Showing 63001 words to 66000 words out of 130351 words
magrib sannan ya wuce masallaci.
ahaka watan haihuwar momy umaima ya tsaya dud wata siyayya sunyota sun ajiye,, ranar wata laraba da safe ciwon naquda ya tasowa momy umaimah babu shiri sukayi asibiti nan kuwa aka shiga da ita labour room,, doguwar naquda tayi sosai daga mahabeer har dadynsa masallaci suka shiga anan ckn asibitin sunawa momy umaima addu'ar samun sauqin naq'uda,
cikin ikon Allah kuwa sai gashi ta haifi d'iyarta mace masha Allah,,
daga momy umaima har mua'zzam saraki kuka kawai suke na farin ciki na ashe zasuga qwansu na gaskia a duniya?,, annah ceke rarrashinsu akan suyu shiru kada yaran su ankare da halinda suke ciki.
haka suka dawo gida bayan dubata da akayi sosai akaga komi normal babu wata matsala.
ummu hani takasa zaune ta kasa tsaye tunda suka dawo asibiti tana nan q'waqume da jaririyar nan kowa yace tabasa sai anyi da gaske sannan take bayarwa, har annah na mata tsiyar cewa "anya kuwa ummu hani in kika samu d'a bayan kinyi aure zaki dinga bari ana d'auknsa kuwa? dan na lura kinada son jarirai,,nabeela tayi karaf tace "nima ay annah bazan bawa kowa nawa ba kada asa masa ciwon jiki,,," annah takama baki tace "oni 'yasu dunyia ta canza yaran zamani ba kunya har kuna cewa bazaku bada yaranku ba??
ai da gudu suka tashi suka bar d'akin.
momy ni'ima da Momy umaimah sunata musu dariya.
kan kwana 3 dud 'yan katsina sun cika gidan kuwa anata zaman barka da Allah raya,,,
ranar suna kuwa anyi shagali sosai sosai yarinya taci sunsn manal.
bayan suna ne 'yan katsins suka koma da d'umbin tago mashi na arziqi.
Beby manal samun kulawa take daga kowane b'angare kuwa na gidan,
kowa son d'aukarta yake dan yarinya ce mai shiga rai, a haka har suka shiga wata na 4 da haihuwa.
lokacin baby manal ta fara wayau hatta mamanta wani sa'in qyuya take son yi mata muddin tana hannun sabuwar ummu mmnta hani,,, kamar yau ta kama alhamis da misalin qarfe hudu na yamma momy umaima ta shiga d'aki ta samu barci ummu hani kuwa tana riq'e da baby manal suna zagaya falon tana mata wasa yarinyar na wangle mata baki,
zama tayi tareda fiddo wayarta tana qoqarin kiran nabeela taji ko ta dawo daga kasuwar dataje kaiwa a dinko musu rigunan nan na roba dogaye masu gyale.
sai kawai ganin saukowar sa daga saman benen dakinsa tayi da sauri da laptop a hannunsa yana q'wallawa annah da momy kira amman ysai shuru,, zubewa yayi bisa kujera yana sakin ajiyar zuciya babu abinda ke cinsa sai tsabar murna da farinciki domin school din London wacce yayi request na son shigarta a kwanakin baya shine yanzu yana dubawa a laptop dinsa yaga sun yi accepting nasa, kuma sunce a wannan watan sukeso yazo sabida sufara project dunsu.
Murmushi kawai yake saki umnu hani kuwa kallonsa takeyi dan abun mamaki ya bata,
ita dan bata taba ganin zallar farin ciki irin nasa ba kamar na yau tun byn haihuwar baby manal.
tab'e lips tayi gamida jan tsoki, karaff kuwa sai a kunnensa kuwa.
da sauri ya d'ago tareda ware idanunsa dukkansu a kanta ya dubeta tareda watsa mata harara da idanunsa cikin masifarsa yace
"ke wane shegen kike wa tsoki??" Murgud'a d'an bakinta tayi tace
''yo kajini da mlm, koko kaji nace dakai nike abina ne bare?? waro idanuwa yayi waje tareda fad'in ''kutttt,,..ke?? ubanwa kika raina wa wayau ne wai ma.....?? Miqewa tsaye taga yayi yana shirin nufota, haba aida gudu ta sungumi baby manal a kafada tayi dakin annah da ita,, bata qara fitowa ba saida tasan yabar falon sannan ta afito cikin sanda tabar gidan ta nufi wajendu baffanta.
tana shiga ta gaida baffanta dake zaune bakin gate, ta wuce wajen maman ta ciki.
biyota baffa kaddo yayi har cikin dakin mama binte din yace "Yawwa ummu na dama ina Allah AllAh ki shigo kuwa..
Dubnsa tayi tace "baffa lpia kuwa,?
"a'a lpia lau kam, kwantar da hankalin ki daman maganar kudin da za aiwa mommanki aiki ne, to jia cikin ikon Allah alhj mua'zzam daya fudda zakka wlh bawan allah nan har nan ya kawo mun *zakkata* dubu d'ari da hamsin cuff cuff kingansu nn ma, nanya fiddosu cikin aljuhu ya gwada mata sannan ya d'ora da cewa "shi kuma d'azun mai gidan nan yabani albashina shima dubo d'ari wlh ummu hani,
shinefa dana zauna na lissafa kud'in namu naga har sun kai ma yanda ake buqata aiwa mmnki aiki harda ragowar dubu 35 ma ummu hani,
kinga ai Alhamdulilla,,
kuma insha allah cikin satin nan za aiwa mamanki aiki kinga komawarmu gida yatafo cikin yardar Allah, dan gskia ban tunanin zamu qara sati 2 ma a garin nan batareda mun koma qasar muba nijer,,"
har aran ummu hani taji farinciki sosai na ganin Allah yarufa musu asiri sun samu kudin aikin mamanta daza ai ta warke sumul cikin yardar Ubangiji Allah, amman babban tashin hankalin ta yaya zatayi da mutanen data saba dasu ne harta tatafi ta barsu lokaci day'a kuma?
kawai bazato taji hawaye na zubo mata, mama bintey ta rungomota jikinta dansu a zatonsu kukan murna ne kawai takeyi basusan hadda na sabo ba, mama bintey tace
"kidaina kuka ummu hani na godia ga Allah shiyafi kinji ko?
"gyada kai tayi tana share hawayenta. ganin baby manal tafara mutsu mutsun son yin kuka na alamun yunwa yasa mama bintey tace" kije ki kaita tasha mamanta",
tashi ummu hani tayi jiki a mace ta fice baffa ya biyo bayanta yana sake fad'in
"niko Alhamdulilla wlh bnda abunda zancewa mutanen kirkikin nan sai godia ga Allah,, nan ya zauniyarsa bakin gate yana cigaba da lazuminsa tareda goga aswakia bakinsa.
ita kuwa fucewa tayi tana cigaba da share qwalla.
Koda momy umaimah ta tambayeta dalili cewa tayi batajin dad'i ne sam shiyasa momy umaimah ta tausaya mata harta bata magani tace tasha, fakar idanun Momy umaimah tayi ta xubar dasu tajawo malullubi ta rufe jikinta bisa gadonta tareda jimamin kewar zata tafi tarabu da mutanen kirki bayan sabo yashiga tsakaninsu hakamai tsanani kuwa.
haka ta kwanta da hawaye a saman fuskar ta, da safe kuwa haka ta tashi jikinta sanyi qalau tayi sukuku harda busasun hawaye a bisa fuskar ta sun mata sawu.
wanka ta shiga tana fitowa daure da towel ta zauna gaban mirow tana son tayi shafa amman abin duniya ya faskareta, saima kife kanta da tayi a jikim disc na miron ta lumshe idanun ta, godia takewa Allah na ganin yankewar wahalar da mamarta kesha yazo qarshe, gskia mutanen nan mutane ne na gari, haqiqa sun musu abinda har gaba da abada bazasu tab'a mancewa dasu ba, dole kuwa tayi kewarsu wacce ynxu haka kewar ce tasa jikinta sake mutuwa mururusss,
jitayi an dafata da sauri ta miqe zaune, ganin nabeela ne yasata sakin ajiyar zuciya ta qaqalo dan Murmushi tace "sister yaushe kika shigo banji ki ba?, zama nabeela tayi gefen gadon dakin tana cire mayafin after drees din jikinta tace
"to daman sister ta ne yaya har zakisan shigowa na? kinzurfafa haka inata miki magana amman sai dai tsitt tabani amsa kamar dai baki a room din? anya kuwa sister lafiyanki? Pleas tell me sister kinsan damuwarki shine nawa kinji ko? Ummu Tanaso ta fad'a mata gaskiar cewa sun kusa rabuwa zasu tafi gida amman tana tunanin halinda nabeela zata shiga na qunci, expecially ma su Momy umaimah insukaji batun nan batasan yanda zasu qarke ba, gwamma dai ta bari baffa yai musu bayani in lokacin tafiyar yayi zaifi mata sauqi,
akan ta tada masu da hankali tun yanzu gskia ta qwammace itan taita zama cikin uqubar damuwar ita kad'ai.
shiyasa akace ba mutuwa akewa kuka ba sabo,,
sakin ajiyar zuciya tayi takai dubnta ga nabeela data zuba mata ido tana sauraronta,
d'an murmushin qarfin hali Ummu hani ta kalato tareda cewa
"nooop sister na kada ki damu kawai dai ina jin ciwon kaine tun jia da dare shiyasa," nabeela tace "a'a sister ns ciwon kai fa yafi gaban a kirawosa d'an kawai, bari naje na fadawa momy inyaso sai ta baki magani kisha ko? tayi maganar tana qoqarin miqewa tsaye, da sauri ummu hani ta ruqo hannunta tace cikin sanyin muryan ta "aa sister banjin ciwon komi yanzun haka kuma momy tabani magani nasha ay, kidaina damuwa haka please sister".
dubanta nabeela ta sakeyi tace "are you assure sister??, gyad'a kai ummu hani tayi cikin sanyin murmushin ta tace "yesss my sister i sure calm down pleass,
zama nabeela takoma tayi bayan sakin ajiyar zuciya datayi tace
"wlh dole hankalin nan nawa ya dugunzuma ya tashi ai sister ,,wlh kinji na rantse rantsuwar d'an musulmi kuma knn ko?
ni sam ban daukeki qawa ba sai dai 'yar uwa, jinki naje cikin jikina da jinina sosai ummu hani wlh bn qaunar abinda zaizo ya rabamu koda kuwa dai-dai da second d'aya ne shi abun.
nan da nan kuwa ummu hani idanunta suka fara tara ruwa na jin tausayawa kansu gashi tana shirin barin garin lokacin ne kuma wata sabuwar shaquwar ke qara shiga tsakani, Lallaikm Ubangiji Allah mai had'a jinin bayinsa a ko ina kuwa,
da wayau da dubara ta shanye hawayen nata ta hanyar maidasu datayi ta hanasu zubowa, amman maqoshinta har wani d'aci2 taji yana mata nason tanason sake wani kukan kota samu relief na damuwarta amman babu damar hakan dan kasantuwar nabeela a wajen ya hanata.
"sister na dan Allah ki yarda mu auri hussain saurayina tare inda kinga bikin mu ya matso baifi wata 5 ba kinga kema sai yai miki lefenki kuma ya ajiye mu gida day'a kullum muna tare da juna koba haka ba sister?
Nabeela tayi maganar cikin kallon ummu hani tana Murmushi tareda fatan amincewar ta,,
zaro fararen idanuwanta ummu hani tayi tace "amman dai kinyi hauka ne i think sister ko?! murmushi nabeela tayi tace
"wlh seriously sister please you agree w... saurin katseta ummu hani tayi tace "na roqeki dan Allah mubar zancen nan sister,,
shiru nabeela tayi ganin kamar ran ummu hani din ya bace,, dole ta canza firar tasu da cewa "wlh qawata kinada kyau mai sanyi ga body musamman breast da hips gskia wanda zai aureki ya more cikakkiyar mata,,"
hararar ta ummu hani tayi tace
"kedai kika sani da surutunki tayi maganar ne da yarensu na buzaye,, zaro idanuwa nabeela tayi waje tace "lalala, kaddai zagina kikayi ban saniba wlh yanzun na na tofa miki albarka, dariya ummu hani keyi abinta tana shafa manta dan gaskia zuwan nabeela yasa tarage damuwarta kashi 60 cikin d'ari shiyasa ake cewa mutum rahma ne,, duban nabeela tayi tayi mata gwalo tace "eh man zagine banace kizo in koya miki ba tuntuni kikaqi ba waike wahala?, to bake kika saniba itama kuma wannan maganar data qarsheta saita sake yiwa nabeela da yaren nasu, aida gudu nabeela takawowa ummu hani raruma ita kuwa ta gudu toilet tasa lock Sunata qyalqyata dariya abunsu, saidaga bisani tafito sunata dariyarsu ta ida shafan ta sanya kayanta suka sauko qasa, Kai tsaye dakin annah suka shiga suka taras tana sallar walha sunsan kuma inta gama zata dora salatul tazbihi ne shiyasa suka juya suka shige dakin momy umaimah, sunsameta tana shan kunu cikin wani farin bokiti qarami wanda kunun nan dud wani nau'e na kayan gyaran mata masu kyau an tanadesu a ciki, bayan sun gaida momy umaimah ta amsa cikin fara'a da sauri ummu hani ta zuge gadon baby manal ta d'aukota tana mata ''shihhh-huuu na wasa, baby manal kuwa na ganinta tahau wangle mata baki tana dariya ,,
zama tayi sunata mata wasa a kumatu suma suna tayaya ta dariyar. momy umaimah tayi dariya tace "Allah sarki, mai d'a wawa,, Murmushi sukayi, cups guda biyo dogaye qananu su ta cika musu kowanne da kunun nan tabasu tace su shanye tas hakan kuwa akayi har suka shanye basu ankara ba suna fira,, bayan sun gama ne momy umaimah tace "yawwa 'yan matana kuzo zan aikeku gidan hjy aina ku amso saqon kayanku na sawa wanda nace ta fidda muku kuma,
murna suka hauyi dan sunsan kayan dasu momy suke d'aukowa qarshe ne wajen kyau,, tashi ummu hani tayi tabawa momy baby tace ''yawwa bari naje na d'auko mayafi na to,, fita tayi da sauri harta hau sama kwata kwata bataga tahowar mahabeer ba dan lokaci day'a maganar komawar su gida yasake fado mata mafarin knn hankalinta ya dauke kawai daga hanyar kwata2 sai jitayi kawai qirjin ta ya bugi qasan nasa da qarfi dan yadarata tsawo.
da qarfi yasa hannayensa 2 ya turata takoma dabaya ta fad'i turus a qasa, "ashhh washh! ta fad'a a hankali cikin sagewar qugo da buguwar bombom nata dazafi,
cikin tsawa yake fadin
"banzan wawiyar yarinya stupid again isay double wawiya, koke makauniya ne dazaki dunga fado mun ajiki da wannan banzan jikin naki eye?! maganar yayi mata cikin zaro idanuwa nabeela dake tafowa tace
"yah mahabeer kayi haquri dan Allah, wani dogon tsoki yaja yace "dalla shutup your mouse stupid girls kawai halinku day'a ai na tsabar wawanci sakarkaru kawai,," haka yayi wucewar sa suka bisa da kallo banda jifan bayansa da harara babu abinda ummu hani keyi a lokacin. Kama hannunta nabeela tayi ta miqe tsaye dafe da qugu tace "mugu d'an masara,!
wlh nabeela inaga amakson saiya lalatamun qugu da bombom nawa kafin nabar gidan nan nasu,, nabeela tace "kamarya kibar gidansu sister banganeba?
to kije ina kenan?
da sauri ummu hani ta canza zancen da cewa "oh sorry ina nufin kamin mu fice yanzun sorry ,, nabeela tace "ahow yanzu na fahimta ai,taci gabada faduin "ya kuma zamuyi inda munsan halinsa ai sai dai muyi haquri zomuje mu d'auko mayafin mutafi, qwafa ummu hani tayi tace
"ay wlh amakson dayanada mata dasai naje na zugeta ko cin hanci ne inbata dan kawai ta displa manashi koma samu mu huce hushinmu ta nan,, kwashewa da dariya nabeela tayi tace "yashigeki da yawa gskia mutuniyar, sorry zo muje kawai, haka suka dauko mayafin suka karb'i key wajen Momy sannan suka fice, suna shiga falon gidan suna cin karo da hannat ta d'auki wani shegen dressing kamar ba 'yar musulmai ba, tana ganinsu ta dunga jifansu da kallon banza tana hura musu hanci tareda tabe manyan labbanta tai musu tsoki tai wucewarta tana karkad'a key din motar ta ahaka tai wucewarta.
dariya suka kwashe da ita harda tafawa da hannuwa bibiyu sannan da sauri kuma sukasa hannu suka rufe bakinsu suka koma yin ta ciki, basu jima ba hjy aina ta fito bana ganinsu kuwa tace "ah ashe har kunzo ina ciki ban saniba? ynxun muka gama waya da hajiya umaima din tace gashi nan ta turoku, amsan kayan da aka fudda muku, nabeela tace
"eh munata sallama munji shiru shine muka zauna jira, "ayya kuyi haquri 'yan matan umaimah bari naje na kawo muku kayan to,, komawa daki tayi ta dauko musu kayan cikin leda ta miqa musu sukai mata sai anjima suka tashi suka tafi tana nan tsaye tabi bayan ummu hani da kallo cikin jin haushi,
ta sa yatsa a baki ta ciza tace "gskia bnji dad'in rashin samun wannan dirarriyar yarinyar da bnba dana sameta aidana qara zama multimiloneir ta hnyar ta da wannan kyawun nata, amman gashi can ta zauna inda saidai taci tasha ta tsoma goma tasa biyar basa nemn kudi da ita??
cije lebe tayi tace "kai Allah tsinewa asara da rashin rabo ma wlh basuyi ba arayuwa"
tatab'e baki tace
"ya zanyi inda rashin rabo ya hauni sai haquri ai.
haka tayi juyawarta ta shige daki.
da daddare ne bayan mua'zzam saraki yagama kallon sa na N.T.A, ummu hani tana d'aki kwance, sanin datayi amakson din ta na falon shiyasa taqi fitowa ta jawo wayarta tahau chat itada nabeela. annah tana gefe itada mahabeer yasa mata rigiman saiya gyara mata zungurunta daya sassako.
saida ya gyara mata sannan yayi komawarsa ya kwanta kusada dady mua'zzam saraki yace
"dadyna tun safe nikeson ganinka in maka albishir, momy bata gaya maka bane naji bakace komi ba?, dadymua'zzam yace "albishir nami kuma sojana?
duban Momy umaimah mahabeer yayi cikin marairecewa yace "momy kin manta halan baki fad'a masa ba? tace" bn mnta ba mahabeer na inda harna fadawa annah mah, shima dadyn naka dan bainan shiyasa, kuma da yadawo masallaci ya wuce, yana tasowa kuma kaga labarai ya tsaya kallo amman inda gaka gashi saika fad'a masa inda ance waqa a bakin mai ita tafi dad'i, babu b'ata lokaci kuwa mahabeer yace "dady daman maganar school din nan ce ta London wacce kasa natura request nason yin apply akan tsarin school dinsu na harkar sauqaqa kudin petroleum na qasanmu to shine d'azun da safe sukai accepting nawa ta hanyar @mail da suka turomin,
sunce cikin wannan month din zasu fara project ga d'alibai, shine nikega a satin nan zan fara shirin shirye shiryen tafiya,r dama munyi da bash zai zauna min a office yana kula da komi kamin na dawo",,
cikin fara'a mua'zzam saraki ya miq'a wa d'an nasa hannu suka jinjuna as usual sannan yace "dhat is gud sojana, haka nada kyau kam saika fara shirin tafiya, Allah shi temaka
"amunn"
cewar momy umaimah.
Annah tace
"uhumm kun gama??
nace kun gama tsarin naku kaida iyayen naka marasa tunani suma ko dukanku?
to naji naku bayanin Saura nima ku saurara kuji nawa bayanin da zan muku yanzun nan basai anjima ba. dukkansu da kallo suka dinga bin annah cikin mamaki suke sake duban annah cikin qarfi hali dady mua'zzam yace ''annah yi haquri dan Allah wani abunne ya faru??
Annah tace "abinda zai farun ne dai ne nike shirin dakatar dashi in kuma kukabi abinda zance to falil lahil hamdu,, shiyasa koda umaimatu ta tunkaroni da maganar tafiyan nasa d'azun shiru nayi da nufin sai naji yanda kai zakace sannan, yanzu kai mua'zzamu da hankalin ka da tunanin ka zaka barsa yatafi har can qasan turawa batareda mata ba? to wlh bazan amince ba in ku kun amince,
haba wannan qasashen da suke cike da marassa ta ido dud yanda mutum yakai ga kame kansa