Showing 60001 words to 63000 words out of 69834 words

Chapter 21 - ABIN CIKIN RUHINA BY MISS BB.txt

Miss Bb   

10 Jul 2024

8255

harshena.........kafin ya janye bakinsa muryarsa ta dishe sosai yace"kisani duk randa namutu cikin wannan halin kece da kaso sittin da alhakin hakan,zan kyaleki bazan sake maki wanan maganar,tunda har bazaki tayani yak'in da nakeyi ba,sannan har kice kina sona kindamu da halin da muke ciki,haba baby kinmun adalci kenan shikenan muje gida"
Abunda yace kenan ya tada motar,zan iya cewa har muka iso gida nidashi babu wanda yasake cewa komi,jikina yayi masifar sanyi da kalaman sa,bakin get yayi parking ya bude zai fita nai saurin rik'o hannu sa kwallah share share cikin idona.


"Don Allah karkaga laifina,wlh yah maah zata dauki mummunan mataki kaina muddin na kware mata baya,ka fahimceni,wlh na damu nadamu sosai akan wannan halin,karka yiman bahaguwar fahimata,wlh inasonka banda burin daya wuce kasancewa dakai tsawon rayuwata karka ce zaka hukuntani ahaka zuciyata bazata iya daukaba,wlh inajin ka tamkar fitar numfashina karkayi man haka don Allah..........na fashe da kuka ina shashsheka......zare hannunsa yayi yace "idan da kinsan kalamin dani ummi ta yiman akan gujewa wannan auren ke bazakice haka ba,amma kasancewar ina ganin idan na biyeta abanza zan illata rayuwata,dole tasa nadage wajen ganin nasamo kanki,amman shine zakice ke bazaki iya ja da umurin maah ba,yes hakan na da kyau bance kija da umurnin taba,amman ai saikisan hanyar da kika bi don ganin ta gane cewar kinson kasancewa dani,inba dai kema kin gwammace mutuwar tawa da rayuwata ba."


Sake rik'e hannunsa nai ina kuka sosai "yah karka gujeni wlh ina sonka zuciyata takai limit d'in da bazata cigaba da daukaba amman kasani daraja da kima sun wuce komi,gara ka rasa komi daka rasa su.........cikin wani irin yanayi ya juyo afusace wanda ya tsoratani,,,,,,,har jijiyar kansa ta fito sosai.......idonsa yayi jaa sosai kwallah sun kwanta ciki muryarsa ta dishe sosai yace jinjina"is ok hakan ma ya isan."
Ya fizge hanunsa ya shige cikin gida yabani zaune ina kuka mai tsananin tafasa zuciya,daker na tada motar bayan nadawo inda yake na shiga cikin harabar gidan.
Parking nayi lokacin sha biyu na dare,ta baya na shige cikin gidan dakin yah meena nayi masauki........bacci suke don dagani sun gaji don duk dakin na same su salma ma k'asa tayi shimfid'a ta kwanta...........silalewa nai kasa bakin kofa naita rusa kuka na,yazanyi da maah ne wai meyake son nace mata,wai ko yamance irin zafin zuciyarta idan ranta yab'i da abu,ba ayenta bane tayi man mugun duka wlh,wata shawara tazo man nai saurin amuncewa da ita don idan ba haka ba banda wani hanya,kewaye na shiga nayi wanka nazo nai sallar isha,i na kwanta duk da ba baccin nakeji ba duniyar tunani natafi wai yau yah Areef ne yafurya man kalaman da nashekara aru aru ina tsumayinsu daga gareshi.yau iyae man kuka da idon sa akan yana sona,wannan kadai ya isan farinciki haka na lalalce ina tunaninsa bansan sadda bacci yayi awon gaba dani bah.


**********


Washe gari daurin aure ant hidima nikuwa bacci kurun nake har wajen sha d'aya saboda ban samu nayishi da wuri ba jiya,kukan Airah ya tadani.
afigice natashi ganinta nai ita kad'ai tashi nai naisaurin daukota ina dariya.
"Oh my sweetie,I miss u so much muuaahhh naringa kissing dinta babu k'ak'k'autawa itama ganin sai dariya nake ina kiss dinta,itama saita bangala dariya tana mamuk'eni mukaita dariyar naji anturo k'ofar Anty shida ce tasha gayu na fitar shari,a tayi masifar kyau saidai kuma fuskarta hawaye nagani,dariyar tau tab'ace tashi nai na dauki zanen goyon Airah na goyeta nace"anty lafiya kuka kike fah don Allah kibari yaufa ranar farin cikin kuce."
Rungumeni tayi tana shashshekar kuka tace"kinanan anacen ana tashin hankali cikin gida,wai maah da ummi suke fad'a cikin taron mutame khairat,kawai saboda keda Areef,gashican dangin zulfa,a sun maido lefe suna wulakanci da cin fuska,wai ummi ce ta roki alfarmar hadin auren saboda anata alkawarin kujerar minister of communication,yanzu wannan dacewa ne har k'asa yah Areef yake rokonta ta barshi ya aureki amman tasa k'afa ta halbeshi,gashi can anfita dashi asbiti.......mafarin kenan maah takai karshe wajen zuciya take aya ma ummi magana cewa,ta saida mutuncinta da darajarta wajen mutanen da basu da mutunci da kirki,gashinan sun watsa mata kasa ga ido ranar auren sun maido komi sunce basuyi........ta gwammace d'anta ya mutu bacin tanada halin taimakonsa......shinefa taji haushin maganganun ta mari maah,itama maah ta rama wlh khairat abun babu kyan gani dole akakira su Abbu awaje,yanzu haka ummi ta yi oarking kayanta wai barin gidan zatai.........ga mutane kahirat cikin taro wace irin masifa ce wannan wlh duk naji natsani ma auren....."
Kina kasa zuwarmun yayi saboda wani irin abu daya kulleman ga zuciyata,wani yanayine nakejina da ban tab'ajin zuciyata ciki ba,saidai gani na tayi na zube kan gadon ga Airah ga bayana......wata k'ara ta fasa wadda ta janyo utanen dake falon Annie,kuka take sosai ta sauke Airah dake kukan itama,umminu dr ce ta ansheta Annie ta shiga shafa mata ruwa amman ina ko sake motsawa batai ba,aguje aka kira Dadyn su yah meenah shima ya rud'e daukar ta yayi annie biye dashi yasata mota,
Daman maah da su mimi duk sunacan wajen areef da Abbu,
Dadyn su mimi yaga sadda aka dauko khairat lokacin ya na tama ummj balbalin masifa,ya ce "wlh wani au yasamu yaran nan saint kinyi danasani wlh."
Mota shima yashiga yabi bayan dadyn su yah meenah........inda aka kai yah can aka kaini cikin k'an kanen lokaci aka ansheta,........likitan ta nana lokacin wanda ke dubata lokaci lokaci,dashi aka shiga don ceto ranta......kuka maah keyi kamar ranta zaifita,Annie keta bata hkr itama Annie kukan take abbu ko ya dafe kai da duk hannayensa.
Dadyn su mimi ya iso yana tambayarko ansau ka d'aya daga cikinsu,girgiza kai kurin Abbu yayi.
Dadynsu yah meenah yace"inaga dole ai sanarwa andakatar da daurin auren sai zuwa sadda hankali yakwanta ko inaga hakan zaifi don dukan mu bamada kwanciyar hankali."


Abbune ya d'ago idonsa yad'an canza yajasu gefe yace"aa jafar(dadynsu yah meenah kenan)baza,ai haka ba amuje ad'aura aure tunda akwai sauran lokaci nanda karfe biyune bazamu iya dakatar da mutanen dasuka taso daga wata uwa duniya ba don halartar daurin auren ba,sai sunzo kuma ace anfasa hakan baidace ba.abunda za,ai kawai kai kamal(dadyn su mimi kenan)ka zauna anan u zamuje muji da mutane kahid da ya iso da imran sai shahid dadyn su mimi yace "Aa muje duka wani cikinsu sai ya tsaya."
Likitan da ke kula da yah Areef ya karaso yace"ku kwantar da hankalinku munankan kokarin cetoshi,insha Alkah cikin kankanen lokaci zai tashi,kuje ga hidimarku harkun gama kudawo insha Allah zasu sama very save."
Jinjina kai sukai sannan suka bar angwayen sukatai,lallashin su maah sukaitayi yayinda sukansu suna cikin damuwa,kamar daga sama suka ga ummi taniso wajen tana kuka,babu wanda ya kulata cikin su maah harda su Shahid.
Sai jahid ne yaketa bata baki rungumeshi tayi tana kuka tace"nayi dana sani mujahid nayi nadama,wlh son zuciya da kwadayi suka kaini ga haka amman duk duniya banda kamar ku yarannan,wlh bank'i Areef da khairat don inso ba,shedanne yyi nasara cikin xuciyata.........kaje kace wa iyayenku don Allah suyi hkr su daura masu aure yau hakan shine zai dawo dasu sucikin hayyacinsu."
Agigice maah tatashi daga duken dabtake tana kuka,share kwallar ta tayi tace cikin tsananin fushi da bacin rai.
"Hafsa!"
Zaro ido tayi ummi tana kallon maah da mamaki bama ummin kadai ba har su dake wajen abun ya basu mamaki,don basu tab'ajin ta kirata haka ba saidai yaya koda yaushe.
"Ehy hafsa,koba sunanki bane to idanma mafarki kike kifarka hakan bazai tab'a yuwuwa ba,khairat bazata auri d'ankiba kije kibashi duk wacce kike ganin itace ta cancanta,."
Ummi kuka take tace"haba saudah,Areef fa nakine kece uwarsa...............ada ba ada nasan nice uwarsa amman ayanzu nabar maki kayanki saboda kin nuna man ikonki akashi,kibashi budurwa sabuwa dal aleda,ba dai jawara ba wacce ta haihu."
Annie tai saurin rufewa maah baki tana cewa"haba saudah! yazaki koma kamar yarinya,duk wannan bai dace ba kufa y'an uwane ciki daya kuka fito yazaku bari aganku arana,kidufa yadda mutane suka gaye mu,acan gida kunyi yanzu ma nan bazaku hkr ba."
Maah kuka ta fashe dashi ta rungume Annie tace"wlh gara munke saudbu miliyan akan hafsa,ta nuna man ni bakowanta bace ta tozartani cikin tarona ta wulakanta yarana danice na tarbiyantar dasu ta anshi d'anta da itace taban da hannunta,duk saboda abun duniya sabida mulki shege abun banza da wofi da zai kaika jahannama..........ta jefa rayuwar yara cikin garari gasunan kwance cikin halin mutuwa da rayuwa.mezanyi danita wlh tfita raina tafita daga cikin raina narantse da wandake busa man numfshi babuni babu.................aguje ummi ta rugo ta rufe bakin maah tana kuka sosai,duk tafice hayya cinta har numfashinta yi yake kamar zaifita,........"karkice haka narokeki karkice haka ni takice ke tawa ce saudah bazan iya rabuwa dakeba,kekadai garan sai jabir taya kikeson nayi rsyuwa babu ke..........Annie ta janye daga maah umi ta samu damar rungume maah kamar zata maidata ciki......kuka suke suduka idan kagansu saikayi masu kwallah........duk wanda ke wajen kukanyake masu shahid da imran barin asibitin sukai mujahid ne kurin ya tsaya shima kukan yake,daker yake basu hkr durkushewa kasa sukai rungume da juna kowace tana jin son yar uwarta ya ratsata........ba wacce ta sake cewa komi sai kuka da ajiyar zuciya.






Mrs bb ce
Mom muhseen.πŸ˜˜πŸ˜‚[7/10, 3:04 PM] Mom Muhseen: πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•
🌹
*ABIN CIKIN RUHINA*


Writing by mrs bb
Mom muhseen.


Wattpad name
Humaira7531.


DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.


51.


Suna nan durk'ushe suna kukan likitan Areef ya iso wajen,saurin sakin juna sukai suka mik'e jahid ne ya taresa yana tambayar ko yafarka.
"Cikin ikon Allah mun samu mun daidaita matsalar,amman gaskiya kozai farka sai nan da gobe ko cikin dare,don muna son zuciyarsa ta huce daga zafin data d'auka,don waje guda yafara kunbura."
Zaro ido duk sukai cikin kuka ummi tace"don Allah likita katai makemu ka ceto mana shi,karya mutu donAllah karka bari yamutu."
Annie ce tarik'ota tana cewa"haba yaya,raida mutuwa suna hannun Allah shi zamu roka ya bashi lfy,kibar cewa haka."
Jahid yace"yanzu zamu iya ganinsa don Allah kodan musamu natsuwar zuciya."
Jinjina kai yayi yace b komi kushiga ku ganshi amma don Allah karkuyi Abunda zai tasheshi,idan kunsan kuka zakuyi plsss karkuje."
Ummi tai saurin share hawayenta,tace"mun daina bazauyi ba insha Allah."
Hanyar d'akin suka nufa kowa yana saurin shiga don ganinsa........kwance yake kan gadon,cikin awannin da basukai biyar ba ya yi wata irin rama kamar wanda ya kwana goma yana gudawa.
Ganin ummi zata fashe da kuka yasa jahid fiddata........suma bajima suka fito maah hankalinta duk yana kan khairat,zaman zuru suka cigaba dayi har zuwa sadda su dady suka dawo daga wajen d'aurin aure.
Masha Allah an daura aure saidai muce Allah yaba ma,auratan zaman lfy cewar Abbu dake sanar dasu maah.
Likitan khairat ne yafito yace insha Allah anjima kadan zata tashi,tashiga shock ne amman dasauki jikin.
Jin haka yasa Abbu yace duk su wuce gida,abar annie wajensu kawai itada salma..ke mimi kije ki kula da Airah tunda tafi sakewa dake........badan sun so ba duk suka juya zuwa gidan,yadda nazaci bikin zai watse sai ba haka ba gidan acike suka samai da bak'i.
Dole maah da ummi suka saka fara,ar dole kan fuskokinsu aka shiga hidima ba kama hannun yaro.


Amman duk hankulansu suna tare da yaran nasu,bayan sallar la,asar aka kawo Husna wajen ummi aka sauketa,don daman duk gidaje guda zasu zauna.
Abbu ya fidda manya kudi masu kauri ya narka masu gini na gani nafad'a,Areef ya saka yazana masu gidan kasancewar yasan hardashi yasa yafidda k'yuya yazana tsantsarere,tunda akagama gidan Kowa yaje saiyayi masifar burgeshi,an narkar da kudi don ma Areef ya kama ma Abbun aka idasashi,50/50 sukai shima daker Abbun ya amunce.
Kowace amarya cikinsu anmata jere na gani na fad'a kowace set din gado da kujeru uku uku,komidai anyishi cikin wadata iyakar karfinsu sunyiwa yaransu hidima sosai.
Wajen karfe shida na yama nafarka daga dogo baccin dana tafi,dakin nake kallo cikin dimuwa don na mance mema ya kawoni nan.......runtse idona nai ina son tunowa.........jinai kaina ya sara dandanan naji wasu kalamai suna amsa kuwaa cikin kunnena.


_har k'asa yah Areef ya duka yana rokonta tabarshi ya aureki amman tasa kafa ta halbeshi,gashi can anfita dashi rai hannun Allah_


Cikin tsananin kara na kwala kiran yah Areef,kuka nake ina fizge drip d'in da aka saman,dirowa nai daga kan gadon daidai fitowar salma daga kewaye.........da sauri ta rikoni,tana cewa"khairat ina zaki bakida lfiya fa don allah kidawo jiba fa hannunki jini yake,kincire drip d'in,nashiga uku na don allah kidawo."
Fizgewa nai ina kuka "kibarni ki kyaleni wajen yah zanje wajensa zani zoki rakani,wlh bazan dawo ba saikin kaini wajen yah karya mutu ban ganshiba haka ma dr ya mutu bamu wani gana ba kibarni nace kibarni."
Ita kanta salmar kuka take ganin irin wannan kauna maizafi,akullum tana mai danasanin shiga tsakaninsu da yanzu sun mance da sunyi aure,tunda itace musabbabin duk wad'annan matsalolin.likiane yashigo jin ihu sa kururuwar marar lafiar.......salma tana sha re hawaye tace"Doctor yawa gata nan wai saitaje wajen yayanmu d'ayan marar lfiyar,gashi nan har tafizge drip din hannun yana ta jini."
"Saketa."
Saki na tayi na ruga zan fice yyi saurin tareni yace"kinsan inda yake ne zomuje in kaiki amman ki natsu inba haka ba bazan kaiki ba."
Share hawayena nai ina sauke numfashi yajani har d'akin dake gaba danau......baka k'ofar nai har lokacin bai farkaba Annie ce ta gama sallar mangaruba ta ganni..........ban tsaya ko inaba sai bakin gadonsa kuka ya sake kubceman,ganin yadda duk yasake lalacewa na tuna hirar mu dashi jiya.


_plss babyna karki bari arabamu,zanje in samu maah in bata hkr tabarmu da juna nasan Abbu bazai zama matsala ba kamar ita,na rokeki karki gujeni inada heart attack kuskure kadan zai iya jefa rayuwata cikin hadari,kece kadai zaki iya cetona plss babyna_
Wani kuka na rushe dashi ina faduwa jikin annie,
"Annie kice yatashi wlh bazan iya rabuwa dashiba,kice mai yafarka nidashi mutu karaba wlh yah inasonka bazan bari arabamu ba kaine farincikina..........."banda lallashi babu abunda annie keyi.......tashinai daga jikinta na isa wajensa na rik'e hannunsa ina hawaye,duk jini ya wanke jikina wanda kefita daga hannuna.likitan yazo ya cire nashi wanda aka sama yah Areef din yamaida shi jikina..........yace"nan kikeso ko."
Daga kai nai ina kuka yace"to sha zamanki gaki ga shi babu mai rabaku sai allah."
Yacewa Annie akyaleni har sadda zai tashi hakan zai taimaka wajen samun saukar jinina,don yace jinina yahau gaskiya.
Jinginanai da bangon d'akin bacci yasace ni.
Ajiyar zuciya annie tayi itada salma,
Annie tace"wannan masifa Allah yaka wo mana karshenta,yara saikace kansu farau soyayya,kijifa yadda tabi ta haukace Allah naga Abunda ya isan,wlh gara azo ayi auren nan kowa yahuta haba wannan masifa dame tai kama."
Salma ta share hawaye tace"wlh Annie tausayi suke ban,har gobe ban daina ganin laifina inajin zafin kaina sosai akan hakan,nayi nadamar duk abunda yafaru wlh,daba danni ba duk daba haka ba dayanzu anwuce wajen."
Jawota tayi jikinta tana lallashi tace"koda badan keba salma dama haka kaddararsu take,dole sai rabon Airah ya shiga tsakaninta da Dr muhd,gashi ko shakara basuyi ba Allah ya anshe dr don hakan ne kurin zaisaka Areef yasameta.saboda rabonsa ce,shiyasa ba,ason kayi shishshigi cikin lamarin aure,don sai Allah ya kasheka kuma ayi abun,Alkah dai yasa abun yazo karshe don fitinar ta isa haka."


Karfe goma daidai Areef ya bude idonsa,jin wani kusa dashi yasashi idasa bude idon,khairat ya gani tana ta bacci jingine da bango........duk da rashin karfin jiki da yake ciki haka ya tashi zaune ita ya kwantar da ita........kallon fuskarta kurun yake ko keftawa baiyi,yana runanin meya sameta ita kuma,don yini guda itama duk ta fita hayyacinta.
Jin motsin kofa baisa yadaina kallonta ba,Abbune da dadynshi Annie na biye dasu sai salma.
Ko kadan baiwaiga yaga ko waye ba,idonsa ker akanta jiyake kamar daya kauda ido zaiga gizo take mar ba ita bace........saida yaji Abbu yace "Areef kafarka yajikin naka."
Hannu ya d'aga mai yace"Abbu kayi shiru karta gudu,kallonta nake idan na kauda ido zanga ba ita bace."
Kadan yahana basu kece da dariya ba.sai dai murmushi dasukai,yace"babu inda zata ka juyo ka hutar da kanka da waige."
Juyowar yayi yana sauke ajiyar zuciya,kallonsu yayi yace"Abbu meya samu khairat kagani harda drip akasa mata."
Dady yace"abunda kayi itama shine yasameta duk kunbi kun tada hankalin mutane don ubanku."
Salma dariya take ita da Annie shima murmushi yayi yana kallon khairat d'in yace"Abbu a sallamemu haka mun warke."
Wannan karon saida Abbu yayi dariya yace"inkai ka warke ita tawarke ne."
Annie tace ga alama kagani Alhaji,tunda har tabaro dakinta kamar mahaukaciya tataho nan,bacinma dr ya kamota ai kila bakin titi zata yi."
Duk dariyar suke sai lokacin Areef yaji duk kunyar duniya ta kamashi,sai soke kai yake k'asa.
Dady yace"ai anwuce wajen kuma."
Bari akira dr ya baku sallama kun idasa warkewar can gida.
Idona nake budewa daker don hayaniyar ce tatasheni.............ganinsu nai tsaye cirko cirko sai raba ido nake,kallon inda nake nai na zaro ido nashiga uku badai nan suka tadda niba.
Ashe afili nai maganar ida naji salma tace ga zhiri ma kingani.ba arziki na diro ina boyewa bayan Annie duk suka saka man dariya,likitan yashigo ana hira dashi yace ai wadannan Kawai alhaji ku aura masu juna,inba haka ba wataran guduwa xasuyi suje suyi aure baku saniba,dariya aketayi nidai tuna na boye bayan Annie ban sak fitowaba.......ruguda mukai sai gida,salma sai tsokanata take ina hawaye,don wlh sai yanzu duk nakejin kunyar abunda nai,don bihakki banson nayi ba,nidai kawai zuciyata nagaya man ai yah ya mutu mafarin nai wannan rikicewar.
Saida salma ta kamani muka karasa cikin gidan don jikina babu karfi sosai.
Aigabaki dayansu suka rungumeni.abunda ma yafi ban mamaki harda ummi,don hawaye take sadda ta rungumeni........ban fita wani na shiga wani mamakin naji tace "kiyafe man diyata kiyafeman,naso kaina najefa ku cikin halin k'ak'ani kaye..........rufe mata baki nai kawai na janye na isa ga mahaifiyata.
Kuka nasa mata inajin kaunar ta duk wanda yarasa uwa yayi kuka wlh,itama hawayen take ina share mata.


*wlh ngaji pls kuyi hkr mu hdu gobe idan allah yasa munkai,inkunga typing error sorry wlh ina sauri ne*


Mrs bb ce
Mom muhseen😘😘
[7/12, 2:38 PM] Mom Muhseen: πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•
🌹
*ABIN CIKIN RUHINA*


Writing by mrs bb
Mom muhseen.


Wattpad name
Humaira7531.


DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.


52.


Abbune yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login