Showing 42001 words to 45000 words out of 72611 words
Chapter 15 - farouk Ko haidar complete by one love.pdf
kuma Salim ya Matsa Kusa dashi Yana kiran
sunanshi.
Kamar Wanda ya farka daga barci k'ok'arin mik'ewa yakeyi Wanda yayi daidai da karasowar
likitan tareda abba.
Cikin sauri abba Ya rikeshi
Likitan yace
Yanzu ya Kake jin jikin naka.
A hankali yace
Da sauki sosai
Likitan yace Da abba
Kubashi abincin da babu nama ko hanta ko alayyahu da kifi da wake
Sannan banda tea.
D'aga Kai Salim yayi.
Bayan likitan ya fita farouk ya Kalli Salim yace
Yadai kayi kuka Ko
Hararshi yayi yace
Bansaniba
Dan dariya yayi yace
Dagani nayi alwala nayi sallah
Dan shagwabe fuska yayi yace
Allah ka kuma irin wannan sai mun bata.
Murmushi yayi yace
Kaga bari nayi alwala nayi sallah sai mu zauna gaba daya
Kamashi yayi suka shiga bayi
Abba yayi murmushi yana mamakin shakuwar Salim da farouk d'in
Duba da yinin yau kwata kwata Salim d'in be ci komai ba
Sai da yayi wanka sannan ya dauro alwala yayi sallolin da ake binshi
Yana idarwa
Salim ya zubo masa sinasir Da miyar zogale.
Zubawa abincin idanu yayi Salim yace kaci mana
Kallon Salim d'in yayi Ya Wani bata rai
Turo baki yayi yace
Kasan bazan Ci ba Idan kaima bazaka ci ba .
Dan murmushi Salim yayi Ya saka hannu
Suna Ci suna fira
Abba duk da baya jin abinda suke cewa amma yana farinciki da Haduwar Kansu.
Wayar Salim tayi kara
Sai da ya Kalli agogo Karfe hudu da kwata
Cikin sauri Ya D'aga
daga Dayan bangaren haidar yace
Yaya Nawan ya farka Ko?
Kamar yana ganinshi ya balla harara yace
Bansaniba bayan barcinka kaje kanayi.
Dan marairaice fuska yayi yace
Wallahi ko kan dardumar ban sauka ba sallah naketa yi.
Dan murmushi Salim yayi yace
Gashi zaune muna fira
Cikin tsananin murna yace
Bashi Wayar please
Farouk na amsa haidar yace
Ashe da gaske ne gani nan tahowa
Be bari farouk yace komai ba ya kashe Wayar.
Minti goma yayi sallama ya shigo dakin
Abba yace
Wai haidar da gaske zuwa kayi
Kiran sallar yasa abba yace
To sai ku tashi Muje muyi sallah ai.
Sun tafi suka bar farouk Akan darduma ya tayar da sallah
í ½í³‘farouk Ko haidar í ½í³‘
     Written by deeja one love
35
Inda aka tanada domin zaman irin hakan Idan ya kama suka tafi.
Farouk wanka Ya shiga shi kuma Salim ya kwanta.
Koda ya fito Salim d'in Danna wayarshi yakeyi
Dan murmushi yayi yace
Salim kasan me
Sai ka gaya
Wallahi inajin Kunyar nayi mata magana yanzu.
Wace kenan?
Salim ya tambaya
Kasan Wanda nake nufi mana kuma Allah haidar zai zo ya sameni
Dariya Salim yayi yace
Me zakayi masa ne ?
Harararshi yayi yace
Bansaniba.
Cikin nishadi suka Cigaba da firarsu har akayi kiran sallar magrib sannan sukayi alwala suka tafi
masallaci.
Acan suka zauna har akayi sallar isha sannan suka dawo.
Har sun shigo harabar gidan Wayar farouk tayi kara
Ganin Faisal yasa ya D'aga Cikin tsokana yace
babu ruwana dakai.
Faisal yayi dariya yace
Nima ai babu ruwana da Mai gaba da mahaifiyarshi.
Murmushi yayi yace
Kayi d'aya kada ka maimaita
In serious tune Faisal yace
Farouk ka tsaya Kaji abinda zan gaya maka Ada haidar naso gayawa sai kuma naga Kai yafi
kamata ka sani
Nan ya kwashe labarin da hajiya Zainab ta bashi Kaf ya gaya mishi yace
Idan kuma baka yarda ba Gashi Kaji Daga bakin ammar
Ammar na amsar Wayar shima Ya zayyane masa duk abinda Ya sani.
Hawaye kawai yakeyi
Yace
Ku bari Idan muka zo anjima zamu tattauna Abin.
Shiru yayi na Wani lokaci
Tabbas an cutar dasu to amma ai babu laifin mahaifiyarsu ko mahaifinsu to amma me ya kawo
hakan
Sai yanzu yayi Wani tunani ai da haidar shima baya kula ta to Ya akayi yake kulata yanzu
sosai?
Dole akwai abinda Ya sani me kenan?
Kuma Meye Salim bazai rasa sani ba
A sanyaye ya shiga gidan Akan dinning suke hakan yasa can ya nufa kawai
Ko abincin juyashi kawai yakeyi Tabbas babu yadda za'ayi uwa na Cikin hankalinta Ta yardar
da yaranta meyasa beyi tunanin Wani Abu ba?
(Oho farouk daga baya kenan )
Daddyn baby ya Dan bugi table kadan yace
Farouk lafiyanka kuwa inata magana shiru?
Girgiza Kai yayi yace
Babu komai.
Abincin dai kasa Ci yayi.
Wajen Karfe biyu farouk ya Kalli Salim barcinshi yake sha babu ruwanshi amma shi Ya kasa
Ya ilahi ya zaiyi ya tunkari mahaifiyarshi domin ya bata hakuri
A hankali Aka turo kofar Maida Idanunshi yayi Ya Rufe
Ba'a kunne light ba sai dai dim light da yake a kunne
Matsowa tayi a hankali ta zo dai dai Kusa dashiÂ
Hannunta ta d'ora Akan fuskarshi Cikin kulawa ta shafa a hankali
Bude idanu yayi Wanda hakan yasa gabanta ya fadi
Juna suka zubawa idanu
Ahankali hawaye Ya sauko daga Idanunshi
Ya tabbatar soyayyar uwa daban take
Mik'ewa yayi Ya zauna
Rumaisa kuwa ta kasa mik'ewa haka ta kasa zama
Gabanta ya tsugunna Cikin matsanancin kunya yace
Dan Allah kiyi hakuri ki yafe mini abubuwan dana yi miki bazan kuma ba yafiyarki nasan zatasa
Allah Ya yafe mini nasan fushi da uwa Abu ne Wanda Allah Ya Hana amma na take sanin nake
aikatawa bansan wane hukunci Allah Ya tanadar mini ba.
Kiyi hakuri ki yafe mini
Hannunshi ta rike tace
Ni yakamata na nemi yafiyarka farouk domin abinda na aikata
Da sauri Ya Rufe bakinta yace
Ke kika haifemu koda kashe mu kikayi kinyi daidai
Rungume juna sukayi suna kuka
A hankali ya Janye jikinshi
Ya Fara goge mata Hawaye yace
Allah yana sona da rahama daya fahimtar Dani Da wuri.
Murmushi tayi tace
Meya hanaka barci ?
Ina tunanin yadda zan tunkareki Daki yafe mini ne kefa Mai Ya hanaki barci?
Ya tambayeta
Nayi barcin zuwa nayi domin na duba ya kuke kasan wannan ne na farko da Wani da sunan
jinina yazo Kwana Anan.
To muna Lafiya ai.
Shafa kanshi tayi tace
Yanzu ka kwanta
Kona kwanta barcin bazai zo ba
To kayi alwala kayi nafilfili
Daga Kai yayi yace
To momma
Wani farin ciki taji har saida ta murmusa
Tana fita yayi murmushi ya shiga toilet yayi alwala Ya fito
A zaune ya sami Salim
Kallonshi yayi Alamar Lafiya
Dariya Salim yayi yace
Finally dai yanzu angama farouk ya kira mahaifiyarsa da momma
Hararshi yayi yace
Nifa gulma ne Bana so
Dariya Salim yayi ya Mike ya shiga bayi alwala yayi
Sannan yazo shima Ya tada tashi nafilar
Wannan sabonsu ne tun a makaranta.
Sai da akayi kiran sallah sannan suka tafi masallaci.
Bayan sun dawo suka kwanta
Basu suka farka ba sai Karfe sha d'aya.
Da sauri farouk ya tada Salim
Hade rai yayi yace
Lafiya daga kwanciyata zaka tasheni.
Nuna masa agogo yayi
Zaro idanu yayi kafin ya mik'e Cikin sauri Ya shirya
Cikin kananan kaya jar t shirt da bakin jeans.
A zaune suka tarar da momma Tana operating system.
D'agowa tayi tace
Tab sai yanzu gaskiya Kun makara d'azu na aika baby ta dubo Lafiya tace Wai barci kukeyi.
Zama farouk yayi Yace
Wallahi jiya barcin da bamuyi bane Gashi yanzu nasan suna can suna jiranmu.
To yanzu kuje ku karya Bari na kira su a Waya Naji suna adamawan ne.
Gaisheta sukayi sannan suka hau dinning.
Fried plantains da oat sai kunun Gyada da kosai.
Farouk dai kunun yasha.
Salim kuma oat yasha.
Momma ta kira haidar ringing d'aya ya D'aga
Bayan sun gaisa tace
Son kuna adamawan ne?
A'a mun dau hanya yanzu muna daf da jos.
Ya bata amsa
Tab to gasu farouk suna nan yanzu suke karyawa.
Dariya haidar yayi yace
Tab sai dai su biyo mu a baya.
To Allah ya tsare hanya
Haidar ya amsa da Ameen
Kallonsu tayi tace
To ku kunji su haidar sun wuce sai dai Idan kun tashi ku tafi kawai.
Wayar Salim tayi kara
Cikin girmamawa Ya gaidashi.
Mai martaba yace
Naji ance kuna taraba zaku biyo ta nan ne?
Salim ya amsa da
A'a kawai yanzu zamu wuce Ta nan ne.
OK to bawa farouk Wayar.
Cikin sakin rai suka gaisa sannan yace
Wajen mahaifiya dad'i ko yau an manta da Mai martaba.
Murmushi farouk yayi yace
Ai Bamu dad'e da barin wajenka ba.
Hakane to Allah ya kiyaye hanya
Ameen Ya amsa
Driver daddyn baby ya hadasu dashi ya kaisu har Zaria
Amma fa sai sha d'aya na dare suka isa.
Wanka kawai Farouk yayi sannan ya kwanta
Mama tayi sallama ta shigo
Tray hannunta ta ajiye tace
Ya haka farouk Ko abinci baka ci ba
Idanunshi a Lumshe yace
Mama barci nakeji ne wallahi.
Tashi Kaci abinci.
To mama ajiye zanci.
Sai da ta rage musu AC sannan tace
To sai da safe.
Salim yana fitowa daga wanka Ya saka kayan barci sannan ya dauko abincin ya zuba.
Kallon farouk yayi dayake ta sharar barcinshi hankali Kwance.
Sai da yaci Ya koshi sannan ya kwanta.
Ai kuwa da asuba dakyar haidar ya tashe su.
Ko zaman addu'a farouk beyiba Ya wuce gida kwanciya kawai yayi sai barci
Karfe bakwai yunwa tace bata San wannan barcin ba.
Haka yasa ya tashi
Wanka yayi sannan ya fita
A kitchen ya tarar da Yusra da mama
Husna kuma na goge dining
Sai da suka gaisa da mama Sannan husna da Yusra suka gaisheshi.
Bude bude ya Fara
Mama tace Lafiya kuwa.
Lumshe ido yayi yace
Mama yunwa nakeji.
Girgiza Kai tayi tace
Allah Ya shiryeka wato jiyan dai bakaci abincin ka kwanta Ko
Kallon Yusra tayi tace
Had'a masa tea ga doya nan sai ki zuba masa
Bread na kan table.
A k'asa ya zauna Ya Fara ci Babu ruwanshi da zafi. (Nace yunwa kenan )
Sai da ya koshi sannan ya Kai kayan kitchen d'in
Kallon mama yayi yace
Mama zan tafi Kano yanzu.
Mama tace
Kano kuma jiya fa muka rabu.
Yace
Mama baffa fa har muka rabu fushi yakeyi Dani
Murmushi mama tayi tace
Baya fushi dakai farouk abinda kayi ne ya bawa Kowa haushi.
Fuska ya marairaice yace
Ai na bata hakuri kuma ta yafe mini.
Mama tace
Yauwa Ko Kaifa ka hakura da zuwa Kano ka bari nanda three weeks kaje kaga yanzu ana
tsakiyar semester
Shiru yayi kafin yace
Mama Nidai ki Bari naje kawai.
Ajiyar zuciya tayi tace
To Allah ya kiyaye hanya kayi sallama da yan uwanka ko?
Yace
Mama kyalesu kinsan halin Salim yanaji zan tafi zai ce sai yaje Kuma ni yau nakeso na dawo
zai wahala sosai.
Ikon Allah itadai Tana girmama wannan soyayya dake tsakanin farouk da Salim wato Bama laifi
bane basu so ace daya yayi a'a harda wahala.
Dariya tayi tace
Ikon Allah kai dayake karfene ai bazaka gaji ba ko?
Shafa Kai kawai yayi yace
Mama sai na dawo
Kallonshi tayi tace
To haka zakaje musu babu komai tsaya ina zuwa
Tirmin atamfa guda hudu ta debo sai kayan kwalliya da turare.
Tace
Kayan kwalliya ka bawa humaira turare ka bawa baffa
Atamfa kuma ummanka.
Godiya yayi
Da driver suka tafi
A hanya ya kira Mamie suka gaisa sannan ya kira daddy hamma shima gaisawa sukayi momma
hajiya Zainab da mai martaba sai daddyn baby da daddyn yola duka ya gaishesu
Karfe goma suna Kano.
Dai dai baffa zasu fita
Da mamaki Ya ke kallon farouk.
   Â
í ½í²•Kherdylurhv í ½í²•
í ½í³‘farouk ko haidarí ½í³‘
        Written by deeja one love
Dedicated to madina m umarí ¼í¼¹
38
Yana budewa msm suka fara shigowa
Ahankali ya fara budewa
Sakon haidar dayake cewa
Nice makaranta tayi Kyau
Murmushi yayi sannan ya shiga group dinsu na family abinda salim ya rubuta ya bashi mamaki
Sarina ta zama birni an gina mkaranta
Sai video coverage daya tura
Fira sukeyi sosai akan makarantar
Ammar yace
Gaskiya ta hadu kamar a India
Emoji na dariya faisal ya turo
Surayya kam harda recording din dariya
Husna ce ma me Dan tarewa kowa tsokanarsu yakeyi
Kashe data yayi ya zubawa salim ido
Ware idanu salim yayi alamar lafiya
Murmushi kawai yayi ya juyar dakai
Washe gari suka shiga gari asibiti da bore holes din duka sai da salim ya dauka ya tura family
group
Farouk kuwa ya Kira mai martaba a waya yayi godiya tabbas makarantar ta hadu
Momma ya Kira itama yayi Mata godiya
Tayi murmushi tace
Duk abinda kakeso inasonshi farouk
Hakan data gaya bakaramin birgeshi yayi ba.
Suna zaune Ana gobe Zasu tafi
Duk sun gama shirya kayansu
Ammar ya Kira farouk yace gashinan yanzu suka sauka
Ya rasa mai yasa sai da yaji gabanshi ya fadi
Ammar yayi dariya yace
Pls kuzo da wuri
Amsawa yayi da to.
Washegari su mama sai da suka biyo suka daukesu.
Tun a hanya haidar ya damesu da waya akan sun Taho.
Karshe dai kashe wayar farouk yayi
Kiran ta salim yayi
Salim yace
Dalla kada ka damemu mu sai ana gobe zamu taho
Haidar yace
Kai salim wallahi zan mareka
Basai ka Mara nagani ba
Hakadai suka karaci shirmensu
Koda suka isa gida ya cika da jama'a
Sai busa ke tashi
Tsaki farouk yayi Wanda yaja hankalin mama
Harararshi tayi
Salim yaja hannunshi suka tafi.
A bangaren fulani suka hadu da haidar da ammar
Haidar yayi dariya yace
Kaga angwaye
Hade rai salim yayi yace
Waye angon may be dai farouk.
Fulani tace
Kai bakaso kazama Ango ne?
Shafa kanshi yayi yana dariya
Fulani ta dubi farouk tace
To me gida yadai kai baka magana
Murmushi kawai yayi.
Ammar yajashi ya zauna
Hajiya salma ta dubi yafindo karima tace
Na shirya mu tafi kawai
Yafindo Karina tace
To muje.
Motar hanya suka hau domin idan suka dau ta gida da Matsala
A bakin wani karamin kauye suka sauka.
Hajiya salma ta dubi dajin tace
Mama badai nan zamu shiga ba
Eh mana nan zamu shiga
Girgiza kai tayi tace bazan iya ba
Yafindo karima tace
Ba aikin kikeso
Wata uwar tafiya sukayi kan su iso bakin wani dutse mai fadi
Hawa kai sukayi
Yar bukkar yar karama da ita
Hayaki ke fita daga ciki
Hajiya salma cikin tsoro tace
Mama mu koma Dan allah
Wani iskace ta taso ta rufe wajen
Cikin kaduwa hajiya salma ta kankame yafindo karima
Wani irin mutum ne Dan karami gajere sai katon kai da katon hanci
Shi kanshi abin tsorone
Umarni ya basu da su zauna
Zama sukayi
Cikin murya mara dadi yace
Ajiye kudin dake jakanki.
Kallon yafindo karima tayi
Nuni tayi mata data aikata hakan
Juyewa tayi
Kallonta yayi yace da wani abun kuma
Girgiza kai tayi
To tashi Ku tafi
Har ta mike ta dawo ta zauna sai kuma tace
Malam maganar yaran fa
Kallonta yayi yace
Basai da nace kada ki bari su hadu da mahaifiyarsu ba kika bari kuje Ku jira mai zai biyo baya
kawai
Hajiya salma tace
To yanzu babu yadda za'ayi
Bokan yace
Kije ki cigaba da sa wannan dan mutunmutumin a wuta har zuwa wani lokaci
Amma ki sani koda wasa wani ya taba to zaki sami Matsala.
Girgiza kai tayi alamar
Ta gane
Koda suka fito yamma tayi da kyar suka sami mota
Hajiya salma tace
Yafindo karima Anya kuwa wannan aikin yanayi kuwa?
Wannefa?
Da wancan da wannan
Yafindo karima tace aikuwa aikinshi naci sosai
Hajiya salma tace
Nifa ban taba jin sun Kira babansu wai basuda lafiya ba kodai kece bakya yi musu?
Aikuwa lokaci zuwa lokaci inayi yauma zanyi musu ki Gani.
Hajiya salma tayi dariya tace
To na zubar da cikin fa?
Yafindo karima tace
Aikada kiyi mamaki idan akace miki yanzu ma ya aika an zubar.
Cigaba da firarsu sukeyi har suka isa gida.
Gidan cike da mutane hakan yasa ba kowa ya fahimci basa nan ba.
Bayan sallar magrib su momma suka ISO
Kowa na murna da zuwanta
Farouk ya karasa kusa da ita ya amshi jakarta
Haidar kuwa hannunta ya rike suka jera cikin shagwaba yace
Momma shine tun dazu inata wayarki baki daga ba.
Murmushi tayi tace
Tana silent ne meya faru?
Turo baki yayi yace
Ai wannan dambun kazan nakeso ki Taho mini dashi.
Murmushi tayi tace
Na taho dashi yana cikin jaka ta
Daddy hamma ya kalli Abba yace
Na lura yaran nan sunfi son uwarsu
Dariya sukayi gaba daya
Daddyn abuja yace
Hamma kodai kishi kake?
Dariya yayi yace
A'a
A falon yafindo hari suka yada zango
Jakar haidar ya hau budewa
Folder paper ya dauko cikinfarin ciki yayi peck dinta a goshi
Salim yace
Ka isa