai cewa kowa komiba.
Anan dai yace mun kowacenku bazata aurai ba kuma aurar daku shine yfiye mashi kwanciyar hankali,yanajin tausayinki don yadda yaga kinason karatunki yanajin takaicin tsigeki yayi maki aure.
Amman Baida mafita sai wannan,da har yace akwai yaron abokinsa zai hadaki dashi,to kwatsam saiga yayanku yazo yake sanar da Abbun cewa ai kinada ma wanda kikeso karyayi maki wannan auren nahad'i............Saboda son da areef kemaki yasa Abbun ku canza ra,ayi kan hakan,yace zayi bincike akanshi kuma yayi ya tabbatar da natsuwarshi da gidansu,."


Zuwa yanzu idona yabushe saidai wani irin masifar zafi dasukeman,zuciyata duka kurun take nace"maah wallahi ni bason shi nakeba kawai mutunci yakeman saboda yasan ni kanwar yah Areef ce baice yana sona ban."
Kallona tayi yace"nasani khairat,duk abunda kefaruwa yayanki ya gayaman,yaban shawarar kuma data dace dake."
Kallonta nake cike da mamaki "wace shawara ken maah."


"Yace in tsaya tsayin daka don ganin kin auri Dr,domin hakan shizai kawarda tsananin kishin da salman keyi dake,hakan zai dauke idonta daga kanki tabarki kiyi rayuwarki cikin aminci,saboda yanzu ta hakura dashine saboda tasan kema bazaki samaiba.
Saboda Areef yatafi kenan harsai anyi aurenku kuntare kozai dawo,don haka kiyi hkr kiyi hkr kiyi hkr khairat,duk abunda yau kaga kanata haukan sonshi baka samaiba to Allah yasan hakan shine alkairinka,bansan dalikin dayasa Allah yasa lamarin yazo ahakaba,nidai nasan zabi nabashi kuma wannan shine zabindaya bamu nidake,don bantaba hutawa ba wajen yimaku adduar samun abokan zama nagariba,don haka karki bani kunya karkibiyewa zuciya takaiki tabaro kirungumi kaddararki hakan shine Alkairinki."
Shiru nai narutse idona ydda nakejin kirjina yana suya injin bakina yana d'aci,yasa nakama ambaton sunan Allah,ina karanta hazbunallahu wani imal wakil.


Munfi minty talatin shiru babu maicewa komi,sai lazimi nake ita kuma tana shashshafa kaina har naji abunda ya tsayaman ga makwogworona ya rage kaifi.
Nace"ita salmar waza ta aura maah."
"Wanine d'an uwan mamanta,sun ma daidaita kansu dazu fadan dakikaji Abbunku namata kancewa ita bazaitayi karatuba ne."


"Ita ma Antynku ai sun daidaita ita jahid,abun yayi man dadi sosai,da ace yayanku zai yarda sai y auri meenah."


Saboda bugawar da zuciyata tayi yasa dole na rutse ido.


Tacigaba dacewa"amman bazan masa tutsuba nabarshi ya huce daga rashin samunki,sai yanzu nasan bankyaita mashiba khairat saboda tunfarko bak'inki yakeba saboda ni yakoyawa kanshi shamaki mur,baya wasa dake bayan yanayi dakowa,yanayine don kema kicire abunda keranki akanshi,yana ganin idan kunmani biyayya zanji dadi.
Inason Areef saboda biyayyarshi gareni,indai zanyi farinciki tokuwa komiye zaiman,zanyi kewarshi sosai dalikin kukana kenan dazun,don nasan wallahi bazai dawo don yanzuba,nakira yaya hafsa nayi mata bayanin komi takuma fahimceni,nace tayi kokari bayan bikinku ta sashi yadawo,takuma tabbatarmun da hakan."


"Ya matsayin karatuna yanzu kenan."


Ajiyar zuciya tayi tace"yananan,kuma kobayan anyi bikin zaki cigaba insha Allah,ai muhammad bazai hanaki karatunkiba kiyi kokri kiyinashi biyayya kikoyama kanki sonshi,nasanma zaki soshi don yanada komi da yadace asoshi.


Anty shida tashigo mun da abinci,don sai yanzu natuna da ashefa ko break banba,tashin hankalin danake ciki yadanne yunwar danakeji,dukda haka wanda naci baia yawa wanka nai nazo nakwanta daker nsau bacci.


Karfe shidda nayi shirin komawa school,gaba d'aya bana cikin yanayi najin dadi,xuciyata ciwo take anya zan iya jure rashin yah tare dani,wai wannan wane irin lamarine,yah Allah kaine ka halittamun wannan zuciyar,kafini sain halin data keciki ka kawo mata agaji.........basan ta yadda zan sarrafa taba goge kwallana nayi bayan nagama shiryawar,fitowa nai na samu duk suna falo,wajen Annie naje narungumeta naji kwallah sun cika man ido,nai saurin sharewa nace masu zanwuce.
Yah meenah tace"saina biyoki gobe,munyi magana da dady ya amunce saigobe idan nagama shiryawa zakiganni,koma kibari mutai tare."
Murmushin dole nayi nace"inada class karfe takwas,bazanso nayi missing ba,saboda lecture tana da muhimmanci sosai."
Jinjina kai tayi tace"da kyau DR KHAIRAT anason irin haka."
Duk dariya sukai Anty tace"dr dama wlh inason inganki,tashi nai banda lfy kozaki dubani."
Dariya ma tabani nawucesu suna ta dariya,nalura sosuke su rageman radadin da nake ciki.
Jikkata na dauko nafito nacewa maah"maah don Allah aban mota hakanan wlh nagaji da yawo kan taxi."
"Kibari kiyiwa Abbunku magana idan yayarda sai abaki."
Sallama nai dasu nafita saboda tunani bansan ma nazo bakin titiba,haka dai na isa makarantar husna bata kai ga isowa ba,zubewa nai kan katifarmu nahau tunanin dai da yanzu nasan mun kullah kawance dashi.


Saidai a class muka hadu da Ita,tace shigowarta kenan wlh da bataso dawowa ba don dai tanason taji yadda akecikine.


Ganin yadda idona yayi raurau zanyi kuka yasa tace"aa karkiyi anan bari agama komi kenan saiki gayaman."
Ranar ba komi nagane ba sosai amman inayin bakin kokarina ganin nafahimta,don akan darasin zaimana test gobe.
Koda muka koma hostel kuka na naitayi sai daker na iya gaya mata duk abunda kefaruwa,ina kuka ina shashsheka ita kanta saida tariga kwallah,rungumeni tayi tashiga bani hakiri,kamar yadda maan tayi,don yanzu babu wata mafita data wuce hakurin.
Wannan dare ban iya samun bacci ba,har garin Allah yawaye sadda za,ace rana tayi wani mugun zazzabi yasauko man,har wata makerketa nake,hakorana suna gugar juna.......duk inda hankalin husna yake yayi masifar tashi,kuma na hana ta takira wani dan gidanmu......karshe dai saboda dole gida nakoma saboda ciwon yaki sauki,zuciyata ciwo take babu kakkautawa saida na dangana ga asibiti,kwana na biyar cikin kwanakin nan kuwa Dr mk zaruarshi bata kilguwa safe rana har da dare ma zaka ganshi,har mahaifiyara yakawo tadubani.
Saida nakara kwana biyu aka sallaman.


Mrs bb ceπŸ‘ŒπŸ»
[6/9, 7:32 PM] Mom Muhseen: πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•
*ABIN CIKIN RUHINA*


Written by mrs bb
Mom muhseen.


Wattpad name.
Humaira7531


DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.


*GODIYATA GA MASOYANA BATA DA IYA KA,SAIDAI NACE MAKU ALLAH YA BIYA MAKU BUKATUNKU,HAKIKA BANDA KAMARKU INAMATUKAR ALFAHARI DAKU.*


LOVE U SAHIBA TA ALLAH YA RABA LFYπŸ˜‰πŸ’•


28.


Gida na koma bayan an sallaman,don maah kin yarda tayi danace abarni makaranta na samu sauki,wai ita aa tafison ina gabanta har na idasa wartsakewa.
Yah meenah kamar ita ke ciwon duk tabi ta damu,kin komawa tai hostel wai saina warke mukoma tare,Abbu kanshi yashiga damuwa matuka inhar yana gida yini yake zarya dakin maah yana dubani,in yatadda ina bacci zai sunbaci goshina yace"Allah yayaye maki ta alkairi,Allah yana tare dake."
Cikin ikon Allah nasamu sauki sosai,har nakan fito falo adanyi fira dani,sabanin kwanakin baya da ko magana banson yi,kuma banson aiman,don idan aka cika man magana zan fashe maka da kuka,dole suka kyaleni amman yanzu ni da kaina nake fita can.
Dr yau yace zai zo ya sake dubani,kasancewar yanzu muna waya ba laifi,don anyi komi game da maganar auren mu,manyan shi sunzo anyi komi cikin mutuntawa.
Han itama salma nata sunzo duk rana daya za,a daura amman nasu Anty shida ba yanzu ba,yajahid yace ayi mashi hkr sai nan gaba akwai abun da yake maimuhimanci.


Nayi kokari matuka wajen ganin na cire damuwa da tunaninsa,amman lokaci lokaci nakan boye nayi kukana don shine abunda zai rageman radadin da nakeji na rashinsa.


Na fawwalama Allah komi na anshi dr matsayin mijina,tunda na lura son da yakeyi man maigirma ne,soyayyar sa mai sanyi da shiga ran duk wanda akemawa,hakika nayarda da maganar maahda take cewa ya nada duk abunda za,a soshi,nafarko dr handsome guy ne dan gayune sosai,daga ya nayin shigarsa zaka gane hakan, sannan ma,abocin son kamshine kamar dai yah Areef,don shi kafinma ya iso waje turarensa ne d first dazai sallama wajen,to shima dr haka sannan ga fara,a ban taba ganinsa yana shan murba ko cikin aji fuskarsa asake,baza kace yana dariya ba kuma ba zakace yana shan mur ba,kadaran kada han,ya iya barkwaci,duk yadda kake cikin bacin rai zai iya saka ka dariyar dabaka shirya ba.


Dr Ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin ya daidaita natsuwata,nadawo cikin hayyacina shiyasa maah takejin dadi duk randa yazo,itace hada wannan itace hada wancen,haka Annie kai duk yan gidanmu kowa yana son dr sosai,amman banda salma don har yau salma bata shiga sabgar kowa.
KO Ameer dinta yazo babu mai wani rawar jiki,idanma ya samu gaisuwar kirki wajen yan gidanmu,saboda shima halinsu guda da ita,daidai gwargwado maah tana kwatanta adalci tsakaninmu duk da cewa ba itace ta haifeta ba,amman duk abunda ta siya man to zata soya mata itama,saboda tace har gobe salma diyace wajenta haihuwarta ne kurun ba taiba,don haka zatai mata duk abunda uwa take ma yarta.
Duk da wannan abun bai saka salma taringa gaida maah ba,bata gaidakowa yanzu,har gara idan yah shahid nanan zai ci ubanta yace kuma sai ta gaida duk wanda ke saman ta,duk randa akai irin haka bata kwana gidan sai tayi tafiyarta gidan inna,wannan abun da ta keyi ya kara sakaman salma tafita raina,don duk wanda bai girmama mahaifana ba nayi dashi.
Abbu duk yasan wainar da ake toyawa baidaice komiba,don inajin inna tayi kalami mai kaushi akan salmar,bansan dai me tace mashi ba.


Rannan Abbu yazo har dakin maah yayi man ya jiki,ya saman ina bacci hirar su ta tadani,sai ban nuna na tashin ba,naji maah tana mashi complain din salmar yace"saudah,kiyi hkr kibar yiman zancen yarinyarnan,tunda kinsan bazan iya yin komi ba,akan kunnenki inna tayi man Allah ya isa idan na sake takurata ko nayi mata wani abu daya bata ranta,kibarta tayi duk abunda ta ga dama kowa rai yaima dadi baya ga maishine,Godiyar danake ma Allah daya bata miji daidai ita,munanan daku Allah shine zaiyyi maganinta."
Maah bataji dadi ba tace"karkayi mata baki Dear,hannunka baya rubewa ka yanke kayar,ya kama ta kayi mata addua kurun."


Murmushi yayi yace"hakika samun mace kamarki mai tsarkakakkar zuciya sai antona,Allah yai maki Albarka Addua kuma ai tunda aka haifeta nake mata ita,don haka kifita batun salma karki ma sama ranki damuwa."


Hakan baisa maah ta daina duk wani shiri ba akan bikinmu,wanda yarage sauran sati uku.


Halin da ake ciki kenan.


tunda yah yatafi baya waya dakowa sai maah da Abbu,kilan kuma sai yah jahid.
Sau daya naji sunyi waya har take gaya mashi nayi ciwo har nakwanta asibiti,sanda na same ta suna wayar zama nai kusa da ita nace taban mugaisa.
"Tace ga shima zata gaidaka."
Sai cewa yai Kyaleta maah kidai ce inamata yajiki.
Wannan abun ya tsaya man garai ranar yini nai in kuka kamar bazan kai ba,sai daker na samu kaina.


Tunda na sanar da maah cewa dr zaizo taita shige da fice nidai iyakata shirya kaina idan yazo,babu laifi dr ya samu gurbi cikin zuciyata,saidai gaskiyar magana soyayyar da nakewa dr ko kwata kwatar wadda nakewa yah Areef bata kamoba,saidai inayin iyakar kokarina naga nanuna mai tawa soyayyar,kuma hakan yana matukar faranta mashi.
Zuwan husna uku gidanmu dubani,saida nayi yadda nai na had'ata da yah shahid har naroki ya maidata makaranta,to sonake na koma naji yadda suka kare don naga tunda ta gaida shi naga yaki tashi daga falon,yana satar kallonta nasan sai wani abu yabiyo baya.


Wanka nashiga ganin yamun text yana hanya,inaji maah tashigo tana fad'a "kullum sai kinga yakusan zuwa zaki tsiri wankan iskanci,kiyi ta shegiyar nawa kishanya bawan Allah yana jiranki,wallahi kishiga taitayinki kafin wata tayi maki kafa."
Dariya ma tabani ina shigewa kurun bance mata komi ba,maah nason dr sosai,tana son aurena dashi.


Yah meenah tashigo kirana lokacin ma nake shafa mai,itama fadan tayi man wai ina gasa shi dayawa,don naga yana sona sosai.
Murmushi nayi mata kurun,don danayi magana zatace nacika gardama,ita tafiddo man kayan dazan saka,riga da siket sunyi mun kyau sosai,kasancewata mace mai dirarran jiki tako ina jikina adire yake,don namafi duk yan matan gidanmu kirji masha Allah,don cib da cib sukaiman,salma kuwa saita had'a da breziya mai soso.
Hips dina shima daidaidani baiyi yawa ba haka baiyi kadanba.
Itace tayi man d'aurin kallabi don yah meenah gwanace indai nan bangaren ne,gyale kalar kayana ta fiddo man sannan tafesheni da turare maishege kamshi,sanna taja ni muka fito falon bakin dake bangaren Annie,don acan ta saukeshi saida taga shigata takoma don kawo mashi abun tab'awa.


Tunda nai sallama ya mike yana wani irin killer smile,ya saka hannayenshi cikin aljihun wandon jeans dinsa,ya karkace kai kallona kurun yake babu kakkautawa.
"Wow wow my princess,irin wannan hadewa sai kija miyauna yayita zuba babu kakkautawa."
Dariya nayi ina sadda kaina don dr badai sakin layiba,isowa yayi gabana yana bude duk hanayenshi,kallonsa nai ya daga a gira

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login