Showing 114001 words to 117000 words out of 130351 words
ya fuce daga office din dan sam baison yayi wani reaction wanda zaisa mahabeer ya fahimci wani abu koda kad'an ne daga tsarin planing dunsa a kan mukhtar din,
yana fita ya daga wayar yace "yadai friend shuru fa har yanzun baka dawo ba?
daga can bangaren daya mukhtar yace "ka zanzameni ay bash, kusan kullum saika bugo kaji na dawo koko na rasa wace muhimmuyar magana ce wannan haka da kake cewa zamuyi?, dan wlh har kasa hankalina ya fara tashi,
yar dariya bash yayi aransa yace hmm maci amana tukun na dai ka dawo,, amman sannan afili yace "kai banza ne wlh kafiye tsoro, just labarin nan nasan inka jisa zakaji dadinsa wlh shiyasa kaga na dameka ay, Allah kuwa bash? Cewar mukhtar din,, sosaima kuwa inji bash,, mukhtar yace "hmm to indai ko hakane gobe goben nan zan dura a gari,, "daka kyauta kuwa" cewar bash, a haka suka gama wayar yadawo office din mahabeer ya zauna yana yar waqarsa ta music cikin jin dad'i ,, d'agowa da kansa mahabeer yayi sannan yad'an tab'e red lips d'insa yameda kansa yaci gaba da danne dannen laptop dinsa sai daga bisani yace "hala zance kaje ma kayi?
sakin dariya bash yayi sannan yace "to ainima gwara dai na motsa koko? harara mahabeer ya sakar masa baice komiba yaci gaba da abunda yakeyi,, matsowa bash yayi sannan yace "towai gifted ya kake ganin za'a shawo kan al'amarin na mukhtar knn
dan iska ne guy din nan?
wlh it's mean kaga ya sake maimaita abinda ya faru kwanaki ko?
dago da kansa mahabeer yayi yace "mubar maganar saiya dawo sannan inji komi free dan nagaji da iskancin mukhtar wlh bash dud kudinsa wajen matan bariki suke q'arewa d'an iskan" ajiyar zuciya bash ya sauke yace dadai yafi kam,, dubn bash mahabeer ya danyi sannan yace "yau bakaje kasuwa bane? (dayake bash d'an kasuwa ne shi a central market yake, shagunansa na atamfofi da kuma su lesuka da materials da sauran yaduka nn suke, kuma yanada yara masu zama shagon shiyasa ma yake fitowarsa shaqa tawa dud lokacin daya so)
dubn mahaber yayi shima yace "no bnjeba tukun yanzun dai nike tunanin zuwa inna tashi daga nan, shiru mahaber yayi bnda tunanin ummu babu abinda yafi addabar zuciyarsa a yanzun, sarai bash na kula da hakan,,,,, a zuciyarsa kuwa cewa yayi ka share hawayen ka gifted dud sanda mukhtar yadawo garin nan gskia zata bayyana insha Allah wanan alqawali nane.
sai da lokacin tashin mahabeer office yayi sannan suka fito shida bash din kowa ya wuce motarsa ya tafi byn sunyi sallama, mahabeer yana yin parking motarsa farfajiyan gidansu kai tsaye ya dauko briefcase dinsa ya shigo falon yaga babu kowa sai baby manal tana barci, har gabnta yaje ya duqa tareda bata sumba a goshinta ya haura sama zuwa dakinsa ya ajiye kayan jikinsa ya shiga wanka ya fito ya shirya kansa cikin farar riga da wani farin jeans sannan ya kawo wata baqar riga mai kama da yar coat mai dogayen hannu wacce iyakar kuwa tsawon ta zuwa belt din jeans dinsa ne, nad'e hannayen baqan rigan yayi, ahakan ba qaramin kyau yayi ba dudda yayi 'yar rama kuwa shima, jin alamun yunwa ya sashi saukowa qasa ya isa dining table ya zauna yafara bude culars ganin danbun shunkafa ne da miyan kifi sai tashin qamshi yake nanfa ya zuba da yawa yaci sosai.
sadda ya gama yaje dakinsa yasake wanko bakinsa da burush sannan ya dawo qasan falon, amn ga mamakinsa saiyaga baby manal bata falon bisaga d'azun, dakin momy ya shiga ganin bata nan ya tuna dasafe suntafi katsina yin gaisuwa itada dady dan shiya zata ma kosun dawo ne, dudda ba kulasa momy keba da dady amman qa'ida ne kullum saiyaje ya gaishesu kosu amsa koko su qyalesa sai yaje shikam.
d'akin annah ya murd'a zai shiga knn yaji muryan annah tace "o'o ni ummu har yanzum taje ta shige madafi kamar mai dafa duniya tabarni da wann rigimammiyar yarinyar?, jiyayi alamun tataso zata fito yayi saurin lafewa cikin labulayen jikin bangon wajen dai dai lokacin annah ta fito ta tsaya bakin kitchen yaji tace "wai ummu shin har yanzun baki gama kayan kwadayin nan naki bane kin fito kicen din nan kuwa? daga kichen yajiyo siririyar sanyayyen muryar ummu hani tana cewa "nakusan magawa ay annah saura kad'an ma na qarasa,, "to kiyi kiyi sauri ga manal nan ta tashi kada ta ankara baki nn ta fara mana wannan sababben kukan nata"
"to annah"
daga haka annah takoma cikin dakinta ta rufo, fitowa yayi kai tsaye kichen din ya nufa ya hangota tagama tsame dan wakenta ta yanyanka masa cucumber da tumatir da albasa da qwai dafaffe tana ci daga gaban kujera tana zaune ta harde qafafunta sai ci take tana faman shhhhh alamun yaji,, yana hangota daga inda yaja ya tsaya, sam itako bata sanma yana wajen ba harta gama yaga ta a jiye plate din a sink ta wanke sa tareda goge bakinta,
sannan yaga ta bude fridge ta dauko holandia yugurt mai sanyi ta bude bakinta ta fara sha tareda lumshe idanunta, da sauri kuma yaga ta ajiye robar yoghurt d'in tana firfita harshen ta da hannunta ga alamun dai zafin tasshin nanan bai bar taba,,gani yayi tanata tsinano baki tareda yamutsa fuskarta yaji tace
"wushhhh-eshhhhhh zafin tasshin nan yawa ne dashi ni ummu hani, mtss gashi ya hana mani samun nutsuwa na, saurin juyawa tayi ta dafa sink din da hannayenta bibbiyu tana tattaro yawu tana tofarwa a tissues paper kamar tai kuka, hakanma bai isheta ba saida taita watsawa fuskarta ruwa,
babu zato taji anyi mata runfa saman bayanta, da sauri tabar abinda takeyi tayi saurin juyowa aiko tayi karo da mahabeer ya matse hanyar babu gaf kwata kwata a tsakaninsu, idanuwansa kawai ya zuba mata farare tass dasu,, da sauri kuwa ta janye idanunta cikin nasa tana b'abbata rai ta had'e fuskarta sosai take watsa masa harara tace "miye haka malam?
plsss excuse me zan wuce bani hanya, gani tayi sai qara matsota yakeyi tareda turo mata harshen sa daya fuddo cikin bakunsa ya nufo nata dashi,, dasauri tayi qasa ta kucce masa zata bar kitchen din kenan taji ya wani damq'ota, cancakat ya d'goata sama ya d'orata a bisa wata 'yar durowa ta cikin kichen din ya azata ya zaunar kamar wata 'yar baby dl,
da sauri ta zamo qasa tana banka masa harara tareda yamutsa fuskarta, cakk ba qara 6ata lokaci ya kuwa qara subgumar tata ya maida bisa, yana binta da lumsassun idanunsa,
cikin tsiwa tace
"wai miye haka nifa yanzun ba matarka bace mlm ehe dan kabarma qoqarin wani tab'ani saboda inka ta6ani wlh wuta bal bal ka tab'aπ,, shi abinma dariya ta basa data fad'i hakan wai wuta bal bal? shiyasa kawai yayi wani qaqqarfan murmushi yace "temaka miki zanyi fa kidaina mun yanga feader na, hararasa ta qarayi snn tace "ban gane temako na ba nami? matso da fuskarsa yayi setin tata a hankali yace "kinje kin wani sha wa kanji papper kina wani shihhhh ko?
to oya sucking my tongue kinsan sweet tongue ne dani zakiji komi normal har kin nemi papper a bakinki kin rasa, cikin tsiwa tace "allah sawaqa in hada baki da maqiyi na wanda bai sona, da d'inma dakaga na qyaleka kanamun yanda kakeso a jikina inaga asiri kai mun ne ma tayi maganar kamar zata fashe masa da kuka, qyalqyacewa da dariya kawai yake famanyi wa mgnr tata, sannan kuma daga bisani taga yawani d'an danyen ce fuskarsa ya dubeta lokacin sosai yace
"hmm eh man ai nai miki asirin sona da qaunata a cikin zuciyarki tuntuni ashe ke baki sani ba feader na?
murgud'a masa baki ta sakeyi da sauri kuma ta sake sakin wani "shissss papper din tana fad'in tasshi dahar yanzun ke damunta, dudda hakan datakeji amman a tsiwace ta dubesa "tace allah sawaqa mun naso wnda bayya sona nikam,, yar iskar sanyayya dake bakinsa ya furzar ya dubeta sosai wai yarinyar dayakeji babu wani waje da ke jikinsa tsoka da b'argo inda sonta bai ratsasa ba amman shine ynzun take titsiyesa tace bai sonta kuma?
koda yake inyai la'akari da yarintar ummu ba lallai bane ta gane soba saidai ace mata kai tsaye ina sonki wance har raina??
to a'a Shikam irin wannan soyayyar tazama tsohon yayi a garesa, ita tasa a aikace zaiyi abunsa cikin wayau da dabara yanda sannu a hankali zakasan ma'anar sonka garesa,
balle ummu daya lura saida wayau da dabara ake samun kanta nan da nan, murmushi yasajeyi ya dubeta sosai a cikin idanunsa yace "kinga albarkacin son da naga kina muni shiyasa nima na d'an fara jin wani reaction tare dake bansani ba ko ni ma ina sonki ne oho?, yayi maganar cikin ta6e red lips dunsa yana wani yamutsa fuska tareda d'age shoulder nasa, dauke fuskarta tayi daga garesa ta sake durowa qasa dan jitake bazata iya jure kallon cikin qwayar idanunsa ba jitakeyi kamar wata magana d'isu ce a cikinsu mau hana mutane yi masa musu a garesa dud in sun so a amince masa tofa idanunsa kayi kad'an kace zaka bijire masa kuwa inhar ya ka yadda kuwa ya ritsaka dasu,
tana cen tana tunanin hakan kuwa babu zato bare tsammani sai dai taji saukar tafukan hannayensa bisa (manyan breast feeding nata) wato magunguna sa, aikuwa a razane ta durqushe qasa
nan tasaki qara 'yar siriya dan kawai ya bata hnyar guduwa amman yaqi, dai dai nan ne sukaji muryan annah da kukan baby manal, annah tace
"wai ummu kwana zakayi a kitchen din nan ne har yarinyar nan ta fara kuka?
ai da gudu ummu hani tabar kitchen din cikin wata matsananciyar kunya jin yana cewa saita tsaya ta basa magungunan nasa yasha,,
yana ganin ta fice dagudu hkn tasa shi sakin wni murmushi ya tsurawa tafukan hannayen nasa idanuwa still yakejin gizon tsabar wani kalar taushin magungunan nasa sosai har ma kamar yanzune yakejin ya tab'a su a hannun nasa,
aiko gaba d'aya yaji jikinsa ya canza da sauri shima ya fice kichen din ya nufo falo ya taradda annah nata fad'a wa ummu yayinda take miqa mata manal, ita kuwa baby manal tana ganin ta nan ta hau murnar ganun ummu din ,,
har annah zata juya ciki ganin fitowar mahabeer kichen shi yasa ta sakin baki galala cikin mamaki saita dubesa ta kuma dubi ummu wacce takejin kamar qasa zata tsage ta shige ciki ta 6uya dan tsabar kunyar daya sata taji,
shikuwa mahabeer ko a jikinsa acikin ma basarwa ya fauze ya fice waje,, daq'yar annah ta samu ta dube ummu tace "au ashe daman kuna tare kuka maidani tsohuwar kakarku kuna jina kunyi bulum dan tsabar shegantaka irinta yaran yau?? kasa magana ummu tayi da sauri ta shige dakin Momy umaima danta hadawa baby manal madarar tea dinta, da kallo annah ta bita ta riqe hab'arta ta da hannu tace "ikon Allah, to Allah sawaqa muku bari kuma su yayen naku su dawo suma su sameni saidai asan biri asan gata, dan babu yadda za'ayi yara baligai ku dunga yin wnn rayuwa hka kurkusa irinta ma'auratan gsken alhalin kuwa basu bane a yanzun, to nikm sam sam dai bazan juri iriyar kallon wannan shashancin naku ba a gidan nan gskia .
ahaka ta shige d'akinta tana faman cigaba da fadan ta,,,.....
(Hmm annah knn. )
*Xexen Fasaha*
f. o. w.
[10/11, 2:49 PM] Xainab Documen: πππ
*MAHABEER*!!!
πππ
Story and writing
by
Xayyneb π€π€
πππππ
Fasaha online writers f. o. w.
*π³impacting valuable knowledge and Entertainment is our concernπ³*.
πππππ
π
Ώ5β£3β£
πππ
Saida ummu hani ta samu baby manal tai barci sannan ta lallab'a ta kwantar da ita bisa kan dan gadonta sannan ta shafa mata addu'a ta shiga toilet tayo wanka tareda dauro alwala, tana futowa tayi shirin sallar magrib koda ta idar tana nan zaune saida aka yi isha'e ta jima tana adduar allah ya sadata da dukkan abunda yafi zama alheri a cikin rayuwar ta gaba day'a, a hankali ta miqe tsaye ta nunke sallayar da hijab d'in da tayi sallar,
mai kawai ta murza ta d'auko wasu riga da wando masu sulbi ta sanya ta zauna gefen gado ta had'a wani tagumin, tunani takefa ace yanzun in tagama iddar ta gskia zata lallaba su dady su barta ta koma can qasar su ta Niger taci gaba da rayuwa ciki fami (familys) nata kota samu nutsuwarta data rasa ta dawo,, lumshe idanuwan ta tayi a zuciyarta kuma sai taji sam babu dad'i datace zata tafi tabar gidan shin miyasa taji hakan?
wata zuciyar tace kada ki damu knki ummu Allah yasa daman can baki fara son mahabeer ba bare rashin sa yasaki damuwa,, lumshe idanuwa tayi sosai tunowa da iriyar kulawar da ya dunga bata a can London gabda faruwar hakan takeyi ,,
jitayi gabanta ya fad'i data tuna da lalurar ciwon sa, koya warke ne ma? ta tambayi zuciyar ta, zuwa can ta tabe pink lips dinta tace
"to ni inama ruwana dashi da zan zauna haka in dinga wani tunanin sa? mtssss taja tsoki,
jin tunanin nasa dai yaqi barinta hakan yasata yin saurin toshe kunnenta da hannayen ta biyu na yatsu amman dudda hakan har ila yau muryarsa gizau take mata dai dai inta tuno da inda yake cewa samun lpiar ciwonsa to shine kula da shan magungunan data fara basa nata kamar ynda doctor yace ai masa din,
da sauri kuwa ta miqe tsaye tabar dakin kota samu ta yakice tunanin abun daga ranta wanda inta tunano irin lokuttan su na baya shi da ita na yar rayuwar su ta auratayya da sukayi sai taji har wani yarrrrr tsikar jikinta ke mata wani iriyar tashi dashi,,
kwata kwata batta son tunowa da irin lokuttan da suke kasancewa da mahabeer sabida inta yarda ta xurfafa tunanun nata tofa nan take takejin sake buqatuwar mijin nata a da,,
mafarin knn da taga ta fara tunanin yanzun ma shiyasa tabar dakin.
kai tsaye dakin annah ta tafi tana shiga ta isketa harta kwanta,
zama tayi gefen bed din tace ''annah nazo tayaki fira nr naga kuma har kin kwanta da wuri haka?
annah tace "eh ni kyaleni shashashan yarinya kawai miji ya sakeki amman kike yarda dashi? cikin wata iriyar Marairaice wa tace
"laaaa wlh annah ba haka bane,, hararar ta annah ta sakeyi tace "kudai kuka sani ay ni jeki ki barni barci nikeji bazan qara biye miki nayi wannan doguwar firar ba kisa na kasa tashi sallar dare,, turo dan bakinta tayi tace "kai annah please to muyi firar ko babu yawa ne,,, annah tace "kije falo kiyi kallonki du Allah ki qyaleni haka ummu, cikin shagwabe fuska ummu hani ta miqe tsaye tace "shiknn natafi annah inda kin kore ni yau nima bari naje nai barci na,, annah ta dan dago kai daga lullu6inta tace "ato dadai yafi yemiki,
falo ta dawo ta zauna ita kadai tana ta lallatsa wayarta saiga kiran nabeela ya shigo d'gawa tayi cikin muryarta tace "hello sister nabee, nabeela tace "how your night sister?
"fine sister"
cewar ummu,
daga cen nabeela tace "kai naji dad'i danaji muryanki ya sauko yanzun ba kamar lokuttan baya ba, dan Allah qawata ki daina damuwa akan abun nan danni ni inaji a jikina wlh kuwa bai shine yayi sakin ba insha Allah gskia zata bayyana ku koma zamanku keda yaya mahabeer dan wlh ni ganinku nike dud duniyar nan baku dace da kowa ba face junanku,,
tsoki ummu hani tayi tace "ke dakata nifa babu digon son amakson a cikin raina kima daina tunanun wai hakan, daga can nabeela tace "a'a wlh ban yarda ba ki kuma rantse da Allah babu 6ur6ushin sonsa a cikin zuciyarki ummu ko yayane?,
da sauri umnu tace "ca66 nikam bazan rantse ba ga gskia ga kuma rantsuwa? dariya nabeela kawai ke mata tace "wlh kuwa sister da ace bakison yaya mahabeer sam bazakiyi kishin sera ba kamar ynda kika ban labari ta furta miki tana sonsa, sannan kuma daba zaki damu kiyi kuka kuka na sosai ba a lokacin da akace ya sakeki koko zaki musaman ma wannan?
tsoki ummu hani tasakeyi tace "dallah mlm jeki naji saida safe surutun naki ya isheni barci zanyi,, tana gama fad'an hakan bata jira taji komi ma nabeela zata ceba ta kashe wayar ma dukanta, ta kwanta nan bisa 3 seater tareda lumshe idanunta,
nan zuciyarta ta hau dinga tariyo mata maganganun da nabeela tai mata akan cewa tana sonsa, to da gaske tana sonsa? tambayar dataiwa zyciyarta knn,,
turo baki tayi tace "to miye dan ma naji kishin sera?
ai ko baka son mutum indai mijinka ne ance zakaji haushin hakan, wata zuciyar tace to sanda su dady suke marinsa ranar miyasa kina kuka kika hanasu kikace baki son ganin hakan shima?
nanma da sauri ta miqe zaune takasa ba kanta wata qwaqqwaran hujja ma taqamaimai,
jin motsi da tayi a kujerar kusa da itane yasata qara waro idanuwan ta waje sosai, nan take gabanta taji yayi mata wata iriyar azababben faduwa ganinsa da tai kwance wajen ya zuba mata gaba day'a narkakkun boil eyes nasa, wayyo ni ummu kada dai ace yaji firar da mukayi da nabeela yanzun dan wlh phone d'ina qaran speaker ne dashi,, tabbas yanda yake kurkusa d'in nan dani nasan kam dole ma yaji inda dare ne babu motsin komi bare hayaniya ya hana yaji,,
gskia taji babu dadi kam, satar kallon agogon wayarta tayi taga 9 saura kwata na dare, cikin sanyin jiki ta miqe tsaye tayi kamar bata gansa ba tazo gittawa ta wajensa knn shiko ya fizgo hannunta sai kuwa gata ta fad'o saman faffadan qirjinsa ya maida hannunwan nasa ya zagaye bayanta dasu ruf,, mutsu mutsu kawai takeyi tana son qwatar kanta gunsa amman ina sam ta kasa,, dole ta nutsu cikin muryarta tace "karabu dani niba matarka bace bare kace zaka riqeni, cikin