Showing 33001 words to 36000 words out of 72611 words
Chapter 12 - farouk Ko haidar complete by one love.pdf
na kira Salim
Dan murmushi yayi yace
Bazaku iya tafiya babu shi ba kenan dama jarabaku nakeyi nagani abotar Tana nan.
Umarni ya basu da su shiga mota
Bude musu akayi suka shiga
Mai martaba ma Ya shiga Yana tsakiyarsu haidar yace
Gashi zamu tafi baka kira Salim d'in ba?
Nuna mishi gaban mota yayi
Salim ke zaune Yana game a Waya
Dariya haidar yayi yace
Wallahi Allah Ya taimakeka amma Bari Mu dawo zaka sani
A hankali motar ta Fara tafiya yayinda sauran motocin suka biyo su a baya
Tafiya sukayi sosai kafin haidar yace da Mai martaba
Wai ina zamuje ne
Siyar daku zanyi
Rufe bakin shi yayi yace
Allah Ya huci zuciyarka
Duka yan Motan sai da sukayi dariya saboda yadda ya Wani zaro idanu ya kuma Tab'e fuska.
Farouk kuwa murmushi kawai yayi Ya juyar da Kai
Wajen Wani k'ato halla sukayi parking wajen ya tsaru sosai.
Ciki suka shiga direct
Daga gani mutanen wajen Manya ne
Sai dai ana yiwa sarki iso suka Mike gaba d'aya
Bayan ya zauna su haidar dai na Kusa dashi.
Mik'ewa yayi Godiya sannan ya gabatar dasu haidar a jikokinsa da suka bace
Ya k'ara da cewa Shiyasa Nace
Bari nazo dasu ku gansu na kuma gabatar dasu
Kowa a wajen taya sarki murna yakeyi da ganin jikokin nasa
Sannan masu yi musu kyauta sunayi
Kafin atashi Daga wajen sai da suka sami kyautar miliyan Dari uku da dubu tamanin da biyar da
motoci Guda goma sha biyu da filaye guda takwas gidaje guda biyar
Masha Allah farin ciki wajen sarki ba'a magana domin yanason me son abinda Ya fito daga jikin
modibbo
Sai wajen hudu suka bar wajen
Gaba d'aya Dan anci an sha Kowa yayi murna
Wajen Wani guri suka wuce Kamar company ginin irin storey building ne Mai Martaba ya Fara
shigar dasu wajen Wani garden yace to ku jirani Anan kafin na fito six.
Zama sukayi shi kuma ya wuce Ya tafi Yana Mai farin ciki.
A bangaren rumaisa kuwa kuka me tsanani ta Cigaba domin gani take Kamar sun rabu kenan
gashi sai yanzu tayi Tana tsananin son yaranta.
Daddyn Abuja yace
kadai ji me Mai martaba yace ko
Dan haka ka bata hakuri ku tafi kawai
Daddyn baby yaje ya dafata yace
Kiyi hakuri ki taso Mu tafi taraba may be Idan muka bi umarninsa ya yafe miki
Hawayen ta goge tace
Ka rokeshi yayi hakuri ya Bari mu koma South Africa.
Cikin matukar tausayinta yace
Zan rokeshi.
Dagata yayi tsabar Jikinta babu karfi Kamar zata fadi haka takeji.
Bangaren yafindo Hari ya kaita
Ita ma dai hakuri da kwantar Mata da hankali ta rinka yi.
A haka ta tashi ta shiga wanka
Ta shirya
Daddyn baby yazo Ya dauki kayan Ya kai mata mota
Yafindo Hari ta rikota suka fito Dan Tsayawa tayi Tana kallon bangaren Fulani
A sanyaye tace
Idan na shiga bazata yi mini komai ba
Cikin tausayawa yafindo Hari tace
Wallahi ban saniba
A hankali tace
Muje wajenta.
Nan suka tarar da su mama da Inna Mari da Mamie sunata fira
Sallama sukayi suka shiga
Fulani tace
Me zan gani haka bakida Lafiya ne
Hawaye Ya gangaro mata ta tsugunna tace
Ki yafe mini jafar miki da jikokin ki da nayi.
Dagota Fulani tayi tace
Kada kice haka ai yaranki ne duk yanda zan shiga tashin hankali Bai Kai Wanda zaki shiga ba
ganin gaki gasu amma bakida damar kije Kusa dasu sannan ki sani ba karamin sa'a kika taka
ba ubangiji na sonki da rahama Shiyasa Ya dawo dasu kinada rai amma Da Ya zakiyi da
hakkinsu ubangijinki ya miki kyauta kin nuna bakiso. Kuka ta kuma fashewa dashi tace
Wallahi nayi nadama Fulani
Allah Ya yafe mana baki daya Allah Ya kyauta gaba.
Tana Gama fadin haka tayi gaba abinta.
Kallonsu Mamie tayi tace
Na gode sosai da kuka rike mini yarana da amana abinda na kasayi kuka aikata Allah Ya saka
da alkhairi Inna Mari ta ce
Kada ki da mu da na Kowa ne ai
Juyawa tayi yayinda yafindo Hari ta riketa suka tafi
A parking lot suka had'u dashi sun Gama sallama da daddyn baby kenan
Kallo d'aya yayi mata Ya dauke Kai
Cikin sanyin jiki ta shiga mota
Fahad da farida ne suka taho da gudu suka rungumeta
Mommy ina zakije baki tafi damu ba
Hawayen fuskarta ta share tace
Yanzu nake shirin kiranku
Amma kuje ku dauko takalminku ke kuma ki hado da hijab
To da sauri suka amsa
Suka juya da gudu domin su dauko.
Kuka ta fashe dashi lokacin da driver yaja motar
Gidan ta kuma Juyawa ta kalla
Tabbas daddyn baby tausayi take bashi
Driver yacewa Fara kaimu modibbo hospital.
Acan suka tarar da daddy da daddyn yola
Magani aka bata sannan suka tafi
To Nidai Anan nake cewa Allah Ya kiyaye hanya Ameen í ½í¹
Haidar d
í ½í³‘farouk Ko haidar í ½í³‘
Written by deeja one love
Dedicated to madina m umar í ¼í¼¹
26
Sai shida da Rabi sannan Mai martaba suka fito daga meeting din
Duka mik'ewa sukayi suka shiga mota
Haidar yace da Mai martaba
Dan Allah mu biya shopping mana
D'an murmushi yayi yace
Shopping ni kuma
Had'e rai yayi yace
Eh mana
Ya riko hannunshi yace
Haba aliyu da girmana da kimata ace zan je shopping kuma.
Juyaddakai yayi yace
Ai daga yau mun bata
Dan murmushi yayi yace Da driver
Ka kaimu modibbo shoprite.
Haidar Abin mamaki yake bashi Idan yaga sarki na bin abinda haidar yakeso
A fili yace ikon Allah
Suna parking ya kallesu yace kuyi sauri
Make kafada haidar yayi yace
Sai dai mu shiga tare
Zaro idanu sarki yayi yace
Ni mu shiga tare kace fa?
Cuno baki yayi yace
Eh mana
Kallon dogaransa yayi yace
Ku mu shiga
Kowa a wajen mamaki yakeyi Dan basu tab'a ganin sarki yazo shopping da kanshi ba
Su Kansu ma'aikatan na wajen mamaki sukeyi
Manager ya fito da sauri yace
Ranka ya dade da kiranmu kayi ai da munzo
Hannun farouk ya rike yace
Kaga wa'inda suka kawo ni nan shopping suke so
Shi kanshi yayi mamakin jin abinda sarki yace
Kujera aka kawo mishi Ya zauna yayinda suka shiga siyayya
Kowa sai da ya d'auki abinda yakeso sannan suka fito
A gajiye suka taho
A hanya suka wuce Wani suya spot daru haidar yasawa sarki sai da ya tura aka siyo musu
Bayan sun Fara tafiya ya dubi haidar yace
Amma mamienku na kokari
Ya dubi farouk yace
Bakaga yadda Dan uwanka yake ba
Turo baki yayi yace
To aishi daban ni daban.
Dariya Salim yayi yace
Wlh Mai martaba Ko a makaranta haka nake fama dashi
Dan murmushi farouk yayi yace
Kake fama dashi ko nake fama daku kaima ai ba baya bane.
Dariya Mai martaba yayi
Yace
Kace kana kokari
Ya mutsa fuska Salim yayi yace
Mai martaba wasa yake fa.
Mai martaba yace
Gashinan ko yanzu kayi ma.
Dariya akayi gaba d'aya yayinda farouk yayi murmushi.
Suna isa direct masallaci suka wuce
Sai da sukayi sallar magrib da isha sannan suka shiga Cikin gidan.
Daddyn yola yace
Mai martaba tun d'azu muke sa ran ganinka mukaji shiru har muna tunanin bin hanya.
Dan murmushi yayi yace
Ina tare da tagwayen maza ne
Dariya sukayi gaba d'aya
Abba yace
Yanzu dai an soke mana walimar yau kenan
Eh gobe ayi Idan yaso jibi sai su tafi.
Su Salim kuwa hanyar shiga bangaren su sukayi
Daidai lifter suka had'u da Faisal da ammar as usual
Faisal yace
Ikon Allah akarade har an tafi yawo Allah yasa ba ku bane jikokinsa na farko balle ku dinga
tinkaho.
Dan murmushi gefen baki farouk yayi Ya bude lifter ya shiga
Ammar ya riko hannun haidar yace
Ka bawa Dan uwanka hakuri and congrats for been part of this family
Faisal da mamaki yake duban ammar
Murmushi haidar yayi yace
Tnxs bro sannan zai fi kyau Ka bashi hakurin da kanka.
Yana Gama gayan haka ya bude lifter ya shiga
Salim yabi bayanshi
A zuciye Faisal yace
Me hakan ke nufi
D'aga kafada yayi yace
Nifa bazan Cigaba da munana musu ba alhalin yan uwanane su.
Da mamaki Faisal yace
Kenan bazaka tayani yaki dasu ba kenan
Calm down my brother yanzu fa su yan uwanka ne wane yaki kuma ana zaune
Shikenan tunda ka koma tsaginsu
Yana fadin haka ya tafi ya bar ammar a tsaye
Haidar kuwa suna shiga Kamar yadda suka Zata har ya shiga wanka yana fitowa Salim ya
shige shima haidar ya shiga
Husuma ta tashi Tsakaninsu kan Wanda ya Riga
Farouk yana jinsu yayi banza dasu
Dan Kansu suka gaji suka Bari
Salim ya Fara wankan sannan haidar
Blue t shirt da Wanda blue black suka saka duka Su ukun
Suna bud'e kofa daidai ammar ya karaso dariya yayi yace
Kaga yan ukun Mai martaba
Duk da haushin shi da farouk yakeji saida Ya murmusa.
Kallon farouk yayi yace
Am sorry
Kara Had'e rai yayi
Ya juya ya tafi
Duka jikinsu sanyi yayi
Dafashi Salim yayi yace
Kayi hakuri zamuyi masa magana
A bangaren Fulani suka sameshi shida daddy hamma suna zaune da alamu magana sukeyi
Daddy hamma yace
Yauwa haidar karaso nan mana
Inaso ku yafewa mahaifiyarku kunji ko
Shiru sukayi Kamar basa wajen
Haka ya gaji da magana ya kyalesu
Wayar farouk ce tayi k'ara
Da sauri Ya D'aga
Muryar Indo yaji Cikin kuka take cewa
Yaya farouk kaje adamawa ka manta dani ko?
Runtse idanu yayi yace
Kin taba ganin mutum Ya manta da numfashinsa?
To Idan ni numfashin kace meyasa ka ki kirana
Kada k damu kina zuciyata
Ya gaya Yana d'ora hannunsa daidai zuciyarshi
Haka suka dinga fira har ta yanke Alamar kudin Ya k'are
Salim ya Kalli haidar yace
Nifa Ina mamakin mutumin dayake nuna shi babu ruwanshi Agefe kuma tantirin Dan iskane
Wai kin taba ganin mutum Ya manta da yin numfashi
Ya gaya yana nuna yarda farouk yayi
Filo ya jefa masa yana dariya
Da sauri yayi hanyar stairs
Dan Tsayawa yayi Ya saka hannunshi a daidai saitin zuciyarshi Ya Lumshe idanu yace
Kada ki damu kina zuciyata
Da sauri farouk ya Mike zai bishi
Salim kuma ya juya da gudu Da Mamie yaci Karo Wanda yasa tayi saurin cewa
Kai Kada ku karyani banga yan dagwai dagwai ba
Dago fuska yayi yace
Nasu wa kenan
Naku mana
Rufe fuskarshi yayi yana Wani kakkare jiki Kamar an bude kwaila Tana wanka.
Dariya haidar ya kuma tuntsirewa dashi.
Dariya harda hawaye
Daddy hamma daya ke kallonsu tun d'azu yayi Ajiyar zuciya
Salim yaja hannun Mamie ya zaunar da ita ya kwantar da kanshi a Jikinta
Mama tace
Me zan gani haka maza dagata
Shafa kanshi tayi tace
Barshi kinji dama kwana biyu ba'a hadu ba.
Gwalo yayi wa haidar
Haidar yace
Yaro ni jikin umma zan kwanta
Dan Had'e rai farouk yayi yace
Bakada Kai ne salon ka karyata
Mama tace
Kai farouk wannan qeqe da qeqen fa wato kada a karya maka uwako
Da sauri Ya juyar da Kai yana murmushi Dan yama manta suna wajen
Hannun haidar Inna Mari ta rike tace
Ai suma yarana ne
Dariya Salim yayi yace Bari na baki labarin yadda Dan uwa ke tadi TV
Da sauri farouk ya Mike ya Rufe masa baki
Dariya haidar yayi yace
Wai fa Kin taba ganin mutum Ya manta da numfashin.....
Da sauri Ya karasa ya Rufe masa baki Yana Zaro idanu
Salim ya Lumshe idanu ya Kai hannunshi kan saitin zuciyarshi yace
Kada ki damu kina zuciyata kodayaushe.
Ai kawai farouk fita yayi saboda tsananin kunya
Yana jiyo dariyarsu gaba daya
Can wajen wata canopy ya je ya sami kujera ya zauna
Daddyn Abuja ne ya karaso yace
Haidar Ko farouk
Da sauri Ya dago kanshi
Ganin daddyn Abuja yasa yace
Farouk
To mai martaba na kiranka
Inda Ya nuna masa Ya kalla
Can wajen Wani hadadden balcony ya hango Mai martaba d'in
Yana zuwa ya janyo shi jikinshi
Cikin kulawa yace ina yan uwanka
Kamar bazai yi magana ba yace suna bangaren Fulani
Dan murmushi mai martaba yayi yace
Ikon Allah magaji mafiyi
Kallonshi farouk yayi yace
Me kenan
Yadda Kake da miskilanci haka mahifinka yake shima kuma a wajena yayi gado hakan yasa
take sonshi Kaf Cikin yarana
Dan murmushi kawai farouk yayi
Tashi Muje can wajen
Tafiya suke a k'asa suna tafe Mai martaba yana bashi labarin kuruciyar daddy hamma bayi
kuma na miko gaisuwa
Sai da suka shiga Wani waje
Karamine Mai kyau
Kananan kayan wasa ne
Wani Dan karamin doki haidar ya tsugunna ya d'auka
Mai martaba yace
Wannan shine wajenda mahifinka yafiso tun yana k'arami
Wai'nnan kuma kayanshi ne na wasa tun yana k'arami
Rufe wajen yayi sannan suka nufi bangaren daddy hamma
Wani daki ya bude musu suka shiga
Hotunan wasu kyawawan yarane guda biyu tun suna jarirai
Hannu farouk yasa ya d'auka
Mai martaba yace
Wannan shine hotunanku tun kuna kanana a duk lokacin da yaga Wani Abu daya birgesshi sai
Ya siyo muku shi Ya ajiye Ance kun mutu amma shi akullum karyatawa yakeyi.
Daddy hamma dayake tsaye ya k'araso Ciki yace
Kuma ko a India haka dakin yake
Da sauri farouk ya rungume daddy hamma yana zubar da hawaye mai martaba ya hadasu duka
ya rungume yanajin son su yana karuwa
Mai martaba yace
Kayafe mini Kaji na hukuntaka duk da nasan kuskure ne.
Daddy hamma yace
Ban taba rikeka ba ko sau d'aya a Raina.
Har kofar bangaren samarin Mai martaba da daddy hamma suka rako farouk
Kallon yadda suka jera yayi yayi murmushi ya juya ya shiga
Yana fita daga lifter suna haduwa da ammar Cikin sauri yace masa
Sannu da dawowa.
Ko kallonshi farouk beyiba Ya wuce Ya tafi
Faisal yaja tsaki yace
Allah Ya kara kaita tura kanka yana gwasaleka.
Dan murmushi kawai ammar yayi Ya shiga lifter
*** **** **** **** *
Rumaisa na shiga Cikin gidan ta fashe da kuka
D'aki Ta wuce direct kan gado ta kwanta Tana Cigaba da rera kukanta
Kanwarta hamida ta Kira Tana kuka Tana fada mata abida Ya faru
Hakuri ta dinga bata tana tausar ta
Cikin sheshsheka tace
Haba hamida sunki su kulani kwata kwata Gashi Mai martaba ya goya musu
Baya
Itadai hamida hakuri ta Cigaba da bata
Zazzabi ne ya rufeta kan dare
Daddyn baby na shigowa Ya ganta Tana Kwance tana rawar sanyi
Cikin tashin hankali ya tarota yace Muje asibiti
Babu musu suka tafi
Suna zuwa likitan yasa mata drip sannan ya Debi Jininta domin ayi test
Hajiya Salma tace dole mu sake shawara
Hajiya Zainab tace
To wannan karan babu ruwana gaskiya
Yafindo karima tace
Wawiya Yar uwar taki kike cewa bazaki taimaketa ba
Hajiya Zainab ta Mike tace Kunga tafiyata.
Gaskiya ba lallai gobe da jibi ku sami two page saboda zan je makarantar hadda kuma sai
shida zan dawo so Idan kuka sami one page ma ku godewa Allah.
Bye bye.
Murussss lols
í ½í³‘farouk Ko haidar í ½í³‘
Written by deeja one love
Dedicated to madina m umar í ¼í¼¹
Kuyi hakuri am not feeling well ne Shiyasa kuka jini jiya shiru but ga wanna kuyi hakuri dashi.
Idan na sami sauki zakuji ni sosai.
27
Hajiya Salma tace
Yanzu abinda Ya kamata musan me ya kamata muyi gaba.
Yafindo Hari tace
Ai shawara na gareki ki gode Allah mahaifiyarsu mukayi amfani da ita wajen batar dasu Da
yanzu asirinmu ya tonu.
Hajiya Salma tace
Yanzu dai zamusan next step da zamuyi.
Tashi tayi ta fita
Ammar yayi sallama ya shiga farouk Ke Kwance yana danna Waya yayinda haidar da Salim
suke buga Mario Kart racing
Farouk tunda ya d'ago ya kalleshi ya maida Kai Ya kwanta
Ammar ya Matsa Kusa dashi farouk yayi saurin tashi ya shiga bathroom
Jiki sanyaye ammar ya koma wajensu haidar
Daure da towel ya fito Alamar daga wanka yake
Sai da ya shirya tsaf sannan yace
Kai ku tashi Mu fita mana