Showing 6001 words to 9000 words out of 69834 words
aka cire mani drip, tana kallona kallon da ban tab'a ganin Anni tayi Mani shiba jinai tace mun.
"y'ar gidan Anni yajikin naki."
idona ya ciko da kwalla nace,
"Anni Ina kwana."
Murmushi tayi tace,
"lafiya lau yajikin naki."
"da sauk'i Anni saidai inda yah ya dokeni jiya Anni ciwo yake mun ko zaki gasa mun."
tausayi ta bata Amman ta danne bata nuna hakan sosai bah tace,
"Ayya sannu kinji bari Antynku ta kawo ruwan zafi sai agasa maki."
"nagode Anni nah ke kad'ai ke sona ko."
Murmushi tayi mata tace,
"Aa y'ar gidan Anni kowa yana sonki, meyasa kikace haka. "
"Anni yah Aree baya *kaunata* yafison salma akaina."
Gabanta ya fad'i meke faruwa haka, Khairat yarinyar da bazata Gaza shekara 13 ba tasan kishi, danne fargabanta tayi tace,
"Haba y'ar gidan Anni Waye yace maki haka, aduk cikinmu in banda Abbu da Maah babu mai son farincikin ku sama da Areef."
Hawaye suka zubo mani nace,
"no Anni wallahi yah baya sonah jiya naga haka yau ma naga haka, nidai daga yau babu ni babushi, Anni kinsan abunda yasa na fad'i jarabawa ta."
Tana kuka take maganar hawaye share_share ga fuskarta,Anni gabanta banda duka babu abunda yake, sunan Allah kurun take anbata,don wannan lamarin na Khairat to saidai akira sunan Allah kurun.
sake danne yanayin da take ciki tayi tana yak'e tace,
"Ina jinki y'ar gidan Anni,meyasa kika fad'i exam dinki har kika bari aKai maki repiting."
Wani kukan ta rushe dashi saida tayi iyakar Inda take so sannan tace,
"Anni don Allah karki gaya ma kowa kinjiko idan yah yasani sake dukana zaiyyi."
Ai Anni jitake kamar ta zura Aguje,
(ππππ yo baki bari Kiji komiye tun yanzu har kin shiga rud'u.)
"Namaki Alkawarin babu Wanda Zaiji wannan maganar sanar da ni kinjiko."
share hawayena nayi nace,
"Anni tun daga ranar da Abbu yace su Yah zasu tai wata k'asa karatu nashiga cikin bak'in ciki, kullum saidai na b'oye toilet nayi ta kuka, ko idan naje makaranta inyi, har Cikin dare yi nake Anni saboda banson ya tafi, gashi maah tace idan suka tafi sai sunyo shekara shidda ko bakwai zasu dawo, Anni banson yah yayi mun nisa inaji kamar inbishi ko ince karya tafi, Anni kinsan abunda yake bani tsoro har yasa naki sanar da kowa."
Anni tayi Wata irin zufah duk AC din dake sambad'owa ad'akin kuwa, daker ta had'iye wani kakkauran miyau amak'oshin ta tace,
"Aa ta Alkhairin Abbu meke baki tsoron."
Sake share hawayena nayi Ina cewa,
"akwai ranar da sweetheart bata je makarantar islamiya ba, malamin mu ya gama mana darasin sa akan mutanen da ya halitta ka aura, da kuma wanda bai halatta ka aura bah, ban fahimce shi sosai bah Anni sai na bari da aka tashi naje har office d'in Su nasa meshi nayi masa tambaya,
"malam don Allah ko mutun zai iya Auren yayansa wanda suka fito ciki d'aya."
Kallona yayi yace Meyasa nai masa wannan tambayar nace,
"wata ce tace na tambayar mata Kai."
Jinjina Kai yayi yace mun,
"Aa Khairat haramun ne babu aure tsakanin su har abadan."
Banjira sauran bayanin sa ba na tashi na taho,
Ko drivern mu banjira ba ranar nataho ina kuka, gida ban bari ko salma tasan me yafaru bah."
"kinsan me yasani kukan Anni."
Kallonta take tana jinjina kaifin tunani irin na Khairat,kafi tace"Sai kin fad'aman."
Wani kukan ya kucce mani Nace,
"Anni ba komi ne ya sani kukan bah illah yadda nakejin yah Areef acikin raina, Anni ni Yarinyace nasan da hakan, Amman nima ina mamakin yadda akai har nasan *so* Anni bansan tsawon lokacin da na samu kaina tsundum cikin *kaunar yah Areef* ba, wallahi ban saniba kuka yaci k'arfina naci gaba da cewa, wannan abun da nakeji yasa nayi ma malam tambaya, sai kuma naji cewar babu aure tsakani da shi har abadan,kinji dalilin fad'uwata jarabawa na gaza sanar da kowa saboda dai wannan Abun kunya ne awajen kowa............kuka yaci k'arfina Anni kiyiwa Allah da manzon sa karki gaya ma kowa, don nayarda dake ke bazaki dakeni ba shiyasa na sanar dake.........."
Tabbas wannan lamarin ya hargitsa kan Anni, duk ta diririce Lallai Allah mai hikima tunda har hakan tafaru akwai abunda da Allah ya b'oye,amma Duk da haka yarinyar na buk'atar lallashi da ban baki,zatayi wannan k'ok'arin Insha Allah.
lallashina take cikin kalamai masu kwantar da hankali,tare da cewa"ki fawwala ma Allah tunda shine ya sanya maki hakan, kiyawaita sallar dare nasan ki da wannan k'ok'arin,to kici gaba sannan kiyi yak'i da zuciyarki akan shi kiringa jarumtar danne komi kikeji Akansa, Allah zai yaye maki kinjiko y'ar gidan Anni,ki rage kuka ki rage taurin kai sannan yanzu so nake ki janye daga gareshi,ban kuma ce kidaina gaidashi ba Amman kijanye mashi idan bashine yakiraki ba karkije,hakan zai saukaka maki komi kinjiko y'ar gidan Anni."
"to Anni nah Nagode zanyi Insha Allah daman ina tsoran gaya ma wani ya bigeni shiyasa nace bari ke in gaya maki, dama na yanke shawarar janye mashi."
Haka taita lallashina har naji duk damuwata ta ragu sosai.
Bajima wa Anty shidah ta shigo da Kayan break tayi mamakin ganina cikin walwala, har ina yimata dariya ruwan zafin Anni ta had'a ta d'age mun rigata na yi kwanciyar rufda ciki take Gasa mun, tana cewa ai dole yamaki zafi duba kiga yadda ya fasaki.......tana Cikin gasawar Ya shigo....... Lumshe idona nayi inajin dadin gasawar.
Gabansa ya fad'i duk ni nayi mata wannan dukan, innalillahi dole kiyi fushi dani sweetheart,amman afili sai dai yace mun sannu kawai, tunda nace Yawwa ban sake ko kallon shiba komi Anni tayi mun, brush da wanka ta kuma bani abinci naci, Zuwa can saiga Maah da Dadyn meenah sai Abbu, sunjima kafin Su tafi sunata tsokana ta.
Har aka sallameni ba muyi wata magana da shiba, haka muka koma gida salma sai nan nan take Dani, idone nawa kawai.............
Na warke sumul Amman na shigo da Wata sabuwar d'abia ta rashin magana, bana shiga shirgin kowa haka duk maganar da zakai mun zan tarasu in baka one ansa.
Anni ce kurun nake hira da ita ko salmar na banzatar da ita,duk Inda hankalin Areef yake yakai k'ololuwar tashi saidai duk maitarka bazaka gane halin da yake ciki bah.
Kwamci tashi ba wuya wajen Allah har Gashi jibine tafiyarsu UK.............
mom muhsen ce
Mrs bb ππ»
love u fan's ππβ€
[5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: ππππππππ
*_ABIN CIKIN RUHINA_*
Written by [Mrs bb]
Mom muhsen
*____________________________________*
*ππ°AINUWA πΌRITER'SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
3.
Alhamdulillah gida ya tsaru iyakar tsaruwa,babban gidane mai fat Kala Kala wanda saboda girman Abota irin ta su Alhaji farouk yace da Amininsa jafar yazo su zauna tare,har kuka yayi saboda farin ciki haka suka dawo gidan rana guda, komi sabo aka loda masa yayinda tuni angyaare ma Inna wancan gidan ba zaka tab'a cewa shine bah.
Rayuwar ta cigaba da kasance masu Cikin jin dad'i da kwanciyar hankali,yayin da Wata irin shak'uwa mai K'arfin gaske ta shiga tsakanin *AREEF* da k'annensa *khairat da salma* idan Sun dawo makaranta shine wankansu ya shiryasu ya zubo abinci yaringa basu har sai sun koshi, sannan assessment d'insu zai zauna ya tusasu gaba yana guarding d'insu yaga Sunyi shi lafiya lau, Areef saboda k'annensa ko fita baya yayi, Duk nacin *mujahid* haka zai rabu dashi, haka shahid da shahida Duk yadda suka so Cikin weekend ya ringa binsu shopping sai yace bazai bisu bah, saboda suna cin zalin sweetheart dinshi,dole sukai hakuri saidai driver ya kaisu shikuma Ya ware rana ya kaisu da kanshi.........wata guda kenan da kammala secondary d'insa,tunda twince suka girma Maah ta hana yaringa masu wanka da shiryawa,tunda yanzu ko wacece zata iya yiwa Kanta wanka da shiryawa, yanzu suna js one yayinda shahid da shahida Suke ss2, Muhajid tare sukai graduation da Areef, Neenah ce take js3.
Shirye shiryen tafiyar Areef da Muhajid ake zuwa UK jamia,wanda idan suka tafi baza su dawo bah sai Sunyi har masters d'insu........
Motarsu na tsaya wa suka fito Aguje suna kyalkyata dariya,kowa so take ta riga y'ar uwarta isa cikin gida wajen yah Areef kafin Su shiga saiga su sun fito shida mujahid Aguje sukai kanshi, dariya suke masu shida mujahid......kafin ya ankare *salma* ta mamuk'eshi tana dariya har da yiwa *khairat* gwalo aikuwa me zatayi banda kuka, bilhakki da gaskiya ta shige gidan tana rera kukan shagwaba,duba Maah tayi bata ganta ba yasa ta nufi b'angaren Anni tana shiga sukai kacib'is Anni ce ta tatareta.
"lalalala kairyn Anni waya tab'aki zo zo taho muji."
Ta jata jikinta Maah tace,
"Uhm bai wuce rigirmarsu ita da salma, yanzu haka riganta tayi isa wajen Areef."
Annin tace,
"wai haka ne yar gidan Anninta."
Wani kukan ta sake fashe wa dashi tana cewa,
"Anni kingani salma ko, kullum sai ta ringa rigana wajen Yah Aree,kuma nace mata yau ta barmun in rigata shine ta k'iya,gasu can suna mun dariya."
..........ta sake rushewa da kuka.
Dariya Maah tayi tace,
"ai na gaya maki kullum rigimar kenan, salma ta rigani,salma ta rigani tunda ke lusara ce komi babu hanzari,ba dole komi salma ta rigaki ba ko wanka da shiryawa sai bakina yayi tsawo kike gama wa inhar Areef baya nan."
Anni zatai magana Areef ya shigo rik'e da hannun salma, har tayi wanka da ga dawowar ta ga lollipop nan Areef ya bata tana ta sha.
"Ayya sweetheart gamu munzo biko,ke baki yin zuciya kiringa riganta kema, Amman kullum sai Kinyi kuka, Kinga zo zo mu shirya."
Maah dai ficewa tayi tabarsu Inda sabo sun saba wannan fad'an basu wuce d'an lokaci kad'an sun shirya.
Anni ta mik'e tace,
"sorry y'ar gidan Anni kije yayanku zai shirya ku,sanan kiyi wanka anjima ma zaku rakani unguwa."
Salma tace,
"Anni irin wannan gurin da kikaje damu rannan,har aka bamu chocolate."
Dariya tayi tace,
"shazumamu sarkin Shan zaki bacan ba,wani wajene kama hannun y'ar uwarki kuje ki taya ta shiryawa. "
Kan ma salma ta iso wajenta ta fashe da kuka,
"ba zanje wajensu bah."
Ta ruga can cikin gidan Annin ta barsu sake da baki."
Don irin hakan bai tab'a faruwa ba, Duk yadda suka b'ata da juna to kafin anjima sun shirya kansu, ko kuma wata sa, in Yah Aree ya shiryasu.
Salma tace kamar zatayi kuka, don idan sukai fad'an duk rud'ewa take ko kau itace aka kwara.
"Yah Kaga sweetheart ko."
Idonta ya cika da kwallah
Murmushi yayi ya d'an sunkuyo yace"kar kidamu my Angel, sweetheart dinki zata huce zo muje muci abinci."
Anni tace,
"zan lallasar maki ita kinjiko salma yar albarka."
D'aga Kai tayi tana sake goge kwallarta,janta yayi suka fita, Annin ta wuce wajen Khairat d'in.
ππππππππ
Wasa wasa Khairat ta k'i shirya wa da salma, haka Shima Areef d'in ta daina shige masa,tama koma gaba d'aya wajen Anni bacci ne kurun yake maido ta cikin gidansu, hakan ya saka salma cikin damuwa saboda tunda suka taso irin haka bata faruwa tsakaninsu.
shi kanshi Aree ya shiga damuwa ba kamar k'iriniyarta da tsalle tsallenta, da rigimar ta.
Amman duk yadda yaso ya jawota jikinsa ta k'iya,don da ya tunkarota zata fashe da kuka,dole zai barta don subiyun baya son kukansu.
shahida ce ta sameta b'angaren Annin tace tazo Yah Aree yana kiranta,
Dole tataso suka taho shahidar nayi mata fad'an fushin da take da salma, wadda gata can bata da lafiya saboda taurin kanki Khairat.
Cikin muryar kuka tace,
"da gaske kike Addah."
"gata can ma tak'icin Abinci har yah Aree yayi yayi Amman ta k'icin komi. "
Aguje ta k'arasa cikin gidan falon farko ta same su,
Zube wa tayi gabanta tana kuka tace,
"sweetheart Miye haka, don kawai Ina fushi shine zaki wani sheme kina wani pretending,kinga ki tashi na huce bazan sake fushi da sweetheart d'ina ba,tashi kici kinjiko inhar baki son na cigaba da fushin."
Kamar almarah haka suka ga salma ta Mike tana cin abincin,suna hirar su cike da so da kauna.
Areef wani sanyi yaji don ko kad'an baya son fushin ko wace cikinsu.
Cikin k'an k'anen lokaci komi ya daidai ta, saidai fah Khairat ta canza salo ta daina shigewa Areef, ko assignment ne ta k'asa yah mujahid shine zata je ya koya mata, ta daina rigima da salma akan Areef, ko k'iriniyarta da take masa ta daina Magana ma sai ta Kai makura take masa........gashi lokacin tafiyarsu ya taho don yanzu bai wuce 2 weeks masu zuwa.
Amman gefe guda Khairat kullum cikin lissafin tafiyar take, duk kwanan duniya sai tayi kuka ahankali ta fara ramewa duk ta fice hayyacinta,haka akai jarabawa tashiga js3 aman saboda rashin maida hankali saida aka mata repiting......wannan dalilin ya jawo b'atawar *Khairat da Areef*
Taufah ana wata ga wata.
Mrs bb ce
Mom muhsen [5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: ππππππππ
*_ABIN CIKIN RUHINA_*
Written by [Mrs bb]
Mom muhsen ce
*____________________________________*
*ππ°AINUWA πΌRITER'SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
6.
Nasan da labarin tafiyar su Amman ko Anni ban nuna ma halin da zuciyata take ciki ba, tabbas inajin babu dad'i ba kamar jin danai wai salma zata yi masu rakiya har can, ita da Abbu da Dadyn meenah.
Wanda da sanda ana maganar tafiyar Abbu cewa yai hada ni za,a rakiyarsu shine yanzu don banyi k'ok'ari ba za,atai abarni basu san yanzu duk abunda zai had'ani da Yah Areef ba bana sonsa, ko sunyi mun tayin zuwa zance bana zuwa.
I think kun san yadda feeling d'in missing yake, Wanda da kaji wannan yana yin gara kayata rusa kuka, to haka Khairat takeji,duk yadda taso yin kukan abun yayi mata wuya saidai zafin da takeji cikin ranta, haka tak'i bari Anni ta fahimci komi akan tafiyar tasu,wanda hakan halin Khairat ne inhar bakaso gane abu ba is hardly ka fahimci yana yinta.
tana kwance kan gadon meenah wanda yanzu d'akin ya koma nasu su biyu,karatun English novels nake na soyayya, jin abud'e k'ofa yasa nayi saurin b'oyewa don yah mujahid ya hanani ni kuma sun shiga jikina bazan iya daina waba.
Ganin salma ce yasa nafiddo naci gaba daga Inda na tsaya, suna rage mun k'uncin da nake ciki,zama tayi kusa da ni ban kulata bah ganin kuma ba kulatan zanba yasa tace,
"sweet............"
Katseta nayi da cewa,
"pls idan kinsan takura ce ki barni don Allah."
Shiru salma tayi don iya wuya yau Khairat ta kai salma, wannan halin ko inkulan da take mata ya isa haka, ba ita takar zomon ba rataya aka bata.......cikin k'uluwa tace man.
"enough is enough *Khairat* haba ko ni nayi maki laifin iyakar horan da zakiyi mun kenan, Amman taya zan ringa binki kina mun wulakanci,to nagaji nagaji haka nan idan kin gadama Kizo yah Areef na kira."
Anni ce tashigo taga ficewar salma rai b'ace abunda zaka jima baka gani tare da ita ba, mutunce mai hakuri sosai Idan don ita zata jaka fad'a zaku shekara aru aru bakuyi bah, tabbas tasan Khairat ce ta tun zurota.
Cikin fad'a Anni ke tambayarta abunda ya had'asu, banji komi ba nayi mata bayani fad'a tashiga yimun tana cewa tunda banjin magana tafita harkata, gashinan naja wadda keta son ganin farinciki na tayi fushi dani, kuma intashi maza inje kiran kafin raina ya b'aci, muddin naci gaba da wannan halin zamu b'ata da ita sosai.
Ganin duk yadda ta tada hankali tana fad'a yasa na bata hakuri ashe k'ara kular da ita nayi,moper ta d'auko zata maka mun na tashi na rugo ina dariya, ban tsaya ko Ina ba sai falon su Yah mujahid shida yah Areef.
Kuka na samu salma nayi tana gaya masu,abunda ya faru, sai naji tabani tausayi matuk'a jiki babu kwari na shiga can gefe na zauna na gaida yah mujahid sannan Shima Nace masa,
"yah ina wuni."
Kallona yake bazan iya fassara shiba, kawai dai nasan kallon mai laifi yake mun kafin ya Kauda idonsa yace,
"haka zan tafi kuna fad'a da junan ku ko,na lura kin fara rainani *Khairat* sunan da ya anbata yasa babu shiri na kallesa, akai sa,a idonsa na kaina kallon Cikin ido mukai ma juna, sai naji ko kad'an banji dad'in sunan da yakira ni dashi bah, sadda kaina nayi naji kamar kwallah zata zubo mun,danne wa nayi daker ta tsaya.
Yace,
"kiba ta hakuri abunda kika mata, idan kuma kuka sake naji labarin kun sake b'atawa Allah takakkiya zan maku oya maza Kunshirya ina gani."
"tabarshi kawai Yah bana so."
Cewar salma.
B'ata fuska yayi.
yace,
"bana son taurin kai Kin sani salma ban sanki da haka ba, don haka karki fara kwai kwayon halayen da basuyi maki kyau kinji *my Angel*."
Saida kirjina ya yi Wata irin bugawa na runtse idona kawai jinai ya dakan tsawa.
"zaki bata hakurin kokuwa sai na tattakaki awajen nan."
Yah mujahid yace,
"haba Areef Meyasa Kwanan nan kakoyi yiwa yarinyar nan tsawa ne,ehyi ba halinka bane kadaina."
Bai kula saba jikina yana rawa kaina na k'asa Ina zubar da kwallah ba tare da Sunyi shawara dani bah,bakina yana rawa Amman na kasa furta komi........ Azafafe ya tashi ya d'auko dorinarsa jinai zau zau ga bayana..........k'ara na fasa inafashewa da kuka Yah mujahid ya anshe dorinar yana masa fad'a,kamar zai dakesa Shima Cikin zafin ran da bansan yana da shiba yace.
"wallahi muddin ba ta bata hakuri ba jikinta sai ya gaya mata, raini ya fara shigowa tsakani da ke ko, to mun k'ulla kenan nida ke daga yau wlh, zan saukar maki da wannan girman kan naki."
jikina rawa yake kamar mazari, sosai na tsorata da dukan sa yanzu kam tsoran sa yafara shiga ta tabbas,don babu abunda yake firgita ni kamar duka, ganin zai fizge ya yo kaina yasa na sake rushewa da kuka ina mamuk'e kujera.
Saida Yah mujahid yace,
"oya Khairat ba y'ar uwarki hakuri kinjiko ai ba fad'uwa kikai bah."
Bawai inajin k'yashin bada hakurin bane taurin kai ne irin nawa, Amman ganin zai sake dukana yasa nace ina kuka.
"kiyi hakuri bazan sake bah."
Amman salma tai mun shiru jin haka yasa yace sai nayi ta bata har sai tayi magana.
saida na bata sau uku sannan tace tayi.
Zuwa lokacin fuskata tayi jajawur kamar tumatur, tashi nayi zan tafi ya fizgoni nayi wata irin fad'uwa saida yah mujahid ya tadani........saboda haushin abunda yayi fita yayi yabar falon.
d'akin yayi shiru sai shashshekar kuka nakurum, da karar AC.
Ina jin sanda Ya ke Ajiyar zuciya kamar mai iska naji ya fara magana Cikin taushin murya,abun mamaki yabani yanzu fa yake kamar zai tashi sama saboda zuciya, Amman jibeshi kamar bashi bah.
"zan tafi na barku don haka kusan mekuke ciki, kar na sakejin wai kunyi fad'a,sanan maganar