Showing 129001 words to 130351 words out of 130351 words

Chapter 44 - MAHABEER Complete Document by Xayyneb.txt

Xayyneb   

29 Jan 2025

9944

ko kunya ya biyo feader sa nan ya dawo gidan ya tare wato angulu ta dawo gidanta na tsamiya knn😹😝.
wanshekaren data dawo kuwa da azhur naquda ta taso mata gadan gadan nan da nan su momy ni'ima sukayi asibiti kai tsaye labour room akayi da ummu kamar ta mutu takeji dan azaba, sunan Allah kawai take kira sannan ta dawo qwalawa momy ni'ima kira akan akirawo mata yaya mahabeer ta nemi gafararsa dan ita mutuwa zatayi.
su annah sun tausaya mata matuqa addua kawai suke mata dan sunsan muddin aka fadawa mahabeer halinda take ciki haukace musu zaiyi shima nan wajen.
sai gashi cikin ikon Allah da qarfin addu'a ta sunyulo kyakkyawan yaronta sak babansa mahabeer,
babu jimawa wata sabuwar naq'udar ta taso mata sai ga baby girl itama sak ummuhani ta biyo baya sai tsandara kuka suke suna wutsul wutsul.
su annah hamdala kawai sukeyi saida aka gyara mai jego da babys twins d'inta ta samu bed rest sannan su annah suka shigo sukaita mata sannu kowa ya dauki jariran kuwa sam baison ajiyesu dan tsabar farinciki, nan annah tai musukiran salla a kunnen su na dama iq'ama ana haggu kamar yanda sunnar manzon rahma tazo mana dashi.
sai wajen la'asar sannan aka basu sallama suka dawo gida.
mahabeer na dawowa yayi tozali da twins babys nasa zokaga farinciki tsantsarsa jiki na rawa yaki bash aiko ba'a jima saiga bash har dakin momy umaima nan ya gaida annah da momy ni'ima da mmn nebeela ya dan jima sannan da zai tafi kuma ya ajiye wa babys rafarsu ta yan dubu guda 2 sannan suka fito shida mahabeer waje dai dai zai shiga mota yaja ya tsaya ya dubi mahabeer yace "gifted kasan kuwa mutumin mu mukhatar ya gudu yabar gari kusan sati day'a knn? "zuba masa idanunsa mahabeer yayi sannan yace "guduwa kamar yaya bash? "bash yace "hm wallahi kuwa kasan qaninsa ai daman yana daya daga cikin yarana a kasuwa to shine yake cemin ashe da akayi gwajin jininsa an gano yana daukeda da hiv aids tunda lokacin yaketa surfawa matarsa zagi yana cewa itace ta goga masa wajen yawon ta da 'yan iskan samarinta, itama tana tsine masa da cewar shine yasa mata, wajen neman matansa na banza musulmai da kiristan , koda aka sallamosa yana daddogara sandarsa washe garin ranar yabar takardar wasiqa wa matar tasa na ya saketa saki 3 shi kuma bazai iya zama mutane na masa dariya ba dan haka ya shiga duniya, to kajifa yanda abun ya ida kasance masa cewar bash din"
girgiza kai mahabeer yayi yace "cin amana sakamakon sa muninnika ne dashi bash AllAh ya kyauta dai"
bash yace "amin ya rabbi" nan suka yi bankwana shikuma ya koma wajen twins dinsa a zumud'ance.
kwana 6 da haihuwa har 'yan katsina sun zozzo da 'yan niger su nahee da sauran 'yan uwa,
ummu hani taso koda mommonta baffan ta ne ya bari tazo amman ina saidai mamar nahee tazo wato matar baffa indeh dudda hakan kuma taji dadi koba komi taga 'yan uwanta itama kusa da ita.
momy umaima na tsaka da shafawa hasan powder saiga hjy aina ta shigo bayan ta musu barka nan momy umaima ke tambayarta hannat danta daina ganinta kwana 2,
har lokacin kuwa hjy aina tana jin kunyar abin kunyar da tayi a asibiti kwanaki na nuna maitarta datayi a fili gameda naman da taso ummu hani taci lokacin mai asirin nan, wanda shine yanzun hakan qaiqayi yamusu koma kan masheqiya kamar yanda boka zalimu ya fada, annah kuwa sai kallon uku aho take wa hjy aina din, cikin matse yar qwallar nadama hjy aina tace " ai hannat tayi aure sati daya knn da tarewarta" kallon mamaki kawai suke bin hjy aina dashi daqyar momy umaima tace "kuma baki fad'a munzo miki murna ba hjy aina? " cikin muryar kuka hjy aina tace "murnarmi zakuzo auren da akayisa hankali tashe wlh wani mugun malamin tsubbu ta gamu dashi yai mata wani mugun asiri tabi ta rude ita batason kowa sai shi almajirai ma yake koyawa karatun allo gidansa, matansa ko fita basayi saita kama to kunji dalili wallahi kuwa dai"
(hmmm to ashe fa wannan naman da mahabeer yabayar mlm zayyanu ne yabawa,shima yazo asibitinne lokacin dubiya,
mlm zayyanu mugun malamin zaure ne, to kuma kamar yanda boka zalimu yace kowa yaci naman nan to kowayeshi saiya sota to hakan ta kasance da mlm zayyanu kuwa, har gida ya bita ganin zata raina masa wayau aiko yaje yai mata zama day'a rak kan buzunsa sai gashi tazo da kanta tana basa haquri tana kuka, sati daya da haduwarsu aka daura aure ta tare sabida yanda tabi ta dagawa hjy aina rai dole takira ubanta akayi mgn sannan. niko nace qarshen mai son zuciya knn tsaf zata kaika ga maquntacen rayuwa qarshenta knn).
saida ta jima sannan ta tafi sukuwa abun mamaki yaita basu a zuciya.
ranar suna namajin yaci sunan haseen macen kuma haseena, mai jigo taci kwalliya taqin qarawa sai faman walainiya take a dud inda ta gifta kuwa.
suna nan har saida akayi arba'in ranar jumaa ne da dadaddare momy umaima da momy Asma'u suka maidata gidanta bayan tasha gyara na musamman kuwa ciki da waje.
shi kuwa yana cen tareda bash sai qarfe tara da rabi ya shigo falon gidan nasu da gudu kuwa baby manal ta nufosa aiko ya ca6eta yana shillata sama tana qyaleta masa dariya ya saukota yace "baby na kin ga auntynki ummu da qannenki? dayake ba mgn ta iya ba sai dai "errrn ''errn da take ce masa na gwarancin ta.
murmushi yayi yace ''jeki ki dauko mun haseen da haseena to" aiko ta koma ciki tana dugwi dugwi na tafiyarta, daga bayansa yaji annah tace " haba aimu k'wakwar ta ishemu haka shiyasa nasa a tattara maka iyalenka gida tyn dazu " da sauri yace "wow kai annah da gaske? harararsa tayi tace "daman kasan qarya nike maka ja'irin yaro ko? tayi maganar tana sanya zungurunta, aiko da gudu ya dauki keys na motarsa ya fice, annah tace "oh o'ni yaran yanzun kunya tai musu q'aura? bajimawa momy umaima taci gaba da sawa annah lallen nan annah take fada mata yanda suka q'arke dashi suna dariya.
falon yaji tsit, shiyasa ya haura sama ya shiga dakinta nan yaji motsin ruwa a toilet alamun wanka take.
gadon su twins dinsaya leqa yaga sunata barcinsu abinsu ya sumb'ace su tareda musu addu'a ,kayansa ya cire ya daura towel ya shige toilet dun shima, babu zato ta jisa a cikin shower dinta yana cigaba da murza mata kunfan a saman mamannita, itako tana ganinsa ta buntsuro d'an bakinta dole ko ta haqura ya yi musu wankan, ya daura mata towel itama saman qirjinta sannan ya daukota suka fito sai murmushi suke sakarwa juna.
saida ya gama busar mata da gashin kanta ya sakesa saman jikinta dan yafi sonsa hakan.
saida ta jasa dining sukaci abinci sannan sungumeta jikinsa tun anan ya fara tsotsar wuyanta ita kuwa hannunwata na saqale da wuyansa idanunta a lumshe, cikin blanket suka shige ya hade fuskarsu waje day'a yace " feader na i miss you kema kinyi missing nawa ko? d'age masa girarta tayi tace "yeas i miss you too yah mahabeer nayi rashinka har naji babu dad'i "yana shirin magana ne yaga tayi saurin zare towel dunta tahau feading nasa da manyan dukiyar fulanunta cikakku dammm kamar an qara hura mata su irin balloons dinnan. hmmm daren ranar har kukan dad'i suka dunga yiwa juna, yalla6ai mahabeer jiyayi kamar lokacin ne ya fidda ummu hani a ledar budurcinta. haka suka dunga rayuwar su cikin farin ciki.
dud byn dan lokc suna zuwa niger da mecca dan sada zumunci ga 'yan uwa kuma.








*TAMMAT BIHAMDULLA*📘🖊

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login