Showing 69001 words to 72000 words out of 130351 words

Chapter 24 - MAHABEER Complete Document by Xayyneb.txt

Xayyneb   

29 Jan 2025

9966

wacce zata iya yiwa wannan mutanen kirkin ne? Kuma wace alfarma ce wacce zasu roqa a gareta indai tanada halin abun taqi yi musu shi kuma? Cikin rawar murya tace "dady matsayin baffa na nike ganinka dashi dan haka kafadi koma miye insha Allah bazan gaza yimuku shiba indai inadashi.
"masha Allahu to" abunda dady mua'zzam yace knn yana Murmushin jindadi, sannan ya dora da cewa "niko ummu hani inada sha'awar hada ki aure da mahabeer inhar kina ganin babu takura a alamarin, wanda nasan hakan shine zai dad'a qara qulla qullin zumunci a tsakaninmu,wannan itace alfarma danike nema ummu daga gareki naroqeki ummu hani kada kice aa d'iyata,,
Kamar am watsa mata ruwan zafi ga jikinta haka taji kalaman dady mua'zzam sun dabaibayeta.
a mugun firgice kuwa ta d'ago kai ta dubi annah taga fuskar annah cikeda murmushi hakama data kalli momy umaimah tsananin farinciki ne kwance a cikinta 'yar dariya dariya takeyi mai tafe da d'an sauran maqalallun hawayen fuskarta. juyawa tayi gefen nabeela taga yanda nabeela ta ruqo hannunta duka biyun da hannayenta cikin jin dadi ganin yanda nabeela tamarairece mata hadda kwantar da kai a bisa wuyanta tareda yimata alama da idanunta data amince dan Allah, hakan ba qaramin tashin hankaline yaqara baibaye ummu hani ba, ita kuwa tasan inhar ta yadda ta auri amakson tasan kashinta ne zai bushe tsab bisa tafin hannunta,
anya kuwa inta amince da aurensa bata yaudari kanta ba tareda jefa kanta tashin hankalin da sai illa masha Allah yayewarsa daga gareta?,, runtse idanunta tayi da qarfi lokaci daya tareda girgiza kanta ta bude idanunta ta dubi dady mua'zzam cikin bugawan zuciyarta wanda daqyar ta bude bakin ta datakejin mugum nauyinsa a lokacin kamar an dora mata bulo,cikin muryan kuka tace ''wlh dady a rayuwata babu abinda na tsananta tsana face m,....






*Xexen Fasaha*.
f.o.w.
[10/11, 2:48 PM] Xainab Documen: 🌊🌊🌊


*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊
Story and writing
by
Xayyneb πŸ’€πŸ’€


🌊🌊🌊🌊🌊


Fasaha online writers f. o. w.


*🌏impacting valuable knowledge and Entertainment is our concern🀝🏻*.


*Kuna inane*
*my mom sadeeq* *(hawwas)*.
*my qawas (raheenat Mahmoud)*. )
*my zahra mai gari (jikas)*.
*my Attibi (Attabi)*.
*my Aunty marwa*.
*my Matar doctor* .


*Kuzooooooo ku cicci gyad'a πŸ₯œπŸ₯œπŸ₯œmarau marau banda kuma wawasoπŸ˜¬πŸ˜³πŸ€’πŸ€ͺπŸ€£πŸ˜‚πŸ€£.*


🌊🌊🌊🌊🌊
πŸ…Ώ3⃣9⃣
🌊🌊🌊
Cikin muryan kuka tace "Wlh dady a rayuwata ba abinda na tsananta tsana face muhinmancin alaq'a dake tsakanin mutane taja da baya akan abinda baifi qarfin mutanen nan ba da suka roq'i abin ba daga gareka ba kai wanda kake tareda su din ba,
sai nikega babu kyautuwa da har za'ace mutanen nan da kuke tare akan yarda da amana tareda q'aunar juna har sunemi wani abun daga gareka Kai kuma ace ka gaza yi musu abin nan sai nike kallon hakan a matsayin butulci ne, to kuma balle inaga yau ance mutanen da suka kyautatawa rayuwata data iyayena suzo suna neman Wata alfarma daga gareni wacce batafi q'arfina ba ace wai nakasa yi masu ita?, dady bazan so haka ba, nayarda na amince dady Wlh kama had'a ni da koma waye zan aura nasan bazaka badani inda zan dawwama a cikin cutuwa ba dady, har a raina nike jinka kamar baffa na, na yarda2 dady wlh zanyi biyayya akai ni kuma, bazan taba zama butulu a gareku ba"!
tana gama fad'an hakan ta fada cikin jkn momy umaimah tana kukan dole, babu abinda take hangowa illa irin muguwar azabar dazata sha wajen amakson muddin ta auresa kuwa,
towai yasanma da maganar mane kuwa,? wata iriyar azababben faduwan gaba ne ya kuma tsirgata dan gani takeyi suna haka ma acikin gida fad'a kamar kaji inaga sun yi aure kuma zasu qara kusantar juna ma alokacin knn fa? , qwamna nan gida intai masa laifi zata iya boyewa tsawon kwanaki taqi barima ko ganinta yayi ma to can fa?
shida gidansa ta ina zata b'oye masa bai sameta ya nakad'e ta yacicci aniyarta son ransa ba? fashewa tasa keyi da wani kukan mai saka ciwon kai.
mamakin kaifin basira da iya tsararrun kalamai daga yarinyar dady mua'zzam da annah kawai sukeyi, dady mua'zzam yace "to Alhamdulilla Masha AllAh Ummu yi haquri kidaina kukannan dn Allah inda har kin amince zanje na sanar da iyayenki kuma domin inji daga garesu suma kamar yanda na ji daga gareki kema, kitashi kije Allah shi miku albarka gaba dayan ku,, amunn suka amsa nabeela ta kama hannun ummu hani ta miqe tsaye suka haura sama zuwa dakinta suka bar su dady nan suna cigaba da tattaunawa carbin annah na hannunta tana lazuminta.
suna shiga dakin nabeela ta daka wani uba uban tsallen murna ta rungume ummu hani tana qyalqyata dariya tana fad'in "waini Allah ya temakeni yau da naga idi zindir ummu hani na zata gudu garinsu ta barni da kewa, lokaci daya nashiga damuwa cikin ikon Allah kuma take a wajen Allah yakawo mana mafita, mafita wacce zatasa har kullum zan dinga jin ummu sister na kusa dani, kai naji dad'i wlh, maganar takeyi tana fad'awa saman gado cikin murna, fashewa da kuka ummu hani ta sakeyi tana cewa "wlh sister baki sona,,
zaro idanuwa nabeela tayi bayan tatashi zaune ta matso kusa da ummu hani din datake d'osane gefen gadon ita kuma, nabeela tace "Kamarya ban sonki kuma sister dan Allah? dago da idanunta ummu hani tayi ta dubeta tace "eh man dakina sona bazakiyi murna da kasance wa mata ga amakson ba, bayan kinsan yanda mike takun saqa dashi bawani shiri mike ba bayya sona zalika nima kuma ban sonsa"! Murmanshi nabeela tayi tace "haba sister miye nawani batun so da bwakkwawa juna shi a yanzun? Ai kawai da kunyi auren zakiga kamar zaku cinye juna dan tsabar soyewa,
nabeela tayi maganar cikin son tsokanarta, duka ummu hani ta dora mata a baya takuwa gantsare tana "washh! billahel azeem da zafi fa sister, harararta ummu hani tayi ta ci gaba da kukanta kamar wacce akace yau babu baffa kaddo da mama bintey.
Cikin son sake tsokanarta nabeela tace "haba amaryar yaya amakson kiyi shiru mana kada kisa hawayenki suyita zuba kiwa yaya mahber asaran su,, da sauri ummu hani ta miqe tsaye ta shige toilet ta maido qofa ta rufe tayi zamanta acan tana qara bude sabon shafin kukan nata dan taga alama nabeela bazata barta ba taci kukanta ba ta qoshi yanda ranta yai mata tunkan ta koma hannun mugun can qwamma tafara trening din iya zybar da hawaye kala kala a cewarta,
banda dariya kuwa baby abinda nabeela ke mata hakan kuwa ba qaramin qona ran ummu hani yakeba sai dai kaji taqara sautin jiniyar sabon kukanta din, nabeela ta koma bakin qofar ta murd'a ta jita a datse tace "haba sister na wai ke kuka bai miki wuya ne da sam bakya gajia dashi ne?, bakya tsoron kada ma kanki yazo yana ciwo kuma? ki fito haka nan please sister,, banza ummu hani tayi mata taci gaba da kukanta, nabeela tace "wlh inbaki daina kukan nan ba zanje in fad'awa su dady cewa gaki nan kina rufe kanki cikin toilet kinata kuka" aiko tana jin haka yanda kasan daukewar ruwan sama haka kukan da ummu hani takeyi ya bi sarkin shanu ya dauke daf, jin haka yasa nabeela tasaki Murmushi tace "yawwa sister kokefa, ki fito dan Allah to kinji ko? saima kiga dinku nan rigunan namu dan karbo mana su yanzun"
sam ummu qin tankawa tayi haka nabeela tayi tayi da ita akan tafito amman sam taqi,, dole ta haqura tafita daga dakin kuwa.
jin alamun ta fita ne yasa ummu hani din fitowa daga toilet din taje ta rufe qofan dakin ta dawo ta kwanta bisa gadon tana faman sakin ajiyar zuciya had'eda kukan zuci dan na filin ma ta gagara yinsa.
mahabeer kuwa yana fita daga gidan kai tsaye qofar gidansu bleesing yaja burki da motarsa yayi mata waya da cewa gashi nan kofar gida,, nan da nan kuwa sai gata ta fito daga gidansu ta shigo har cikin motar ta zauna.
yana duqe da kansa a styarin motar,
a duniyar ne yarasa mike masa ma dad'i tukun,
"hello my heart na what happened to you? tell me your problems pleass i hear you"
a hankali ya dago kansa tareda kallon ta da jajayen idanunsa kaida ganinsa kaga wanda hankalin sa ba kwance ba,
rai a b'ace fuskar nan a daure yace
"ya kukayi da dadyn kine ya amince zaki musulunta dun koko?
kallonsa kawai take tagaza gane kansa ita gaba ma daya tun xuwansa, daurewa tayi tace
"Sorry my heart na wlh nayi nayi da dady yaqi amincewa amman mizai han ma mu gudu wani garin can sai muyi auren mu? ''Keeeee???!! ya daka mata wata firgitacciyar tsawa wacce batasan sanda ta fice daga motar ba ta fito waje tana zare idanuwan ta dan tunaninta duka kawai zai kawo mata a tym din.
fitowa shima yayi daga cikin motar ya iso har gabanta cikin isar takunsa yaja ta tsaya, sake daure fuskar sa yayi sam babu d'igon fara'a a gareta hakan kuwa ba q'aramin qara fiddo masa wani fannin nasa na kyau yayi ba, dai dai gabnta yaja ya tsaya yace "miye amfani guduwan?!
koni an gaya miki irin shashashan mazan nan ne masu b'ata hankalin su ga mata harsu gudu subar gida em?
toni ba haka nake ba, kince kuma dadynki yaqi amincewa da musuluntar kiko? cikin sauri blessing tace "eh.. eh..cewa yayi ma zai yanka ni inna sake yi masa ma maganar musulunci, zuba mata idanunsa kawai yayi yana kallonta, da sauri kuwa ta janye idanunta daga nasa dan bazata iya jurar kallon kaifafan idanun saba takeji.
wani tsoko yaja cikin takaici yace
"Mtsssss ok no problem inda haka dadyn naki ya zartar amman kuma kisani wannan itace rana ta qarshe nidake relationship namu ya qare na wani so haka or something like this hope you undarstand me?
Kuka bleesing ta fashe dashi ta zube qafafunta gabansa tana roqonsa akan yaci gaba da sonta itadai zata shawo kan babnta, har ransa yana tausaya mata yanda ta dauki sonsa da muhimmanci haka ta azawa rayuwar ta, wanda shi ko kusa baima yi mata irinsa, shi kawai dama tun usuli
ra'ayin auren jinsin sune yakaisa ga fara kulata ynda taga tana nace masa dinnan tun school dinsu bawai wani son taba, ganin yanda take qara sautin kuknta ne yasahi cewa
"kiyi haquri.., nayi fatan danazo yanzu inji kince dadynki ya amince da musuluntar ki daba haufi zan nunaki darect a matsayin fiance na, amman inda har yaqi amincewa i'am sorry to say babu lokaci nina wuce,, yana gama fadin haka ya koma motarsa ya dauko check ya rubuta mata kudi masu yawa ya kamo hannunta ya sanya mata takardar a jiki tareda fadin "kyayi wani abu dasu, nina wuce till another day"
daga haka ya koma motarsa ya tasheta a guje yabar gun yabarta nan tsaye dafe dakai da gudu takoma gida tana rusa irin ihunsu na kiristianity kamar zata fasa musu anguwar dan maqotansu harsun fara fitowa leqe dan a zatonsu wani mugun abinne yafaru.
daga nan wajen bash ya wuce ya iske dakin bash din a bud'e amman shi baya nan, waje ya samu ya kwanta bisa katifar bash din dake shimfide a tsakiyar dakin ya kwanta tareda sa hannuwansa 2 ya rufe fuskarsa yarasa mike masa dadi kam har yanxu shi.
yana nan kwance har akayi sallar magrib daqyar yatashi yayi alwala yayi salla yana nan zaune kan praymat din har aka yi isha'e har lokacin bash bai dawo ba,
gashi koda ya kira ya kira wayarsa a rufe yakeji, yana gama sallar ya miqe tsaye ya fice daga dakin ya shiga motarsa yayi gida,
dady mua'zzam ne ya fito daga saman dakinsa yana ganin shigowar mahabeer din yasaki Murmushi yace "yawwa sojana ina son ganinka daman" daramm!!! mahabeer yaji gabansa ya fad'i batareda yasan dalili ba,
shikam yanzu yana shakkun dud wata magana dazata fito daga fannin ahalin gidansu.
zama yayi kusa da inda dadyn nasa ya zauna yace
"thom dady"!
dady mua'zzam yace "well daman gameda maganar matar da mike nema maka ne to cikin ikon Allah ba'a'je da nisa bama mun sama maka yarinyar da mukasan zata dace da rayuwarka, wacce annah da momynka dukkansu babu wanda baiyi na'am da ita ba,
ba kowa bace kuma face ummu hani tanan gidan"
da wani irin mugun firgici ya dago kai ya dubi dadyn nasa baisan sanda yace "what dady?!!
'yar aiki nan gidan fa kake nufi?
daga bayansa yajiyo muryan annah tace
"oh daman a kundin tarihin rayuwar auratayya an shard'anta cewa ba a auran 'yan aiki knn? tayi maganar tana mai zama kujerar dake kusa data dady mua'zzam din,
kamar zai fashe da kuka ya maida kansa qasa dan baison iyayen nasa su fahimci zabin nasu yana taqaddama dashi,
annah tasake maimaitawa da cewa "bada kai nike ba ne em zaka wani sunne min kai qasa kamar wani mumini?
haba yaro dud kabi ka hayyaci yarinyar mutane a cikin gida koko kana tunanin dud abinda kake mata bamu sane ne aye?, kuma ka bude kunnenka da kyau kaji gargad'ina muddin ka kuskura kaci zalin 'yar amanar mutane saina ci mutuncinka saffa saffa, yamutsa fuskarsa yayi baidai ce komi ba, babu abinda yake mamakantawa a zuciyar sa face yarinyar nan tana hayyacinta kuwa harta iya amincewa da aurena da ita? tab d'ijam lallaikm muddin hakan ta faru ta daukarwa kanta gammon wahala dan babu lamuni a tsakanin su itama tasani kuma.
shi mamakin abin ma kawai yake maganar yake jinta kamar a mafarki ma shi, can wata zuciyar tace masa to mima zaisa ka damu kanka akan wannan yarinyar?
aikai sauqi ma kasamu, yanda zaka juyata son ranka,sannan kuma kai mata barazanar muddun ta kuskura ta kawo qararka ga iyayenka zata d'andana kudar tane,
wani dan murmushi ya saki na ganin target din da zuciyarsa ya shirya masa yai masa dai dai, dan haka cikin Murmushi ya dago kai dubi annah
"yace kai wannan tsohuwar kin fiye saka mun na jiyamu na lura a cikin gidan nan fa,
to ki kwantar da hankalin ki ni bazan mata komi ba,
to mima nike mata neni annah a matsayin qanwa ta fa nike kallon yarinyar shiyasa ma innaga tayi abu nike mata fad'a fa annah ta, yayi maganar kai langwabe, hararsa annah tayi tace
"kai tafi can komi zakace kasan sarai nike kallon ka ay ja'irin yaron kawai, kuma dai kaji abinda nace maka da babban murya"! Murmushi kawai yayi mai ciwo sannan ya dubi dady mua'zzam yace ''dady inda itada bama 'yar kaba ta amince nima na amince dady da zabinka gareni"!!! maganar yake can qasan zuciyarsa na masa qunci ,aiko cikin fara'a dady mua'zzam yace
"kai sojana naji dad'i yanda kaima kayi saurin karbar xabina batareda kokontoba kamar yadda itama taimun, tashi kaje Allah shi muku albarka baki dayanku, amunn annah ta amsa da, shima can kasan lips dinsa ya amsa daqyar yasamu ya miqe tsaye zai haura sama momy umaimah data shigo tun bayan shigowar annah itama ta koma
gefe ta zauna tana sauraron maganar tasu tunda suka fara.
har a ranta taji dadin sake dawwamar ummu hani cikin su ranta qal farinciki,
ita kanta bazata iyakance qaunar ummu hani a cikin zuciyar taba, ganin yana shirin shigewa daki yasa tace ''mahabeer na ga dinner lunch dinka can dining, dan dakatawa yayi,
d'an murmushin basarwa ya furzar da iskan bakinsa sannan yace "ok momy bari na yo wanka zan dawo yanzu, daga haka ya wuce saman ya fad'a dakinsa, yana shiga bakin bed dinsa ya zauna ya had'a manyan yatsunsa na hannu guda 2 yana sosa qasan hab'arsa dasu idanunsa a lumshe banda searching babu abinda brain dinsa ke masa lokacin,
ya dan jima zaune agun sannan yaje toilet ya watsawa jikinsa ruwa ya fito yayi shirin barci ya kwanta kan bed knn phone dinsa yayi ringing a zatonsa ko bash ne ma amman yana dubawa sunan blessing ne yafito kan wayar, tsoki yaja ya ajiye wayar danshi yanzu yariga yagama da rufe babinta a garesa dan bazai cigaba da b'atawa iyayensa akan tarayyarsu ba inda basaso indama ace ta yarda ne ta karbi musulnci dada sauqi ma,haka taita kiran wayan sama da mores missed cull amman kota kan wayar bai biba, an dauki tsawon minti 15 sannan wani kiran yasake shigowa dubawa yayi ganin hannat ce ya sashi sake jan wani tsokin tareda kashe wayar tasa ma gaba day'a dan ya fuskanci bawai barinsa zasuyi yaji da damuwar sama ba data hayyacesa.
soyake ya rufe idanun sa ysyi barci koya samu sauqin abun amman Jin yanda cikinsa keyi ne yasashi shafa cikin da hannunsa shi kansa yasan rabonsa da abinci tun na safe shine har yanzu cikin cikinsa dole kuwa yaji cikinsa na kukan yunwa knn.
agogon wayarsa ya duba yaga 10:26 tashi yayi ya fito daga dakin yasauko qasa kai tsaye dining area ya nufa ganin yarinyar yayi zaune akan d'aya daga kujerin wajen wanda hakan ya tabbatar masa da itama yunwar ce ta fito da ita, hakane kuwa ya canka dai-dai dan rabon data sanyawa cikinta wani abinci tun lokacin da dady yai mata maganar amakson koda momy umaimah tazo tai mata maganar ga abinci can dato mah kawai tabita ita momy umaimah tayi tsammani ma tasauko ta debi abincin ta koma dakinta dan wani lokacin haka take daman wato taqi zama dining din saidai ta sauko ta d'ebi nata abincin cikin plate ta koma sama taci acan , saida taji yunwar na katsar tane yanzun mafarin knn ta leqo qasan falon taga bakowa shine tazo ta zauna tadebi abuncin ta fara ci ko six spon batayiba shima ya fito, ganinsa kawai tayi yaja kujera mai pacing dinta ya zauna, har a ranta ta tsorata da ganinsa a lokacin haka tsoron harya bayyana bisa fuskar ta tazaro fararen idanunta waje cikin dabara tafara qoqarin miqewa daga wajen, tsumammun idanunsa ya zuba mata cikin nata da kashedin karta sake ta motsa daga wajen, dauke fuskarta tayi daga garesa tana yamutsa ta kamar bata fahimci abunda yake nufi ba tayi.
plate taga yajawo ya zuba abinci sosai ya faraci idanunsa still su na kanta ita kuwa sai tsakurar abincin take kad'an kad'an dan a mugun takure take jinta a wajen, saida yaci abincin sosai yasha lemo ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login