Showing 54001 words to 57000 words out of 72611 words

Chapter 19 - farouk Ko haidar complete by one love.pdf

Advertisement

One Love   

23 Mar 2025

5837


ayi.

Sai da suka Kara kwana sannan suka tafi taraba,kowa zolayarsu yake akan angwaye,duk da
babu mai wata matsalar da azahirance sai haidar wanda a fili yake nuna bayaso,shi kuwa
farouk nauyi abin yake mishi.

Momma cikin farin ciki ta amshesu,sai zolayarsu take,haidar ya tabe fuska yace"momma pls ki
dena".

Salim yayi dariya yace "bakasan me ba wai salim da mata!,haidar yace"za'a ga shiririta",hararar
haidar farouk yayi,yana dagowa suka hada ido da momma kauda kai yayi yana murmushi.

Da dare momma tayi sallama ta shigo,farouk ke duba takardu,,salim da haidar duka sunyi barci.

Murmushi farouk yayi yace"barka da dare momma",hannunshi ta rike tace "sannu da aiki",shiru
sukayi na wani lokaci.

A hankali momma ta murza hannunshi tace"hadin yayi maka?,saukar da idanunshi kasa yayi
yace"wanne fa?"

Murmushi tayi tace"Wanda mai martaba yayi"kallonta yayi yace"idan beyi ba za'a canza
ne?daga kai tayi tace"idan har bakaso sai a canza",murmushi kawai yayi yace"momma kina
nuna bambanci,"
Katseshi tayi tace"kamar yadda kake nunawa ko?,

Hannunta ya rike yace"ba haka bane haidar Dan uwanane awajen haihuwa tare aka haifemu
haka zaman da mukayi a mahaifarki don haka duk wanda zanso a bayanshi yake.

Jinjina kai tayi tace"hakane na yarda da abinda ka gaya"tambayarta yayi yace"to ke me yasa
kike nuna bambanci?,kanshi ta kwantar a jikinta tana sa hannu a cikin sumarshi.

Ahankali take shafa kanshi har barci ya daukeshi,murmushi tayi sannan ta gyara mishi
kwanciya tayi addu'a ta shafa mishi,wajen haidar ta matsa shima addu'ar tayi ta shafa
mishi,hakama salim,sannan ta kashe light ta fita.


Sai da akayi kiran sallar asuba sannan suka farka,koda suka idar da sallar suna dawowa barci
suka koma.


Sai goma sannan suka tashi,wanka sukayi sannan suka fito domin karyawa,a dinning area suka
samesu duka domin yau weekend ne.

Murmushi momma tayi tace"sai yanzu?
Dariya salim yayi yace"Allah momma kinsan nan yafi adamawa dadin zama,dariya sukayi gaba
daya,farouk kuwa murmushi kawai yayi.

Daddyn baby yace"kaima zama da farouk ya sa kana neman kaki dangi ko?",haidar ya cuno
baki yace"Damuwace kawai tayi yawa acan.

Da mamaki momma tace"adamawar?",daga kai haidar yayi yace"kullum busa ke tada mutum a
barci kamar ana farauta,salim ya kara da cewa"ga kuyangu da bayi duk inda kayi ana damunka.


Daddyn baby yace"da har zan bawa mai martaba shawara akan cewa idan ya tashi murabus ya

dora ka,da sauri haidar yace"wa kenan?"gimtse dariyarshi daddyn baby yayi yace"kai
mana,haidar da salim suka kalli Juna suka fashe da dariya.

Salim yace"da kuwa anga shiririta"harararshi haidar yayi yace"wallahi ka fita idona nine
mashiriricin?"salim yayi dariya yace"eh mana ai hakanne"haidar ya daure.

Momma ta mikawa farouk tea tace"nidai Ku bar maganar haka shima tsokanarka yakeyi,haidar
ya cuno baki yace"momma ai wallahi banason wannan tsokanar",salim ya kwashe da dariya.

Haka suka cigaba da shirmensu har aka gama breakfast din,baby da momma suka kwashe
kayan.

Su farouk kuwa palour suka koma shidai farouk channel ya kamo na news,salim da haidar
kuma suka cigaba da shirmensu.


Da yamma suka shirya suka fita,a wani mall suka fara tsayawa sukayi siyayya ,shidai farouk
yana makale da humaira duk inda tayi yana binta,salim yace"mutumina kaga abinda Dan uwa
yakeyi kuwa?"haidar yace"to sai me shi zai jawa kanshi raini",salim yace"to nima na tafi,


Haidar ganin kowa ya tafi nashi wajen yasa shi matsawa kusada surayya,harara ta aika mishi
shima harararta yayi ya kauda kai,jin shirun yayi yawa yasa surayya ta nufi mota,ganin ta tafi
yasa shima binta,a motar suka zauna har su farouk suka gama siyayyar suka taho.


Kowa motarshi ya shiga sannan suka dauki hanya wani garden suka tsaya,haidar ya hade rai
yace
Meye haka kuma,hannu ya fito dashi ta glass ya musu nuni da lafiya?,salim ya nuna mishi
Alama da su shiga.

Tsaki yayi sannan ya fito,itama surayya ta biyo bayanshi, kowanne wajen zama ya nema.


Farouk ya kalli indo yace"me za'a kawo miki?",sai da tayi fari tace"coke ma ya isa,kasa cewa
komai yayi shikuwa waiter tafiya yayi domin kawo mata.


Farouk yace"waya koya miki?",tace"me kenan?
Dan juyar da kai yayi yana murmushi shidai yasan baya kin humaira haka baya jin xai iya zama
da ita amatsayin matarshi.

Haidar ya dago ya kalli mutanen wajen yayi tsaki ya cigaba da danna phone dinshi,surayya
itama tayi tsaki ta dauko wayarta ta danna ,kiran yusra tayi suka fara fira(kasancewar su
kowacce mai martaba yace Wanda zai aureta shi zai kaita hakan yasa yusra take adamawa
wajen ammar sai gobe zai kaita Zaria daga nan ya wuce India ita kuma husna yau suka tafi
abuja da faisal sai gobe suma zasu wuce Zaria), haidar dai kallonta kawai yakeyi"wai wannan
ita zai aure she is too prideí ½í¸!


Ganin bazasu tafi da wuri bane yasa shi mikewa,a Mota ya tsaya jiran surayya,ita kuma ganin
be ce Mata ta taso ba yasa tayi zamanta,ganin taki tahowa yasa yaja motar da sauri ya bar
wajen.


Dariya salim yayi yace"Dan rainin Wayo",sumayya tace"meya faru wallahi no nasan za'ayi show
mai dadin kallo a gidansu.


Farouk ya dubi ya salim da hannu ya nuna mishi alamun lafiya,salim ya daga kafada alamar be
sani ba.

Farouk ya dubi humaira yace
"Zo muje kinga haidar has gone ya kamata mu wuce muma,murmushi tayi sannan ta mike.


Ganin duk sun mike yasa surayya itama mikewa,motar farouk ta shiga.


Koda suka je gida motarshi bata nan,da mamaki farouk yace"ina to yaje?"surayya ta tabe baki.

Koda suka shiga azaune suka tarar da momma,kunyace kuma ta kamasu,humaira dai bayan
farouk ta boye,ita kuma sumayya tayi sama da gudu.

Momma tayi dariya tace"yaran zamani wato kun gama soyayyarku yanzu kuma zaku zo kuce
kuna jin kunyata.

Shi kanshi farouk din kamar kasa ta bude ya shige haka yake ji,shafa fuskarshi yayi sannan
yace"barka da yamma.

Amsawa tayi cikin farin ciki domin tasan sunyi na'am da zabin mai martaba kenan
*📑FAROUK KO  HAIDAR* 📑

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~💫💫💫*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~â„we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our
creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u
np pain~*

written� By Deeja One Love

54-55

Momma tace"ina haidar ne?"farouk yayi saurin cewa ya biya ta wajen wani abokinshi ne.

Haidar kuwa sai dare sannan ya dawo,a tunaninshi duk sunyi barci Dan haka wanka kawai yayi
ya kwanta.

Yana kwanciya farouk yace"da gaske baka sonta?,girgiza kai yayi yace"a'a kawai her pride
extend the limit."

Dariya abin ya bawa farouk,murmushi yayi yace"Allah ya kyauta"ameen,haidar ya amsa.

Bayan sunyi break fast da safe momma tace"kuzo muje  wani waje"cikin farin ciki suka Tashi.

Unguwar dake gaba dasu kadan sukayi horn a dai dai wani gida,plat mai kyau,sai santi sukeyi
dan dai-dai ne.

Haidar yace"momma nan ina ne?"hannun farouk ta rike tayi murmushi tace"gidan dana siyawa
baffa ne inaso su dawo nan,farouk besan lokacin da murmushi ya subuce masa ba.

Sun zagaya gidan yayi kyau sosai kuma sunyi murna,salim yace"su humaira za'a shigo birni.

Murmushi kawai farouk yayi,haidar ya hade rai yace"momma kina ganin nawan ko bambanci
yake nunawa.

Farouk ya kalleshi yace"me kuma nayi?",haidar ya harareshi yace "da nine na fadi abinda salim
ya gaya da yanzu ka harareni,amma da yake Dan gwal ne murmushi kawai kayi.

Dariya salim yayi yace"jealousy",sumayya tace"Allah ko ni haka nake gani wallahi yaya haidar
kada ka yarda,harararta salim yayi yace"waya saka baking",haidar yace"gulma fa"tsaki surayya
tayi tace"Allah ya Kara"

Kafarta haidar ya taka da karfi,tsabar azaba batasan lokacin da tayi Kara ba,cikin sauri momma
tace"lafiya kuwa?"

Suna hada idanu da haidar ya galla Mata harara da sauri tace"babu komai",murmushi momma
tayi .


Suna komawa gida suka shirya domin tafiya kamar yadda sukazo haka suka tafi kowa a
motarshi.

Farouk ya dauke hanyar kano su kuma suka wuce adai-dai Zaria sumayya ta koma motar
haidar ya ja suka tafi,shi kuma farouk ya tafi gida.


Yau satin su daya da dawowa farouk yana zaune humaira ta shigo,kallo ya bita dashi,tab
wannan za'a aura masa hmm! Da sake aradu😄.


Gefe ta nema ta zauna kallonshi tayi tace"yaya na kawo maka abinci,girgiza kai kawai yayi,shiru
tayi tana wasa da yatsan hannunta.


Shi kuwa zuba Mata idanu yayi yana tunani,inna Mari tayi sallama ta shigo ,da murna tace"ga
baffanku can ya dawo yace kuje"a tare suka mike suka tafi,

A zaune yana cin abinci,yana garinsu yayi murmushi yace"alhamdulillahi dazu mai martaba ya
kirani yake gaya mini abin arziki.


Da mamaki farouk yace"me kenan?",Dan murmushi yayi yace"mai martaba ya biya mana hajji
wannan Karan zamu sauke faralli.

Dariya farouk yayi yace"Allah ya sanya alkhairi zan kirashi na mishi godiya,shafa kanshi yayi
yace"Allah ya muku albarka ga kanwarka nan Dan allah ka riketa amana.

Sunkuyarda kai yayi yace"insha Allah baffa dame zan saka muku irin abinda Kuka yi mini.

Baffa yace"kai dana ne farouk Dan haka duk abinda nayi maka sauke hakkine ,sannan insha
allahu bazaka tabe a rayuwa ba iya biyayyar da kake mini ko Dan Dana haifa sai haka.

Shiru wajen yayi kafin baffa yace"kunci abincin?",girgiza kai farouk yayi,baffa ya kalli humaira
yace kawowa farouk abinci mana.

Washegari da yamma farouk ya shigo gidan waya a kunnenshi da alama waya yake yi.

Humaira dake wanki ta amasa sallamarshi ta cigaba da wankinta daga nesa ya  ya tsaya

yace"haba salim idan kayi wani abin sai kace yaro karami haba yaushe muka rabune.

Sallama momma tayi ta shigo,da mamaki farouk ya kalleta human kuwa da gudu taje ta
rungumeta,shafa kanta tayi tace"anata wanki ne"daga kai kawai tayi.



Farouk ta kalla tayi mishi alama da yazo,murmushi yayi sannan ya matso kusa da ita,cikin sauri
ta rungumoshi,wanda yayi dai-dai da fitowar inna Mari.
Momma cikeda kunya ta sake shi,inna Mari kuwa yi tayi kamar bata gansu ba.


Washe baki tayi tana musu sannu da zuwa,karasawa tayi,bayan sun gaisa sannan inna Mari
tace"bari a Kira baffan.



Bayan farouk ya Kira baffan,yana shigowa ya ganta shima cikin murna ya Mata sannu da zuwa.


A varender suka zauna,humaira ta kawo Mata ruwa da drinks,murmushi tayi tace"sannu da
aiki".


Bayan Tasha ta kalli baffa tace"abinda ya kawo ni nan shine naji ance mai martaba ya biya
muku aikin hajji,to shine nace mai zai hana kuyi parking ku koma gidanku idan yaso sai ayi biki
kunacan"


Murmushi baffa yayi yace"hajiya banki ta taki ba sai dai inaso ya kasance bikin farouk a kano
za'ayi shi zai zama zamu je mu amso mishi auren hunaira a wajen yan uwana idan akayi haka
sai washe gari a wuce adamawa",



Shiru momma tayi na Dan lokaci kafin tace"shikenan hakan ma yayi,idan Allah ya kaimu bayan
biki sai Ku koma"


Inna Mari tace"ni aganina mai zai hana idan mun dawo saudiyya sai mu sauka acan"


Baffa yace"kwarai kuwa kin kawo shawara mai kyau hakan za'ayi".

Momma tace"to bayan wannan inaso idan babu damuwa a bani amarya na tafi da ita"baffa yayi
dariya yace"wannan kuma keda yar ki amma ni ango yana nan.


Dariya itama momma tayi kafin ta kwalawa humaira Kira,cikin sauri humaira ta fito,momma tayi
murmushi tace"dauko hijab mu wuce ko.


Humaira ta Amsa sa to,sai da ta Kara gyara fuskarta sannan ta dauko hijab din.


Inna hadiza tace"aifa dama akuyar daure ta sami sake babu tamabayar ina za'a je babu komai.


Humaira ta rufe fucks tace"ai nasan momma bazata kaini inda zan cutu ba.


Kowa na wajen yaji dadin maganar data gaya,farouk kuwa ji yayi kamar ya janyota ya
rungumeta,momma ta kalli inna hadiza tace"to kinji ko?


Har bakin mota farouk ya rakasu,momma ta kalli farouk tace"to sai bayan an daura aure ko?"
Shafa kanshi yayi yace"momma!.

Kudi ta ciro ta mika mishi tace"gashi ka rike wannan a hannunka,sati mai zuwa zan aiko maka
da sako"murmushi yayi yace"to momma Allah ya kiyaye hanya,ta Amsa da ameen,shigewa
Mota tayi ta barsu domin suyi sallama.



Shiru wajen yayi,ahankali humaira ta dago,idanunshi na kanta hakan yasa idanun nasu
haduwa,a lokaci daya zuciyarsu ta buga,tunda aka sa musu rana yaune ranar da suka tsaya
cikin kwanciyar hankali suka kalli juna.


Momma ganin kallon yaki karewa yasa tayi musu horn,cikin sauri farouk ya zare nashi idanun
ya maida kan momma,da hannu tayi mishi alamar lokaci.


Humaira kuwa sunkuyar da kai tayi tana wasa da yatsun hannunta ita kadai tasan me take ji
azuciyarta.

Farouk cikin dashewar murya yace"yanzu ya za'a yi mu dinga magana ko shikenan,girgiza kai
tayi tace"ka kira ata momma kawai.


Murmushi yayi yace"to shikenan amma ai bazan dinga ganinki ba,kasa tayi da kai tace"za kayi
missing dina ne?,waro idanu yayi yace"kefa?"daga kai tayi tace"sosai ma,
Lumshe idanu kawai yayi zuciyarshi na bugawa.



Momma ta Leko tace"ko na tafi na barku ne, da sauri humaira ta nufi motar,har ta bude murfin
kofar ta tsaya da sauri ta juyo tace"kai fa baka bani amsa ba.


Ido cikin ido ya kalleta yace"zanyi fiye da yadda kike tunani,murmushi ta saki shima haka ya
daga Mata hannu alamar bye.shiga tayi ta maida murfin ta rufe,momma tayi murmushi taja
motar.

Nidai nace"hmm su farouk an iya soyayya babu ko kunyar momma�



One love😘 taku ce â¤
*📑FAROUK KO  HAIDAR* 📑

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~💫💫💫*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~â„we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our
creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u
np pain~*

Written �by deeja one love


Dedicated madina m umar🌹


56-57

Direct Zaria suka wuce,mama ta taresu cikin farin ciki,humaira kuwa wajensu husna ta wuce.


Suna zaune salim ya shigo,cikin murna yace"oyoyo momma zuwa babu sanarwa,kallon
humaira yayi yace"momma kin biya kano ne?"


Daga kai tayi,cikin sauri yace"kin taho da farouk ne?"mama tace"ikon Allah farouk din yarone da
sai ta taho dashi.


Dariya sukayi duka,tabe fuska salim yayi yace"to ai nasan zai biyo ta ne,mama tace"ya biyo ta
yayi me?turo baki yayi yace"yazo wajena.


Rike haba mama tayi,momma kuwa murmushi kawai tayi,mama tace"to ai kai kasan inda yake
sai kaje,Kara turo baki yayi yace"ba abba ya hanani ba".



Dariya ma ya basu duka,momma ta rike hannunshi tace nan da sati both ne fa zaku hadu a
adamawa fa,Sosa kai kawai yayi.

Washe gari momma tace"dama fa Nazi tafiya da amare ne domin su zauna acan.


Abba yace"to ai babu matsala,ya kalli su husna yace"to ai sai Ku Tashi Ku shirya,humaira kuwa
murna takeyi za'a tafi dasu.


Daganan kaduna suka wuce,basu sami kowa a gidan ba sai surayya,tayi Murray ganinsu sosai.


Momma tace"ina mamien taking?",surayya tace"tana wajen aiki"momma ta kuma tambayarta
ina haidar fa tace"yana hospital tare da daddy.


Daki surayya ta kai momma tayi sallah sannan ta kwanta kasancewar batazo da kowa ba duka
a taraba ta bar yaran.


Sai shida mamie ta dawo,ganin momma tace"au ashe da baki a gidan,murmushi kawai momma

tayi.


Haidar kuwa sai bayan magrib ya shigo da murna ya matsa kusa da its yace"dazu ai salim ya
kirani ya gaya mini kinzo,hannunshi ta rike tace"eh da yau naso na koma amma ban same Ku
ba yanzu dole sai dai gobe.


Kanshi ya dora a kafadarta yace"shikenan hakan yayi ai.


Washe gari da wuri suka shirya,shima har parking lot ya kawota momma ta ciro kudi ta bashi
tace"sati mai zuwa za'a kawo muku sako in allah ya yarda.



Mota ta shiga ta barsu domin suyi sallama,gefe ya kalla ita kuma ta cigaba da Danna
wayarta,ganin shirun yayi yawa yasa ta dago ta kalleshi.


Dan tabe baki tayi ta juya ta fara Tasia,hannunta ya rike a hankali yace"Allah ya kiyaye
hanya,da sauri ta kalleshi kamar bashi yayi maganar ba Dan ko kallonta be yi ba,a sanyaye
tace"ameen.


Be saki hannun ba haka ita ma bata kwace ba,sunfi five minutes a haka Sannan ya saketa a
hankali,cikin sauri ta tafi har ta bude kofa sannan ta juyo ta kalleshi ,shima ita yake
kallo,murmushi yayi ya juyar da kai,itama murmushin tayi sannan ta shiga.



Tana shiga yusra ta kalle ta tace munafikai kuna so kuna kaiwa kasuwa,harararta surayya tayi
tace"ke kuma kina sa ido ko?,dariya sukayi,itadai momma batace komai ba.


Farouk ya kira mai martaba yana dagawa yace" abokina ya dai"?,murmushi farouk yayi sannan
ya gaisheshi,yace"mai martaba dama na Kira ne nayi godiya".


Mai martaba yace"tame fa?farouk yace"baffa yace ka biya musu saudiyy........'cikin sauri mai
martaba yace"ya isa haka Dan na yiwa su baffanka abu bai zama dole ka Kira kayi godiya
ba,umar ina son mahaifinka da mahaifiyarka sosai su kuma suna sonka,,,dole ne naso abinda
suke so ko?Dan na cika masoyin gaskiya�,abin dariya ya bawa farouk.

Bayan sunyi sallama da mai martaba ya kira momma,bangajiyar sauka lafiya yayi Mata,momma
tayi murmushi a ranta tace"shiyasa yafi Dan uwanshi shiga rai domin yasan meya kamata.



Farouk yace"momma me kike tunani ne,tace "babu komai farouk,shiru yayi yana so yace ta
bawa humaira kuma yana jin kunya.


Karshe dai sallama sukayi,shiru yayi kan can yayi murmushi,wayar surayya ya kira,a lokacin
suna zaune duka har momma a falo.


Bayan ta daga,ta gaisheshi,a hankali yace"ina humaira"?tace"gata a zaune,to bata.


Humaira ta mikawa wayar,tana amsa ta mike ta bar wajen,husna da yusra suka fara
tsokanarta,sumayya na tare mata,momma kuwa murmushi tayi,wato yana jin kunyar yace ta
bawa humaira kenan.



Kamar me rada humaira

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login