Showing 42001 words to 45000 words out of 69834 words

Chapter 15 - ABIN CIKIN RUHINA BY MISS BB.txt

Miss Bb   

10 Jul 2024

8275

zabo mansu da mukaje saudiyya red ce sai kwalliyar golding tun daga sama har k'asa,ta fitar da shaf dina ga dan cikina yafito d'an wata biyar,zari ido nai ganin yadda rigar tayi masifar daukata,ta fiddoni sosai,don yanzu nayi wani irin haske ga hutu ga ciki,har wani daukar ido nake,daman bana saka komi ga fuskar sai farar power da liptis saboda bushewar baki,amman duk dahak nai kyau sai murmushi nake,sanan Dr idan yaganni kilan gaban ummin zai daukeni ya rungume.,don shi kunya ba isar sa tayi ba bana saka turare tunda na samu cikin nan saidai yar sure danake goga ma anfit dina da matse matsina saboda smeling.


Fitowa nai da sauri don dauko wayata dake falo naji kamar sadam yana kwalan kira anan kirana,
Sauri sauri haka nakeyi inje ga wayar nason Dr ne yaketa kira kilan ya iso aje adauko shi,,,,,jinai kaina da kirjina sunbugi abuu bansan nace washhh Allah na tsaki naja nawuce do k'amshinsa kadai ya isa yaga yan waye yashigo.


Mikoman wayar yayi yana cewa "Number Dr ne sai kira ake."
Ansa nai ina wucewa karamin falo don induba abunda nasaka ko yayi sanyi yadda nakeso,ina tafiya ina duba wayar kiransa nakeson inyi still yanzu ma karon mukai sosai,har wayar ta silale kasa ta fad'i...........wani kululu yazo ya tokare man wuya duk yadda na tsani kwayar idona ta kallai doke tasaka na zuba mai idanuna dasuka fito waje dukansu,,,,har wata ruwan kwallah naji suntaru acikin su bakina naji yana fada cikin jin haushi.


"Wai meye hakane ehy d'azu kabanke ni na kyale nai hkr yanzu ma kuma haka gashi kafasan waya mijina sai kirana yake yaz..........."shut up stupid girl"


Sake dalalo idona nai ina kallonsa tuni kwallah sun cika idon tab,nace"ni ......nice stupid.....ni...cikin tsawa yace "eh kedin! ba stupid din bace,kina tafiya kamar makauniya bakya kallon gabanki,,,comon ban waje nawuce nonsence....."
WanI malolon kunci da bak'in ciki suka cika man zuciya.....kafin nayi magana ya janyeni gefe ya wurgar,bacin bango danai saurin dafewa da sai dai kan cikina zan fad'a.........durkushewa nai ina kuka bak'in ciki rabona da kuka bazan iya tuna waba.....mimi ta karaso cikin sauri.
"Subhanallahi khairat lafiya,meyafaru mekikamai."
"Mefa me zan mashi kawai zalincine da kuma daman jirana yake....banka ta fa yayi har saubiyu danme zanyi magana kina gani nan kadan ya hana bai turani k'asa ba da kan cikina zan fad'a......hakri taban taa tattara man wayata da ta tashi aiki,sim dina nacire na saka cikin wayar mimi nashiga kiran dr amman ban samu ba,kuka na kubce dashi yanzu haka akwai abunda zai ce man gashi nan yayi man sanadin rashin samunsa........koda ummi ta dawo banji ko dar ba na gaya mata ai kuwa ta hau balbalin bala,i kamar zata ari baki.....sadda ya dawo daddare har lokacin wayar Dr bansamu ba,,,duk nashiga halin damuwa ko yana ina ya iso bai iso ba ina ya taya oho.....ina kwance kan cinyarta idona saboda kuka har yayi fushi....koda ya shigo shida imran suna hirar kwallon k'afa ummi tabishi da harara baisan ma tanayi ba,
Imran ya wuce dakinsu shikuma ya wuce karamin falo.....inanan kwance kamar ance dago ki kalli can dagowar dazanyi na hangoshi ya dauko wannan sweet cake d'in ya yanko kusan rabinshi kan plet,ga spoon dinsa yana yankowa yana saka wa baki.....kamar anzungura man Allura na tashi afirgice na nufi wajen da yake......
Tun kan na isa inda yake yasha mur kamar bai tab'a dariya ba,yace"ke..... kee.......karki sake ki iso maninan,wai bakida hankaline "ina zuwa na kab'ar da plet din ina hawaye nace"Wallahi da kacishi gara ya b'are ai bakai akaima wahalar ba,na rantse kuwa kozai tsutsa da hunhuna inhar wanda naimawa mijina baici ba kaima kuwa bazaka tab'acin sa ba......."keee............ni ....nikike gaya ma magana,don kinga ina ragar maki,zan daukeki da mari awajennan........"ummi tace da kuwa baka kara marin wata mace ba aduniya Ashe baka da hankali Areef,yarinyar da ciki kakeson kassarawa,oh abunda kayi mata d'azun bai ishekaba yanzu ma gabana kake kirarin zaka kwad'amata mari,to kafara dani kafin ka yi mata nata."
Juyawa yai yashege b'angarensu cike da b'acin rai......lallashina taitayi tana ban baki,har nahkr daker nasha maltina da cake din na wuce daki nai sallar mangaruba na kwanta,wayar nake kallo inajin kirjina yana dukan tara tara hankalina ya gaza kwanciya ......me yafaru da Dr na hawaye suka silalo man,,,jinai kawai zuciyata tana karkarwa dandanan jikina yafar daukar wani fitinannan zafi.....mimice tashigo "Khairat ga wayar kisake jaraba kiransa ko za,adace saurin tashi nai don inaji ajikina zan sameshi insha Allah.....hannuna har wata karkarwa yake ina danna kiran,jinginanai inajin yadda zuciyata take duka jinai kurun kiran yashiga.........kafin bakina yaimagana naji wata murya bansanta ba tana cewa *MAI WAYAR GASHINAN ASIBITI SUNYI HAD'ARI KUYI SAURI KUZO YANA GAF DA RASUWA.*


wata k'ara na fasa wadda tasani rugawa ni ma don kunnena fashewa zaiyyi.........


Mrs Bb Ce
Mom muhseen.
09034722970
[6/27, 9:41 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕
🌹
*ABIN CIKIN RUHINA*


Writing by mrs bb
Mom muhseen.


Wattpad name
Humaira7531.


DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.


*_ABDOUL-NASSER (ALFAH) COMING SOON INSHA ALLAH,NASAN ZAKU NISHAD'ANTU DASHI KUCIGABA DA TSUMAYINSA SOON INSHA ALLAH.*


KUYI HKR KWANA BIYU KUNJINI SHIRU WLH JIKINE BANJIN DADINSA FATAN ZAKUYI MAN UZIRI,ALLAH YAYI MAKU ALBARKA YA KUMA BIYA MAKI BUKATUNKU NA ALKAIRI AMEEN INA SONKU IRIN BABU IYAKAR NAN.😘😘😘💕💕💕💕🌹🌹🌹




Not edited


40.
Wannan karar dana fasa yasaka gaba d'ayan su kuka runtumo aguje gareni,shashsheka nake ina dafe da cikina da ya wani irin juyawa............nishi kurun nake hawaye jage jage suna bin fuskata.......mimi ce a rikece ta d'agoni "kharat lfy maya faru ina Dr bai zo bane ina yasauka me yace maki."
Cikin tashin hankali na dago nakaleta n kalli ummi nace"ummi........numfashina yayi sama kamar zai dauke daker nace......"yana asibiti hatsari sukai sunce muje da sauri yana gaf da rasuw.............ban k'arasa maganar ba numfashina ya fizga suduka duk sun gigice afirgice imran yashigo yana tambayar lafiya,,,,,,,"imran maza maza fiddo mota Dr yayi hatsari wane asibiti yace ankaishi khairat ki natsu mimi dauko mata ruwa tasha."


Koda na sha ruwan daker ya wuce kuka kurun nake ina shashsheka........"ummi ban sani ba baigaya man ba,ummi kutai maka man kukaini inson ganinsa ummi banson rashi idan dr ya mutu yabarni nima mutuwar........"karki sake fad'an haka insha Allah zaitashi bani wayar maza maza imran sake kira kaji wane asibitine."


Ansa yayi ya shiga kiran number ba jima wa aka dauka,
"Don Allah wane asibitin aka kawo mai wannan wayar."


Mutumen yace"kuyi kokari kuzo yana nan FMB HOSPITAL sai neman makusantanshi yake don aiki za,a shiga dashi ba lallai ai nasara ba,matarsa yaketa faman kira ita yake son gani kuyi kokari kuzo kafinan da minty talatin.......wyar ta yanke......tashin hankalin da na shiga bazan iya kwatan tashiba wani irin rawa jikina yake bansan ma me bakina yake furtawa ba,ga cikina da yadunkule waje guda ban iya mik'ewa tsaye aduke na isa motar......ummi ke rik'e dani muka shiga motar dagani sai ita da imran,
Lallashina take sosai har muka isa,,,,,tunda muka doshi emergencybanda karkarwa babu abunda jikina yake.....yah imran ne yasake kiran wannan mutumen yagaya mashi inda zamu samai..........ba,a barin kowa shiga d'akin babu inda baya rwa jikina hawayen ma sun k'afe kaf.
Mutumen yayi man iso cikin d'akin.........Idan kaga dr bazaka tab'a iya gane shiba......fuskarsa tayi kaca kaca babu inda babu rauni,jikinsa gab'a daya nannad'e yake da bandage...........idanunsa baka ganin komi cikinsu banda jini dake kwance......kuka ya kubceman "innalillahi wa inna ilaihir raju,un hazbunallahu wani imal wakil,,,,,,,nashiga ukuna wayyo Allahna dr na kaine haka dr na Allah yasa mafarki nake,Allah ka farka dani daga wannan mummunan mafarkin,,,,jinai yarik'o hannuna......muryara kanta ta canza ba kajinta yadda ya kama ta,saida na kanga kunnna saitin bakinsa wanda ansaka mashi oxygen........magana yake son yayi mni,shiyasa na cire mashi shi.......bakin kanshi babu kyan gani,,,,,


"My love.......ki kula man da yarana,Allah baiyi zamu cigaba da rayuwa tare ba,naso in kasance dake iyakar rayuwarmu.....amman da alaman burina bazai cimmaba.......kikulaman da abunda ke cikinki banson hukuncin Allah ba da ya jarabemu da wannan kaddarar,Amman inaji ajikina zakoyi rayuwa mai kyau.......zaki samu mijin dazai kuka da ke fiye da yadda nakeyi maki,ina kuma kyautata zaton yadda zaisoki haka zaiso yarana,idan Allah yasaukeki my love in twins din danake fata kika samu,,,,ina rokon Alfarmar ckinsu kibarwa ummina guda,idan kuma dayane nabar wasoyyar arubuce nabarmakishi har abadan domin kisamu abun kallo kina tunawa dani,,,,,kiyi hkr kidaina kuka zakiyi farinciki nan gaba........tari yake kasa kasa kirjinsa yana d'agawa yacigaba"inarokon ki alfarmar da kidunga man Addua aduk sanda kika kai goshinki k'asa,my love zan tafi da tsananin kaunarki,zanso ko lahira kizama matata kiyi alkawarin bazakiyi man kukaba,,,,domin kinsan illar da yakewa mamaci karkiyi man alkawarin haka........kuka nake ina shashsheka bakina karkarwa yake "Aa Aa Dr na kabar fd'ar haka na rokeka kadaina cewa zaka mutu,bazaka mutu kabarni ba inhar katafi nima binka zanyi,yazanyi da kewarka ina zan saka kaunar ka,kataimaka katashi mutai gida kaganifa yaranka najinka tab'akajisu takai hannunsa saman cikinta.......idanunsa ke kakkafewa yayinda wani uban tari ya tirnik'eshi babu kakkautawa.....dandanan jini yaringa anbaliya ta hanci tabaki.....afirgice nake kallonsa yafice daga hayyacinsa likitocin dake kulawa dashi suka iso cikin gaggawa,fita dani suke ina rizgar kuka,,,,ni subarni naga mijina subarni muyi hirar bankwana......su ummi suka mik'amani kuka kurun nake ina kiran dr......suna can aka shiga dashi operation don tunda dama aka kawo masu accident din shine wanda yarayu zuwa yanzu sauran duk babu wanda yarayu.
Don kafarsa guda jijiya kurun ke rik'e da ita dole suka cire ta don bazata tab'a gyaruwaba,,,,,,akwai wani karfe daya soki hunhunsa sunyi nasarar ciresa tun sadda aka kawoshi, yanzu aikin cikin zasuyi mashi,aikin yana da had'ari sosai don sai maitsawancin kwana da rabo yake rayuwa,amman dayawan mutane sun rasa ransu wajen irin wannan aikin.


Nayi kuka har muryata bata fita,su kansu su ummi kukan suke suna share hawaye,,,,,, tun yamma har dare suna nan suna jiran tsammani har baccin wahala ya daukeni.........su ummi ne sukajira anfito aikin susan wace akeciki.......tsoranta daya kar dr ya mutu in yamutu ba karamin tashin hankali khairat zata shigaba,ga cikinta zai iya samun matsala.........likito cin basu fito ba said wajen karfe d'aya........sunce sukara hkr zuwa safe aga yadda jikin zaiyyi,sun kwantar masu da hankali sosai sukace suje gida da safe su dawo lokacin ya farka.


Haka mima koma gida har lokacin bacci naked,van farka ba saida mukaje gida.......anan dadynsu yake tambayar me yafaru nan take sanar dashi halin da ake ciki...........ban iyayin bacci ba wannan dare tun bayan wanda nafara asibitin,yanzu kuwa ko alamarsa banji saboda tashin dake kaina......waya mukai da umminsu tace sunana isowa da safe yanzu jirgin zatashi zuwa shidda na suba sun so.......lallashina take sosai tana kwantarmun da hankali wanda nima nasan itama tana cikin wanda yafi nawa,saboda ita d'anta ne bata iya sake haihuwar kamarsa,nikuwa zan iya sake wani mijin.........kuka shine yatayani hira kafin gari yawaye.....saboda kerma har raui aji aman ba dauba daker nayi sallar asuba na k'agu muje ko naganshi insamu natsuwa.......zuciyata karkarwa take sadda nafito zamutai jikina kamar ansakani cikin frig k'arara.......bayadda ummi batai dani ba akan inci wani abu amman nace bazan iya cin komi ba dole ta rabu dani hada dady muka tai wannan karon a harda Areef.
Wanda nakejin wata iri tsanar sa saboda duk shine yayi silar faruwar komi,,,,,,alokacin dabai bankeniba nasan zan samu dr ya gaya man inda yake aje adaukosa......amman dayake mugune shi azzalumi gashinan tasilarsa Dr na yasamu mummunan illar dako yarayu balallai ya zama yadda yake daba........muna isowa kofar asibitin naji wani mummunan fad'uwar gaba ta riskeni......cikna yawani motsa har saida na dafe marar.
Kamoni ummi tayi na rungumeta inajin jiina amar ansakaman electric.........banda rawa babu abunda yakeyi.....idona kuwa banda hawaye babu abunda yake fitarwa......ina hango umminsu da su jalila harda Abbansu durkushewa nai kusadasu ina rizgar kuka........mai tsuma zuciya d'agoni tayi ta rungume duk da cikina daya turo sosai.......itama hawaue take gogewa su jalila kam kuka suke sosai itada fati.........adaddafe dai aka gaisa kafin likitan yazo yace "mutun uku kurun zasu shiga don baison hayaniya..........nida umminsu da Abbansu muka shiga kafafuna kerma suke hangoshi danai, kuka kurun nake inajin zuciyata tana kakkaryewa........idonsa kurun yake waje yanzun ma Izzy ne hancinsa da bakinsa........hannu ya mik'oma mu duk muka karasa gareshi....umminsa kuka tafashe dashi tana cewa,
"Muhd,kaine haka muhd garin yaya innalillahi ya Allah katashi kafad'ar wannan bawan naka wayyo Allahana idan narasa ka muhd yazamuyi ina zamu saka ran mu muji dadi.......kuka taitayi Shikanshi Abban kasa magana yayi saidai hawaye dayake sharara daga idonsa.......hannunsa yasaka daker ya cire oxygen din......muryarsa adishe ta shak'e yace"kudaina kuka ummi,,,,,,,don Allah ko na mutu karkuyi man kuka hakan zai cutar dani.........ummi koda na mutu nabar wasiyya arubuce tana dakina cikin drowar na komi na rubuta don Allah ayiman......sannan ina rokon ku dakuyita yiman Addua,,,,,,,,,kallona yayi yasakarmu wani murmushi zan iya cewa tunda nake dashi ban tab'a ganin yayi manshi ba,yace"inasonki matata,inasonki zanbarki badan raina yaso ba,ummi Abba kuyi hkr inata fadan maganganu gabanku,ban da yadda ina iyane idan ban fad'a yanzu ba banda sauran lokaci dazan sake ganawa da ita........rike hannunshi nai gagam ina rusa kukana muna cikin haka yafara wata irin shak'uwa.........dandanan na rikice ina rik'e da hannunsa har lokacin.......aguje likitocin suka shigo,suka roki su Abba dasu fita amman nace babu inda zanje,,,,,sai dai su dubashi gabana daker da sidin goshi akajani waje kuka nake kamar raina zaifice.........kowa hankalin sa yayi kololuwar tashi ganin andauki awa guda babu alamar zasu fito......ina jikin ummina likitan yafito sai uban gumi yake......Abbansu dr ya fara nufa yajashi gefe amma bama jin mesuke fad'a......Abban mukaga ya silale kasa yadafe kai nana take naji wani irin duka ga zuciyata.......kaf kaf kaf kawai jikina yake dadunsu yah imran ne naji yana cewa ma su umminsu dr.


*"sai hkr Allah yayi masa rasuwa......*


Saidai sukajini nazube kasa timmm..........




Mrs bb
Mom muhseen.
Love u my All fans 😘😘😘🌹🌹🌹💕💕💕
[6/28, 2:12 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕
🌹
*ABIN CIKIN RUHINA*


Writing by mrs bb
Mom muhseen.


Wattpad name
Humaira7531.


DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.


Not edited.


41


Gaba d'aya hankalinsu yayo kaina sadda zasu dagata jinine male male yakebin kafafunta...........hankulansu suka kara tashi ko kagani wajen kuka yake share share da hawaye,har su dady hawayen suke........dandanan aka anshita akai emergency da ita........dady da Abba suka fita don zuwa fara hidimar shirya dr akaishi gidansa na gaskiya............Areef ke lallashin ummi yana bata baki don shikanshi lokaci lokaci yana share hawayensa,shikenan Abokinsa ya tafi bai tab'ajin mutuwar data ratsashi irin wannan ba,tausayin khairat ya lullub'eshi yarinya karama ta zama zajawara,,,ga karamin ciki wane irin ciwo takeji cikin ranta,ai komi tayi bai wadatar da kuncin da rad'ad'in da zuciyarta kemata,dole zata yake jiki tafad'i............likitoci uku ne kanta kowa yana aikinsa,domin samun ceto abunda ke cikinta don jinin dake fita idan yacigaba da fita ba tantama za,a rasa cikin.iyakar kokarinsu suke har Allah ya tai makesu cikin yadaidaita.....sannan suka shiga nemo numfashinta Amman abun yaci tura,abu guda zai nuna masu cewar ta da rai shine bugun zuciyarta,inbashi ba babu wata kafa ta jikinta dake nuna tana da rai.........sunyi mata iyakar abunda zasuyi mata suka kyaleta zuwa wani lokacin.
Koda suka fito daya daga cikinsu yake ma ummi bayani cewar,ansamu nasarar daidaitar cikin saidai har yanzu numfashinta bai dawo ba,munyi mata allurai insha Allah zuwa gobe ko anjima da dare numfashin zai iya daidaita,karku damu zata samu lfy shikuma Allah yajikansa."
Areef kurun ya iya ansawa saboda daga unmin dr har ummin yahAreed kuka suke sosai.........tsawon lokaci sunanan zaune kowa da abunda yake sakawa,,,,,,sun hkr sunbar kukan saboda yadda yarok'esu kar suyi mashi kuka.........su dady sunzo sun dauki gawar antai anyi mashi suturra ankaishi gidanshi na gaskiya,sunkira gida sun sanar da rasuwar zuwa safe zasu juya zuwa nigeria..........jin haka yasa suma su ummi sua koma gida don shirya kayan su,Areef da imran sun tafi ummin dr da dadynsu sun wuce masauki,ummina ce kurun akabari tabada sakon asanar da mimi manyan akwatunan su zata shirya masu kayansu,don ita tana saka ran bama zata dawoba daman don Abbansu yana aiki nan ne shiyasa,to yaringa zuwacan karshen wata.....kasuwamcinta kuma zata san yadda tai tamayar dashi Abujar....tafison zamakusada yar uwarta da kuma khairat.


Can cikin dare na farka gaba d'aya nayi losing abunda ya faru,kallon dakin nake ina son tunawa amman nakasa,idona ya sauka kan ummi dake ta bacci ban tasheta ba na koma na kwanta,nasan dai na fad'i amman miye dalilin faduwar tawa shine nakasa tunawa........abunda yasa kuwa shine likitan sukai shawara da Areef kan cewar idan sunyarda zasuyi mata allurar mantuwa na wucin gadi,yadda za,asamu daidaituwar abundanke cikinta,don muddin ta tatashi mutuwar zata sake dawo mata sabuwa,kuma cikin yana bukatar hutu da natsuwarta,kuma hakan zaiyyi wuya karshe arasa cikin,amman idan akai allurar zata manta har zuwa kwana biyu sannan cikin ya samu sauki don yanzu baida isassar lfy idan tayi abu mai karfi zai iya fita.........hakan yaa Areef yace suyi mata kawai,yaje yayiwa ummin bayni itama tace ayi hakan shine samun natsuwarsu,don sun tabbatar tashin hankalin da zata shiga shine nasu tashin hankalin........kai jama,a mutuwa babban tashin hankalice ubangiji ya kyautata makwancinmu Amee.


Washe gari ummi ce ta tai maka man nayi sallar asubah,sai dai ta fakaici idona ta share hawayenta,bayan nayi break da youghout shikadai nasha sannan nayi wanka,riga kawai na zira kwanta don jikina kwata kwata babu karfi,hakanan nakejin zuciya ta tana kareyewa,,,hawaye suka ziraromun ina kan cinyar ummin kuka nake can k'asa k'asa.... Batace mun komi ba don bazasu iya hanani kuka ba. tabbas sadda na farka adaren nan banzan iya tuna komi ba,aman gari na wayewa komi ydwo ma sabo,jin abunda ummi ke sanar wa da maaah da suke waya tana gaya mata allurar da akaiman,shiyasa nai iyakar kokarina wajen ganin ban tadawa kowa hankaliba,kuma ahalin yanzu babu abunda nakejin ina mutuwar so sama da abuna ke cikina,inajinsa tamkar fitar nufashina shiadaine abunda zan gani inaji sanyi cikin raina,domin kuwa dr mutunne harda rabi,yayi soni ya nuna man kauna da gata tsawon watannin da mukai dashi.
Yanzu babu shi doran k'asa saidai yaransa idan Allah yasaukeni lfy,zanyi fatan nima na haifi twins din domin inbawa ummi itama ta ringa ganin photocopy din d'anta.........gobarar dake ci cikin zuciyata kad'ai ta isan,basaina na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login