Showing 3001 words to 6000 words out of 130351 words
umaimah tace "eh yayi,
shi mike so abamu."
dunan nanny d'in su mutumin yayi
yace
"nanny d'anki yazo a sa'a, duka duka yau kwanansa hudu da kawowa,"
Har a cikin zuciyar nany d'in tasu bataso rabuwa da jinjirin ba kamar zatayi kuka batasan miyasa ba tafi jin sa akan sauran,
kodan bashida fitina akan sauran ne oho?
Ammn Koba komi taji sauq'i 2 inda mutumin kirkine zai kar6esa ya renesa.
Daurewa tayi tareda murmushi tace "hakane muna roq'on Allah ya tayasu riqo to".
Anan suka koma ofis d'in suka zauna,
Umaimah kuwa na rungume da balaraben jinjirinta kamar ta lashesa take ji.
Bayan sun zauna
Anan ogan yace
"to Alhj Amman da sauran bayani.,
Mu'azzam saraki yace "kamar Yaya knn mlm mukhtar?"
Gyara zama yayi sannan yace
"to wannan yaron yau kwanansa had'u knn da wata dattijuwa ta kawo mana shi a rud'e ta ajiyesa sannan tace bayanin komi na cikin wata farar takarda wacce Ke jikin jinjirin zata dawo d'aukarsa in komi ya lafa,
Daga haka ta juya ta fita tana waiwayen jinjirin yaron tana kuka.
Bayan fitarta ne na kirawo ita wannan nany d'in nasu mai kula dasu jinjiran,
Nan Nasa ta d'auko yaron, saiga wata takarda fara ta fad'o jikin showwl din yaron.
Bacin mun bud'a takardar abinda Ke a rubuce ciki shine
''Nice mai aikin mahaifiyar shi wnn jinjirin,
iyayensa masu mutuncine da temakawa bayin Allah,
katsam aka haifi yaron wnda haihuwarsa ta tsonewa wata mata daga cikin family nasu ido,
wato matar babansa ta 1, sakamakon yawan dukiyar uban yaron, ita kuma tana uwar gida ace bata haihu ba, sai amaryace zata zo ta haihun tagaje dukiyar gidan knn ma duka?
To wlh bazai yiwuba,!
dare nayi wai zata sa aje a sace jinjirin a kashesa.
ni kuma sai Allah ya q'addareni dajin mugun q'udurin nata lokacin da nazo kawo mata jinjirin data aika In d'aukosa dan aminanta.
Mafarin knn najuya da sauri na maida sa ga mamarsa Nace tace bazata kar6i yaron ba.
To dayake mamar yaron tasan rashin kirkin waccen matar kishiyarta, sai tayi murmushi kawai batace komiba.
Nakasa nutsuwa nikuma nasan kona fadawa uwar d'akin nawa wannan maganar zatace jita jita ne,
Ni kuma ina son tai rayuwa da d'anta, mafarin knn naje na d'auko yaron a boye lokacin mamarsa ta shiga wanka na kawo muku shi nan ajiya da nufin in komi ya lafa zan dawo in kar6esa nan bada jimawa ba.
Gashi nn na barshi riq'o @ hannun ku, Allah shi raya mana kai *MAHABEER*!!! zan dawo lokaci kad'an insha Allah na sadaka da mahaifanka bisslam saina sake kuma juyowa gareka d'an uwa ta gari....!
Yana kawowa nan yace to wannan shine taq'aitaccen tarihin na jinjirin nan *MAHABEER*,:da muka tsinta a tare dashi, kuma da
wannan ne muke roq'onku da cewa koda yaushe ne ita wannan baiwar Allah ta dawo da zummar kar6ar yaron to zamu kawota nan wajenku ta kar6i yaron su kamar yanda mukayi alq'awali da ita.
Yana kaiwa nan
ya miq'ewa tsaye ya d'auko wani q'aton photo album na ajiyan hotunan tarihi na gidan marayun snn ya budo wani shafi yace "wannan hotunan suma still mun samesu ne a jikin showl na jinjirin,
Anan nagane harda ita dattijuwar matar a hoton,
Kungan ta nan ma.
Nan yafara nuna musu kowa na gani cikin mamaki, Wannan daga ganin kamarsu itace mamar shi jinjirin *MAHABEER* nikega,
inda gashinn hannunta kuma.
Sannan ya q'ara nuna musu wani photo inda aka d'auki MAHABEER d'in shi d'aya yanata barci abinsa lpia.
Tashin hnkali ya ziyarci zuciyar umaimah a lokacin dataji abinda mutumin Ke fad'a na zai rabata da MAHABEER d'in ta in iyayensa sunzo karbar abinsu, Wanda takeji duk duniya batajin akwai abinda zaisa ta iya rabuwa dashi dan a shirye take data bada ranta fansa ga jaririn...
Xayynebπ€π€.
[10/11, 2:44 PM] Xainab Documen: πππ
*MAHABEER*!!!
πππ
Story and writing
by
Xayyneb π€
πππππ
Fasaha online writers f. o. w.
πππππ
π
Ώ3β£
πππ
*Q* ara ware idanunta umaimah tayi kan hoton tana kallon mamar shi mahabeer d'in, wnda kowa ya gnta kuwa yasan tabbas itace dai mamarsa sbd kamarsu d'aya sak,
Sannan ga kuma ita wannan dattijuwar matar da akace ita ta kawosa a gefen mamar MAHABEER d'in suna dariya aka d'auki photon. Maganar da taji mu'azzam sarakin na cewa ne yasa hankalinta dawowa wajen kacokam!
"To shiknn mlm mukhtar bakomi, Allah shi kaimu lokacin da rai da lpia kuma,
ay kasan shi cika alq'awali abune muhimmin gaske a dukkan rayuwar d'an Adam."
Nan mu'azzam sarakin dai ya cike file d'in da shi mlm mukhtar d'in ya basa ya ciken,
da kuma dai sauran abubuwan daya kamata yayin duk yayi su lokacin gaba d'aya,
Sannan da zasu tafi kuma ya cikasu da kyaututtuka suda kingin marayun gidan,
A lokacin kuma suka kamo hnya suka dawo gida.
Suna shiga falon gidan kuwa umaimah tayi saurin kar6ar yaron daga hannun Annah tana murmushin murna ta shige d'aki dashi ta goyeshi ram a bayanta ta fito falo tana zagayawa dashi,
shi kuwa sai mutsu mutsu yake yana q'oqarin tura hannunsa a baki ga alama mamansa yake son sha bai ishesa ba.
Annah kuwa sai binta da murmushi kawai take yi,
Sannan Annah d'in ta d'auko wayanta tafara gayawa 'yan uwa da abokan arziq'i haihuwar,
nan da nan kuwa akaita kiran iyayen jaririn ana musu murna sukuma suna amshewa cikin farin ciki.
Ranar kamar umaimah ta zuba ruwa a q'asa tasha Dan murna,
nan mu'azzam ya kirawo family doctor d'in su yace yana so ya siyo masa madarar da yasan ana bawa jinjirai in ruwan nono yaq'i biyawa.
Ba'a d'au tsawon lokaci ba sai gashi kuwa doctor d'in ya kawo madarar katan katan.
shima yai mamakin ganin jinjirin nasu.
Amman kuma da suka fad'a masa abinda suke fad'awa sauran sai ya yarda shima, duba da shi kansa ma yajima rabon sa da garin sai kwanan nan ya dawo sakamakon canjin wajen aiki daya samu.
Nan aka had'awa baby milk d'insa,
ita ya wuni sha abinsa.
Washe Gari kuwa abokanan umaimah sukaita zuwa ganin jinjirin kowa ya gnsa sai yayi santin yaron matuq'a.
'Yan katsina suma tun ranar suka fara durowa gidan haihuwar har zuwa ranar suna inda akasha shagali na kece raini kusan sati ana shagalin kuwa bai q'are ba,
Hatta abokanan mu'azzam saraki sukan zo takanas dan ganin jinjirin tareda ajiye masa kyaututtuka masu nauyin gaske.
Gskia kam baby yasamu dukiya ta ban mamaki, shiyasa babansa mu'azzam saraki ya bud'e masa account kawai yana zuba masa kyautarsa daya samu.
Kullum Annah tana tare da MAHABEER itama bacci kawai ke maidata d'akinta dan tana matuq'ar son sa itama sosai.
Haka suke rainon d'an nasu cikin farin ciki har yau gashi yayi wata 6 zuwa lokacin harya karya qafarsa wato ya fara rarrafawa knn abinsa gwanin sha'awa.
A lokacin ne Annah ta koma katsina cike da kewar MAHABEER.
Amman tun zuwan MAHABEER gidan Annah bata d'aukar tsawon lokaci bata zoba gidan d'an nata ba kamar da ba da zasuyi ta fama da ita ma akan tazo sai ta q'iya wai a cewarta jikin tsufa ciwo baison tafiye tafiye...
Shima MAHABEER ya fara sanin Annah shiyasa daya ganta tazo gidan har wani murna yake da zullon son ta d'aukesa Dan ya tantanceta a yanzun shima sosai.
Kullum kyansa q'ara fitowa yake na sak jinin larabawa....
'Yan magana sunce shekara bata gadon shekara yau har MAHABEER ya cika shekara 5,
A lokacin har an sanyasa nusry one a school.
Akwana a tashi har gashi ya gama nusry t primary har ya shiga secondary lokacin.
Allah yai masa brain shiyasa yai suna a school d'in su kowa a frnds d'insa zakaji suna fad'in
Gifted MAHABEER.
Tun su umaimah na zullumin yau ko gobe za'a zo d'aukar MAHABEER har suka daina dn ganin an Shari wad'annan shekarun haka Amman kuma shiru kukeji .
Kulawa kuwa ta fannin iyayensa kullum sai abinda yaci gaba kuwa takai yanzun in dai ya samu Hutu shida kansa yake matsawa dadynsa yakaisa katsina wajen Annah Hutu.
Haka zasu tafi kuwa su kaisa shida momynsa umaimah....
Haka lokaci yaketa tafiya kwanaki na zama shekara har gashi yau MAHABEER yayi degree d'insa da masters degree yagama duka.
A lokacin kuma ne
Ya zama wani irin murd'adden mutum q'arfaffa, wato irin giant d'innan ne,
ya ida riked'ewa ya zama hands some guy wani muskilin mutum naq'in q'arin kansa, d'an shekara 29.
A cikin satinne kuma mu'azzam saraki ya tursasa masa fara zuwa office d'insa dashi yayi murabus a kan kujerarsa ya d'ora MAHABEER akai a cewarsa yanzu ba kamar daba, ayyukan zasuyi masa yawa, q'wamma ya tsaya kan fita q'asashen wajen sa yana fiddo da kayan business d'insa abun zai zamo masa da sauq'i hatta al'amurran gidajen man sa da motocinsa na company dinsa ya damqa ragamar komi ga MAHABEER d'in,
Giant man knn,
nera kamar tai masa kuka ga kyaun usuli,...
'Yan mata kuwa komin nacensu garesa jin kansa da isarsa bazai ta6a iya bari ya d'aga kai ya dubesu ba, muddin bashine yaso ba dan Karin kansa ba.
**
Yau dai a matuq'ar gajiye MAHABEER ya dawo gida,
Parking motarsa yayi sannan ya sa6o labcote d'insa da brife case d'insa, fuskar nan a had'e ya tura q'ofar falon nasu ya shiga.
Ganin saman q'ofar dak'in ammi d'insa a rufe ya tabbatar masa da tana hospital d'in datace masa zataje ganin diyar q'awarta nahnah.
D'akin sa ya wuce ya tulla kayan hannun nasa kan gado sannan ya cire kayan jikinsa ya d'aura towel iya q'ugunsa ya shige toilet.
Yana fitowa kuwa yaji phone d'insa ta fara ringing a d'an duban harara ya kallo wayar dan baison wani Abu ya gitto ynxu ya damesa a ynda yakejin ya gajinnan over,
Wayar ya d'auko ya duba ganin sunan bash ne yasa shi d'an sakin fuskarsa kad'an shima, sannan ya d'aga yace
"yadai bash kun dawo ne?
Daga can bangaren bash yace
"kai gifted wlh mukhtar d'an iska ne,
yau rabon iv d'in nan na bikinsa da mu kaje nida mas'ud ba q'aramar wahalar damu yayi ba harda imran,
tun safe fa sai ynxun ana magrib muka dawo gida ,
Kai kai kai huhhh,!
Rabon iv ko masifa,
Shiyasa Nace masa
wlh gobe weekend dole ka fito dan a ida rabon nan dakai kaima kaji ynda abun yake inda gobe shine last day na rabon iv d'in.
Ta6e lips yayi yace
"ba inda zanje guys dan kuma sani,
Ni gobe ma KT zanje na dauko Annah ta,
Da sauri bash yace
"kai Dan Allah gifted?
You seriously?
Indai haka ne nima zanje kuwa ka jirani zan zo to muje dan nayi missing Annah wlh a lot nima, Amman Allah sadai ba jirgi zamu hauba?
Dan na sanka kamar tsuntsu kake wajen yawo a Sama."
ta6e lips ya sakeyi yi dan gajiya da yayi d mgnr sannan yace "don't mind bash,
a motor zamu indai zaka, but kuma wlh karkamun iskan cinka na lates African time, dan by ten i think zamu wuce ma ok?."
"OK babu ji ay gifted"
Cewar bash d'in.
Ajiye wayar yayi ya ida goge sauran leman ruwan jikinsa da towel d'in kansa, sannan ya murza sansanyen cream lotions d'insa ya fiddo wata baq'ar Riga irin ta shan iska mai gajeran hannu,
inda ta bayyana masa kwantaccen gashin jikinsa lu6 lu6 gwanin sha'awa. sannan ya zura tree quater d'insa blue shi kuma, fita yayi izuwa kan dining table nan ya iske fried rice wacce Tasha kayan q'amshi, baje baje take da kifi sosai, dama haka yake son ganin fried rice, shiyasa abinda Momy d'insa tafi girka masa knn dan tasan shine choice cook nashi a rayuwa.
Sam baya wasa da cikinsa shiyasa daya zauna sosai yaci abincin sannan yaje yai brush ya nufi wajen games d'insa inda yake motsa jiki nan wajen harabar gidan,
qaton d'aki ne babu abinda ke cikinsa sai kayan exercise a ciki manya da q'ananu an zube su a cikinsa.
Yakai one hour yana exercise a wajaje daban daban na wurin, yayi gudu ya d'aga q'arfe q'aton gaske da hannayen mabanbanta, yayi ta rubda ciki, yayi ta duq'e,
shiyasa lokaci d'aya wani irin mugun gumi ya jiq'esa sharkaf kamar Wanda ya fito cikin ruwa dudda esin dake wajen Sama da guda 5 kuma.
Saida yaji ya gamsu yaji dud wata sauran gajiyar daya kwaso ta ware sannan ya fito yana share zufa a saman fuskarsa da jikinsa da farin towel d'insa,
Nan ya fito ya koma cikin swimming pool yayi iyo nan ma sosai son ransa sannan ya koma d'akin sa ya canzo wasu q'ananun kayan farin jeans da farar Riga mai gajeran hannu Wanda ta bayyana Masa shatin murd'a murd'an qarfin arms d'insa na maji qarfin qarfaffen namijin gsk, yazari keys d'in motar sa ya fito yana shirin shiga motarsa knn yaga shigowr motar mamynsa a gidan.
Da sauri ya nufi wajen cikin takunsa a sassarfa na son ganin momyn tasa.
Amman lokaci d'aya ya tsaya cak dan ganin wacce suke tare da ita a gefenta.
Tuni ya q'ara d'aure d'aurarriyar fuskarsa katamau.
ita kuwa Hannat sai wani fari take masa da idanunta tana karye karye,
Wani dogon tsoki yaja yayi kamar bai gama momyn ba yana shirin kwana ya shige motarsa yaji momyn tasa tace
''ah MAHABEER_? baka ga momyn taka bane ba? ba welcome ba komi alhalin da katafo kuma saika juya?
A hankali ya juyo ya sauke zafafan idanunsa a....
Xayynebπ€π€
πππ
*MAHABEER*!!!
πππ
Story and writing
by
Xayyneb π€π€
πππππ
Fasaha online writers f. o. w.
πππππ
π
Ώ4β£
πππ
*A* hankali ya juyo ya sauke zafafan idanunsa a fuskar Hannat a wulaq'anci,
na kallon raini.
duk a cikin lokaci q'anqani yayi hakan, Ita kuwa momyn tasa ma bata lura dashi da abinda yakeyi ba lokacin ta juya danta d'auko jikkarta daga cikin motar tata data barota.
Isa yayi wajen momyn ya amshi jikkar hannun nata yace
"welcome Momy''
Dubansa tayi a wasance tace masa
"MAHABEER bazan amsa ba inda kana ganina kayi kamar baka ganni ba kana shirin ficewar ka ko?
"oh Momy I say sorry please,,,,,!
wani abune ya d'auken hankalina shiyasa"
Pleassss my mom kinyi haqurin ko ynxun?"
Ya q'arshe maganar yana langwa6ar da kansa tareda amsar jikkar hannun nata ya hada da hannayen sa alamun sorry.
Murmushi tayi tace
"To shiknn naji,
Amman da kake shirin fita haka da sauri ina zuwa?
Dan da alama yanzun ka dawo office ko hutawa baka samu kayi ba amman kuma kake shirin ficewa?''
Shafa kwantacciyar sumar kansa yayi ya d'an turo baki kad'an sannan ya manna mata jikkar ta ga hannunta yace
"yeah momy na, yanzun nan zan dawo Momy ba wani jimawa zanyi ba bye bye Momy".
da sauri ya juya ya shige motarsa ya bata wuta ya fice daga arear wajen, dan bai son ganin nataccen kallon da hannat take masa.
Hannat da kallo ta bisa tana fatan ace yau gashi dai MAHABEER ya zama mallakinta. data gama morewa quruciyar ta kuwa na mallakar wannan giant man d'in mai raunana zuciyar 'ya macen data sake tayi arba dashi ko a shirye koba a shirye ba.
Hasali ita fa bata San MAHABEER ba sai cikin satinnan data zo Hutu wajen momynta daga gidan babanta. dayake basu tare da baban nata ynxun. kuma ita momyn tata aminiyar mom d'in MAHABEER d'in CE tarema suke business d'in su.
a ranar da tazo ta iske momyn nata na shirin zuwa gidan su shine ta biyota a yinin ranar da sukayi a gidan su MAHABEER d'in har yayi dai dai da lokacin dawowarsa office anan ta gansa lokaci d'aya ta rikice da ganin halittar kyaun nasa mafarin knn kwana ukun nan da zuwanta kd wajen mamar tata tofa kullum saita zo gidan tun safe bata komawa sai ya dawo ta gansa sannan take samun lisilaman q'arfin gwiwar komawar ta gida.
Tun bai lura da manufarta a kansa har takai ga ya lura ta hanyar alamomin datake nuna masa a aikace hakan yasa Sam ko ganin ta tazo gidan bai ra'ayi, Dan a rayuwa ya tsani macen da take ballagazar da kanta da taga namiji, shiyasa Sam shi baida ra'ayin yin soyayya da yarinyar Hausa Fulani dan ganin su yake duk d'aya ba kamun kai.
Shiyasa yake daurewa yana d'an kula blessing towmy firind dinsa wacce take matuqar qaunarsa kamar ta mutu kuwa.
tun da suna cikin school ma take nace dashi har kuma yanzun da suka qare karatun, dan wani lokacin ma har gida take zuwa nemansa.
Jiki sanyaye hannat tabi momy cikin gidan bayan taga shigewar motar sa waje a guje.
Ita kanta tasan dai MAHABEER bata kanshi sam3.
Zama tayi kan one seater ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana tsinewa *so* a zuciyar ta daya kaita inda bata da galihu a muhallin wajen.
haka ta wuni gidan har dare yayi bataji dawowar saba,
dolenta kuwa badan taso ba ta haqura da taga babu sarki sai Allah har goma saura dole ta takira drever d'in su yazo suka tafi gida.
*Niger state*.
A yankin buzaye na asali a wata mazauna cikin wata Anguwa da ake kiranta darul Islam.
Yankine mai lumana da kwanciyar hnkali a cikinsa a koda yaushe 'yan uwa buxayen nan zaka gansu suna tattalin junan su, ga kuma kiwonsu da sukeyi gwananin sha'awa. ta kowane fanni rayiwarsu nai musu dad'i matuqa gaya sukeji.
Sai dai kuma babban abinda ya damu shugaban adalin yankin wato mlm kad'do shine rashin lafiyar mai d'akinsa binte, wacce yau a samu sauq'i gobe a koma jinya.
Dud wani jiq'e jiq'e da sukasan yana maganin Irin ciwon sunyi sa Amman sauq'i sai wajen mai duka.
Kamar yau ma haka ya baro q'ofar gida ya shigo gida jikinsa a sanyaye yake jinsa.
sakamakon kiran sa da *Ummu hani* tayi, wato babbar yarsa 'yar kimanin 18 years.
dan yazo yaga yanda ciwon Maman nata yake hawa da sauka a lokacin.
Zama yayi gefen bukkar tasu dake tsakar gida wacce ita binte d'in ke kwance idanunta na kallo sama.
sai cije baki takeyi tana motse motse da jikinta, dan ita kadai tasan irin azabar da zuciyarta ke mata a lokacin. ta kama ciki ta dafe gadaqam.
Zama yayi gefenta yana mai furta
"Assha!
sannu binte ciwom ne kuma ya taso da rana tsaka?
Ya Allah!
Ubangji Allah ya kawo afuwan miki wannan ciwo,,"!
Cikin xubar hawaye da matsanantan kyawawan fararen idanunta tace "Ameeen Baffa,
Dubanta yayi jin muryarta na rawa rawa yace
"haba ummu hani na?
bazaki daina kuka kan ciwon nan da Allah ya saukowa naman kiba knn ko?
Jinya lada ce fa,
tana kankare zunubbai haka kika karanta a cikin littatafan addinin Dana koyar dake kuma kinsan hakan, Amman danmi zaki dinga zubda mata hawaye Ummu hani?
Cikin 6oyayyar muryanta mai rawan kuka kuka, da maganar buzanci itama ta fara mayas masa da maganar muryarta na cigaba da kyarma tace "Baffa na daina to kayi haquri"
Girgiza kai yayi yace ''kullum na kamaki kina kuka haka kike cewa nayi haquri Ummu hani, Amman kuma dai hakan bazai sa kiqi qara kukan naki ba da zarar jikin nata ya motsa ba''
Shiru tayi bata qara cewa komi ba ganin Baffa d'in ya