Showing 75001 words to 78000 words out of 130351 words
girgiza kai ummu hani tayi tace uhmm to inba shi ba waye kike ganin zaimun haka ne? bama ki kalli lips dina ba knn kikaga yanda yaqara mayar mun dasu ja sosai ba? da sauri nabeela takai hannunta ga lips din nata tace "aikuwa wlh gashi nan har wani pink pink colour yamayar miki dasu kalar nasa kai wannan amarcin nakufa so matching,hararta ummu hani tayi tace "wlh inkika saki na tashi bazan qara zama ba,
rufe bakinta nabeela tayi tace sorry sister na, harararta ummu hani tasa keyi tareda jan wani d'an siririn tsoki,
wardruf nabeela ta bude ta fiddo wasu manya manyan baqaqen ledoji ta dawo saman gadon ta zazzage su dukknsu nan, tace "ga gudummuwata nan sister dan nasan kina son inglesh wears sosai shiyasa na karb'i kud'i wajen dady na isassu tun jiya da dare naje boutique na siyo miki su shine nike cewa zan miki surprise dasu ay".
cikin mamaki dajin dad'i ummu hani tace "kai sister thanks so much wlh amman wannan dud ni day'a basumin yawa ba? cikin murmushi nabeela tace "kinfi qarfin irin haka sau dubun dubbata a wajena sister, kuma basu miki yawa ba kamar yanda kika fad'a , murmushi ummu hani kawai takeyi tana d'aga kayan tace "kai sister kayan nan akwai a tsokani shari'a sosai a cikinsu fa? dan na gama kusan ma dud su sukafi yawa saikace wata wacce zatayi auren soyayya bare in rinqa yiwa hubbyn nawa kwalliya dasu? ,sai nikega irinsu dake yadace saiki dinga yiwa amrinin dinki gayu dasu, girgiza kai nabeela tayi tace
"a'a wlh sister bazan dauka ba dan nikena sawowa snn kuma inada tabbacin cewa zakiji dad'insu kuma zakiga amfaninsu nan gaba,
dan aunty sadiya qanwar momyna tace mu'amala da wad'an nan kayan suna qara jawo hankalin miji akan matarsa inda da sune matan waje har suke nasarar iya cin galaba akan mazanmu,sai nikuma nikega why to muda mike matansu mizai hana muyi fiyeda yanda su nawajen ke musu,?
yamutsa fuskarta ummu hani tayi tace "hmm sister na kenan inda ake soyayyar knn kiketa fad'a ai badai gani ba da wancen farin mugun,, bnda dariya kuwa babu abinda nabeela keyi tace "kai sister yanzu yah mahabeer d'in ne ya koma miki farin mugun knn, cikin tab'e lips tace "yess shifa da knsa sister bawani ba,tayi maganar tana mai mi miqewa tsaye.
murmushi kawai nabeela tayi tana yar dariya tace "hmm Allah kawo muku mafita mudai muna nan nijeria zamu sha labari daga gareku 'yan qasan turai,, tana maganar ne tana mayarda kayan cikin ledarsu.
banza ummu hani tayi mata harta gama suka fito ummu hani taiwa maman nabeela hjy asm'u sai anjima suka fito tareda nabeela saida sukazo bakin gate tabawa ummu hani kayan sannan tace "by sister zan shigo anjima"
a haka ta juya ta koma gida, ita kuma ta ida shiga cikin harabar gate d'in gidan, da sauri ta b'oye jikin wata bishiya maiyawa daga qasanta koriya ce shar, dan hango sa datayi shida bash zaune can wajen swimming pool inda suka saba zama, tarasa ta inda zatabi dole tadinga bin ta bayan bishiyan nan harta isa ga qofar shiga gidan dud abin nan kuwa datake bash na lura da ita tun shigowarta gate din gidan yaganta. murmushi kawai yayi a boye ya raya kuma a zuciyarsa da cewa dud yanda akai ta had'ota ne da mutumin nasa shiyasa take faman bo'yo batta son ya ganta.
ita kuwa tazo shiga falon gidan kenan ta jiyo shassheqan tashin kuka a falon gidan,
gabanta ya fadi sosai kuwa, d'an dakatawa tayi jin magana tayi ance "haba hjy umaimah dole hannat tayi kuka ai wlh, kinkuwa san irin son datakewa yaronki mahabeer a cikin zuciyarta? amman shine har kika iya amincewa aka basa wata banzar yarinyar buzuwa can dangin asiri?!" murmushi na mamaki momy umaimah tayi tace "dole na yarda kuwa hjy aina inda bani na had'a ba iyaye ne suka had'a kuma nima da yardata dan ummu hani yarinya ce tagari wacce kowace uwar miji tagari zatayi kwadayin ta zamo mallakin ta, hjy aina tace "aho wato mu mune surukn banza kenan kk nufi ko hjy umaimah? cewar hjy aina, momy umaimah tace "badai kiji hakan daga bakina ba kam sai dai inke kika dorawa kanki,, muryar annah taji ta fito tana cewa "waimi ke faruwa ne tun d'azun haka nikejin hayaniya da kuma koke koke,
Nan momy umaimah tayi mata bayanin komi nagameda kukan da hannat takeyi wa uwar tata tun a gida hatta sa uwar tata tafowa nan babu shiri.
jiyowa annah tayi tace "toke hjy aina antab'a sha'anin tursasawa haka? basai kibawa 'yar taki na annabawa ba(haquri) inda hukuncin an riga an zartar gameda kyakkyawan zab'in da a kaiwa yaro? du AllAh hayaniyar nan ta isheni kudaina haka musamman muryankin nan da kukan yarki wlh sun hanani saqat a daki ina hailala,, tana gama fadin haka tajiyo takun tafiyar annah ta koma dakinta.
jiyowa hjy aina tace "shiknn hjy umaimah ngd da abinda yafaru, tana fadin hakan kuwa ta jawo hannun hannat din da qarfi sukayo waje, rab'ewa tayi awajen tabasu waje harara hannat keta sakarwa ummu hani kamar idanunta zasu fado qasa tace "banza shegiya dangin ma'asurta.
da sauri ummu hani tace "kul wlh niba shegiya bace da ubana kan wani can adaina zagarmun iyaye, tayi maganar cikin gatsine fuskarta.
cikin masifa Hannat tace anzagi iyayen naki ko wata tsiya ce daku baccin ta asiri ne eye? cikin gatsine fuskarta ummu hani tasake cewa "oho dai naji kuma wannan, ngd Allah inda dai har banzo nayi kuka akan ba'asoni ba na zubda q'imata ta mace kamar yanda wata tayi ynzu, hjy aina ta jawo hannun yartata tace "nace kirabuda ita kizo mutafi ko? inda kin jawo mana abin fad'i ba shikenan ba hankalin ya kwanta ba 'yar banzar yarinya sai nacin tsiya uwa matar shugaban mayu na dudduniya haba har abin ma ya isheni wlh bagaira ba sabar kinsa na gayawa aminiyata magana "!!! Hannat kuwa sai turo baki take ta yiwa uwar har suka shige motarsu suka bar gidan.
da harara ummu hani tabi bayansu harta shige falon itama taga momy umaimah ce kawai, anan ta gwada mata kayan da nabeela ta siya mata momy umaimah ta yaba itama sosai nan sukaita fira abinsu sai daga bisani suka shiga kichen dan d'aura girki baby manal taba maqale jikin ummu hani taqi sauqa.
a can waje kuwa bash ya tsurawa leben mahabeer ido ganin yanda yayi tabon digon baqi dan siriri daga gefen le6en nasa yace "miya samu le6enka ne haka kuma gifted?
laso le6en nasa mahabeer yayi da halshensa yaja numfashi mai zafi ya furzar sannan ya shafa kwantacciyar sumar kansa yace "wafa ce bayaga hayatacciyar mage ta ta gidan nan"!!! kallon mamaki bash yakeyi masa yace "wacece kuma dai hayatacciyar kyanwar ka a gidan nan kuma wacce ban sani ba?
hararra mahabeer ya sakar masa yace "okey inda baka santa ba shiknn, basah yace ''okeeyyy naganeta kam yanzu,kawai kacemun amaryar mu ummu hani, ai wlh serous naji dad'in wannan kyakkyawar maja din da momy ta fad'a mun dazun wadda dady ya jagoranci hada maku kaida 'yar magen nan taka, shege mukhtar ma hot-storyn nan ya wucesa ay tunda nai nasa text ynxu na tura masa na gameda maganar shiru kkji dudda nakira layinsa yaqi shiga kuma.
Mahabeer yace "bansan iskanci fa bash wlh wannan bad story din kake yad'awa friend namu kuma?
Pleass naroqeki ka daina kada ka jawomin abin kunya danni wannan wlh abin kunya ne a gareni bako qarami ba"!!!! bash yace "idan har na daina fad'awa friends namu Allah yai mani albarka, tsoki mahabeer yaja kawai yaci gaba ma da type dinsa cikin laptop dinsa kota kansa bai qara bibama dudda yanajin yanda yake bugawa sauran friends dinsu batun auren wannan satin,
washe garin ranar kuwa masu tafiya dud sun gama shiryawa hadda su baban momy umaimah yazo daga katsina shida da amininsa baba sani dan zuwa neman auren mahaber a nijer din kamar yanda dady mua'zzam da annah suka shaida musu.
shatara ta arziqi haka dady mua'zzam da alhj Muhammad suka hadawa su baffa dan Shikam baffa kaddo harya rasa bakin godia sai sabuwan add'ua dayake tasake binsu dashi.
Mota biyu sukayi dady mua'zzam najan su momy umaimah da annah tareda ummu hani da nabeela, sai dayar motar dady Muhammad ne shima ke driving su momy ni'ima da baban momy umaimah da abokinsa, doguwar tafiya ce sukayi sosai wacce ta daukesu tsawon awowi sai wajen biyar sannan sukai isa cikin garin niger har cikin anguwarsu ummu hani wato darul islam, dai dai qofar gidan baffa indeh suka tsaya, dayake kusan jere gidajen su yake dana baffa kad'do,
dukknsu suka fito cikin motan ummu hani tana shaqar qamshin iskar garinsu Saidata murmusa sosai sukuwa su nabeela da sauran mutanen wajen sai kallon rayuwar da jama'ar garin sukeyi haka cikin Godiya Allah, baffa indeh ne yafito cikin gida da 'yar butarsa ga hannu kansa da nadi irin nasu na buzaye yana arba dasu baffa kad'do kuwa yasaki butar qasa yayo kansa ya riqesa gam nan sukaita murna ahaka baffa indeh yayi musu jagora zuwa cikin gidansa. qaton buzu maman nahee ta shimfida musu tana maraba lale dasu bintey da kad'do da sauran mutanen, dama shi baffa indeh ko zama basu kaiga yiba ya fice da sauri yaje ya farfadowa dangi kaddo ya dawo da matarsa da ummu hani saigasu ko sun shigo gidan dayawa sosai, nabeela tana ganin shigowar fararen buzayen nn q'idaga guda dasu yasata yiwa ummu hani rada da cewa "sister wannan taran al'umar da suka shigo suwaye,, murmushi ummu hani tayi tace *fami* *(family*)nane su duknsu wannan mai baqin nadin akai shine baffa indeh qanin baffa na wato baban qawata yar uwata nahee kamar yanda nake miki labarinsu nahee da sahee abokina na nan, nabeela tace to ina shi yaya baroma da kika bani labarin sa shima? girgiza kai Ummu hani tayi tace "bayya nan cikinsu shi.
maganar da baffa kad'do kewa yan uwansa ne na gameda jinkirin daya samu wajen dawowar dakuma dai sauran bayanai na abubuwan da suka biyo baya dudya fada musu, gaba dayansu sukaita godia gasu dady mua'zzam na irin taimakon dayaiwa dan uwansu da iyalinsa, baffa indeh yace "haqiqa hankulan mu sun tashi sosai gamida shirunku gashi na baka numba na waya na amman tsawon lokaci banji kiranka ya shigo gareni ba har akayi bikin nahee da qawarta watan daya wuce, amman yanzu Alhamdulilla inda kundawo lpia , babu bata lokaci dady Muhammad yashigar musuda nemawa dansu auren ummu hani, sunkuma fahimci har baffa kad'do shima yayi na'am suma kuwa babu bata lokaci suka amunce anan dady mua'zzam yake tambayarsu yaya al'adar su take ta sadaqi??? sai nan baffa indeh yayi gyaran murya yace al'adar mu bada kudi ake biyawa yara namu sadaq'i ba da raqumma ne, baffa kad'do yaso yace abar hakan amman babu yanda ya iya inda haka al'adarsu yake tun usuli.
nan dady Muhammad yace "to babu komi zuwa juma'a din wato ranar daurin aure in sunzo saisu bayarda kudin raqumman a siya, nan aka kaisu masauqi sukaita kai musu abubuwan ci kala kala irin nasu har zuwa washe gari, su dady mua'zzam suka wuce da nufin sai ranar daurin aure sannan.
nabeela kawai aka barwa ummu hani sukuma suka dauki hanyar komawa gida. Lokacin su baffa kad'do sun koma gidansu suma a ranar kuwa saida ummu hani tasa aka kaita har gidajen su nahee amare tagansu suma sukaita murna da ganinta, sai dare sannan suka dawo gida.
dud kullum kuwa sai ummu hani taraka nabeela ganin gari nasu datace yayi matuqar burgeta sai marece suke dawowa.
dady mua'zzam kuwa dud ya sanarwa yan uwa da abokanen arzuqa daurin aure.
yau takama juma'a su momy umaimah ne suka fara isa gidansu amarya saisu dady suka biyo su a baya shida d'umbin mutanen sa 'yan zuwa daurin aure,mota na bin mota sama da kasa qilguwa kuwa. anguwar darul islam ta dinke d'uf da 'yan d'aurin aure bnda manyan motoci nasu abokan su dady mua'zzam baka ganin komi a wajen daurin aure.
haka akataru aka daura aure lpia batareda ango ba, dan qaryar ciwon ciki yaiwa su dadyn harda lafewa kan bed kamar gaske, sai dai freands dinsa su bash da muktar da sauran abokanansu da iyayen.
jama'ar wajen sai Allah sa alheri sukewa su dady da baffa.
a can cikin gida kuwa cike yake da mata 'yan biki anata sanwace sanwace, kota ina ka gitta dangin amarya da ango ne ciccike awajen .
amarya ummu hani zaune cikin daki tasha adonta cikin kayansu na buzayen usuli na
al'adar auren su. baqaqene kayan masu adon zaruruwa a gaban rigar na ja da baqi da brown an mata nad'i akai na baqin gadonsu an saki jelar nadin ta kwanta gadon bayanta.
kanta yasha kitso gwanin sha'awa yasauko mata kuwa har saman dukiyar fulanin ta, nabeela ta gyara mata girarta ta sake fitowa 'yar zurut da ita baqa qirin gwanin burgewa, momy umaima tace "kai 'yata Masha Allah ahsanul khaliqin, kinga kyanki kuwa ummu hani na?, kigodewa Allah ummu hani na, barima na qara haskaki nima, tana fad'in haka ta zuge jikkarta ta fiddo wani sarqa da 'yan kunne na gold mai kyau da maqudan kudin gaske kuma, sabuwa ce dal ta siyawa ummu hani din dan irin wannan ranar daman, tana gama sanya mata kuwa tuni taqara haska amaryar kamar ka saceta ka gudu harsu nahee da sauran mutanen wajen saida sukayi santin kyawun ummu hani suma kallonta kawai sukeyi cikin sha'awa, gashi uwa uba tayi dace da uwar miji ta qwarai. Nabeela ta jawo hannun amarya ummu hani suka fita ta bayan gida wajen fili ne sosai harda qoramar ruwa daga nesa dasu can. babu mutane masu wucewa sai jifa jifa tazaro wayarta tace "dan Allah tsaya nai miki pic yanda kika sha kyaun nan inna d'orasa a media wa friends d'ina bnsan yaza suyiba in suka ganki, wooo Allah danice da kyawun nan naki sister wlh dasai na kwad'a yaya mahabeer son raina dashi,, nan da nan ummu hani ta daure fuska jin sunan amakson dinta da nabeela ke mata zancen sa, nabeela tace "sorry sister saki fuskar kiyi Murmushi kona sa miki kuka tayi maganar cikin marairaicewa wanda hakan yasa ummu hani kallon nabeela din tana sakin wani Murmushi wanda yayi matuqar qara haska kykkyawar farar fuskarta dai dai lokacin da baffa indeh yazo wajen yanadaga bayan ummu hani cikin shigarsa ta mnyan kaya masu ruwan zuma da baqin nad'insa akai ya juya fuskarsa gefen yana qwallawa nahee kira daga cikin gidan bikin a dai dai lokacin ne kuma nabeela ta dauki foton tabasu one plasher itada baffa indeh din. tadaka wani uban tsalle kuwa tace "wow kamar sarauniyar kyawawa wlh,,, gskia sai kin biya kudin ganin hoton nan sister kinga yanda kika haska cameran nan da kyakkyawan murmushun ki kuwa????? ....
*Xexen Fasaha*
f.o.w.
[10/11, 2:48 PM] Xainab Documen: πππ
*MAHABEER*!!!
πππ
Story and writing
by
Xayyneb π€π€
πππππ
Fasaha online writers f. o. w.
*π³imparting valuable knowledge and Entertainment is our concernπ³*.
πππππ
π
Ώ4β£1β£
πππ
A can kuma jama'ar gidan 'yan biki ne suka fad'awa nahee cewa ga baffanta can waje yana kiranta, sai gata kuwa ta fito da sauri nan.
tana zuwa tace ''gani baffa"
nan ya umarceta data kirawo masa innarta ciki da sauri ta koma tana fad'in "to baffa"
ummu hani kuwa na lura dashi tasha a wajen dud saita sha ma jinin jikinta dan tasan yanzun zai korasu, aikuwa jitayi yace "kukuma wane sakarcin ne ya fiddo waje yanzun?
maza ku koma ciki nace ko?, dasauri kuwa sukabi ta inda suka fito suka koma ciki, kamar jira ake su koma kuwa cikin gidan dan dama an fara neman amaryar,
nan aka kama amarya dud dangi suka rurrufeta sukaci gaba da yanda suke bukukuwansu.
har wajen azhur sannan mutanen su dady mua'zzam suka fara d'aukar wasu daga cikin 'yan kai amarya suka tafi,
kan la'asar sun miqi hanya dukkansu kuwa.
ummu hani a cikin mota ta duq'unqune kanta cikin sosai a cikin mayafinta sai kuka take sosai musamman ma inta tuno da nasihohin su baffa da mamarta gareta gameda zaman gidan miji ta tsorata sosai da irin yanda taji baffa yace "tabbas haqqin miji zai iya kai matarsa wuta muddin zatana bijera masa akan umarnin sa na halal, dan haka ki kiyaye 'yata ummu dan mijinki shine aljannarki in kin gyarata tayi kyau in kuma baki gyara ba to kiyi qoqarin gyara tan dan gobenki yayi kyau 'yata".
haka yaita mata nasihohi masu kashe jiki.
cikin motar kuwa
banda rarrashinta babu abinda momy umaimah da momy ni'ima da maman nabeela sukeyi amman kamar suna qara turata takeji dan gaba day'a kewar iyayenta take qaraji tana shiga jikinta, lallaikm rabuwa da iyaye ya zama dole ga d'iya mace, bayaga haka batajin akwai abinda zai iya rabata da momonta da baffan ta masu sata farin ciki,
haka sukaci gaba da tafiya basu isa kaduna ba sai wajajen sallar isha'e sannan suka dura lpia.
tun daga lokacin su momy ni'ima suketa kaikawo na faman yin d'awainiya da dangin amarya da 'yan katsina suma har tsawon kwana 2 sannan kowa ya koma gida cikin 19 ta arziqi na kayan biki aka bar amarya nan gidan surukanta tanata 6ul6ula kukanta na ganin dai abun da gaske ne inda gashi danginta ma sun koma abinsu gidan yayi tsit kamar yanda suke da lokacin kansu koma garinsu, amman gashi gidan shiru yanda kasan ba'a tab'a taron d'umbin jama'a ba a gidan,, ango mahabeer kuwa ganin su bash na niyyar takura masa sai anyi party yayi sulalewar sa hotel ya kama d'aki da komi a cikinsa enough yayi kwanci yarsa hankali kwance, dan gaba day'a ma wayoyinsa rufesu yayi, su bash ranar babu irin kiran da basuyi masa ba amman shiru take basu amsa dai.
yau kwanansa biyu a hotel wato tun lokacin da 'yan nijer suka kawo amaryar tasu shima a ranar yabar gidan yai masa hijira.
kwance yake ya mimmiqe samb'al bisa gado yana cin cheese idanunsa a lumshe suke dukknsu gashin idanunsa sun kwanto bisa kwarmin idanunsa, cikakku dasu masu kyau baqaqe ne sosai, zuciyar sa kece masa sam babu wani