Showing 18001 words to 21000 words out of 130351 words

Chapter 7 - MAHABEER Complete Document by Xayyneb.txt

Xayyneb   

29 Jan 2025

9948

dawowa gareku hjy umaimah insha Allah cewar alhj Muhammad yana dariya amman idanunsa nakan mahaber da yake cemasa "dady morning,,,
lpia lau d'an saurayi,
baisan miya fad'ar masa da gaba ba da ganin yaron ba, saiya rasa cikin kuma a family dinsu matarsa ni'ima a cen mecca dawa yk masa kama?
koko dai gixo ne yakega ma kawai.
ahaka dai ya 6arar da zancen, sannan ya dubi muazzam saraki yace "haj mu'azzam wannan ma saurayin yaron family dinka ne shi?
yayi tambayar yana mai nuna mahaber din cikin murmushi, da son yaron kuma.
hakanan shidai yaji son saurayin ya shigesa a ransa batareda yasan dalili ba,,,,,,




Fasaha online writers f.o.w.πŸ“˜πŸ–Š
[10/11, 2:45 PM] Xainab Documen: 🌊🌊🌊


*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊
Story and writing
by
XayynebπŸ’€πŸ’€


🌊🌊🌊🌊🌊
Fasaha online writers f.o.w.


🌊🌊🌊🌊🌊
πŸ…Ώ1⃣5⃣
🌊🌊🌊
*M* u'azzam saraki cikin murmushi shima yace yace "eh d'ana ne haj Muhammad,
amman bazaka san saba daman, saboda a watan da aka haifesa na nemeka in shaida maka tun ranar amman ban samekan ba saidai sauran abokanmu na sanarwa,
cikin mamaki alhj Muhammad "yace ikon Allah knn,
kaima kamar ni kk sai bayan tsawon lokaci sannan muka samu namu rabon kuma inaga a satinne nima aka haifar mun yaro na,
to Masha Allah masha Allah, Allah shi riqa mana amman ya sunnan d'an nawa to?
mommy umaimah tayi saurin cewa *"mahabeer* sunan sa,,,
dammmmm alhj Muhammad yaji gabansa yawani iriyar yankewa ya buga da qarfi,, cikin rawar murya yace
"ma,,, mah,,mahabeer fa kikace?
cikin mamaki suke kallonsa wannan karon harda shi mahabeer d'in dayabar latsa phone dinsa a wannan karon ya zubawa abokin baban nasa idanu najin mamakin sunansa da yaketa maimaitawa.
alhj mua'zzam saraki ne yayi qarfin halin furta cewa "eh abokina sunansa knn mahabeer, ince kokaima kasan sunan ne a wani wajen?
share zufar kansa alhj Muhammad yayi da hankicerf d'in sa sannan yace
"sunan yarona ne daya 6ata knn shima mahabeer, shiyasa kaga nayi mamakin sake jin sunan nasa danayi a yanzun, dan tunda nake ban ta6a jin mai irin wannan sunan ba saifa sanda aka haifesa mahaifin ni'ima daga can mecca ya bamu shi sunan muka sanya masa tokaji fa dalilin mamakin nawa"
ya qarashe maganar yana mai sakin fara'ar dole.
sun qara tausaya masa sannan daga bisani suka rabu akan gobe zasu had'u insha Allah inda yadawo gari yanzun parmanet.
a haka alhj Muhammad d'in ya tafi yana ta satar kallon mahabeer kamar ya daukesa yakeji ya tafi dashi.
abinda yabawa alhj mu'azzam saraki a mamaki a lokacin shine ganin yanda cincirondon 'yan jarida suka wajen suka baibayesa maza da mata suna qoqarin fara watso masu tambayoyin nasu knn a lokacin kuma manyan likitocin cikin asibitin sika fito dukkansu sukayi masa jagora har saman benayen d'aku nan da su marassa lpian na asibitin suke kwankwance cikin jigata dakuma neman temako mawadata bayin Allah.
Sukuma yan jarida d'in suna mara masu baya cameras dinsu tuni ta fara daukan vidous na rahoto.
gadajen wa'anda ambaliyan ruwa yatafi musu da muhallansu da dukiyoyinsu tanan yafara bi yana musu ya jiki suna amsawa cikin tsananin son mua'zzam saraki a ransu na kirkinsa da kulawar sa garesu,
dud gadon da suka zo saiya zauna a seat d'in wajen ya gayar da patient d'in cikin girmamawa batareda tunowa da tazarar dake tsakanin suba nashi mai kudi su kuma talakawa amman dud hakan sam bai damesaba dan yasan Allan nan dai dud shi ya haliccesu baikuma banbanta d'aya ba dan yafison d'ayan ba.
mahabeer shikuma yana bayan mahaifin nasa tsaye kamar soja fuskar nan tasa bazakace yana daure ba kuma bazakace yana a sake ba, amman har a zuciyarsa tausayin mutanen nan yana ransa sosai,
briefcase d'in dake saman shoulder dinsa babu abinda ke cikinta sai kudi bandir bandir,
Shiyasa in shi mua'zzam saraki d'in ya zauna wajen patient d'in kanya tashi saiya umarci mahabeer d'in daya ajiye musu rafar 200 thousand sabida kulawa dakai da siyen magani kuma,
kowane gado haka suke masa har saida suka gama tanan bangaren suna shirin komawa ta 'yan 6angaren accident ne mua'zzam saraki ya kirawo babban doctor d'in yazo cikin sauri yadan rusuna danji yake kansa har wani hiyaqi hiyaqi yake cikin dinbin jama'ar wajen mua'zzam saraki ya kirasa.
"ranka shi dad'e gani,,,,,
mua'zzam saraki yace "yawwa doctor lurwan, yanzu mutanen da suka rasa muhallansu zasu kai kamar mutum nawa knn?,
d'an dakatawa doctor lurwan yayi yana mai bin wajen gadajen da suke kwance da kallo,
in few minutes ya gama q'ilgasu sannan yace "mutane 58 ne ranka shi dad'e,
"ok dictor kaje daga yau har qarshen satin nan na baka kwangilar samomin gidaje 58 wad'anda zasu koma a ciki in sun samu lpia,
cikin rawar jiki doctor lurwan yaji wannan garabasar kamar daga sama nan danan ya fara fad'in "to,,, to,,,,ranka shidad'e insha Allah zan samo maka su cikin satin nan da yandan Allah,,,
ya qarashe mgnr tasa baki a washe.
sudai yan journalist aikinsu kawai sukeyi suna biye dasu ko ina, suma a zuqatansu cike da mamakin yawan alherin mutumin.
daga nan layin 'yan hatsari suka dinga bi suma suna basu kudin kamar ynda suka bawa sauran,
su baffa kad'do sune last bed na dakin gaba d'aya,
haka mua'zzam saraki ya isa nasu wajen suma ya zauna mommy umaimah na gefensa na dama yayinda mahabeer ke tsaye as any tymes ago,,
baffa kaddo ya fara gaishesu yayinda maman ummu hani ta samu barci ummu hani kuma ta gewaya baya tana wanke masu kayansu can wajen famfo,,,
a zuciyar mommy umaimah taita mamakin miya kawo buzaye kuma suma anan?
sai tayi tunanin cewa kuma ko sun shigo cikin gari ne hatsarin ya samesu mafarin zuwan nasu knn yau,
Kuma ga alama ita wacce ke jinyar ta fara samun sauqi ganin yanda wajen dataji ciwokan a jikinta suka fara q'aqqamewa.
nan shima mahabeer ya ajiye musu 200 thousands baffa kaddo yanata godia kamar yanda yaga sauran nayi,
amman shi nagode 2 kawai ya iya fada da hausa dan ba iya yaren hausar yayi sosai ba,
ahankali mommy umaimah ta qara dafe kanta datakejin yana dan jujjuya mata tun farkon shigowar tasu hospital d'in amman wannan karon yafi lokuttan da suka wuce juyawa sosai,,,
suna shirin fitane daga wajen tayi saurin ruqo mahabeer da yafi kusa da ita ta sulale
a qasan wajen a sume,,,,
da sauri mahabeer ya duqa tareda ruqo hannayenta yana fad'in "momy, momy, miya sameki kitashi pleas!!???
dud ya rude ya gigice,, mua'zzam saraki shima ba qaramin dauriya yayi ba da ganin tashin hankalin daya samesu ba a lokaci daya,,
ga doctors sunxo sun zagayesu cike da tausayin halinda matar tasa ta fad'a a ciki ynzu, suna son temakawa su dauketa suje suyi checking dinta amman suna ganin kamar kuskure ne yin hakan dan aganinsu yafi qarfin ajiye iyalinsa a cikin wannan general hospital d'in tasu ta kowa da kowa, sai dai ta kud'i,,,, jin mua'zzam saraki na cewa cikin rawar murya "ku d'auketa doctors dan Allah ku duba min ita kunji,,,miya faru da ita?!!!
basu bari mamakinsu ya tsanan taba nan da nan sukabi umarnun sa kuwa, nurse d'in asibitin suka kawo keken da ake dora marassa lpia, mahabeer ya dagota cak ya dora a saman keken zuciyarsa na wani irin bugu fat! fat! fat!,,,
shiga sukayi da ita emergency nan danan doctors sama da 5 suka rufo a kanta suna binciko matsalar tata yayinda a can waje kuma 'yan jarida suka rufu akan mua'zzam saraki suka hau tambayar sa akanmi yayi ra'ayin ajiye matarsa a irin wannan asibitin? wanda masu kudi da dama suke qin kawo iyalensu dan suna tunanin babu wasu q'wararrun likitoci da zasu duba musu familyn nasu kamar sauran private hospital inma baa dangana da qasashen qetare ba koda kuwa ace dai dai da ciwon kaine common bare kuma ace wai rasa numfashi gaba daya a lokaci daya, mizakace kai kuma game da hakan ranka shi dad'e??????




Fasaha online writers f.o.w.πŸ“˜πŸ–Š
[10/11, 2:45 PM] Xainab Documen: 🌊🌊🌊


*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊
Story and writing
by
XayynebπŸ’€πŸ’€


🌊🌊🌊🌊🌊
Fasaha online writers f.o.w.


*Didicated to zahra mai gari*


🌊🌊🌊🌊🌊
πŸ…Ώ1⃣6⃣
🌊🌊🌊
Maganar da d'an jaridar yakewa mua'zzam saraki ita mamaki ma kawai ta bashi gaba d'aya,
duban bayin Allahn dake kwance a wajajen ya sakeyi ga kuma matarsa itama acan kwance,
kawai bud'an bakin sa sai cewa musu yayi, "to sabodami harni zanfi qarfin ajiye iyalina a cikin bayin Allah musulmai,?
Siyo lafiyan zanyi knn?
kun mance damai bada lpiar ne?
girgiza kai yayi sannan yace
"ninan da kuke ganina nasha ban ban da sauran,
dan ban raina mafari, komin q'anqantar waje wlh zan iya kawo iyalaine wajen nima a dubamun su muddin jama'an Annabi na halartar wajen, ban damu sai inda keda fanka da eci ba, shiru ya danyi sannan ya ci gaba da fad'in "kutuna neman lpia ya kawo kowa a wajen nan bawai hutawa ba, dan lpiar itace kowane irin hutu na rayuwan d'an Adam muddin bakada lpia tofa jin dad'i bai ganka ba aduniyar nan, kuma nasan kunsan haka kuma,
wlh koda ace nine ke ciwon nan zan tsaya anan su dubani kamar yanda ake duba sauran, dan nasan inada compidence akan asibitin nan,
*barau dikko hospital* nasan yana kulawa da jama'a ynda ya kamata komin qaramin qarfinka zasu baka kulawa ynda ya dace bazasu banzatar da kaiba,
dan haka maganata ta qarshe shine kusani Allah d'aya na sani kuma shi ke bada lipa akowane wuri mutum yake bawai sai za6a66en waje ba".
dukkansu jikinsu yayi sanyi da maganar mua'zzam saraki dan haka kowa ya sauke abin maganarsa daga garesa cikin karewar gwiwa tareda qara tabbatar da gaskiar abinda ya gama fada ynxun a cikin bakinsa,
wani daga cikin sune yayi q'arfin halin cewa "am to ranka shi dad'e zamu iya tsayawa anan har sai munji sakamakon ciwon mai d'akinka na samun sauqi dan masoyanka su gani kazo aikin alheri kuma ga ynda ta faru da iyalinka?
d'aga masa hannu mua'zzam saraki yayi yace "banda buq'atar hakan,,, kuma inda hali ku goge vidio d'in nan da kuketa d'aukanmu tun d'azun, ban son ni innayi aikin alheri sai an gwadawa duniya kowa ya gani, na roqeku daku goge dudda nasan dan kasuwanci da son qara daukaka kukeyin sa,
tsabar qwarjini dayai musu ne yasa kowanensu ya danna wajen gogewa kawai suka barshi a matsayin zasu buga labarin temakon majinyan da yayi a asibitin a newspaper dinsu inda aikinsu ne hakan,
umartar mahabeer yayi daya bawa kowanensu bander bandeer suma,
nan da nan kuwa ya cika umarnin dadyn nasa, sukuwa 'yan jarida gani suke riba biyu aisu gaba ta kaisu ma a zuwan asibitin dan d'aukan rahotan,
shiyasa basu q'ara d'aukan wani dogon lokaci ba suka tafi.
dafe kansa anan wajen mua'zzam saraki yayi yana adduar Allah bawa umaimahn sa lpia,
ba'a jimaba doctor lurwan ya fito daga room d'in da aka shigar da umaimah fuskarsa a sake cikin fara'a ya iso wajen,
mahabeer ya zuba masa ido a tun a daga nesa, zuciyarsa yaji ta d'anyi sanyi dan ko ba komi yaga alamun nasara akan fuska ta doctor lurwan d'in.
yana zuwa gaban mua'zzam saraki yace "ranka shi dad'e muje office danjin bayanin komi,
suna shiga office d'in suka zauna mahabeer ya zauna akan kujerar dake setin dadyn nasa yayinda doctor lurwan ke fuskantar su.
yafara magana da cewa "ranka shi dad'e iyalinka ta farko lpia amman ta koma barci ynxu sakamakon q'arin ruwa da muka jona mata sannan kuma munyi kowane irin gwaje gwaje ga ita mai d'akin naka har fitsarinta mun d'iba munyi reaserching akai kaga result d'in da muka samu nan ma,
nan ya isa wajen wata na'ura dake wajen yayi wasu danne danne saiga wata farar paper ta turo a qasan na'urar tasu ta aiki ya dawo ya zauna tareda miqawa mua'zzam sarakin result d'in shi kuma ya kar6a tareda fara dubawa,
abinda ya gani ne yaji jikinsa na wani irin tsumammiyar tsuma ta kyarma a lokacin, nan take farin ciki ya wani iriyar baibayesa,,, ganin abin yakeyi kamar a mafarki sai faman qara maimaita karanta takardar yakeyi wai yau shine Allah ya azurtasu da samun rabo na ciki abinda suka jima suna fata da roqon Allah shine yau Allah ya dubesu da idon Rahma ya basu abinda dukiyanka bazata ta6a siya maka shiba komin yawanta,
baiyi aune ba yaji wasu irin d'umammun hawaye nabin idanunsa suna fitowa na farin ciki.
wai yau matarsa keda 6oyayyen ciki har na tsawon wata 6 batareda sun sani ba kuma?
Kai shiko yau wace irin iriyar godia zai nunawa Ubangijin nasa yau?
Kawai saiya daga hannayensa a sama dukkansu hawayen murna na q'ara fito masa ya sunkuya qasa tareda yiwa ubangiji sujada sai fad'in Alhamdulilla ya Allah kawai yakeyi tareda kirari wa sunayen Allah kyawawa.
fiddo idanuwa mahabeer yayi da sauri ganin hawaye nabin idanuwan dadyn nasa bayan ya koma ya zauna yayinda fuskarsa ke kan qara kallon takardar da likitan ya bashi.
cikin mutuwar jiki mahabeer ya taso ya dawo wajen dadyn nasa ya leqa kansa ya fara bin takardar da idanuwa shima, ganin abinda ke rubuce shima ya basa mamaki dan tun tashinsa a gidan nasu bai ta6a ganin wani q'aramin yaro ba bayanshi,
sai ynxu ne yasan ma'anar zubar hawayen dadyn nasa na farinciki ne ba komi ba.
rungume juna sukayi shida dadyn suna murna,,, doctor lurwan kuwa sai binsu yake da kallo shima yana fara'a,,
Hamdala dady mua'zzam saraki kawai yakeyi bayan sujada da yayi ta nuna farin cikinsa ga mahalicci,
lallai sad'aqa da temakon bayin Allah ba q'aramar turba bace mai kaiwa ga gaci ba a rayuwar d'an Adam kai harma bayan ransa zata bisa ta zame masa garkuwa a ranar sakamako.
Mua'zzam saraki ya rasa inda zaisa kansa dan murna da sauri yake fad'in cewa "doctor lurwan haq'iqa naji dad'in wannan albishir d'in naka gareni dan haka na baka kujerar mecca 10 ta wannan shekar a matsayin tukwicin ka,
washe baki doctor lurwan yake tayi yana fad'in "godia nake ranka shidade, aransa yake fad'in yau kam ya dace da wannan rana yaushi washar kam.
Har d'akin da momy umaimah take kwance doctor lurwan ya kaisu lokacin ta farko, amman sai doctor lurwan yace ya kamata abarta ta qara hutawa sosai dan qwarin jikinta ya dawo normal duka.
bayan fitar doctor lurwan mua'zzam saraki ya matsa kusada ita ya zauna yace muna qara godia ga Allah wifeyna dayai mana irin babban wannan kyauta a wannan shekarar wacce ta fiyemun dukiya ta duka,,
Kallonsa kawai takeyi takasa gane nufin nasa, duban mahabeer dady mua'zzam saraki yayi yace "zoka fad'a mata abin farin cikin daya samemu my son,
yayi maganar cikin tsananin q'aruwar Murnar tasa,
har wajen kanta mahabeer ya duq'o ya rad'a mata da cewa "momny na nanda 3 months zaki bawa dady baby ni kuma q'ane a gareni haka doctor yace"
jitayi maganar kamar a mafarki abin wasu hawaye taji suna neman sulalo mata a fuskanta itama da sauri ta miqe zaune ta shige jikin dady mua'zzam saraki tana hawaye,
a zuciyarta godia kawai takewa ubangiji Allah babu adadi,, cikin rawar murya ta fara fadun "nuree... nuree kawai a take fad'a jikinsa shikuma ya
qara rungume suna dariyan murna, a fili suke qara bayyana hamdala ga buwayi gagara misali mai kyauta asanda yaso batareda tursasawa ta wani abin halitta ba,
Kwantar da ita yayi tareda shafa kanta ya sumbaci bakinta cikin so da kulawa ta tsohuwar soyayyar tasu,,,
shi dai mahabeer cikin burgewa yake kallon iyayen nasa soyayyar tabbas bata tsufa ya shaida hakan tuni batun yau ba.
lumshe idanunsa yayi sannan ya bud'esu lokacin dayaji dadyn nasa nace masa ''zaije gida ya d'auko annah ya jirasa yanzun zasu dawo,
"to dady ai kyau ace kabari ni zanje na kaiwa annah ta wannan surprise d'in" ya fad'i maganar a shagwabe kansa na mai lwangwabe,
"cikin faraa mua'zzam saraki yace "nima ina son inga kalar farin cikin da kagani a fuskar mamanka lokacin da ka fad'a matan ynxun to nima inason inga irinsa a fuskar mahaifiyata koya kace my son?
"dhat is true dady adawo lpia ina nan muna jinya nida momyna"
ya fad'i hakan tareda kwanciya gefen gadon da mommy umaimahn taken.
sukuwa iyayen dariya sukayi masa. ahaka dady mua'zzam saraki ya fice zuciyarsa cikeda farin ciki uwa ya zuba ruwa qasa yasha.
mommy umaimah ta dubi mahabeer tace "ina son shan ruwa mahabeer dina, da sauri ya miqe tsaye har Bluetooth din kunnen sa na fad'owa saman jikinsa yace
"to momy bari naje na samo miki swean water a nan waje ko,
girgiza kai tayi tace
"na zartsi nake son sha ay son"
to momy ina zamu samu na zarts,,,, maganar tasa ta katse da dawowar doctor lurwan cikin d'akin tun bayan futarsa dazun, anan yaji abunda momy umaimah tace ta so.
mahabeer yace
"doctor i don't know place,,, kokasan wajen da zan samu irin ruwan da take son sha d'in anan kusa sainaje?
doctor lurwan yace "eh inka fita anan ka zagaya ta baya akwai fanfon mono wajen wata darbejiyan icce zaka samu anan"
"ok doctor thanks bari naje tom"
anan ya fita yabar doctor yana qara gyarawa mommy umaimah drip d'in hannunta.
ta inda doctor ya kwatanta masa tanan yabi wajen ba hayaniyar komi tsit sai wata matashiyar yarinya daya fara hangowa daga nesa wacce sam sam baiga really fuskarta ba, sakamakon ta rufe rabin fuskar nata,
sai dai gazar gazar d'in baqaqen gashin idanunta da gashin girarta kawai ke bud'e dayake tasa wani baqin qyalle mai kauri ta rube rabin fuskar nata, tana duq'e tana linke kayanta data gama wankewa sun bushe tanason komawa cikin d'akin dan bata sani ba ko mamanta na son wani abun kuma.
cikin tafiyar takunsa na qasaita ya iso wajen yaja ya tsaya gabnta batareda yace uffan ba dan yarasa ta ina zai fara mata maganar ynda kan famfan yake dan ba wai sanin kansa yaiba,
jin motsin taku a bayanta yasa ta jiyo da fuskarta a hankali dan tanada tabbacin cewa babu kowa a wajen face ita dan tun d'azun sauran mutanen wajen suka gama nasu aikin suka tafi itama dantana sanyin jiki ne na aiki shiyasa takai har yanzun ,,,,,
ganin mutum tayi a bayanta a tsaye, ita tsoro ma taji hakan yasa da d'an sauri ta miq'e tsaye tareda kwasar kayanta ta matsa daga wajen taci gaba da linkin kayan ta batare da ta qara kallonsa ba.
shi sam hankalin sa ma bai wajenta ta sosaia lokacin, shi babban matsalan sa yanda ake samun ruwan su fito baisan ynda ake yiba, shiyasa ya tsaya wajen yana mai qara nazartar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login