Showing 1 words to 3000 words out of 72611 words

Chapter 1 - farouk Ko haidar complete by one love.pdf

Advertisement

One Love   

23 Mar 2025

5810

 📑farouk Ko haidar 📑

Story and written
-by- deeja one love �


Dedicated to madina m umar.🌹

Bismillahir rahmanirrahim.

Wannan littafin kirkirarrene bawai ya
Faru da gaske bane.

Godiya gareki Dijency saboda da taimakonki na Gama littafina me suna MATA TA GARI.

0⃣1⃣
Rana ake yi me zafin nan Wanda har Tana makogoronka zakaji yana kokarin fashewa saboda
azabar kishi,
Dai dai sha biyu da Rabi yayinda
Ya keto tsakiyar k'auyen su, tafiyace me tsayi yayi kafin ya k'araso Cikin garin.
A gajiye yake ga zufa ga yunwa da kishirwa, kusan ya Saba da hakan tunda mutane daidaiku
ne ke Karatu a k'auyen
Kasancewar mutanen ciki basu Wani damu da karatun ba hakan yasa ko primary babu a Garin.
K'auyen Sarina kenan dake Wanda mutanen Garin suka fi bawa noma da kiwo mahimmanci,
Garin Darki dake gabansu garine babba Wanda kan mutanen ciki yafi na Sarina wayewa
Hakan yasa sukeda makarantu da sauransu.
To sai Ya kasance Idan kanaso kayi Karatu sai dai kaje can wannan Abin shi yafi bashi haushi.
Duk da agajiye yake zaka iya shaida kyawunshi
Farine Wanda ba irin na tashin hankali ba.yanada tsayi Wanda ya dace da daidai jikinsa. Yatsun
hannunsa Zara Zara Wanda yake sanye da Wani irin zoben azurfa Mai kyau irin na da d'innan.
Idonshi Manya ne sosai yayinda suke a Fuskarsa me Dan tsayi.
Hancinsa dai dai Wanda ya dace da yanayin Fuskarsa Wanda bakinsa ya kasance karami dake
zagaye da pink lips.yanada dimples Wanda duk lokacin daya motsa bakinshi zai lotsa.
Ba Wani babba bane a shekaru sosai tunda yanzu ne ya Kai shekaru goma sha takwas.
Dai dai Wani gida ya tsaya Wanda a haka zaka dauka karamin gidane amma sai ka shiga Ciki.
Gidane me sa-sa da yawa
Tundaga zauruka zaka Fara shaida hakan dakuna ne jere inda nanne samarin gidan ke zama
Daya daga Cikin dakuna nan samarin Ya bude ya shiga
Tsaki k'arami yayi kasancewar yadda ya bar d'akin haka ya dawo ya sameshi
Tabbas iro be gyara dakin nan ba
Littattafansa dake baje a k'asa ya kalla Cikin takaici
Hadawa Ya yi Ya maida su inda suke
Kafin ya Soma cire kayan makarantar murmushi yayi Tunawa da yayi yanzu fa Allah Ya

taimakesu shi kenan angama da secondary Dan yau suka Gama zana NECO
Cikin gidan Ya shiga
Tun daga farkon gidan har k'arshe d'akuna ne.
Yawancin matan suna zaune Kowacce
Da d'aurin k'irji.
Wasu na sana'a wasu na aikin su. Bangaren baffa mudi kenan shine babba Wanda yakeda
mata hudu babbar matarsa tanada Yara goma sha biyu, sai Mai bi mata Inna uwale tanada yara
goma cif cif itakan masifaffiyace hakan yasa Kowa baya kulata.
Sai Inna saude Wanda take da yara goma sha d'aya itakan mata ce me kawaici da sanin Ya
kamata
K'aramarsu Inna Hari fitinanniyar matace ta bugawa a jarida yaranta takwas.
Sallama ya kuma yi kafin su amsa
Gaishe dasu yayi sannan ya wuce
Wani bangaren still ya kuma shiga Wani bangaren nan kuma bangaren baffa habu kenan shima
matansa hudu yara ashirin da hudu.
Shima dai gaishesu yayi wasu sun amsa wasu Ko kallo be ishesu ba
Bangare na uku shine bangaren baffa Adamu bangarene tsaftatacce me kyau
Daga gani na cikinshi Sunada tsafta
Shi kuma mata biyu gareshi kacal
Matarsa Inna Mari da Inna hadiza
Inna Mari matace me ha'kuri da sanin Ya kamata itace matarsa ta farko ta dade bata haihu ba.
Sai Inna hadiza matace me tsananin fad'a amma Idan ka tab'o ta kenan sai dai suna zaman
Lafiya fiyeda sauran 'yan gidan.
K'ofar d'akin Inna Mari yayi sallama ya shiga Tana zaune Tana yanke farce
D'agowa tayi tace
Wa'alaikumussalam sannu da dawowa.
Murmushi yayi yace
Inna na gaji.
To zauna mana sai na amso maka abincinka
Ta gaya Tana k'ok'arin mik'ewa.
Dakata Inna ki Bari zanje da kaina
Cire rigar jikinsa yayi Ya fita
Bokiti ya dauka Ya Debi ruwa Ya shiga bayi yayi wanka .
Yana fitowa ya shiga d'akin Inna hadiza akwance ya sameta.
Sai wata 'Yar budurwa zaune gefenta da tire da alamu talla zata tafi
Had'e rai yayi yace
Ke humaira
Da sauri ta d'ago idanunta kasancewar tasan shi kad'ai yake kiranta da wannan sunan dariya
tayi Wanda kyawunta ya k'ara bayyana.
Meye haka ina zakije ne?
Inna hadiza ta dago ta kalleshi tace
Jarababbe ka dawone?
To talla zataje naga ta yadda zaka hanata Dan yau baka isa ba

Juyawa tayi kanta tace
Kin d'auka kin tafi ko sai na tashi na b'allaki.
Da sauri Indo ta d'auki tiren ta fice.
Kai kuma Idan zaka shigo ka d'auki abincinka to Idan kuma Tsayawa zakayi Anan to kayita
Tsayawa har mahadi ya bayyana
A zafafe ya saki labulen d'akin Ya juya Ko d'akin Inna Mari be koma ba ya fice.
Can wajen wata bishiyar mangoro yaje ya zauna kasancewar ranace duk sun tafi gona Ko kiwo
ya sa shi kad'ai Ya zauna a wajen.
Rik'e kansa yayi dake barazanar fashewa.zuciyarsa Kamar zata Faso haka yakeji.
A hankali ya dinga sauke numfashi har ya daidaita
Yafi minti ashirin a zaune sannan ya tashi ya yi hanyar Bayan gari Ya nufa
Tafiya me nisa yayi Tsakanin gonaki wajen wata gona ya shiga.
Zaune a inuwa suke su shida wasu na cin abinci wasu na alwala.
Daya daga ciki Wanda da alamu Ya girmeshi yace
Barka da dawowa 'yan makaranta.
Waje ya nema Ya zauna Gefensa Ya kalla yace Ina baba?
Dayan daya Gama alwala yace
Lafiya kuwa Kake farouk? Kanaji musa na maka magana kayi banza dashi
Yace
Ya mutsa fuska yayi yace
babu komai
Musa ya Kalli Wanda ke zaune Yana cin abinci yace
Audu kira baba kace ga Dan Gata Ya dawo.
Yanzu fa zai dawo ka bari yazo mana
Kallonsu yayi dukansu duk 'ya'yan baba Adamu ne duk da sun San baban yafi sonshi basu
tab'a damuwa da hakan ba.
Musa yace
Ibro ku kyaleshi Dan Allah kunsan yaya lafiyar kura bare tayi Hauka.
Ku Bari zaizo ne yanzu
Shidai farouk be ce musu komai ba
Kusan minti sha biyar sannan baffan ya bullo ta tsakiyar duhun Dawa
Tsoho ne Dan ya Fara tsufa
'ya'yansa guda takwas ne.
Bakwai maza d'aya mace
Babansu shine k'asimu sai Mai bi masa musa sai ibro Wanda wajen sa'an farouk ne sai bello
sai Audu sai k'araminsu harisu maccer kuma Aisha Wanda suke ce mata Indo
Yarinyace 'Yar Gata a wajen yayyenta komai suka samo Nata ne.
Dukkansu Kansu a Had'e yake daga k'asimu sai musa su kad'ai ne sukayi aure
Su bakwai yaran Inna hadiza ne farouk ne kawai d'an Inna Mari.
Tashi farouk yayi yaje wajensa yace
Baffa sannu da aiki.
Yauwa sannu yarona.
Andawo an Gama kuma?

D'aga Kai kawai yayi
Kallon 'ya'yansa yayi yace
Waye Ya b'atawa umar rai kuma daga dawowa.
Ibro dake alwala Ya mik'o wa baban buta yace
Gashi baba sai ka wanke masa.
Dariya sukayi duka
Farouk kuwa murmushi yayi yace
Baba nifa Inna k'arama ce.
Dariya suka kuma yi kafin musa yace
Fad'anku waye zai shiga ku bashi kunya.
Ato dai ai kunfi Kusa yanzu kaci abincine?
Baba Ya tambaya
Girgiza Kai yayi yace
A'a
Juyawa baba yayi yace
Kai Audu zubawa Dan uwanka abinci.
Zuba masa yayi kad'an yaci Ya tashi shima yayi alwala sukayi sallah dukansu sannan suka
Fara aiki.
Duk da kansa Kamar zai fashe amma haka ya daure yake yi domin iya kawaici da mutunci suna
yi masa
Zaije makaranta tun yana k'arami su suna noma kuma Idan lokaci yayi na biya masa kud'in
makaranta Haka za'a d'auki abincin da suka noma a biya masa ko siyan litattafai.
Yanzu haka tunda ya Fara jarabawa suka sauka barinsa yana aiki sai dai yayi karatu.
Tun sauran 'yan gidan na magana har sun gaji sun Dena ma.



📑farouk Ko haidar 📑


Written by
Deeja one love �

Dedicated to madina m umar

0⃣2⃣
Suna isa gida yamma tayi matan
Kowa Na hada hadar d'ora girki
A sasan su ma Hakane Inna Mari ce keta iza wuta
Sannu da aiki sukayi mata
Yauwa sannunku Ya aiki
Alhmdllh Inna Bari na tayaki
Farouk ya gaya yana tsugunnawa

Tabbas yasan daurewa kawai yake amma da wuya Idan ba ciwon kan sa bane zai tashi
Gashi maganinsa ya k'are
Inna ta tab'ashi tace
Lafiya Kake kuwa?
Eh Inna lafiyata lau Ina Indo.
Inna tace
Ta d'auki gyad'a ta fita talla.
Had'e rai yayi yace
Kina kallo kuma ta d'ora mata.
Toh ikon Allah sai kuma a k'i d'ora mata talla Wai Meke da munkane
Abin fifita Wutar Ya ajiye Ya fice daga gidan
Jinjina Kai Inna Mari tayi tace
Allah Ya kyauta
Yana fita Dandalin Garin ya nufa na yamma
Maza da mata ne dank'am Kowa na harkarsa
Can ya hangota gefenta sani ne zaune sai faman fira sukeyi
Da sauri Ya koma da baya Ya jingina da itacen mangoro dake wajen
Runtse idanu yayi zuciyarsa na masa zafi
Hannunsa ya hade Waje d'aya ya matse yana Jan numfashi da k'yar
Dafashi akayi
Yana Juyowa yaga d'an uwansa Audu ne
Lafiya Kake kuwa?
Audun ya tambaya
D'aga masa Kai kawai yayi
Tsugunawa yayi a wajen ya dafe kansa
A sanyaye Audu yace
Kan ne.?
Ido jajir ya d'ago yace
Audu banason tallan da Indo takeyi duba ka gani dariya takewa sani Idan nayi magana kuce
Wai Na hanata neman kud'i
Na rasa meyasa bakwa fahimta.
Dafashi Audu yayi yace
Kada ka damu muna sa ido sosai akanta kaga bazata fad'a wata hanyar ba.
Kauda kansa gefe yayi kawai
Meyasa basa fahimta ne Oho?
Sun dad'e a nan suna fira kafin ayi kiran sallar magrib su tashi su tafi masallaci
Suna dawowa gida suka nufa
Kowa yana d'aki suka shigo
Farouk yacewa Audu
Ina zuwa Bari nayi wanka
Dariya Audu yayi yace
Ai Ko agwagwa bazata nuna maka wanka ba.
Shidai be ce komai ba ya dau bokiti ya ja ruwa a rijiya Ya shiga wanka

Yana fitowa ya tarar da duk sun fito domin cin abinci Dan a tsarin gidan Idan akayi magrib to
Akan shinfid'a k'atuwar tabarma ne domin cin abinci
Gaba d'aya 'ya'yan baffa Adamu ne zaune suna cin abinci
Sallama baffa yayi Ya shigo
Da sauri farouk Ya mik'e ya amshi ledar hannunsa
Wajen Inna Mari Ya ajiye sannan ya dawo ya zauna
Fruits ne Wanda ya Saba siyowa.
Kasawa akayi Kowa Ya d'auka
Bello ne yasa hannu ya dauki na Indo
Ihu ta saka Tana sai Ya bata
Audu Ya daka mata tsawa yace
Dalla rufewa mutane baki wawiya kawai
Harara farouk ya aika masa yace
Kaga malam ka Barta tayi kayanta
Kai bello bata kayanta kafin na tashi
Da sauri Ya ajiye mata ya bar wajen
Baffa yace
Ni Na rasa wannan soyayya dake Tsakanin farouk da Indo
Inna hadiza tace
To ai kuma gashi ya shagwab'ata kuma gaba ina jiye masa ba.
Dariya Inna Mari tayi tace
Sunfi Kusa dai
Tab'e baki Inna hadiza tayi tace
Hakane kam amma Aini a wajena zata sha wuya.
Dariya sukayi kafin baffa yace
Ikon Allah ni na rasa meke faruwa kwana biyu Tsakaninki da d'an naki kwana biyu.
Wai Dan na Fara d'orawa Indo talla
Murmushi farouk yayi Ya mik'e yace
Humaira let's go
Harara Inna hadiza tayi tace
Kaga ka kiyayeni wace gulmar Kake mata.
Shidai gaba yayi be ce komai ba
Da Dan D'aga murya tace
Ni nake maka magana kana tafiya Ko?
Juyowa yayi Ya nuna mata kanshi.
Dan sauri suka Fara tambayar lafiyanshi
Har tausayi suka bashi wannan wace irin k'aunace?
Inna hadiza tace
Allah Ya sauwake Audu ya siyo maka maganinka a wudil gobe
Baffa yayi murmushi yace
Hadiza kenan kuyi fad'a da d'anki ku shirya Wanda ya shiga kuma yaji haushi.
dariya tayi tace
Duk abinda Kake so muna tayaka sonshi

Allah dai ya muku albarka
Ameen suka amsa gaba d'aya
Bangaren farouk kuwa
D'akinu Ya shiga Indo na bayanshi
Kallonta ya yi yace
Ya kin iya na jiya ?
Eh
Ta bashi amsa
To karanto
Thank you -na gode
Where are you -kana ina
How are you -ya Kake
Pls borrow me your ball -dan Allah ara mini k'wallonka.
Murmushi yayi yace
Gud gal yayi yanzu ki Bari gobe na k'ara miki.
to
Ta fada Tana wasa da yan yatsunta .
kiran sunanta yayi yace
Humaira Meye d'azu sani yake gaya miki kike dariya
Zaro idanu tayi tace
Yafa ce kada na gayawa Kowa
Gabanshine ya fad'i yace
Kamarya gaya mini.
ganin babu wasa a Fuskarsa yasa ta cewa
Dama cewa yayi yana sona
Zaro idanu yayi yace
Da gaske
D'aga Kai tayi Alamar Eh
Zuface ta Fara keto masa Ahankali Ya koma ta kwanta
Shiru d'akin na wani lokaci kafin yace
kuma kema kina sonshi
Daga Kai tayi Alamar Eh
ganin kallon dayake matane yasata saurin girgiza Kai
A zafafe ya mik'e ya fincikota
Yatsunta guda biyu ya matse
Tsabar azaba hawaye kawai ke zuba daga idanunta.
Tabbas tasan ya farouk akwai mugunta
amma Ta yau ta tsorata da ita.
📑farouk Ko haidar 📑


Written by deeja
One love �

Dedicated to madina m umar 🌹

0⃣3⃣
Cikin hasala yace
Bana ce kada kiyi soyayya da Kowa ba?
D'aga Kai tayi Cikin azaba tace
Bazan kuma.
Ta saki kuka
Ahankali Ya saketa Ya koma ya kwanta.
Hanyar Waje ya nuna mata
Da sauri ta fice Tana kuka
Bata shiga d'akin Inna hadiza ba Dan tasan halinta
D'akin Inna Mari ta shige
Inna Mari na uwardaki tajiyo kuka
Fitowa tayi Tana fadin
Indo keda waye?
Cikin sheshsheka tace
Ya farouk ne
Ikon Allah me kuma ya had'aku?
Inna Mari ta tambayeta
Wai Dan sani yace Yana sona.
Shiru Inna Mari tayi Tana mamakin wannan Abu
Janyota Jikinta tayi Tana rarrashin ta
Ki Bari da safe zan masa magana
Bangaren farouk kuwa Tana Fita ya mik'e Ya zauna
Tabbas babu aure a Tsakaninsu tunda mahaifinsu d'aya to amma Kamar yadda yayi alk'awarin
shi zai Nemo mata miji to bazai Bari taso Wani ba (Kaji farouk da K'ok'ari�)
Da safe yana tashi yaji Alhamdulillah kan ya Dena ciwo hakan yasa ya shirya da wuri suka
wuce gona
Suna zaune suna fira ta ratso hanyar
Kanta d'auke da kwano gefenta wata k'aramar yarinyace
Tasha ado irin na garinsu.
Bello da Audu suka Kalli farouk suka Fara dariya
Had'e rai yayi Ya juya fuska
Sallama tayi musu suka amsa
Kallon farouk tayi tace
Umaru gafa abinci
Ko kallonta beyi ba bare tasa ran zai amsa
Audu yace
Ke Abu ki ajiye mana zaici ne
Harara ta balla masa tace ina ruwanka
Dariya yayi yace

To daga gwaninta ai sai ki bada himma
Kallon farouk tayi tace
Umaru kanaji ina magana kana banza Dani
Mik'ewa yayi Ya bar wajen
Kallo ta bishi dashi
Duk iya daurewar da su Audu sukayi sai da sukayi dariya
K'ara k'uluwa tayi ta tashi ta tafi Tana kuka
Audu mik'e yaje Kusa dashi yace
Haba farouk ka Dena mata wulak'anci mana
Shiru yayi
Audu yace
Nifa wannan miskilancin naka haushi yake bani fa
Still beyi magana yayi
Indo ce ta k'araso ta gaishesu ta ajiye musu abinci
Farouk yace
Humaira
Da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login