Showing 51001 words to 54000 words out of 130351 words

Chapter 18 - MAHABEER Complete Document by Xayyneb.txt

Xayyneb   

29 Jan 2025

9956

leqa fuskarta yayi yaga baccinta take sadidan,,cikin dubara yayi mata wayau ta hanyar zame jikinsa daga nata a hankali harya kwantarda ita ya dauko mata mayafinta dake qasa sannan ya koma mazaunin direba bayan yarufe
qofifin motar ya had'a kansa da styarin na motar ya kwantar,, kwata kwata yarasa abinda ke damunsa a lokacin sakamakon wani irin daurewar da marar sa yaji tayi a lokaci day'a,, hannu yasa ya dafe wajen yana addu'a ahaka yakusan munti 13 sannan yaji ciwon marar ya lafa masa,, ruwa yasake sha sosai sosai sannan yayiwa a motar key, wannan Karon a hankali yake driving din nasa kamar wanda ya dauko crate crate na qwai cikin motan bai son ya fashe,,kai tsaye barau dikko hospital Suka miqa,,,,
Suna shiga yafito daga motan ya nufi inda ya hango doctor lurwan din tsaye wajen labour room shida wasu sisters,
shima doctor lurwan din yana hango mahabeer din yanufosa yaja ya tsaya,,,,cikin sauri mahaber ya isa
wajen a gurguje sukayi hannu da doctor lurwan din🀝🏻,a gaggauce yake fad'in "doctor nazo da patient ne amman bata iya takowa Tana cikon moto kwance,,
"Assha"! cewar doctor lurwan nan da nan yasa sistocin nan bin bayan mahabeer da dan keken daukan marassa lpia,, a lokacin harta farka dan haka shiya taimaka mata ta fito ya dorata a keken su kuma suka koma da ita cikin asubitin yana biye dasu batareda yasan dalilin bin nasu da yake ba,,
koda doctor lurwan
Yayi tozali da wacce bata lpian ashe ma ummu ce yayi mamaki sosai,, dubn mahabeer yayi tareda boye mamakin nasa yace "amm miya samu ummu hani ne hakn hakan yallabai????
wani irin kallo mahabeer yajefo masa ba shiri doctor lurwan ya ladaftan da harshensa yabawa sistocin umarnin shigar da ita dakin gwaji shima yabi bayansu,,
kamar ya rufesa da duka mahabeer yaji a fili yace "kaji dan iskan doctor ko gidan ubanwa ma yasan sunanta ma bare harya ambacesa??
tunowa da yayi sun zauna asibitin ne suma yasashi ta6e pinks din lips dinsa ya koma cikin mota yayi zamansa yana karkada qafa tareda touching din phone dinsa.
amman kuma bai san ya akayi tunanin halin daya da yarinyar ke ciki ba ya tsaya masa cak a qasan ransa...




*Xexen fasaha*
[10/11, 2:47 PM] Xainab Documen: 🌊🌊🌊


*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊
Story and writing
by
Xayyneb πŸ’€πŸ’€


🌊🌊🌊🌊🌊


Fasaha online writers f. o. w.


*In deducated to my mom Sadeeq (hawwas)*
🌊🌊🌊🌊🌊
πŸ…Ώ3⃣4⃣.
🌊🌊🌊
A can doctor lurwan kuwa duba ummu yayi ya rasa inda keda ciwon ma a jikin nata dan hankalin sa baima kai kan qafafun nata ba da suke kumbure, illa q'irjinta ta dayake ta satar kallo hakan ya ankarar da ita tayi saurin jawo gyalen ta ta rufe jikinta dukansa sannan ya umarceta data biyosa a baya,,
suka dawo babban office dinsa suka zauna ya dubeta sosai sann yace
"hm wato ummu kin tafi kin barni da dumbin tunaninki a cikin zuciya na yai mun qaqa gida ke ko a jikin ki ko?
kauda fuskarta tayi a hankali daga setin sa, babu abinda zuciyarta take jiwa tsana fiye da ciwon ma dake jikinta sama da mahabeer,, lallai rashin imaninsa yakai bada gudu ba ashe,,,
"haba ummu hani na ya inata miki magana zaki share masoyinki abin qaunarki em?
rage muryan sa yayi tayi qasa qasa yace "nifa wlh ina nan kan bakana gameda shawarar dana baki tun kwanakin baya na gameda yiwa mamanki aiki a kyauta muddin kika bani dad'in ni'ima irin taki na kwankwad'a"
yayi maganar yana kashe mata idanu da lashe gefen bakinsa irin na cikakkun 'yan duniyar nan,,
a haukace ummu hani ta juyo cikin tsananin takaici dama ga baqin cikin irin muguntar da mahabeer ya gama rad'ad'a mata bata gama shanyewa ba shi kuma yazo gaba ya tusata yana mata maganganun iskancinsa akai,
ai batareda ta san lokacin data d'aga hannunta ta wani yarfawa doctor lurwan wani qwaqqwaran maruka biyu ras bisa kumatukansa masu rai da lpia kuwa, cikin kuka take fad'i
"d'an iskan likita kawai ka matsawa rayuwata?? Mina tsare maka ne? Wai ku dud maza haka kuke ne bakuda imani ne?? koni kaga alamun irin kace watsattsiya?? dazaka tusani gaba da munanan kalamnka wanda badon shi aka kawoni cikin asibitin nan taku ba,??
cikin tsabar takaici tayi shiru ta dafe kanta sannan ta dago tana kallon sa hawaye na zubo mata,,, dud a cikin hausarta da bata fita sosai taci gaba da cewa
"in kuma danshi kake ganin an kawoni bari naje na fadawa wanda ya kawoni din saika qara maimaita masa bitar magungunan daka gama cemin asai mani su insha yanzun,,,,,"!!!
da wani irin azababben sauri doctor lurwan ya zube gabanta tareda kama kunnuwansa bayan yasaki kumatunsa daga radadin zafafan marukan da suka gama ratsa masa kwanya, qwarai yayi mamakin ynda ta iya fidda hannu ta zabga masa wannan marukan, dama haka take da zuciya yarinyar?
yanzu in har ya kuskura taje ta fadawa yalla6ai mahabeer ai ya rigaya da sanin kashin sa ya gama bushewa tuni, wataqila ma hakan na iya janyo masa yayi ta aikin sa.
mafarin knn ya zube gaban ummu hani yana tuba yana ahi da rantsuwar cewa ya daina mata kalar maganganun insha Allah,,,, ya dade a zube kasa gabanta saida yaji ta tsayar da kukan nata sannan ya tashi ya koma ya zauna ko fuskarta ma ya gagara iya sake kallo, a haka yace
"na gode madam ummu hani da ahin ki gareni,, harara ta zabga masa taqi cewa masa komi,, ciga yayi da cewa "amman ban san mike damun kiba madam???
saida ta sake watsa masa harara sannan ta fada masa yanda takejin qafafun nata na matan,,,
nan yayi nazari sosai a gameda yanda tai masa maganar ya fallo wata farar takarda kenan da zummar rubuta mata magungunan da yadace tasha da wnda zata shafa bisa qafafun yaji an turo qofan office din nasa an shigo,
afusace ya dago da zummar ganin waye haka ya shigo masa office ba excuse kuma?? ganin wnda ya shigo dinne yasashi ya koma yayi laqwas,
mahabeer ne ya shigo office din wnda shi kansa samun kansa yayi da fitowa daga motan nasa ya dawo cikin asibitin, anan wata sister budurwa ta gamu dashi mai shegen surutun tsiya da rawan kai sai faman wani kwarkwasa take masa dan kaf fad'in garin nasu babu yarinyar dabata shaida ganin wannan kyakkyawan fuskar guy din mahabeer mua'zzam saraki ba a akwatin television da jaridu ba,,,
Jikinta har rawa yake ganin gata gashi kurkusa nan tahau cewa "am yallabai patient dinka ka dawowa ne?
ko kallonta baiba amman kuma matuqa gaya yanason sanin halinda yarinyar ke ciki mafarin knn daya kasa zaune waje day'a a cikin motan nasa da ya koma ya zauna,
shi dama can tun asalin fari yaji yatsani doctor lurwan shine musabbabin ma dawowar tasa cikin asibitin dan ganin anyi komi a gabnsa saboda tsare lpiar 'yar amanar momyn tasa,,, shiyasa ma har ya iya tambayar ita sister din cikin gimtsewan fuskar tasa da huscy voice nasa yana sake jan ajin sa cikin izzarsa batareda ya ko kalli inda take tsaye ba, shima dan yana buqatar sanin inda yarinyar take ne shiyasa yace
"emm, , tana ina ne???
har wani lumshe idanuwa sister nadiya take sannan ta ce "ay tana office din doctor lurwan ne yana m.....
tunkan ta ida maganar tata yayi gaba abinsa inda yaji amsar da yake son ji to mizai tsaya jira???? da gudu sister nadeeya ta bisa har tana haki ganin Yana niyyar 6acewa ganinta a yanda yake dogon taqin nan nasa na isassun maza,,
tace
"waitt!!,, waitt"!!,, yalla6ai please ,,,!!
tsayawa yayi cak ya dubeta yace "wani abun??
da sauri ta kauda fuskarta daga tasa ganin yanda idanunsa suke cike da wani sirri wanda ta kasa fassara sa ma, tadaiji idanunta sun kasa iya jurar kallon nasa ne,, fiddo phone dinta tayi a aljihun farar riganta ta sistoci tace ''dan Allah in bazaka damu ba muyi selfie mana ko guda day'a ne yalla6ai ,,,"
shiru yayi mata tareda bin wayar da kallo a zuciyar sa yace waisu matan nan almost dinsu basuda kamun kaine komi?
Ya tsani mace da rashin halayen kamewa sam 2,, shiyasa har gobe a tsarin burinsa babu auren hausa fulani,, ita kuwa kallon sa take da fatan Allah sa handsome dinnan ya amunce mata suyi selfie din nan tare kota samu na dorawa a instagram da twitter da face book gamida whatsapp dan ta ciri tuta wajen friends dinta na ganinta da mai farin jini a cikin al'umma manya da qananu,
yaro da kudi abokin manya knn,,
ga kyau ga yaran banki baja baja,, wani Murmushi tayi tace ''please and please yalla6ai accept me my requesting,,, hard'e arms dinsa yayi a chest dinsa ya dubeta sosai sannan yace
"i don't need it,, banda buqatar hakan ok??"
daga haka yayi wucewarsa itako ta saki baki ta bisa da kallo sai daga bisani itama ta juya tabar wurin cikeda sanyin gwiwar ta, fuskar mahabeer mua'zzam saraki ne fall ta mamaye mata zucirya ta,,, wata zuciyar tata ke cewa Allah sarki nadeeya kema kinji abinda dud kowace budurwa keji gameda shi knn muddin tayi tozali dashi tuni take kwaye masa,
farin jini garesa kamar yashi,,,...inji sister fauziyya itama.
shi kuwa gogan naku tsuka yaja abinsa, a haka har ya iso qofan office din doctor lurwan din excuse dinma a ciki ciki yayi sa mafarin knn sukaga shigowar tasa kamar daga sama.
waje ya samu ya zuna tareda harde legs nasa, lap under lap haka yayi zaman nasa ko kallon ummu hani baima sake yi ba tun kallon farkon da yayi mata tun shigowar sa office din, duban doctor lurwan yayi yace
"yaya doctor hope komi normal ???,,,
Cikin sauri sauri da tsoro 2 doctor lurwan ya fara magana da cewa "e..ehh everything it's normal yallabm6ai,,, gama takardar da za'a siyo mata medicine daya kamata tafara sha, yayi maganar yana satar kallon ummu hani dan gani yake kamar zata budi baki ne ta fadawa yalla6ai mahabeer din maganganun da yayi mata na banza., shiyasa gabansa ke dukan tamanin da uku uku a lokacin.
Baima san ita Ummu hani ba daga shi har mahabeer din bata tasu take ba hankalin ta gaba day'a naga su baffanta dabata je wajensu ba yau, kamar yanda ta saba, kuma tasan suma suna cen hankalin su na knta,, karbar takardar mahabeer yayi ya dan duba sannan yace
''ok,,"
duban ummu hani yayi bayan ya rubutawa doctor lurwan check ya basa yace
''oya oya muje inada abinyi,,"
gaba yayi itama tabiyosa a baya Babu abinda take aikawa bayansa dashi illa hararar.
suna dura harabar gidan momy umaimah da annah suka tarbata shikuwa juya kan motan yayi yabar gidan,, haka momy umaimah taita kulawa da ummu hani har tsawon sati sannan qafafun suka sace sakamakon magunguna datake sha,,
da wata safiyan lahadi dataje wajen su baffa kuwa ta fad'a musu ciwon nata har fad'a baffa yayi mata akan taqi bari a gaya musun,
ai koba komi sayi mata addu'a.
duqar da kanta tayi qasa tace "kuyi haquri baffa banason hankalin ku ya tashi ne shiyasa."
son 'yar tasu ya qara tasiri sosai a zuqatansu har kullum suna godia ga Allah daya basu nutsatssiyar yarinya day'a tamkar da 1000.
tajima nan wajen su sai wajen 11 sannan ta dawo gida,,
falo ta dan kwanta da zummar kan lokacin girki yayi ta tashi ta dora musu.
da yake annah ta tafi katsina jia dacen zata tafi wajenta suyi fira.
motsin fitowar momy umaimah taji daga kichen hannunta daukeda cup,, tana ganin ummu tace
''yawwa ummu na kin dawo knn??"
"eh mah bnjima bama ay d dawowa"
"yawwa to taso ki kar6i cofee dinnan ki kaiwa mahabeer Yana can saman sa,, ban san hawa benan nan saboda cikin nan wlh nauyi ne dashi ina nishi ina komi nake samu na hau sa",,
Karba tayi tana fad'in to mah sannu,,
''Yawwa ummu na nagode"
harta fara tafiya momy umaimah tace
''af na manta ummu koma kitchen ki dauko masa tea spon dinsa ki had'a masa dashi kikai ni zan shiga ciki na warwatsa ruwa yanzun zan fito insha Allah "
"to mah,,"
wucewa momy umaimah tayi dakinta ita kuma ummu hani ta shiga kitchen din kai tsaye inda ake ajiye roban yaji da gishiri ta dosa,, taji dadi sosai da cofee din ya kasance mai duhu ne, dan haka ta samu tarugu jawur ta hada da gishiri da tasshi harda citta da karamfani ta zuba ruwa kadan a ciki ta hadesu ta tace, sannan ruwan data tace din ta juyesu cikin cofee din nasa tasa spon ta jujjuya tana sakin Murmushi sannan ta dauko cup din ta fito ta haye samansa ta tura dakin tareda sallamarta,,
jin motsin ruwa a toliet ya tabbatar mata da yana bath ne,, qwarai taji dad'in hakan shiyasa tayi saurin ajiye masa cofee din ta fice daga dakin nasa ta koma falo tai kwanciyar ta tareda lumshe idanun ta tana bitar suratul Muhammad a cikin zuciyar ta cikin jin dad'i,,
koda ya fito daga wankan cikin sauri yake komi dan sunyi dasu bash zasu hadu after 25 mint's zasu zo gidan,,
saida ya sanya kayansa jan T-shirt ne da farin wando jeans, sumar kan nan nasa sai qyalli take ta ko ina zubda qamshin perfume yake, shi mutum ne mai son qamshi a rayuwar sa.
gashine kwance lub lub a fatar jikinsa dukansa,,hakama sajen fuskar sa ba qaramin qara qawata kyakkyawar fuskar tasa yayi ba gwanin sha'awa abin,,,
sai dai fuskar nan datake a tsuke tamm, amman hakan ma datayi ba qaramin qara kyau yayi ba, girarsa har wani tudu tudu tayi sabida tsaban yawanta da cikarta black sosai kamar an d'ora masa ita a seti,
pressing cap dinsa fara ya daura a kai sannan ya zauna gefen bed dinsa ya d'auko laptop dinsa ya d'ora a laps dinsa yana duba wani message da yake tunanin shigowar sa tun safiyan yau,,
tsoki yaja tareda rufe laptop din ganin har yanzu basu turo accepting nasu ba, ,,
(requsting ne ya tura a can wata school dake London akan qara ilimi kan hanyar haqo mai ta hanyar hadin gwiwa dasu turawan,, wanda dama sune suka bude school din suka fara yada manufofinsu akai ga sauran qasashen duniya wanda yasa yanzun haka school din Saura wata 5 ta fara aiki,
dady mua'zzam ne sukayi maganar dashi jia akan ya tuntuba yaji koda sauran gurbi na karbar dalibai a cikinta in bai cike ba, ta hnyar tura musu message nason shiga school din, instead dady mua'zzam yaje sai shi mahabeer din yaje,,
suna son yin hakan ne dan sauqin samun farashin mai ya wadatu a cikin alu'mma ta nigeria a ko'ina, da sauqi mai rahusa.
hannu ya miqa ya d'auki cofee din knn wayar sa tahau ringing baibi ta kan wayar ba dan hankalin sa tafi da ynda yaji copee din na qamshin wasu abubuwan masu dadi yau,, mafarin knn ya q'agu dajin son dandanon sa a cikin bakinsa,, ya kafa kai tareda yiwa copee din wata kyakkyawar zuq'a,,
tsananin zafin copee dinne dawani hatsabibin dandano na wani mahaukacin yaji yaji ya gauraye masa dukkan illahirin qwalwar kansa,, tuni ya shaqi copee din ba dai dai ba ba shiri yasaki cup din qasa tareda duqewa Yana sakin wani uba uban tari da atishawa kala2, kansa yaji Yana jujjuya masa kamar wanda yasha q'waya, ba shiri yasa hannayensa ya riqe kansa da qarfi tuni idanunsa suka dinga yoyo da hancinsa hawaye faca faca a fuskarsa yanda kasan an vude fanfon mono,, Gabaki day'a bakinsa ya mutu mururus, nan yayi baya saman gado yafada dafe da cikinsa dayaji shima yana jujjuya masa,,kukan ainahi yake son yi amman abin ya faskara dan wata azabar tafi gaban wata...




*Xexen fassha*
[10/11, 2:47 PM] Xainab Documen: 🌊🌊🌊


*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊
Story and writing
by
Xayyneb πŸ’€πŸ’€


🌊🌊🌊🌊🌊


Fasaha online writers f. o. w.


🌊🌊🌊🌊🌊
πŸ…Ώ3⃣5⃣
🌊🌊🌊
*H* awaye ne sabbi suketa shatata yana daga a idanunsa, kwance yake ya mimmiqe kamar gawa yana faman hucin numfarfashi,
tari kuwa yayi har yaji babu dad'i gamida atishawa,
banda ciwo babu abinda qirjinsa ke masa kuma a halin yanzu kamar zai 6alle daga jikinsa ya fad'o yakeji sabida suyan radadin zafin.
ya kwashi sama da minti arba'in sannan yasamu tarin ya lafa masa da atishawan,,,
lamo yayi bisa gado jikinsa yayi laqwas Kamar wanda yayi gudun wuce sa'a ya gaji liqis banda numfashi babu abunda yake sake saki,,
lokaci day'a yaji gumi na kwararo masa a kowane ga6a na sassan jikinsa,
tashi yayi ya koma toilet ya cire dukkan kayansa ya sake yo wani sabon wankan ya canza kaya ya tsaya gaban mirrow yana kallon yanda idanunsa sukayi jazirrr dasu har yanzu basu washe ba tukun,
Maganezian ya d'auko yasha ba jimawa yaji qirjinsa yabar zafin da yake masan,
tunani zuciyar sa ta zurfafa yi nayaya akayi yau momy tai masa wannan hadin na lahira kurkusa??
Lallaikm ya leqota ya dawo,,
sakin numfashi yayi yace a fili "momy na nasan matsala aka samu inda ba haka kika saba mun ba,,
haka ya sauko falo adai dai lokacin ne momy umaimah ta fito itama daga d'akinta ta dubesa ganin yanda idanun sa sukayi jazurrr yasata saurin matsowa garesa tana shafa fuskarsa take fad'in "0h ya ilahee mahabeer na! mine ya yasamu idanun ka haka ne suka kad'a sukayi ja ne em?!!
Ummu hani dake lafe cikin kujera tana jinsu farin ciki ne fal cikin zuciyar ta na jin ynda haqarta tayi saurin cimma ruwa na gameda tarkon data d'anawa shugaban mamuguntan gidan, shafa wajen saman maqoshinsa yayi zuwa kwantaccen sajensa ynda yake jin suna masa tsabar zunga har yanzu, kamar yanzu ne yasha abin yakeji,,,
sam yaji bai iya cewa sabida coffee dinta ne daya sha ya tsinci kansa a cikin wanna halin,
a hankali ya saki numfashi gamida d'agowa ya dubeta yace "haka nan naji idanuna namun ciwo momy,, amman kada kidamu zuwa anjima nasan zasu washe insha Allah" qwarai sosai taji tayi matuqar tausaya masa cikin karayan zuciya tace
"Allah shi yarda mahabeer na, amman in anjiman yayi naga idon bai sauya kalan saba gskia dole kaje kaga likitan ido hospital"
a zuciyar ummu hani kuwa cewa tasakeyi ''ni dama ya makancen wlh danaji dad'i sai inga dawane iriyar idon ne zaiyi kalla yayi muguntar mun,, miqewa tayi da zummar fita harabar gidan cen inda ta saba zawa wajen kayan games sai lokacin nema suka lura da ita cikin falon,,
karaf idanunsa ya fad'a cikin nata kanya fidda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login