Showing 78001 words to 81000 words out of 130351 words
dalilin da zaisa kaci gaba ma da d'orawa kanka damuwa kan auren wancen yarinyar ba,
baka saba zama cikin damuwa ba shiyasa yana gama tunanin nan a take kuwa ya tattara komi ya watsar ya koma yanda yake abinsa, danshi kaifi day'a ne dud abinda ransa ya basa indai jikinsa ya amunce masa tofa saiya aikata.
dan shi sam bai dauki wannan auren da ake cewa am masa ba a matsayin aure ba, no kawai dai a ganinsa sun sama masa baiwa 'yar rakiya ne a tafiyar tasa,
Axpen dinsa ya fiddo daga kwalinta guda daya ya kunna mata letter ya fara zuqar ta idanunsa sun kada sunyi jajir jijiyoyin kansa sun tattashi sakamakon damuwar daya yakice ta da qarfi daga jikinsa yanzun nan, kara daya da rabi yasha yaji ya ishesa ya gutsire sauran a bed side din da yake saman wani plate na iriyar tangaram qarami, sannan ya jawo wayarsa ya kunna kafin ya fara sarrafa ta saiga kiran dady mua'zzam ya shigo, tsurawa number dady din nasa idanuwa yayi harta tsinke batareda ya ankara ba dan yasan tambayoyi ne saiya shasu wajen dady na ina yaje kwans 2 tunanin amsar daya dace wacce zai fada masa ne ya nema ya rasa mafarin knn har wayar ta sake tsinkewa a karo na 2 da kiran dadyn, yana shirin kiran dadyn ne wayar bash ta shigo ya d'aga knn saiga kuma kiran dady ya sake zuwar masa again dole yasa ya katse layin bash din ya amsa na dady da fad'in cewa "dady barka da kwana? daga can dady mua'zzam yace "haba sojana ina ka shige kwana 2 dud mun nemaka mun rasa hatta su basheer na tambaya amman suma sunce basu san ina kaiba?,
sosa gefen ha6arsa yayi kad'an sannan yace "sorry dady na danje ganin wani dadyn friend dinane a jos to shiyasa, kuma acan motana ya samu matsala mafarin kuma nmta phone dina anan cikin motar da aka kaita can wajen makaniken kuma qarin matsalar dady shine phone din yana rufe ne dady shiyasa amman yau zan dawo insha Allah".
ya qarashe yin maganar yana mai jan astagfurilla domin qaryar daya shatatawa dady batareda yasan ya iya taba dan dai kawai ya kare kansa yasa yayi hakan.
sauke ajiyar zuciya dady yayi yace "assha ai rashin lpia ya kauda komi kayi qoqarin dawowa din kasan gobe da safe ne tafiyar naku k, "yess dady iknow nima inason in dawo da wurin yau sabida karb'o passport din namu da sauran abubuwan daya kamata ace... dady ya katsesa da cewa "noooo sojana kada kadamu da wannan dan na rigaya dana amso muku tun jia, na kuma gama had'a muku komi sojana kaidai kawai kayi koqarin tahowar yau,
cikin muryansa ta rashin jin dad'in komarwa tasa gida yace "okeyy dady,! dady mua'zzam yace ''yawwa sojana sai kadawo din to, katse layin dady mua'zzam yayi yayinda mahabeer yabi wayar tasa da kallo kawai cikin tunanuka kala kala, watch din dake daure a tsuntsiyar hannunsa ya kalla yaga yanzu 12:33.AM.
sauke sabuwan ajiyar zuciya yayi yana qoqarin miqewa ne ya shiga toilet dan ya warwatsa, kirane ya qara shigowa na bash a wayar tasa.
dagawa yayi yace
"yadai bash kana lpia kuwa wannan doubles culling naka sunmun yawa, bash yace "walh gifted dud wani cikakken d'an iska ya biyo bayanka, bacin kana d'an iska zamu nemaka mu rasa ana tsaka da bikinka wato kaine ma ka koma ita amaryar harka samfe mana muka kasa gano mafakarka ko,? babu damuwa hankalin ka ya kwanta inda angama biki mu abokai bamuyi komi
ba nawani party haka da sauransu yanzun saika fito daga ma6oyar taka ko? wata 'yar dariya mahabeer ya saki yace "excuse me mlm bani 1 hour yanzun nan zan fito mu hadu in yaso in mun hadu saika ida amayar da sauran abinda ke cikin cikin naka,
amman ina zan sameka, bash yace "gamu nan cikin gamji nida mukhtar ya jawoni rakiya zaiga wani abokinsa dan iskan ashe qaryan sa sakar mun dan yanzun haka ma maganar nan da mikeyi dakai kaga dan iskan can ya dafi wata cikar cikin mota Yana matsa alhalin kuwa ya baro matarsa can gida"!
girgiza kai mahabeer yayi yace "bash mukhtar baida ranan gyara halayensa ne wai? bash yace "gashi nan dai yayi aure kamar baiba dayake shi kamar wanda jarabar duniyar nan ta son mata aka taru aka had'a masa su waje day'a ba, tsoki mahabeer yayi yace "bari dai na fito din, bash yace "ok gifted saika fiton". yana ajiye wayar ya shigs toilet bai jima ba yafito ya hau tsane jikinsa da towel yana gamawa ya shafe jikinsa da kalar lotion dinsa mai sanyin qamshi ya d'auko kayansa yasa sunyi matuqar yimass kyau yayi shar dashi ya fito angon dashi kuwa sak, dan wani farin boyel ne dinkin new modern ne akai masa, rigar iya gwiwa da hannayenta masu botels shi kansa aiki dake jikin rigar abun kallo ne, ya dora hula saman kansa tai masa masifar kyau kuwa, ammn da yake bai saba ba daya shiga cikin motarsa wurgar da ita hular yayi baya yana tsoki a fili yace "haba dan Allah dud anbi an takurawa mutun an masa aure batareda ya buqata ba,mtsss ni hular ma ko iya sanyata banba abin takaici , """"mtsss yasake jan wani dogon tsokin yana fad'in "huuu banzar yarinya kawai tasa anmun shigar kutse a rayuwata anmun auren dole!,
quta yayi sannan yace ''tabbas kuma kema zaki shaida hakan, jiyake shigar kayan dutta wani irin takurawa rayuwar sa dan qagare yake ya isa gidan nasu ya cire kayan ya canza su zuwa qananan kayan daya saba dasu, qara kallon kayan yayi yanda suka kwanta cikin jikinsa sunyi kyau sun karb'i kalan fatarsa,,,, shifa dud yayi hakan ne danya farantawa iyayen sa rai in sun gansa da kayan suga ainahin sa na angon dudda babu babban rigar qin daukota yayi gida musamman dayake sunsan ba cika tu'ammali yayi dasu ba, shiyasa ya d'auko su dazai futo daga gida tun ranar,
yana wannan tunanin ne har ya isa gamji din ya kashe motar ya fito babu hulan a kansa kwantacciyar sumar kansa banda sheqi babu abinda takeyi hakama lafiyayeen sajensa na fuskarsa kamar ka laso sa kwance lam6as dashi,
fuskar nan tasa ya qara daurewa ganin yanda 'yan matan wajen ke qoqarin dosarsa dan babu wacce bata daukantu da tsananin kyaun handsome guy din mai zallar kyau masani ne shi ga kowa kuwa tun daga cikin garin dama kewayensa, kuma d'an multi bilonoir shima kuma kansa multibilonier ne wato mahabeer mua'zzam saraki, sam ko kallo babu wacce ta ishe sa ma a garesu bare yabita dashi a wajen, dudda wani irin karairayar da sukeyi ata gefensa insun zo giftawa shikuwa ko a jikinsa ganin ma ya duba ne baiga su bash dinba ya fara qoqarin tura Bluetooth dinsa a kunne ya kirasa, nan bash ya kwatanta masa inda suke sai gashi kuwa awajen yana tafiya yana shan qamshin sa harda guzurun dark space dinsa ga fuska ganin idanun matan nan sun gaza barinsa ya sarara.
bash na ganinsa kuwa ya miqe da sauri yana fad'in "wuuuu kags cheif groom namu expensive ga kowace mace, kasha kyau fa abunka kanata fesa ruwan qamshi, hararsa mahabeer yayi tareda kyab'e lips dinsa sannan ya zauna Shima bash ya zauna daga tashin da yai yana sakar masa dariya.
mahabeer yace
"gani tom saika ida maganganun kako, harararsa bash yayi yace "nooo ai kuma it's pass na gama ni ai, inda dai kuma ka rigaya daka tsula mana tsiyarka bashi kenan ba, share zancen mahabeer bayan ya qara yamutsa fuskarsa sannan yace ina mukhtar dinne? juyawa bash yayi ya nuna masa motar mukhtar din yace "hm yana ciki,
ganin fitowar wata qatuwar budurwa sukayi cikin motar mukhtar din tana gyara zip din gaban rigarta k kunya bbu, tazo ta wuce tana karairaya ta gefensu mahabeer din,
zuwa can kuma saiga shi mukhtar din shima ya fito daga motar tasa, cikin tsananin takaici da qyamatar abin daga mahabeer har bash suka dauke kansu sunawa mukhtar fatan shiriya.
mukhtar na qarasowa kuwa da tabarsa cikin baki yana shanta ganin mahabeer da yayi yass yaji wani irin sabon tsanar sa ya durar masa a zuciya.
danshi tunda bash ya gaya masa batun auren sa da yarinyar nan wacce ya qwallafawa ransa ita ta gidansu da kuma son samunta gamida muradin d'andanar nata kalar zumar itama sai kuma gashi mahabeer yai masa katsalanda mafarin knn yaji ya tsani mahabeer tsana kuwa bata wasa ba, kuma har yanzun yanada burin indai ya samu dama tofa saiya dama tan dan ganin ummu hani ta dawo hannunsa ta kuma zama mallakin sa ta har abada dan more rayuwar sa da kyakkyawar durarran surarta daga fuska zuwa jikinta!!!
amman kuma dayake mukhtar cikakken tataccen d'an duniya ne saiya basar da abinda ke cikin zuciyar tasa ya zauna yana kallon mahabeer da wani irin Murmushi yace..."
*Xexen Fasaha*
f.o.w.
[10/11, 2:48 PM] Xainab Documen: πππ
*MAHABEER*!!!
πππ
Story and writing
by
Xayyneb π€π€
πππππ
Fasaha online writers f. o. w.
*π³impacting valuable knowledge and Entertainment is our concernπ³*.
πππππ
π
Ώ4β£2β£
πππ
"gifted ango gifted ango kasha qamshi kafara kwasar garar amarya knn kaketa qyallin goshi haka? kayi fiyau ka qara kyau dud sirrin abinne halan?,,, wata kalar kallon mahabeer ya sakar masa yace
"dan iska kawai namamajo"
saidai kwata kwata mukhtar bai damu ba dangane da fadar hakan da mahabeer yy saima dariya da yayi yace "yess indai kan mata ne kirani hakan koma fiyeda hkn, kuma kacemun komi bazan damuba wlh kuwa gifted π€·πΎββ
domin mata sune babban ginshiqin dud wani asalin jin dad'i na duniya,, tsoki mahabeer yasake yi ya miqe tsaye yana duban agogon hannunsa ya dubi bash tareda basa hannu yace "bash ni zan wuce dady nason gani na yanzun, anman zamu had'u dakai anjima" bash yace "ok babu damuwa ango mijin amarya afa gaishe mun da buzuwar amaryar tamu fa sosai ango,, wani takaici ne ya tasowa mahabeer ko kallon bash ma bai sake yiba ya isa ga motarsa yabata wuta yabar wajen, mukhatar yadubi bash sosai yace "wlh bash naji baqin ciki sosai da wannan guy din ya samfemin yarinyar nan ya aureta,, dubnsa bash yayi sosai a mamakance yace "miye haka kake fad'a kuma mukhtar gameda mahabeer?,
dame fuskar sa mukhtar yayi yace "yes abinda ke zuciyata ne na fada ay, girgiza kai bash yayi yace "koma dai miye wlh kuwa yaci ace irin halaccin da mahabeer yai maka ba gori ba har ya dauki abota dakai ta gaskia da gaskia dudda yasan mu din bawai iyayenmu kudi ne dasu ba saidai rufin asirin Allah haka muka taso muna tare tun a school har gashi muka kai ga yanzu ka gama karatunka ka gagara samun aiki shida kansa ya damqa maka jagoran cin babban gidan mansa har kake fantamawarka yanzun da 'yan iskan mata son ranka ka kuma hau dud irin motar da kakeso dud ta dalilinsa amman shine yanzu zakana kwaye masa kuma? girgiza kai bash yayi yace "hakafa kwanaki ka lumar masa da kud'ade maqudai wajen bishasharka da yan matan banzan ka amman inajin tunda yai maka maganar nan sau daya naka gyara bai qara tada zancen ba, wanda wlh nasani kuma kaima nasan kasani dawani ne kaiwa hakan wallahi saiya daureka kuma saika biyasa sannan daga baya kuma kuzo kuyi baran baran, amman shine yanzu dan butulci irin na mutumin yau kake son kwaye masa baya akan matar da Allah ya qaddara tasa ce bakai ba?, kaima inda Allah ya baka qaddarar ka ta matarka ba shiknn an zauna lpia ba kuma falillahil hamdu? , cikin bacin rai mukhtar ya d'agawa bash din hannunsa yace "waitt mlm kada fa kai mun gori akan abinda bakai kai munba dan naga kanata wani zaqalqalewa haka sosai wanda koshi mai abin bai gayan maganar data b'atan rai ba sai kai, dan haka wlh bnson ka daina, miqewa tsaye bash yayi yace"kwata kwata kayi hating din a fad'an maka gskia a rayuwarka mukhtar why why??
amman inda haka kakeso katafi can da halinka zakai danasani nason zuciya irin naka wata rana wallhi"!
yana gama fadan hakan kuwa ya tsallake sa yabar wajen.
mukhtar ya bisa da wani mugun kallo yana sakin wani tsoki ya koma yayi zamansa yana cigaba da shan tabarsa yana faman qara bad'e hayaqin ta a sama.
mahabeer yana tuqi amman zuciyarsa naga tunanin tayaya zamansu zai kasance waima dai tukunna da wannan yarinyar ne a London kuwa?
wani malalacin tsoki ya saki a haka harya isa farfajiyar gidan nasu ya kashe motar ya fito kai tsaye ya shiga falon gidan ya taras da annah ce zaune sai ummu hani tana qara tusa mata jan lallen ta na q'afa, da yake kan wani ya fita take tusa wani ita annah din,
annah akwai son qunshi kam sosai.
wani sabon haushin ne yaji ya qara durar masa na ganin yarinyar da yayi zaune a wajen, wani boyayyen tsoki yaja ya nufu inda suke ya zauna daga gefen annah yace "matas barka da gida ykk? hahararsa annah tayi tace ''ah d'an gudun hijira ne yau kuma a gidan namu kaga dama ka dawo gidan knn? ya bude baki zaiyi magana knn yaji muryan momy umaimah ta bayansa tace "ah mahabeer na har ka dawo sannu ya hanya, murmushi ya saki ya tashi yaje ya rungume hannayen momyn nasa yabasu sumba cikin lallausan kwantaccen murmushin sa yace "eh momy saukana ma knn momy amman kin san mi ma kuwa ke faruwa yanzun?
yayi tambayar kai a langwab'e yana shafa cikinsa a Marairaice, murmushi tayi tace "hmm daga gani kanaji yunwa ne?
"yess momyna wlh momy na wani irin yunwa nikeji dan rabon dana samu isasshen abinci na kwana biyu,,
daga can annah tace "inda wani ne ya hanaka zama kaci abuncin ai sai ka zauna ta ciyar dakai inda kun saba daman ku turawa ay, turo red lips din bakinsa yayi masu kyau yadan sake shafa kwantaccen sumarsa ya dubi annsh yace
"ohh my god!!!!
i thanks our lord... ni wlh tshohuwar nan nagaji da shisshige mun nan da kike fa, zan miki saki ashirin fa in baki yi wasa ba kinbini a hankuls ba, yayi maganar tasa yana boye murmushin dake son kubuce masa yayi saurin had'e fuskarsa ganin sunyi ido biyu da yarinyar, nan da nan kuwa sukabi juna da harara a b'oye.
"to ni ina ruwana kayiman saki ma saba'en da bakwai ma in ka tashi" cewar annah din,, murmushi ya dan sake yi yace "na dawo daga tafiya ko sannu da hnya baki munba amman kinzo kina cika mun kunne da kalar naki kwankwamin tsufan,, annah ta zaburo tace "anqi ai maka sannu din wayasa ka tafiyar ne? kokuma da zaka tafi ka fad'a mana em? danfa mugun hali irin naka yaron nan karasa za6a66en lokaci na q'irqirar tafiyar naka sai ana tsaka dayin bikinka fa kayita?, suda yake iyayen kane ai ka fad'a musu tafiyan ni kuma kakarka ta qauye aika rainani qauye dai shine tushen kowa ah to,,
jin maganar da annah tayi yasa ummu hani ta tab'e lips dinta ko kallon sa batai ba kuma, sarai kuwa shidin mahabeer ya lura da hakan sai dai wata 'yar quta daya saki shima na zaki gane kurenki ne yarinya soon.
momy umaimah tace "waiii afuwan annah muma sai yau dinnan muka san baima garin na shiga zan fad'a miki kema kuma na kuma taras da kina nafilfilun sallolin ki shiyasa na fito, tayi maganar cikin yar dariya.
annah tace ''ba wani nan yimun shuru umaimatu kema, ai kunsaba goyon bayansa daman" mahabeer yajawo hannun momyn nasa yace zomuje kicthen momy kibani abuncin nan naci ki qyale rud'addiyar tsohuwar nan dan wlh yunwar nn da gaske takemun ina jinta, dan na lura yau annah tsufan rigimarta ne ya motso mata, kunnuwana mani har zasu toshe,
annah tace "eh ba sai ka kullen bakin nawa ba ja'irin yaro,, muryar dady mua'zzam yaji daga bayansa yana fad'in "a'a sojana inajinka fa tun shigowarka kaketa samun annah ta hayaniya kada ka gajiyar mun da itafa,,, murmushi sukayi dukkansu yace ''dady itace ay, canza maganar dady mua'zzam yayi ta hanyar miqawa mahabeer hannu suka tamqe hannayen juna suka girgiza as usually sannan dady mua'zzam yace
"ka koma ango sak shigar tai maka kyau fa sosai sojana... masha AllAh haka akeso aga cikakken mutun magidanci mai kamala"
tabe bakinta annah tayi tace "ango babu babbar riga aiba ango bane saidai a kirasa da sunan angulu,
dariya dady mua'zzam yasaka shida momy umaimah dan maganar annah ba qaramin dariyar ta basu ba sosai kuwa.
shikuwa ogan gimtse fuskarsa yayi ko murmushi.
dayake mahabeer dazai fito a motar lokacin dayazo gidan ya bude baya ya fuddo hularsa ya sanya ta akai, to ganin zaman hular baiba yasa momy umaimah ta matso tana gyara masa zamanta bayan ta gama tace "yawwa kaganka ka qara haskawa ai mahabeer na,
dan murmushin qarfin hali yayi ya dubi inda dady mua'zzam yakoma yai zauniyar sa yabude daily trust yana dubawa da farin glass din idanunsa,
kama hannuwan momyn nasa yasakeyi yahada sa da goshinsa yace "tanxx momy na,, kama hab'a annah tayi tana kallonsu tace ''o'h 'o'h ni iyayen zamani kuda kanku kuke sake tabarar da yarenku? Murmushi momy umaimah tayi mahabeer kuwa yace kai annah rigima kullum muka hadu saikin sani doguwar maganar daban shirya yiba,, dai dai nan ummu hani ta gama sanyawa annah lallen annah tace
"ah ummu hani harkin gama sawa ashe? to sannunki Allah shiyi albarka, cikin sanyayyen murmushin ta tace "aminn annah bari naje nai wanka,
to 'yar kirki sai kin fito din, ta gefensa ta rab'asa ta wuce suna aikawa juna wani irin kallo wanda su kad'ai ne suka san ma'anar sa.
ahaka harta shige d'akinta ta shiga toilet tayo wanka ta futo ta shirya kanta cikin riga da sikert na jar super ta atamfa tayi kyau sosai cikin kayan hausa fulani kamar an zanata dan kyan datayi cikin atamfar dan qirjin nan nata sunsake cika fam fam dasu kamar tana shan maganin su,
zama tayi ta dauko wani farin abu ta had'a da