Showing 30001 words to 33000 words out of 130351 words

Chapter 11 - MAHABEER Complete Document by Xayyneb.txt

Xayyneb   

29 Jan 2025

9971

da tayi itama dan yanda fuskarta ta nuna hakan itama a lokacin kamar ta shi dady mua'zzam d'in,nan suka gama shirya in zasu wuce zasuje can gunsu baffa d'in...
ana tsaka da haka Saiga doctor lurwan ya shigo ya qara duba jikin momy umaima yaga komi lpia nan yayi musu bayanin abubuwan daya kamata ta dinga amfani dasu ta fannin ci da sha kuma zuwa gobe da safe za'a basu sallama,,,
yana shirin fitane amman ya dan tsaya tareda yiwa dady mua'zzam d'in bayanin cewa an samu gidajen amman sabuwar anguwa ce guda gidajen suke jere da juna,,
daddy mua'zzam yace"to shiknn babu komi zuwa dare zan ganka doctor "
d'an rusunawa doctor lurwan yayi yace
"shiknn alhaji,,,"
sai alokacin ma ne shi ya lura da ummu hani dake gefe gefen momy ni'ima a zaune knta a duqe,,,
yayi mamakin ganinta tareda wadan nan mutanen amman saiya share kawai yasa kai ya fice,, ummu tana shirin miqewa taga mahabeer ya dawo dakin,, dan haka sai ta koma ta zauna a dabarance da nufin inya ida shigowa d'akin ita kuma sai ta wucewarta,,
dan bata son kusanci dashi ita tunda ta gane shi d'an saurin hawa ne a lokaci qanqani na saninsa datai,,ga kuma taqama irin tasa da nuna isa da fad'in rai dud shi daya tayi mgnr a zuciyarta tana mai yatsina 'yan siraran pink lips dinta,
a bayansa kuma wata mace ce wacce kallo daya zakai mata kasan cewa kiristan ce,, sabida iriyar shigar dake jikinta wani irin mini sikert ne iya cinya sai body hug a jikinta ta dora wani tulin gashin doki bisa kanta sai wani baqin gyale iya kafada data yafa la66an nan nata manya masu tudu dasu sun sha wani pink na janbaki sai shining sukeyi tana faman taunar cwingum q'as q'as wanda Kaida ganinta kasan lallai idanunta suke bude tarr fiyauu dasu da sanin maza iri iri fuskarta har wani yellow yellow takeyi na tsabar mai dataci,,
gaishe dasu dady mua'zzam tayi sannan ta matsa gaban gadom da momy umaima take tadan dafa qarfen gadon ta dan rusuna tace "hyyy momy ya jiki,, tin kan momy umaima ta amsa d'in tayi miqewar ta tsaye tana cigaba da taunar ta,,,
"lpia pha,,,"
Abinda momy umaimah tace mata knn momy ni'ima da annah kuwa mamakin ganin ta kawai suke,,, a zuciyar momy ni'ima kuwa fad'i takeyi miye ya had'a mahabeer da ita wannan kuma datake ta rawar jiki haka,,??
wasu ledoji na oesis ta ajiye gefen qafar annah tace "grandma gashi abawa momy ba yawa,,,
momy umaima tace"angode da hidima"
ummu hani ganin yanda wannan budurwa ke rawar jiki tana shisshige masa shi kuma bai ma san tana yiba dan Yana can wajen su dady mua'zzam shi,,, amman jefi jefi taga yana dan maido hankalin sa wajen fisha sannan kuma ya dauke yana wani ta6e lips.
yatsina masa fuskar ta tayi lokacin da idanunsu suka qara karo da juna harara ta sakar masa a kaikaice sannan ta dauke fuskar ta tareda miqewa tsaye tacewa su momy "zan koma can daki mah kada su baffa suga shiru ban koma ba,,, tana maganar ne cikin nutsuwa,,momy da momy ni'ima sukai mata godia har annah na cewa zata zo itama anjima ganin maman nata da jiki,,,
tazo dai dai wajen su dady suma tai musu sai anjima anan dady mua'zzam d'in yace saimuje tare ko haj Muhammad wajen baban nata muji daga bakinsa shima,,"to shiknn tashi sukayi suka wuce ta gefen mahabeer suka nufi qofan fita dayake ta fad'a musu room d'in 'yan hatsari suke gado na biyu,
"amakson" abinda ta furta masa knn lokacin data zo giftawa ta kusa dashi tai wucewarta tabar dakin ya bita da kallon wato ta sake maimaita mun kalmar nan knn ko??
dafe kansa yayi miyasa yarinyar dabai sani bs har take neman sakasa cikin damuwa da al'amurran tane wai???
mitake nufi da kalmar nan da take yawan jefanshi da ita wai???
runtse idanunsa yayi yasake budesu sannan ya tashi ya koma wajen su annah ya zauna tareda fad'in "annah ki taimakamun ki fad'a myn ma'anar kalmar nan ta *Amakson* da waccen buzuwar yarinyar ke fad'a mun,,, plzzz annah ya qarashe maganar Yana mai had'a hsnnunsa waje daya kamar zaiyi kuka,,, dukkansu wajen da kallo suka bisa harda bleesing data samu zama a dayan kujerar itama ta harde qafafu waje daya tana binsu da idanu,,,,,,
Momy umaima ta dubi annah tace "miya faru tsakanin mahabeer na da ummu annah?
Momy ni'ima tace ''nima dai da tambayar da zanmasa knn kika rigani,,,
Annah tace "ku rabu dashi baida gaskia ne shiyasa take ce masa hakan,,,
nan annah ta fad'a musu abinda ya faru tsakanin nasu da ummu a lokacin,, Momy ni'ima ta dubesa tace
"ayya d'ana,, miyasa haka???
sinne kai yayi qasa sannan yace"ban lura bane momy,,, yo daman taya zaka kula kataho kana sakar wa mutane irin zuciyar ka a hanya ja'irin mutum kawai,,, dariya sukayi shikuwa miqewa yayi ya dubi annah yace "dan Allah fada mun Anna maanar kalmar kinji annah ta???
dayake bleesing ta saba ganin dramar tasu intaje gidan nasu sai abin ya dinga sake bata dariya itama,,,
Annah tace"bafa zan fad'a ba nagaya maka kaje can wajenta ka tambayeta in ka matsu saika jin,,,
Fuuuuu yabar dakin fuskar a tur6une bleesing tabi bayansa bayan tayi musu Allah qara sauqi annah ta bisa da fad'in "haka dai ka saba can kaika jiyo matarka ta banu kam ammn bafa da wannan kiristan nake ba dan babu aure a tsakanin ku nama fad'a ma shashashan yaro kawai wanda bai san inda kan sa ke masa ciwo ba,,,
Momy ni'ima dariya kawai takeyi itada yayinda momy umaima ke fad'in "ni ai nasaba da wannan karon battar tasu indai mahabeer da annah ne,,,,,
dady mua'zzam sun tattauna da baffa kuma shima cikin jin dad'i yanuna amincewar sa,,bugu da qari yace ko goben ma saisu tafi inda likitan yace gobe ne ranar sallamr tasu,,, har a cikin zuciyar baffa kaddo yaji dad'in wannan aikin da ummun tasa tai musu silar samu cikin sauqi da hukun Allah,,basu jims ba suka tafi suma,,, mahabeer kuwa suna barin hospital d'in da blessing school dinsu ya maidata shi kuma daganan ya wuce wajen su bash,,,,
washe gari kamar yanda likita ya fad'a haka ya basu sallama duknsu kuma akayi sa'a dud a lokaci daya ya rubuta musu sallamar dan haka gaba dayansu a dady mua'zzam d'in ya daukesu da kansu a motarsa dayake mahaber ya wuce office shi,,,
driving yake momy umaima na gefensa suna fira cikin farinciki da annushuwa,,jefa jefa kuma takan juyo baya taiwa su ummu hani magana cikin kulawa,, ummu kuwa ita ji takeyi dud sanyin esin motan ma ya takura mata harta fara karkarwa na son yin masassara abinka daba'a saba ba daman,,,
qarfe 2:30 suka dira a harabar gidan mua'zzam saraki,,har wajen annah ta iso tana musu barka da isowa cikin murna dayake ita yau bata jeba asibitin cewar dady mua'zzam d'in ta zauna itama ta huta tunda yaune zasu dawo gida suma,,,
baffa kaddo da bintey kuwa sai bin gidan sukeyi da kallo dan tunanin su babu irin wanan hadadden gida a nan inba qasashen turawa ba,, ita kuwa ummu tana daga gefen mommonta tsaye danji takeyi kanta na sarawa kadan kad'an idanunta sai faman lumshesu takeyi ahaka suka qarasa har falon gidan,,,
sun zauna momy umaima ta cika musu gabansu da kayan lashe lashe daqyar suka samu suka tsakuri kadan dan ba sabawa sukayi da irin abincin ba,, dama ita Ummu yau monday azumi takeyi koda Anna tace ke Ummu baxakici komi bane? kinfa zama 'yar gida kibar d'ari d'ari dan Allah dud daya nefa Allah ma bai banbanta ba dud abin halitta ne daga garesa,,, ,,, qara sunne kai tayi tana qara jawo mayafinta cikin Murmushi tace "si annah azumi nakeyi yau litinin shiyasa,, "annah tace "ohhh Allah sarki yarinya mai ibada,,, nima azumin nan nake yau,, allah shi bamu ladan to,, aminn su baffa da dady mua'zzam suka amsa,,, momy umaima tace "ni wannan lullu6e naki ummu da kikesha narasa gane kansa,, incan asibiti kin boye fuskarki aimu nan sai a saki jiki a bude ko??? tayi maganar da Murmushi a fuskarta,,, baffa yace"Allah sarki hajia ai ita ummu hani haka take ko gida bata cika zama haka ba,,, murmushi kawai momy umaimah tayi ta qudure a ranta lallai zata mayar da yar tata kamar kowa ce cikakkiyar budurwa indai ana kwana ana tashi,,son ummu hani jitakeyi daga cikin jinin tane yake,,"toni zan shiga ciki cewar annah tareda miqewa tana fad'in "bismillahee Allah wahidul qahhar,, bin annah da kallo momy umaima tayi lokacin dataga tashin nata ta koma daki tasan salla zatayi sannan shima dady mu'azzam ya tashi yacewa su baffan su tafo ya kaisu gidan maqocin abokin nasa inda zasuyi aikin,,dukkansu sukaje harda momy umaima d'in sunyi saa alhj Muhammad d'in na nan nan suka tarbesu suma sannan daga bisani suka gwadawa baffa dakinsa na bakin gate wanda zai dinga kwana shida iyalensa, babban daki ne daukeda kujeru guda 5 da carpet inka dauke masaukin baqi dake gefen dakin nasu,, sannan cikin dakin akwai qurya mai daukeda gado sai katifa a qasa harda makewayi keda a cikin dakin da dan qaramin kicin shima,,
anan su dady mua'zzam suka wuce masallaci shima baffa yayi alwala ya shimfida buzunsa nan wajen gate daga gefen benci ya tada kabbara shima ta salla,,,
acan cikin daki momy umaima ta jira saida su bintey da ummu suka yi salla sannan tace"to nima zan tafi da 'yata a namu gidan mamansu,, tayi maganar fuskarta a sake,,, dayake bintey tasan itama ummu hani d'in zata zauna can wajen momy umaima d'in dan tayata wasu ayyukan shiyasa itama cikin faraa tace "to shiknn hjy mungode da kulawar da kukeyi damu Allah saka,,,
amimm cewar Momy umaimah a haka taja hannun ummu hani suka fita daga gidan suka nufi nasu,,,, zuciyar ummu cikeda farin ciki na ganin cewa sun samu mafaka itada iyayenta sai fatan Allah shi ida nufinsu na ganin anwa mamanta aiki ta samu lpia,,,
suna shiga kai tsaye 6angaren ta momy umaima tayi da ummu tace ta zauna nan zata dawo yanzun,,, ruwan wanka ta had'a mata sannan ta dawo ta kamo hannunta takaita har bakin qofar toilet d'in tace tayo wanka,,saida taga shigarta sannan ta dawo falow ta shiga wani daki daban inda kayanta suke na sawa ta fiddo wata farar doguwar riga msi adon duwatsu a gabanta da dan siririn farin mayafinta ta koma wannan gudan dakin data kai ummu tayo wanka ta dora mata su bisa gado sannan ta matso bakin qofar toilet d'in tace "ummu in kin fito ga kaya nan kisanya na ajiye miki su bisa gado,, ina jiranki a falow inkin gama "daga haka ta fita tareda jamata qofar dakin ita kuma ta wuce nata dakin dan gabatar da salla itama,,,,,,




*Xexen Fasaha*✍🏻
[10/11, 2:46 PM] Xainab Documen: 🌊🌊🌊


*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊


Story and writing
by
Xayyneb 💤💤


🌊🌊🌊🌊🌊


Fasaha online writers f. o. w.


🌊🌊🌊🌊🌊
🅿2⃣5⃣.
🌊🌊🌊
A cikin toilet kuwa ummu hani tsananin tsari na cikin toilet d'in ya dauke mata hankali taita bin ko ina da kallo harda ta6awa take ma wani lokacin,,, qarshe dai haqura tayi ta yo wankan ta fito daureda baqin gyalenta babba na kayaynta,,cikin sauri sauri ta dauki rigar datagani wacce tasan itace mah tace ta sanya inta fito ta zura gudun kada wani ya fado cikin dakin yasata ko mai bata tsaya shafawa ba a jikinta,,,
Subhanalla ,,lokacin data zura wannan rigar yanda kasan jikinta aka dinka,,ba qaramin kyau tayi mata ba, ta dan matsa jikin mudubin dake dakin ta kalli fuskarta tayi haske sosai lips d'in nan nata kamar ta shafa musu pink d'in janbaki a hankali tayita bin jikinta da kallo,, ita kanta tasan ta d'an fad'a ta rame sa6anin yanda tazo garin daga garinsu,,
sauke idanunta tayi a q'irjinta da tudunsu yasa har suka dago kwalliyar gaban rigar gaba dayan su yanda kasan tasa foshop amman ba ita bace bra ce normal kawai a jikinta mara soso ma,,, hakama wugunta taga rigar ta fiddo mata shop dinsu gaba daya wanda hakan yabawa shafaffen cikinta fito da nasa kalar shape d'in shima,,,
sauke ajiyar zuciya tayi ta miqe tsaye tareda ware gyalan kayan da nufin ta yafa ta fita can wajen mah d'in dan batasan ko akwai aikin da zai matan ba,, tana gama ware gyalan ta gansa dan firut a hannunta.. Saroro tayi ta na mai bin gyalen da kallo cikin mamaki,,,yanzu ana nufin da wannan dan fingilin gyalen zata fito? "kammmm tabbbb d'i jammm wai,, ,,
abinda ummu tace knn tana mai qara fiddo fararen idanunta waje dan ita kanta tasan wannan gyalen bazai iya saya mata halittar taba da wannan rigar ta fiddo mata su waje,,
daura sa tayi akanta tayi ribom dashi ta hanyar kamo tulin gashin kanta ta qulle dashi da qyar sannan ta tuqe ta saki jelar tana reto a bayanta har wajen bombom nata,, sannan ta dauko mayafinta wanda iskar dakin ta ec tuni ta busar dashi ta yafa abinta bisa kai har ya sauko mata iya tsawon hannayenta sannan taji tayi dai dai,, falon ta nufa lokacin momy umaima harta dawo falon ta zauna tana jiran fitowarta,,dama tayi saurin fitowa ne dan gudun kada ummu d'in ta fito falon ta rasa inda zata ganta dan falon babba ne sosai,,,
da Oyoyo diyata momy umaima ta taro ummu tareda zaunar da ita gefenta ita kuwa ummu hani Murmushi kawai takeyi itama kamar yanda momy umaima take yi itama,,,, gskia kan Allah mai had'a so tsakanin bayinsa ita kanta ummu hani ya zuwa yanxu tana alfahari da mah d'in nata sosai sosai kamar yanda ta dauketa itama,,,
"kinyi kyau diyata sosai,,, cewar momy umaimah tana 'yar dariya, ummu kuwa cikin kunya tace"mah mi zaayi miki ne yanzu na aiki sai nayi miki? "
"aa diyata bari sai kin qara hutawa sosai kinga azumi kukeyi yau amman zo muje kichen na dan fara gwargwada miki yanda zaki yi amfani da electronics na cikinsa,,,,
haka ta kama hannun ummu hani suka shiga kichen d'in wanda yake qaton gaske shima cikeda kayan amfani nan taita gwargwada mata yanda abubuwan suke dayake ummu nada brain na saurin daukan abu koyaya aka koya mata shi shiyasa nan da nan ta fahimci yanda abubuwan suke,, sun jima a kichen d'in sosai dan har har Friedrich momy umaima ta had'a mahabeer d'in nata a gabanta dan tasan Yana kusa da dawowa office mafarin knn ta jefi tsuntsu biyu da dutse daya wato tayi masa girki kuma ummu ta ga yanda ta had'a komin ta,, mafarin knn ta yanke a zuciyar ta kullum zata shiga kichen tofa zasu shiga tare ta rinqa wayar da ita wasu abubuwan da dama danta kula yarinyar nada fahimtar ta,, sai wajen biyar da rabi sannan suka baro kichen tasake jan ummu suka nufi dakin annah wacce ke zaune tana lazumi da carbinta,,
Zama momy umaima tayi itama umnu ta zauna a qasa tasake gaisheda da annah cikin faraa annah ta amsa da fad'in ummu yaya kikaji gidan namu da baqunta ko?
cikin Murmushi ummu tace
"a'a annah"
Murmushi momy umaima tayi tacet"kamar kuwa kin sani annah har yanzu ummu taqi sakin jikinta fa,,, annah cikin sake qaruwar fara'arta tace "zata canza umaima indai tana zaune wajenki,,dariya sukayi tace "hakane annah wlh bnson miyasa ummu tashiga raina haka ba cewar umaima Tana mai kamo hannun ummu d'in,
Annah tace "nima ta burgeni umaima tun sa'ilim da yaron nan yai mata karo Wlh bata nuna bacin ranta ba dudda kayen da tayi qasa sosai,,,
bakomi annan ai haka akeson nutum mai juriya akan kowane abu na rayuwa zakaci riba in kai hakan inji umaima sannan ta qara da cewa"amm annah mi zan girka muku ne na buda baki naga kunada sauran awa d'aya da rabi kan ayi kiran salla,,Anna ta riqe baki sannan tace"a'a umaimtu ya daga dawowar ki daga asibiti jinya zaki koma kichen kuma aiki?
haba haba ki barsa kawai na gode ita ummu dai ta girka nata taci ita,,,
"A'a wlh annah yanzu banjin sauran kowane irin ciwo a jikina yanzun haka ma tun d'azun muna kichen nida ummu ina gwargwada mata wasu abubuwan harma girki nayiwa mahabeer,, "lail'ahaillla ke yarinyar nan da gaske? Yanzu dawowar ki har kika iya shiga madafi kiyiwa wannan tuzurun mijin nawa abinci kina fama?
"Hyyyy my swwet kakus na,,, cewar mahabeer da dawowar sa knn daga office briefcase dinsa ma tana sagale a kafadansa kot dinsa tana riqe da hannunsa sai 'yar farar rigar dake jikinsa da lakatayig din wuyansa ya qaraso wajen ya zauna tareda fad'in "washh ya jinginar da bayansa jikin momy umaima ya saki dan guntun Murmushi sannan yace''huhhhh momy wlh yau tunda naje office ban samu kaina ba sai ynzu,, annah ta dubesa a cogane tace "to wani ne ya hanaka zuwa aikin kwana 2 bare kazo kana cika mana kunnne aiki aiki,,, yamutsa fuskarsa yayi yace "haba annah ta jinya fa na taya momy na asibiti to ina ni ina zuwa wani office dan Allah,, ni kinga bafama dake nake magana ta ba tsohuwar nan kiyi shirunki zaifi,, "naqiyi nayi shirin koko zakasa zare ne da allurai ka dinke mun baki eye??
Wata 'yar siririyar dariya yasaki yana fad'in calm down my kakus maida wuqar irin Dan wasan nan nefa na jika da kaka..... maganars sauranta sai dai yaji ta laqafe masa a tsakan kanin lips dinsa sakamakon arba da yayi da ummu hani zaune daga dayan gefen da momy umaima take tana kallonsa,,,wata iriyar harara watsowa saitin wajen da take baisan sanda ya miqe tsaye ba tareda watsi da kayan hannunsa ya nunata da yatsansa na tsakiya yana magana bakinsa na rawa rawa dan har a cikin ransa yaji ransa ya 6aci na sake gamdakatar da tayi da yarinyar kuma wannan karon har a cikin ma mainhouse dinsu kuma a dakin kakarsa ma abin sonsa kullum farin cikinsa da ahalinsa suyi wasa da dariya abinsu da kakarsa gefe ga momynsa na tare masa shine kuma zasu jajibo musu wanan fitsararriyar yarinyar a gida salon ta qara ganin wallensa tasamu hnyar qara raunsasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login