Showing 33001 words to 36000 words out of 69834 words

Chapter 12 - ABIN CIKIN RUHINA BY MISS BB.txt

Miss Bb   

10 Jul 2024

8269

kin cutar dani da masoyana,plsss na rokeki kifitar mun da wannan masifar,bazan iya cigaba da jurewa ba,inason cigaba da ganin farinciki afusar iyayena............ji sukai kurun na fashe da kuka maitsuma rai,suduka duk jikinsu duk yayi sanyi.......don dajin kukan kasan maiyinsa nacikin kunci da damuwa.


Mrs bb ceπŸ‘ŒπŸ»


Love u All πŸ’‹πŸ’•πŸ˜‰
[6/13, 8:47 PM] Mom Muhseen: πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•
🌹
*ABIN CIKIN RUHINA*


Writing by mrs bb
Mom muhseen.


Wattpad name
Humaira7531.


DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.


Not edited


31&32


Saida nayi iyakar yina sannan nayi shiru,shigewa toilet nayi nashige cikin ruwan sanyi,ko sirkashi banba,shaya ce keta zuba bisa kaina nafi minty goma haka.........injin karar wayana yah meenah na cewa,
"Wannan wankan ya isa haka ga dr nan nata kiranki yanzu haka zowa yayi."
Wani kulutu ne ya tokare man ga makoshi,jinai banson ganinsa bana son jin sunansa..........zafin da zuciyata keman harga jikina don wata irin masassara nakejin tana saukoman.
Dole na jawo towel na daura nafito,kowace ta kama waya sai yitake......tsaki naja nafara shiryawa.
Doguwar rigace nariza nadan shafa lotion,da body spray na zuba abayata har kasa,don inason dogon hijab rayuwata,kocikin lefena da aka kawo akwatinsu daban wajen kala goma shabiyar.......wayar na dauka nafito compound din gidan,motarsa nacan gefe guda kasancewar filin wajen badai girma da fadi ba,mota goma saita shige har asamu sauran waje.


Fitilar ya kunna don nagane shine,tafiya nake kaina kasa inajin babu dadi,bazanso yaga damuwa tare da niba don ban san mezan ce mashi ba,dole na kakaro murmushi nasa ma fuskata........
Budeman gidan gaba yayi yana murmushin sa mai kyau,yasha shadda gizner sai daukar ido take.
Shiga nai ina sallama.


"Wa alaiki salam,gimbiya Amarya da girman kujerarki,Amarya bakya laifi koda kin kashe dan masu gida."


Bansan sadda dariya ta kucce man ba yana tayani,
Nace"irin wannan kirari haka,karkasa kaina ya fashe sir."


B'ata fuska yayi kamar karamin yaro zai kuka,
"Ba nace banson wannan sir dinba,nace maki da munbar school to sir ta kare,saidai my only."
Murmushi nai ina jin nauyin sunan sosai,shiru nai ina wasa da tsuna da suka gaji da kyau,don mai kunshi musanmman yayar Annie tazo mana da ita,ta zane mana kafafu da hannuwa,sai daukar ido suke.
Hannun ya kalla yace"bakiji wani miyau daya wuce man ba,inso samune wannan yan yatsun in tsotsesu."
Bansan sadda nasa abayata na boye fuskata ba.


dariya yake sosai yana sake karkacewa yana kallona yace,
"Aini ban maga kwalliyarba my love,kidan cireman abayar ingani mana,wallahi tunda kikashigo kamshinki yaketa dukan hancina,ni ko wuyanki kibani in shinshina........."


Wayyo kunya kamar zan nitse don kunyar kalamansa,
Shagwabe fuskanai nace"pls si........"


Wallahi dakin ida saina cinye wannan bakin tunda baijin magana.
Shiru nai inajin kunyar fadar sunan da ya keson in fada,jinai yace inajinki.


"Cewa nai pls kabari inkana irin wannan guduwa zanyi Allah ni kunya kake bani."


Juyowa yai gaba daya gabana,ya riko duk hannayen nawa yace"sa idonki cikin nawa,yau kwana nawa rabon dana saki idona,kullum kina man wayau gyaran jiki kike,to tunda angama yau kibarni na mora ganina pls."
Ya karashe maganar yana sunbatar hannayen,har wani lumshe ido yake.
Wani iri naji don dr akwai iya salon kauna.


Jaye hannun nayi inacewa"pls mekakewa sauri gobene fah."
Murmushi yayi yace"shikenan,aidai daga gobe andaina man iyaka da halalina."


Hira mukai tayi dashi duk wata damuwata dana taho da ita ya kawar mun ita,dr mutunne mai sanyin hali,hakurinsa mai girmane tsawon tarayyar mu ba taba ganin bacin rans ba,ko abu nai mashi na bacin rai bazai taba nunaman ba,zaidai ce kibaryin abu kaza babu kyau.
Any time ever moment fuskarsa dauke da murmushi,tabbas nasan na auri dr na gama damuwa,duk irin halin da nake ciki muddin mukai waya or muka hadu ban sanin inda damuwar take rugawa,tabbas maganar Abbu gaskiyace da yace dr shine ya dace dani,nima nayarda na amunce kuma ashirye nake nayi zaman aure dashi mai dadi,nayi damarar faranta mashi har iyakar karshen rayuwarmu.
Zamu yi rayuwa mai kyau da yardar Allah,hakika 100% na yarda dr ya zama mijina uban y'ay'ana.


πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•


*RANA BATA KARYA SAIDAI UWAR DIYA TAJI KUNYA*
*RANAR WANKA BA,A BOYON CIBI,ALKWARIN ALLAH YA TABBAT,UMMULKHAIR FAROUK TA ZAMA MATA GA DR. MUHAMMAD KASEEM,TAREDA MATA GA SHAZALLI YUSUFA DA AMARYARSA UMMUSALMA FAROUK.*


dubunan mutane da bazan iya kwatan ta maku iyakar adadinsu ba suka shaida wannan Auren,Amare sunyi kyau har sungaji.
domin khairat musanman ummi tayo hayar maiyin kwalliya daga dubai,khairat tahadu iyaar haduwa,saidai muce Allah ya tabbatar da Alkairinsa........tunda labarin daurin auren yazo ga kunnena nake kuka,badan komi ba sai don kawai cewar yanzu fa nazama matar Aure,wacce zata tashi daga gidansu zuwa wani gidan,zan fara sabuwar rayuwa da sabbin mutane,shin wace irin rayuwa zamuyi.
Shikenan babuni babu zama gidanmu kenan saidai nazo yawo,lallai Aure abune maigirman gaske,kaduba abunda zai raba uwa da yarta yaraba uba da yarsa,wane abune wanan inbada mutuwa da Aure.
Ina falon Abbu ankirani na gaisa da bakinsa,nasamu kyaututtuka har basan iyakaba,vanyi zaton friend dina zasuzo ba saigashi harda mazan department dinmu sunzo man daurin aure.


Durkushe nake nasha wani dankareren less,sky blue da pink color,nasha takalma na da jikkata duk farare sai mayafina babba da aka rufaman bisa kaina har fuskata.......majina kurun nake gogewa don kukan tunyaa zuwa da sauti har ya barfita da sautin,falon yarage mutane Abbune da daddy,sai maah Annie da ummi,sai yah jahid da yah shahid..............wanine daga can bakin kofar shigowa,takalmansa sawu ciki kurin nake gani farare tasss,tabbas shine yanayin da zuciyatabtake bugawa ya tabbatar mun shine......hakanan banji dadin zuwansa ba hakika rashin zuwansa sai yafimun kwanciyar hankali,domin samun natsuwar zuciyata.
Alamu dai ya nuna fada za,aimun salma akejira tun dazun.
Abbune yake waya da driver da ya aika gidan inna dauko salam,
"Kashiga kace nina turo azo adaukota za,ai masu fada ita da khairat,..........muryar innar mukaji tafito sosai ciki wayar.


"Faruku kafita idona,dolene fad'a tace mun tsoron zuwa take kana iya dukanta,to nima na hana anan za,a dauketa akaota gidan mijinta,ruwanka ne kasamata albarka ruwankane ka tsine mata,inace saudah ce mai yinfadan itada yar uwarya,to itama ga nata dangin uwar nan suna mata,bazata zoba."


Baice komiba ya sauke wayar,ummi ranta yabaci don daman ummi badai fada ba,inhar akatabota.
Yo ba,a tabota din bama wace allah ciki balle antabo........cikin banbami tace,
"Wace irin yarinyace wannan kahaifa farouk,ace yau aurenki zakitai dakin miji bazakizo kiyi sallamar mutunci da iyayenkiba,idan ita wannan ta nuna maah,sannan tacigaba idan ita bata haifetaba kai aikaine ubanta,tazo kasamata albarka.
Kumaninda kara da mutunci saudah ba itace tashayar da itaba tsawon shekara biyu,tatarbiyantar da ita,amman dayake nonon datasha fitsarar dashi tayi ta nuna maku cewar itafa diyar lantana ce Allah yajikanta,ai saudah uawartace idan tasan kanta tasan mutunci,kuma inna saita biyeta inbacin kurun dama jiranmu take......"
Maah ce tai saurin katseta dacewar,
"Don Allah yaya kiyi shiru hakanan,kowa yaza ma nagari don kanshi,ni wallahi taje nayafe mata duk abinda tayi man,Allah yasa Albarka cikin auren."


Magana zata sakeyi ummin dady yace"pls hafsat abar maganar kaima kuma kayi hkr duk yadda ranka yakai gabaci dole zakayi hakuri kabisu da Allah yabada zaman lafiya shi ake fata,shine kawai."


Nanfa suka rufu kaina kowa da abunda yake fada,kukana kurun nake don jinake baza iya barin maah da abbuna ba.


Cikin yayyaena akace idan damai magana yayi mani ga mototci can zuna jiranmu.
Yah jahid yayi man nasiha sosai akan hakuri,yac"nasanki indai akan nan wajenne to kikara domin zamane baa yauba bana gibe ba,Allah yayiwa rayuwarku Albarka yakuma kareki daga makiya."
Kowa yace ameen,yah shahid ma yayi man Anty shidah kiwa kwallah take tayi tama kasa cewa komi,duk ta kwakwumeni,itada yah meenah.


Har yanzu yananan inda naganshi,bai motsaba bai kuma tashiba kuma baice komiba,
Ummi ce tafita don wasu baki da sukazo mata biki,tare da maah suka fita tana cewa yah imran yaje yacewa masu daukar amaryar sukara hakuri gatanan za,afiddota.
Wannan kalamin yasake tunzura kukana har muryata bata fita,sumabyah meenah kukan suke,don Anty shidah yah jahid yajata sunfita.
Abbu da Dady daman suma bakin garesu dayawa zasu sallamesu,don yama tayi wajen biyar harda rabine.


Husna ce taje tasake tattaro man kayana danayi using dasu,babu kowa dakin dani sai yah meenah saishi dake can zaune har lokacin.


Munanan zaune tsawon lokaci banda shashshekar kuka bana yin komi wata irin kewar yan gianuce akejin tana kamani,sonake yayiman magana yakiya,yaki motsawa yaki kallona,yaki zuwa inda nake kowa yana furta albarkacin bakinsa akan aurena,Amman shi ko tanke baice komiba,hankalina bai sake tashiba saida naga ana jana za a fitar daga cikin gidan.......kua nake ina rike Maah da Annie amman babu mai saurarena,Abbu dakanshi ya kamani yasa motar,sanan yashiga gaba dady shike tukamu,sauran motocin suka rufa mana baya.......inaji ina gani nabar gidanmu zanfada wata duniyar daban,bansan kuma wace rayuwar zanyiba........lallashina kirun Abbu keyi har muka isa,baibari nasaka kafata ba saida nayi addua sosai,har yana aranto man ina ansawa sannan adagaafatta dama asakatare *BISMILLAH.*


Mrs bb ceπŸ‘ŒπŸ»πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜ina Alfahari daku
[6/16, 11:11 AM] Mom Muhseen: πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•
🌹
*ABIN CIKIN RUHINA*


Writing by mrs bb
Mom muhseen.


Wattpad name
Humaira7531.


DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.


*I need ur prayers Am not feeling fine.*


Not edited.


33.


Iyayena maza sune suka kawoni har cikin gidan mijina,nayi kuka kuka mai sunan kuka har jinake kaina zai rabe gida biyu,dandanan zazzabi ya rufeni ruf rawar sanyi kurun nake su yah meenah da suka shigo motocin Abokan ango duk sun rude da halin dana ke ciki,don jikina har wani siraci yake fitarwa.......hakika ban taba dauka haka ake jin dacin rabuwa da iyaye ba in aure ya tashi,lallai ajinjina ma Aure.


Anty shidah bata kwana ba yah jahid ne yazo ya dauke ta,Husna dai nan zamu kwana da ita da yah meenah.........sauran kawayen mu duk sun tafi gida suna cewa sai sun dawo gobe walima.


Ganin jikin nawa yayi tsanani yasa suka kira dr suka sanar dashi,aikuwa sai gashi kamar daga sama duk yarude.......waya ya ciro ya shiga kiran dr su ganin dr baima ganin su yah meenah rungumeni yayi abunsa babu abunda ya damai,dole suka bar dakin suka koma daya daga cikin bedroom dina,don babu karya iyayena sunyi matukar komari,Abbu gado biyu duk yayi mana da set din kujeru biyu,amman ni maah da annie da ummi suka hadu suka kara man kala guda,duk da halin da nake ciki hakan bai hana ni ganin kyan bedroom din da nake ciki ba.
Komi maroom dakin sai walwalin fitilu yake,gadon kanshi cycle ne kuma juya wa yake,kana iya tsayar dashi kana iya barinsa.
Abun gwanin burgewa da ban sha,awa.


Ina jikinsa nayi lamo sai ajiyar xuciya nake,kaina kurin yake shafawa yana jeraman sannu,tuni dama ya rabani da gyalena.......saida likita zai shigo ya rufa man shi.


Dubani yayi sosai yace"damuwa ce da kukan da tasha suka sakar mata wannan zazzabin,da tasha pen relief zai sauka kuma tayi kokarin cire damuwa insha Komi zaizama successful."


Godiya yayi mashi ya tafi kwance nake na kudun dune wuri guda,na lumshe idona ina jin kamshinsa kusa dani.


Waya yake idonsa akaina don inajin su suna sakani takurewa.


"Ummi jalila ta hado abinci maidan saukin ci sai taci kafin a kawo na sauran,eh ummi to insha Allah, jikin ai da sauki gata nan oky to."


Ajiye wayar ya yayi yana tab'a goshina........ajiyar zuciya nai yace,
"Sorry my dear tashi ga abinci nan sai kici kisha magani,bazan so wannan ciwonba muna tsaka da farinciki,kokin manta yau wace rana ce bari na tuna maki,yau ranace ta farin ciki agaremu da duk masoyan mu baki daya,burin mu ne ya cika na mallakar juna Allah ne ya nuna mana don haka plss my love,ki tashi mu fuskanci sabuwar rayuwa."


Sake lafewa nai cikin gadon mai dauke da wata irin katifa mai laushin tsiya.
Kofar aka bude aka shigo tare da sallama,


"Wayyo Antinmu kina nufin wannan dinner ba za,ayitaba gaskiya kitashi ki wartsake gidan masoyinki fa aka kawoki..........muryarsa cike da annashuwa yace"Jalila kin raina niko."
Tashi nai ina gyara kallabina dana rufa ma kaina shi,kokarin sakin fuskata nai nace mata.


"Inayini."
Dariya tayi tace"lafiya Anti tunda kinbarmun girman."
Harararta yayi yaceman
"Karki sake gaidata inba haka ba rainaki zatai,kanwarki ce itace zata ringa gaidaki."


Murmushi nake bance komi ba,
Tace"ga Abinci nan Anty amarya aci awartsake mutai party."


"Jalila babu wani party da za,ai matata bata lafiya kibari inkingama ruwan idon zaben saurayi inbikinku yazo saikuyi koma miye ko love dina."


Wayyo kunya kamar tasan yadda zatai dani,
Sunkuyar da kai nai ina wasa da gefen kallabina.
Dariya tayi tace"ashe kuwa zaki sha kunya don bakiga komiba wajen Dr sai ya rungumeki gaban ummi."
Zaro ido nai ina kallonta mezasuyi ba dariya ba har suka bani dariyar nima.
Mikewa tayi tace"nayi nan amarya Allah yabada lafiya,ummi na miki sannu."


Muryata tayi wani irin sanyi sosai nace,
"Nagode kice mata ina ansawa sosai."


Kallona kurun yake duk naji na takure shagwabe fuska nai nace"plss d........jin lips dinsa kurun nai kan bakina........daskare wa nai kamar nayi kankara saida ya tsotsa iyakar yinsa sannan ya dago yana kallona,
Murmushi yayi yace"Aina gaya maki duk randa kika sake ceman wani dr ko sir saina cinye baki,to yanzu ma arzikinki daya baki daafiya da kinsha mamakina tunda bakijin magana."


Juya mashi baya nai kamar zan kuka saboda wallahi rashin kunyar dr tayi yawa,
"Nidai kadaina bana so."


"OK naji wannan juyo maza nabaki inada baki nabarosu ban sallamesuba.,"


Yada yayi alamun babu wasa dole yasa na juyo yana bani yana man hira,yana gaya man irin mutanen da suka halarci bikinmu.........ashe daman yunwar nakeji sosai don kwana biyu bana cin komi sai dan abu me ruwa,saida yaga ina shirin sheka mashi amai yasa ya kyaleni.........ya sunbaci goshina yace,
"Sai da safe ko in dawo mukwanta tare."


Jifarsa nai da filo ya cab'e yana dariya yace"ohodai duk wayon amarya sai ansha manta,kishirya gobe anagama walima zanfara kora don nan gidan zanyi magrib."


Dalalo ido nai baki bude dariya ya kwashe da ita yafice bayan ya jehoman filon.


Komawa nai jagwaf kan gadon,ina ajiyar zuciya tunda nake ba,a tab'aman kiss ba sai yau har yanzu jinake kamar bakin nasa yana kan nawa,numfashi na sauke ina jinjina soyayyar dr,ya iya tafiyar da ita yadda ya kamata.........tashi nai na gama kalle bedroom din sannan nafito na shiga wanda su husna suke ciki ita da yah meenah.


Hira suke konace kowace hira take awaya da masoyinta,don yah meenah tuni tayi nisa wajen kaunar yah imran,love kurun suke bugawa mimi ce keta chat tana ganina tarungumeni.


"Allah sarki Amaryarmu sannu kinjiko yajikin,yayi sauki."
Murmushi nayi nace"nasha magani na samu sauki,kunci abinci kuwa."


Tace"yanzu muka dawo daga cikin gidan,munci mun koshi wallahi khairat kinyi dacen dangin miji kowa maganarki yake,yana yabon halinki ki zauna dasu lafiya kinga wai yadda sukaita hidima damu,abincin nan nama yafishi yawa ferfesun naman kai,gasassun kaji,yan ciki soyayyen naman rago sai wanda mutun yaga damar ci.......mahaifiyarshi tana ta tambayar jikin naki."


Wata natsuwa ke shigata "tabbas ina fatan hakan ya dore,Allah ya kawar da shedan tsakanin mu nidasu."


Tace "ameen muje na rakaki kiga gidanki khairat,wallahi su Abbu sunyi kokari sai fatan Allahb yabiya su."
Tare muka fita dayan bedroom din dake tsakiya muka shiga,Italian bed ne golding color komi golding har fentin kanshi,sai daukar ido yake don yama fi wanda aka saukeni ciki,wanda su Husna keciki kuma komi purple ne da dark pink.........palona biyune babba da karami babban set biyu na royel chairs aka saman,karamin kuma wasu kujerune yan gaske har wani malatsi garesu inzaka zauna zaka danna,wanda zai bakujerar wani irin sanyi ni,ima har haske suke fiddawa da daddare.......saboda farinciki har kuka nai ina gode wa iyayena.
wani abun mamakin shine wadannan kujerun wai yah Areef ya siya man su cewar mimi.


"Bawan Allah gaskiya Khairat yah yayi jarumta yayi karfin hali sosai,kinsan tunda yabaro nigeria yazo nan gida wlh baida lfy in takai ce maki yah baya cin abinci tsawon sati baici komiba,amai dai kurun karshe saida ya kwan ta asibiti,da fadan ummi da hargaginta ya daure ya karfafa zuciyarsa,amman har gobe ke har abadan yah bazai taba son wata mace kwatankwacin wanda yake makiba,ina rokonki kiringa mashi Addua Allah ya sassauta mashi yana cikin yanayi,don baiso zuwa bikin nan ba ummi ce kamar zata cinyeshi danye yasa dole yazo,to gashinan zuwan ya tado aiki don yanzu haka yana asibiti,gobe zasu koma don yaga likitanshi dake dubashi."


Silalewa nai na zauna kan kushin din dake tsakiyar babban falona,hawaye masu zafi suka shiga zubarmun inajin wani ciwo cikin zuciyata.


Zamatai kusa dani ta dafa kafadata tace"kiyi hkr ban gaya maki bane don kiyi kuka ba ko kishiga damuwa ba,nagaya makine don kisashi addua Allah yaba shi lafiya ke yanzu kinriga kin zama ta wani tunanin wani ma inkikai haramunne,ki fawwalama Allah komi shikadai yasan me hakan yake nufi,Amman wallahi nidai idan nice koza,a mutu sai an aura man wanda nakeso,ni banson irin wannan rayuwar taya Allah bai haramta abuba amman mutane su maidashi haramci wannan badaidai bane,ana shiga hakkin mutane wallahi."


Ina share hawayena nace mata"mimi wannan abun babu wanda keda laifi cikinsa saishi,saboda gaban kowa Abbu yake sanar dashi halin da nake ciki akansa,Amman ya sha mur yace wai shi bama ni yake so ba,shibazai iya aurena ba wannan dalilin shine duk ya jawo komi,har mai aukuwa ta auku,wallahi bazan tab'a yarda da cewar ba laifinsa bane mimi,don haka ni kibar ma yiman maganarsa,don nariga na shafe babinsa zanyi sabuwar rayuwa da maisona."


Murmushi tayi tace"kiyi hkr Amman wallahi duk duniya inbanda iyayenmu bakida mai kaunarki sama da yahna,ki dauka haka kaddararku take wani baya auren matar wani."
Mikewa nai nace "nayi nan inje nai sallah na kwanta goma saura,"
Biyoni tai tana cewa"karki tsani yaya ba laifinsa bane."
Afusace na juyo kanta nace"nawaye inba shiba nace laifin waye,inda yana sona da gaske mai yahana shi furtawa tun kafin atsayar mun da mijin aure,plsss mimi karkija najuye maki haushin da bana kiba,kibarni haka kibarni na jida kuncin da nake ciki ehy."
Bata wani ji haushiba don ko itace wanda ma yafi haka zatai,don bata yarda da auren da babu soyayya ba imfact inta sai wanda ma take masifar so yake masifar sonta zata aure.......tace"Allah ya huci zuciyarki nabari,ammafa duk sanda mukai wya dake ko bayan mun tafi zan ringa baki news din halin da yake ciki."


Banza nai mata nashige dakin na banko kofa.


Mrs bb ceπŸ‘ŒπŸ»πŸ’‹πŸ’•πŸ˜˜πŸ˜˜
[6/19, 12:43 PM] Mom Muhseen: πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•
🌹
*ABIN CIKIN RUHINA*


Writing by mrs bb
Mom muhseen.


Wattpad name
Humaira7531.


DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.


*Nga sakonnin gaisiwarku gareni Allah yasaka maku da Alkairinsa*


Not edited.


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login