Showing 45001 words to 48000 words out of 72611 words

Chapter 16 - farouk Ko haidar complete by one love.pdf

Advertisement

One Love   

23 Mar 2025

5834

ka cinye kai daya
Nan fa rikici ya tashi
Yafindo hari tace
Kudai wallahi anyi girman banza
Farouk dai tashi yayi ya fita ya barsu awajen
Momma ta mike ta bishi
Har ya kusa fita ta Kira sunanshi
Farouk
Tsayawa yayi ya juyo yana murmushi yace
Momma
Karasowa tayi tace
Ya akayi ne
Dan shafa kanshi yayi yace
Kawai gabana ke faduwa
Hannunshi ta rike tace
Kayita addu'a
Girgiza kai kawai yayi.
Hannunshi ta kama ta daura mishi agogo tace
Yau kuma an manta ba'a saka ba

Agogon Rolex mai kyau dashi
Murmushi yayi yace
Na gode momma.
Jerawa sukayi suna fira har suka fito
Abakin balcony suka sami daddyn yola da daddy hamma suna fira
Gaisawa sukayi sannan suka wuce
Duk inda suka bi kallon sha'awa ake binsu dashi
Fada suka fara zuwa suka gaida mai Martaba
Kamar wani abu bai faru ba haka sukayi fira.
Sannan suka wuce bangaren fulani
Da murna ta taresu
Ta kalli farouk tace
FAROUK KO HAIDAR.
Murmushi yayi yace
Farouk
Tace
Kace miskili kafi mahaukaci ban haushi
Mamie tayi sallama ta shigo anan suka Dan taba fira kafin su tashi su tafi bangaren yafindo
karima.
Acan suka sami hajiya zainab sa hajiya salma
Da fara'a suka tareta kamar babu komai.
Nan suka Mata sannu da zuwa suka taba fira har fura tasha
Sannan suka tafi
Bangaren yafindo hari suka koma sannan tayi alwala tayi sallah
Farouk yana dandanna Mata kafa har tayi barci.
Yafindo hari tayi murmushi tace
To ai kaima saikaje kayi sallah Dinko
Kanshi ya shafa sannan ya mike
Sai da yayi sallah tareda mai martaba suka jero
Har harabar gidan sannan farouk yayi bangarensu.
Azaune ya tarar da su suna fira.
Faisal yace
Alhamdulillahi gashi ma yazo sai ka dauko muci
Farouk yace
Meyafaru
Ammar yace
Wannan salim din ne wai baza muci ba sai ka zo nan dai suka zauna suna ci suna fira

📑farouk ko hairs📑

         Written by deeja one love�

Dedicated to madina m umar🌹

39
 Cikin barci mama taji kamar ana mintsininta.
Farkawa tayi a gigice domin wata azaba data ji
Cikin sauri ta sauko domin ta fito
Dumi taji a kafafunta wanda yayi daidai da shigowar yafindo hari
Da sauri tace
Nashigesu ni harira mai zan gani rumaisa bari zakiyi
Cikin sauri momma ta duba kafarta
Innalillahi take ambata kawai kafin jiri ya kwasheta.
A daidai wannan lokacin
Yafindo karima ta ciro wani dan gunki wani karamin kaskon wuta ta dauko ta zuba rushi
Wata karamar leda ta dauko
Sai da tayi murmushi sannan ta dauki allura guda daya ta saka a wuta
Dariya tayi tace
Yau zakiga practical
Awannan lokacin farouk ya fito daga bedroom su salim na falo suna kallon kwallo
Ji yayi kanshi kamar ana dafa kwanyarshi
Tsugunnawa yayi ya dafe kanshi
Yafindo karima ta ciro allurar daga wuta
Da karfi ta furta farouk
Sannan ta saita kirjin wannan gunkin ta soka
Farouk ji yayi kamar ana soka allura akirjinsa
Da sauri ya kamo hannun salim ya dora a wajen yana fadin
Salim mutuwa zanyi.
Cikin tashin hankali haidar yayi waje domin kiran abba
Daidai balcony suka hadu da yafindo hari itama a rude
Su abba suka kallesu suka ce
Lafiya
Yafindo hari tana haki tace
Rumaisa ta suma kamar cikin jikinta zai zube.
Innalillahi wainna ilaihir rajiun
Tashi sukayi zasu bita haidar yace
Abba farouk fa mutuwa zai yi
A gigice daddy hamma yace
Kamarya
Riko hannunshi yayi yace
Zo.muje ka gani
Daddyn yola yace
Kai kabiru jeka dauko matarka
Ahmad dauko mota
Mu kuma zamuje muga farouk din.
Iya galabaita ya galabaita

Salim kuwa tasa shi yayi a gaba yana kuka
Farouk kuwa duk inda yafindo karima ta soka allurar nan ji yake kamar ajikin shi ta soka
A guje daddyn baby ya dauko momma ya saka a mota suka tafi asibiti.
Daddy hamma yace
Wane kalar shirme ne haka salim mai makon ka masa addua sai kuma ka fara kuka
Inna mari da mamie ne suka shigo a rude
Inna mari tasa hannu ta rungumoshi jikinta tana addua tana shafa mishi
Ruwa tasa haidar ya debo mata addua tayi ta tofa sannan tayi bismillah ta shafa masa
A take barci ya daukeshi haka zafin jikinshi ya ragu.
Yafindo karima ta daure fuska tace da hajiya salma
Kin gani ko wainnan mutanen bazasu bari mu idar da aikin mu ba.
Hade rai hajiya salma tayi tace ki bari zan koma kansu ne.
Wani wahalallen barcine ya dauki farouk.
Inna mari ta kalli su haidar kowa ya wani marairaice sai suka bata tausayi
Tace
Idan hakan ya faru ku dena masa kuka addua zakuyi mishi kunji
Daga kai sukayi.
Hajiya salma tace
Yanzu yi wa dayan
Murmushi tayi tace
To
Wata karamar kwalba ta dauko.
Da wani yar sanda karamar kwalbar ta bude ta tsiyaya akan sandar
Cikin sauri haidar yace
Daddy idona zafi yake
Mamie tace
Ikon allah daga wannan sai wannan allah ka mana maganin masifa.
Hannushi ta rike ta zaunar dashi
Idanun ya kada yayi jajir.
Hawaye ke zuba kamar famfo.
Ragowar ruwan adduar farouk din ta deba ta shafa mishi a idanun
Ya dai rago amma har lokacin yana da ragowar ja
Kan wani lokacin jijiyar kanshi ta mike
Kwantaciya yayi zuciyarshi na bugawa da karfi
Yafindo karima tace
Yanzu muje muga me suke ciki
Cikin sauri amra ta bar bakin kofar
Sai da suka maida kayan sannan suka fito.
Suna fita amra ta shiga dakin kalle kalle ta fara yi
Meye su mum sukeyi har suke kiran sunansu farouk .
Bincike ta farayi amma bata ga komai ba.
Da sauri ta fita ta bar dakin
A hanya su hajiya salma suka hadu da mama da hajiya zainab zasu fita

Hajiya salma tace
Lafiya halima naga kunata sauri
Hmm kedai bari aunty salma rumaisa ce babu lafiya da alamu ma bari zatayi shine zamu bita
mu duba ta.
Kallon juna sukayi sukayi murmushi
Tana juyowa suka hada ido da hajiya zainab
Hajiya zainab ta banka mata harara.
Zaro idanu tayi tace
Inasu farouk ne.
Mama ta nunfasa tace
Suna section dinsu babu lafiya ma naji farouk.,......
Kafin ta karasa hajiya zainab ta ja hannunta suka shige motar.
Sai da ta fara tuka motar sannan ta leko ta nuna hajiya salma da yafindo hari ta sa Hannu ta
nuna idanun alamun tana sane dasu.
Hajiya salma ta daga kafada alamar
Whatever.
Da sallama suka shiga dakin Cikin farinciki suke kallonsu
Allah ya basu lafiya sukayiwa su mamie sannan suka tattara suka fita
Sai sha biyun dare sannan momma ta farka
Hajiya zainab ta gani kawai
Kallonta tayi tace
Cikin ya zube ko?
Mama ta fito daga bayi tace
A'a
Murmushi tayi
Daddyn baby yayi sallama ya shigo
Bayan ya zauna hajiya zainab tace
Dan allah ina neman alfarma
Daddyn baby yace
Inaji
Tace
Inaso ya kasance babu Wanda yasan cewa cikin na nan bayan mu Hudun nan pls
Daddyn baby yace
Saboda me
Hajiya zainab tace
Nidai pls ku mini wannan alfarmar
To insha allahu.
Murmushi tayi tace
Na gode sosai.
Alwala mama ta taimaka Mata tayi sannan taci abinci
Sai karfe goma farouk ya farka
A hankali ya mike ya shiga bayi sai da yayi wanka sannan yayi alwala
Sallolin da ake binshi yayi

Salim yayi sallama ya shigo
Murmushi yayi yace
Sannu da farkawa bari na amso maka abinci.
Fita yayi saiga haidar da ammar da faisal sun shigo
Kallon haidar yayi idanu yayi Jajir irin jinin nan ya taru
A sanyaye yace kaikuma meyasameka?
Murmushi hairs yayi yace
Kawai ciwo sukeyi mini
Jinjina kai yayi.
Sai da yaci abinci sannan ya shirya ya fito
Haidar da salim suka biyoshi
Salim yace
Ina zakaje ne?
Gaishedasu momma
Haidar yace
Ai tana asibiti batada lafiya
Da sauri ya kalleshi yace
Meya sameta?
Nima bansaniba.
Da mamaki yace
To muje asibitin
Haidar yace to
A parking lot suka hadu da hajiya salma da mamie wai zasu tafi asibitin
Gaishe dasu sukayi sannan suka tafi
Tare
Suna shiga haidar yayi ajiyar zuciya
Kusa da ita yaje ya zauna ya dora kanshi akan kafarta
Shafa kanshi tayi tace ya akayi babyn momma
Cuno baki yayi yace
Nagaji ne yajiki
Salim ya harareshi yace
Kato kawai dashi wai baby.
Haidar ya hade rai yace
Gulma waya saka dakai ni ai karami ne
Kuma yaushe na girma ma Kawai ka wani sakawa mutane baki amegbo.
Farouk ya harari haidar yana dagowa suka hada ido da mamie kauda kai yayi
Mamie tace
Ka kauda kai mana tunda kana nuna mana banbanci.
Momma tace
Wa.kenan?
Mamie tace
Farouk mana a fili yake nuna yafison salim akan haidar
Momma tayi murmushi tace

Ai duk daya suke awajenshi
Haidar yace
Mamie aini ban damu ba nasan yafi sonshi tun tuni.
Hajiya zainab tayi dariya tace
So gamon jini kuma ai salim din yafi kula dashi ne kunga dole ita zuciya tana son mai kyautata
Mata.
Hakadai suka cigaba da fira har zuwa azahar sannan su Abba sukazo.
Hajiya salma ta mike tace
To allah ya Kara sauki
Momma tayi murmushi tace
Angode sosai ki gaida gida
Hajiya salma tace
Allah ya kawo mai amfani
Ameen
Da yamma aka sallameta
Koda suka dawo gida sun tarar da duk an tafi sister's evening
Bangaren yafindo hari aka wuce da ita
Sai da tayi wanka sannan ta kwanta
Kowa tunaninshi Cikin ya zube
Salim yace kuzo mu tafi wajen eve din
Shiru farouk yayi
Haidar yace
Nawan taso muje mana
Tsaki yaja yace
Kuje bazan je ba.
Salim ya riko hannunshi yace
Wallahi sai ka je
Murmushi kawai yayi ya bishi.

📑farouk ko haidar📑

      Written by deeja one love�

Dedicated to madina m umar🌹

40-41
Yau aka daura auren muhammad da amra sai adnan da Bilkisu sai abbas da asma'u aure fa
masha allah domin komai ya tafi yadda akeso
Bayan biki kowa gida ya wuce farouk yayi kano salim Zaria haidar kaduna.
Sati hudu dayin biki akayi posting din corpers
Hajiya zainab ita ta shiga ta fita akabar kowa agarinshi
Farouk cikin garin kano zai yi
Haidar kaduna

Salim kuma Zaria.
Kwana biyar farouk yake shiga cikin garin kano domin services dinshi.
Haidar kuwa asibitin daddy aka barshi.
Komai yana tafiyan musu dai dai
Ammar zaune a garden wayarshi tayi Kara
Da farunciki ya daga wayar
Amra tace
Miss u bro.
Same
Ya bata amsa atakaice
Amra tace
Bro akwai abinda nakeso na gaya maka.
To inajinki
Shiru tayi for some seconds sannan tace
Akwai abin dana gani a dakin yafindo karima su sokawa allura ajiki kuma suna kiran sunan
farouk
Shiru ammar yayi yace
Yaushe ranar da momma tayi bari.
Ammar yace
To meyasa baki dauko ba
Na shiga na duba banganshiba
Ta bashi amsa
Ammar yace
Ke me kike tunani
Shiru tayi tace
Ni gaskiya banace ba.
Ammar yace
Inajin hakanne beda wani amfani ki manta kawai.
To shikenan
Ammar yayi shiru azuciyarshi yace
Kenan mum tana zuwa wajen boka
Ya ilahi!
Tasan abinda takeyi ba mai kyau bane bayaso yar uwarshi ta sani domin hakan zai iya dasa
mata kiyayyar mahaifiyar
Hajiya salma ta tabashi tace
Ammar lafiya kake kuwa?
Daga Mata kai yayi yace
Eh kawai inaso na huta ni dayane akwai abinda nake tunani.
Hajiya salma tace
Ok to kaje daddynku na kiranka
Mikewa kawai yayi ya shiga ciki
Akan sofa ya tarar da daddy hamma
Daddy yace

Dama mai martaba ya kirani yace na tambayeka kai wa kake so domin so yake nanda next year
kuyi aure kai da yan uwanka
Ammar ya shafa kai yace
Daddy yusra ce dama sai dai har yau ban tareta da maganar ba
Daddy hamma ya girgiza kai yace
Ok
Hajiya salma ta kira yafindo karima tace
Mama yau adan tabasu mana
Yafindo karima tace
To zan Dan tabosu sai dai kinsa yadda zakiyi dasu domin malam yace aljanu bazasu iya xuwa
kusa dasu ba
Hajiya salma tace
Kada ki damu yan daba zamuyi hayarsu sure sace haidar idan yaso mu yanka kudi makudai
tunda marikinsa yanada kudi idan ya biya sai muce su kashe shi
Shi kuma farouk guba zamu sa mishi a abinci idan yaso sai muyi amfani da salim ya bashi
kinga yadda suke son juna babu wanda zai zargi salim ne.
Dariya yafindo karima tayi tace
Gaskiya akwai ki da basira yanzu bara na tabosu.
Ajiye water sukayi ammar yayi ajiyar zuciya yana Kara mamakin mahaifiyar Tashi.
Lallai mutum abin tsoro ne.
Yau farouk agajiye ya dawo  ga kanshi yana Sara mishi
Bokiti ya dauka ya ja ruwa ya shiga wanka
Sai da ya shirya sannan ya shiga dakin inna Mari
Abinci ta ajiye mishi
Dakyar yayi loma biyu jikinshi ya dau zafi hakan yasa ya ajiye abincin
Da mamaki inna Mari tace
Yau bakasha maganinka bane
Daga kai yayi yace
Ya karene kuma ban siyo wani ba
Mikewa inna mari tayi ta debo ruwa tayi addua ta tofa
Sai dai yau abin yayi yawa domin jini ta baki ta hanci
Salati ta fara tana kiran inna hadiza
Da sauri ta shigo dakin ganin halin da farouk yake ciki yasa ta rudewa baffa ta bugawa waya
Hankali a tashe ya taho
Da salim sukayi karo ahanya
Ganin yanayin da baffa ya shiga gidan yasan babu lafiya Dan haka yasa shima ya Bishi kawai
Tare suka dauko farouk din suka sakashi  a mota
Cikin sauri salim yake tuki
Kan su karasa wudil  numfashin ya tsaya cakk.
Baffa shiru yayi gabanshi na faduwa
Salim kuwa gudu kawai yake zubawa hankali a tashe.
Mamie ta kalli haidar tace
Wai kai lafiyanka kalau kuwa tun dazu na kawo maka abinci amma ka zauna ka zubawa abincin

idanu
A sanyaye ya daura hannunta saitin kirjinsa yace
Mamie ji yadda zuciyata take bugawa
Ita kanta shiru tayi tace
Haidar kada ka sawa kanka damuwa fa kasan dai bugawar zuciyarka is abnormal za'a iya
samun matsala fa .
Shiru yayi kawai.
Da lallashi ta dinga bashi abincin har ya dan ci da yawa
Kallonta yayi yace
Mamie kaina na ciwo.
Magani ta dauko ta bashi yasha
Wayarshi ya dauka yayi dialing number din salim
Mamie tayi saurin amshe wayar tace
Haidar kwanta kayi barci
Kamar zai yi magana kuma sai ya fasa
Kashe wayar tayi sannan ta fita
A falo wayarta yayi kara
Dagawa tayi tace
Anyini lafiya
Momma tace
Lafiya lau
Bayan sun gama gaisawa sai kuma ta kasa tambayar haidar din
Mamie ta fahimci kunyar tambayarta takeyi hakan yasa tace
Wallahi haidar din ne kansa ke ciwo to shine yasha magani ya kwanta
Murmushi tayi tace
Ayya allah ya sauwake dama zance ko sunyi waya da dan uwansa na kira wayarshi bata shiga
ta salim kuma ba'a daga ba .
Mamie tace
Bari na gwada Kira naji
Itama data Kira ta farouk din bata shiga ba ta Kira ta salim wayar na ringing amma ba'a daga ba
Mama ta kira tace Mata
Salim ya tafi kano
Mamie tace
To allah ya sa lafiya
Ameen
Mama ta amsa
Bayan ta kashe ta kira momma ta gaya Mata
Gabanta ya fadi
A sanyaye tace
To allah yasa lafiya
Hawaye suka fara zubo Mata fahad da gudu ya fita
A palour ya tarar da daddy yace
Daddy zo kaga momma tana kuka

Da sauri ya taso har lokacin hawaye be bar zuba ba.
Daddyn baby ya rungumeta yace
Lafiya kike kuka?
Cikin kuka tace
Daddyn baby jikina yana bani farouk bashida lafiya
Ajiyar zuciya yayi yace
Haba maman baby yazakice haka
Tace
Gashi wayarshi bata shiga
Dan murmushi yayi yace
Nifa na lura ko kawaicin Dan fari bakiyi karara kike nuna kinfi son farouk
Girgiza kai tayi tace
Ba haka bane
Daddyn baby yace
To yane bayan gashi ance dake haidar kanshi na ciwo amma baki damu ba sai farouk da Kika
kira wayarshi a kashe may be ma caji ne babu .
Dan murmushi tayi tace
Kuma fa hakane
Dariya yayi yace
Wlh ke kamar ba bafulatana ba babu Kara babu yunwa.
Shiru tayi Dan ta lura tsokanarta yakejin yi

📑farouk ko hairs📑

            Written by deeja one love�

Dedicated to madina m umar🌹

42-43
Koda suka isa asibitin wudil cikin gaggawa aka amsheshi.
Shidai baffa jikinshi a sanyaye yake
Salim kuwa hankalinshi ya tashi sosai ganin halin dayake ciki
Alokacin mamie ta kuma kiran wayarshi
Dagawa kawai yayi amma ya kasa magana domin yasan yana bude baki kuka zai yi
Mamie ta kuma kiran sunanshi
Um
Kawai yace
Yace
Salim lafiya kuwa anata Kira baka dagaba
Shiru yayi zuciyarshi na bugawa da mamaki tace
Ba magana nake maka ba salim
Cikin karfin hali ya bude baki domin yayi magana amma abu ya gagara
Kuka ya kufce

Shiru tayi tana sauraran shi.
Can tace
Salim meya faru
Hawaye ya goge yace
Mamie farouk bashida lafiya inaji mutuwa ma yayi tun dazu likitocin babu Wanda ya fito kuma
da muka kawoshi jini ta hanci ta baki
Shiru tayi na wani Dan lokaci kafin tace
Salim ka kwantar da hankalinka cuta ba mutuwa bace insha allahu zamu taho gobe idan allah
ya kaimu.
A sanyaye yace
To mamie
Baffa da kanshi ya kira daddyn baby ya gaya mishi sannan ya Kira mai martaba shima ya gaya
mishi ya Kira daddy hamma da abba.
Kankace me ciwon farouk ya zagaya fada
Yafindo karima ta yi murmushi aranta tace
Ai insha allahu daga nan bazaka Tashi ba.
Hajiya salma ta kirata cikin farinciki tace
Kinji abinda naji kuwa?
Dariya yafindo karima tayi tace
Ya zakice haka bayan nice sila daya kuma hakan
Wata dariyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login