Showing 15001 words to 18000 words out of 72611 words

Chapter 6 - farouk Ko haidar complete by one love.pdf

Advertisement

One Love   

23 Mar 2025

5820


Dariya Salim yayi yace da ita
Yauwa k'anwata gaya mishi
Mamie tace

To ai ita surayyan ta gaji ta hakura yanzu
Tab'e baki tayi tace
Ai Abin ne yafi karfina
Ana gobe zasu wuce Kano
Yaya Adnan yace
Suje shop rite
Can ma dai rigimar suka dinga yi Kamar yara kananan karshe dai
Zuba musu idanu farouk yayi
Ganin Abin nasu bazai k'are bane yasa ya Adnan yace duka Su wuce su shiga mota
Kallon farouk yayi yace
Komai zaka d'auka ka daukar muku tare
Duk Abin da Ya kamata su siya sai da ya daukar musu
Har yazo fita wata doguwar Riga ta mata ta dauki hankalinshi Tabbas zata yiwa humaira kyau
Daukanta yayi Dan gaskiya tayi masa
A falo suka tarar dasu ammie dukansu harda yaya Abbas
Direct cinyarta haidar ya nufa
Daura kansa yayi akai
Salim kuma ya zagaya ta Dayan barin ya Dora kanshi a kafadarta
Harara yaya Abbas Ya galla musu yace
Zaku dagata ko sai na taso
Murmushi Mamie tayi tace
Kyalesu Daga yau ne ai sai an kwana biyu kan su kuma ganina
Dariya suka yi gaba d'aya
Yaya Adnan yace
Wlh Dan ma baka gansu a shop rite ba kenan ai da sai sun baka haushi.
Dariya aka kuma yi
Sumayya tace
Ba sai da Nace maka ka d'auki yaya farouk kawai ba .
Surayya ta Dora da cewa
Wannan ai sai mamie Wlh Dan wuni suke Kamar yara
Yaya Adnan yace
Ai kuwa karshe kadasu mota nayi nasa farouk yayi musu siyayyar
To kayi da tsarabar da zaku Kaiwa ummanku Ko ?
Mamie ta tambaya
Girgiza Kai yayi Alamar a'a
Kayya to me akayi kenan tashi maza driver ya kaika ka siyo musu
Mamie ta ce
Daukar key yaya Abbas yayi yace Muje na kaika
Har sun tafi Mamie tace
Yauwa Idan kunje ka biya ka taho mini da phone k'arama me kyau.
Angama
Abbas Ya fada
Koda suka dawo duka basa Falon Dan haka direct d'akinsu Ya wuce

Acan ya tarar da haidar a Kwance Salim kuma yana wanka
Washegari da wuri suka d'auki hanyar Kano
A Cikin motar ma haka suka yi Ta rigimarsu
Shidai farouk be ce musu komai ba
Suna isa Garin yara suka Fara bin motor da gudu
Sai suka Bar rigimar suka koma dariya
Salim yace
Mutumina Dan Allah ji Kamar yau suka Fara ganin mota
Dariya haidar yayi yace
Tab da aiki
Shidai farouk be ce komai ba
Daidai kofar gidansu driver yayi parking
Mata har ta katanga leke akeyi
Ikon Allah sai kallo
Indoce ta fito da gudu
Rungumeshi tayi Cikin murna Tana fadin
Oyoyo yaya
Cikin bacin rai farouk yayi saurin janyeta yace
Ke Meye Hakane bafa ni bane
Kallon mamaki Ta bisu dashi
Jan hannunta yayi Ya juya ya kallesu yace
Amegbo Idan kun Gama gulmar sai ku shigo
Dariya sukayi sannan suka shiga
Kamar yadda yan gidan suka Saba da kallo suka bisu
Duka Suna tsakar gida Dan labari Ya Riga da Ya iso Akan ga farouk can ya dawo
Wajen Inna Mari ya Fara zuwa Cikin murna aka tare su
Sun sha Tarba irin ta kanawan Dabo
Haidar ya d'auki Dan wake Ya saka a baki
Ya Kalli Inna yace
Wai umma sunan da ake bawa Dan wake Ya kamata kuwa?
Kamar ya fa?
Gani nayi yanzu zamani yazo anayin na filawa.
Daga Kai Inna Mari tayi
Ya Cigaba da cewa
To ai kamata yayi a kuma ce masa Dan filawa (lol �)
Hartana farouk sai da yayi dariya wannan karan
Salim yace
Mutum kawai Dan wake na kai masa yana mana santin ga inda dad'i yake
Ai ni an bani labarin kanawa Ada can baya saboda basuda masara da yawa sai suka koma
danbu da Dawa.
Zaro idanu farouk yayi yace
Me? Bansan karya ina aka taba dambu da Dawa
Dariya Inna tayi tace

Tab to wannan labarin waye Ya baka ?
Wani ya diba Ya kai baki yace
A radio mana ana bada tarihin danbu
Ance fa lokacin da ake mulkin mallaka turawan da sukazo Kano danbu aka musu
Da suka Ci
Kawai sai suka Fara fadin
Well-done matawalle
Wai mata ne basu iya fadi ba
Dariya Kowa yayi
Farouk yace masa
To kalarshi Kake ci Ko
Ina! Wannan yafi nasu dad'i harda madara aka barbada mishi fa
Wannan karan harda Inna hadiza a dariya
(Tab danbu na kai maka Salim�)
Sai da suka Gama cin abincin sannan
Haidar yace
Ni Wai baka kaini wajen Audu ba
Tashi farouk yayi yace
Ku jira nayi wanka sai Muje d'aki mu ajiye kayan mu sai Muje inda suke

Sunyi murna da ganinsu sosai
Kamar su hadiye su haka suka dinga murna
Audu ya kallesu yace
Amma fa da mamaki kana gaya mini kamarku amma ban d'auka Kamar ta Kai haka ba.
📑farouk Ko haidar 📑


Written by deeja one love �

Dedicated to madina m umar 🌹

Congratulations for the second tenure malam nasiru Ahmad El -rufa'i Allah Ya tayaka riko.
Ameen

12
Dariya haidar yayi yace
To ai gani Ya Kori ji
Audu ya kuma cewa
Hakane amma Kamar tayi yawa
Farouk yace
Wai ina Salim ne?
Yana can yana barci
Audu ya bashi amsa

Dariya haidar yayi yace
Allah Dan uwanka Ya cika lalaci Kamar wata mace.
Harara farouk ya galla mishi yace
Ina ruwanka to gulma kawai
Daga audun har haidar d'in dariya suka Cigaba da yi
Da yamma suna zaune a wajen wata bishiya suna fira
Abu ce ta taho da sauri
Tsayawa tayi Tana Washe baki
Cikin matukar farinciki tace
Kai umaru kaga yadda ka dawo Dan birni
Haidar ya rike dariyarshi yace
Da gaske
D'aga Kai tayi tace
Yasin da gaske duk da dama Kai daban Kake ko a Da Shiyasa Nace babu Wanda zan aura sai
Kai
Kara sunkuyadda Kai farouk yayi Dan kar ta gansa
Wanda hakan yasa suka kasa rike dariyar
Shagala tayi da kallon shi tace
Kasan me
Girgiza Kai haidar yayi
Idan munyi aure zaka dinga mini irin wannan dariyar Allah Tana birgeni sosai
Abu ta fad'a da kallo suka bita
Tabbas wannan sai a hankali
Fari tayi da idanu Wanda hakan ya kuma basu dariya
Indoce ta k'araso wajen
Ganin haidar yana dariya yasa ta daure fuska Dan itama ta d'auka farouk ne
Cikin jin haushi ta kalleta tace
Wai Meye haka kika zo kika tasa su a gaba kina shirme su kuma suna dariya sun maidake
wawiya
Tsayar da dariyar haidar yayi yace
Haba humaira Abin ne da ban dariya kuma kin San nima ina sonta
Zaro idanu tayi tace
Da gaske yaya farouk
Eh ko Da wani abun ne
A'a babu komai Juyawa tayi ta Fara tafiya.
Hararshi farouk yayi sannan ya mik'e Ya bita da sauri
Abu kuwa tsabar shirme bata ma Lura dashi ba
Shikuma haidar dama abinda yakeso kenan Audu kuwa Dan abi yarima asha kida ne
Wai danma oga Salim baya nan kenan ta Kusa gida sannan ta tsaya Tana share hawaye
Tabbas abinda Ya gaya hakan yake nufi
Humaira
Ya kira sunanta
Juyowa tayi suna had'a idanu tayi saurin Cigaba da tafiya

Ganin ta Kusa shiga gida yasa yayi saurin janyota
Runtse idanu tayi Dan ko ganinshi bataso
Haba humaira ke yanzu Idan aka ce miki zanso Abu sai ki yarda haidar ne ke Mata wasa
Da sauri ta bud'e idanunta Tana kallonshi
Ke in banda abinki kin taba ganina ina dariya Kamar haka.
Shiru tayi Tana tunani Tabbas Hakane kuma fa
Ita tunda take ma zata iya irga sau nawa yayi dariya a gabanta da yawonta
Hannunshi yasa a fuskarta yace
Gaya mini me kike tunani?
Babu komai yaya
OK to Muje na baki tsarabarki
Dariya tayi har hakoranta suka bayyana
Rike hannunta yayi suka shiga gida tare
Rigar daya d'auka a shoprite a kaduna ita ya ciro Ya bata
Amsa tayi Tana farinciki
Har Cikin sasansu Ya rakota d'akin Inna hadiza ta shiga shikuma ya d'auki bokiti ya shiga
wanka
Rigar ta ciro Cikin farin ciki ta shafa Jikinta
Tabbas ta fahimci farouk yana son Abu me purple a jiki Dan duk kayan dayake bata da Kalar
batasan meyasa yake son Kalar ba
Sai da ta nunawa Inna hadiza sannan ta ajiye Akan gobe zata saka
Tabbas yanzu ta Fara zama Yar gayu
Kiran sallar da aka Fara ne yasa haidar dakawa Salim duka
Cikin sauri farouk yace
Meye haka Wai kuna Abu Kamar yara
Dariya haidar yayi yace
To babba Kai Wlh matarka zata Kalli sanabe.
Salim yace
Nidai Allah Ya isa Wlh
Haidar yace
Banza tunda ka mini dariya na ma fasa baka labarin budurwar Nawan
Cikin sauri Salim yace
Da gaske yi hakuri ka bani
Ganin yadda farouk ya daure fuska yasa haidar kwashewa da dariya yace
Mutumina Bari muyi sallah na baka story.
Harda yadda take fari
Ganin bazasu kyaleshi bane yasa shi
Mikewa yace
Idan kun Gama childish din sai ku fito.
Suna idar da sallah suka wuce bakin bingi
Kallon ruwan suke suna fira
Acan gida kuwa
Indo ta Kalli Inna hadiza tace

Amma Inna kinsan yaya farouk yana gari kuma Wlh ni tsoro nakeji yazo Ya ganni tare da
saurayi ballantana sani ma.
Harara Inna hadiza ta aika masa tace
Kaji mini mutuniyar banza Idan kin zauna shi farouk d'in ina kuna sane babu aure a tsakaninku
sannan Idan bakije Kinyi zance ba ta yaya zaki sami Mai sonki har ya aureki zaki wuce Ko sai
na tashi.
Cikin sauri ta Mike tace
To Inna Bari na cire kayan Kinga yaya farouk ya kawo mini
Kallon da innan ta mata ne yasata yin shiru.
Mayafi ta d'auka kawai ta fita
Firar suke amma hankalinta baya wajen
Waige waige kawai takeyi
Gabantane ya tsananta buga hango su da tayi sun taho
Kallon dayake matane yasa Jikinta Fara rawa
Had'e rai yayi lokacin da suka iso
Sallamar da sani Ya musu ma sauran ne suka amsa banda shi
Tsabar bacin rai har jijiyoyin goshinsa sai da suka tashi kallo ya jefa mata Wanda ita kad'ai
tasan me yake nufi kafin yace
I give you two minutes ki sallameshi kizo Idan kika wuce
Murmushin bacin rai yayi Ya wuce
Jikinsu gaba d'aya yayi sanyi
Indo kuwa kuka ta Fara
Tabbas tasan ba karamar wahala zatasha ba yau
Sani yace
Wai shi wannan me yake takama dashi ne
Haidar yace
Ina wanta shi?
Eh
Sani Ya amsa
Salim yace
To Ya bata umarni ne a matsayin na yayanta
Audu kuwa da kyar Ya iya rike hannunta
Ai Kamar ya k'ara zigata ne kukan ta kuma fashewa dashi tace
Yaya Audu ka bashi hakuri Dan Allah
Kema kinsan yana hakuri Akan komai amma banda wannan kawai ki shigo kada ki karawa
kanki laifi.
Wucewa sukayi suka Barta a tsaye
Kallonta sani yayi yace
Kiyi hakuri kinji Nidai fatana Dan Allah ko me zai miki kada ki Dena sona

Wannan ma ta sonshi yakeyi bata ni ba kenan.
D'aga Kai tayi Alamar taji
Wucewa yayi Ya Barta

Ganin bata wa kanta lokaci take yasata nufar hanyar Cikin gidan
Sai tayi Kamar zata shiga sai ta dawo
Tayi ya Kai biyar sannan tayi shahadar shiga
Har ta Kusa shigewa Cikin gida
Ya fuzgota
Da bango Ya hadata
Ta baya Ya matse mata hannu
Har Tana Iska dakyar take Shaka
Ga wuyanta dayake Mata zafi
Goshinta kuwa tasan Ya fashe
Tsabar azaba yasa kukan yaki fita
Cikin fushi yace Mata
Wannan zafin da kike ji bekai Wanda nakeji ba.ina alkawarin da kika yi mini.
K'ara hadata da bango yayi yace
Ba magana nake miki ba
K'ara tayi sannan ta fashe da kuka
Cikin sheshshekar kuka tace
Kayi hakuri bazan kuma ba
Su haidar da ihun datayi ya fito dasu Tsayawa sukayi suna mamaki
Audu ne ya Matsa Kusa dashi ya sa hannu
Yana fadin
Meye haka farouk
Ko gezau beyiba haka be saketa ba
Azaba yasa kuka ma dakyar yake fita
Cikin sauri Audu yace
Ba Tsayawa kallo zakuyi ba kuzo ku taimaka mana
Dakyar suka iya kwaceta
Ai Tana jin ta shaki Iska me dad'i ta arta ana Kare
Kamashi Audu yayi Ya kaishi d'aki zaunar dashi yayi
Ruwa Ya Debo Ya miko masa
Cikin zafin zuciya ya watsa masa ruwan a jiki
Magana yakeso yayi amma ya kasa
Jikinshi har rawa yakeyi saboda bacin rai
Haidar kuwa da Salim jikinsu sanyi yayi Dan basu tab'a ganin ya zuciya Kalar wanna ba
Inna hadiza ce ta shigo
Kallon su Salim tayi taga jikin su a sanyaye
Juyawa tayi ta Kalli Audu taga Ya tsaya tsaki tsamo da kaya a jike

📑farouk Ko haidar 📑

Written by deeja one �

Dedicated to madina m umar 🌹

Kuyi hakuri kun Jini shiru yau abubuwa ne sai a hankali
13
Fita kawai tayi sai Gata ta dawo da kwanan sha cike da ruwa ta kawo mishi.
Babu musu farouk ya amsa ya kafa Kai sai da ya shanye Tass
Sannan ya ajiye
Kwantawa yayi yana rawar jiki
Inna hadiza ta Kalli Salim da haidar tace
Ku kuma fa Kowa Ya tsaya Kamar Wani akuya a gaban kura
Dukda a tsorace suke sai da Salim yayi dariya
Juyawa wajen Audu tayi tace
Kai kuma kaje ka canza kaya mana
Ajiyar zuciya yayi yace
To Inna
Baffa ne ya shigo dakin
Idanu ya zubawa farouk
Kusa dashi yaje ya zauna addu'a yayi Ya tofa masa
Kallon Salim yayi yace
Meyakawo haka ?
Cikin rawar murya yace
Firar da Indo tayi ne
Jinjina Kai yayi kawai yace
Ku tashi Muje
Duka sasan suka wuce acan suka tarar da Inna Mari da Indo a Kwance
Allah sarki Inna Mari akwai kawaici
Waje suka samu suka zauna
Kallonsu baffa yayi yace
Tunda har farouk baya son firar da Indo take fita to daga yau na soke shi kubarshi muga abinda
yake nufi
Babu Wanda yace komai har ya Gama
Tashi yayi Ya fita
Su Audu ma suma fita sukayi
Salim ne ya Kalli kofar dakin yace
Mutumina kuje bakin bingin nan yau bazan je ba
Haidar yace
Saboda me?
Inaso na zauna wajen Dan uwana ne
Dariya haidar da Audu suka yi kafin Audu yace
Kaga ba ma fa lallai bane ya farka yau watakila sai zuwa gobe kaga Muje kawai
Yau dai zaman be musu dadi ba
Duk shiriritar Salim kasayi yayi
Hakama haidar da Audu
Jungum Kowa Ya zauna

Haidar ne ya katse shirun yace
Wai dama yana yin haka?
D'aga Kai yayi yace
Amma sai Idan ranshi ya bace ne
Ajiyar zuciya yayi yace
Allah Ya kyauta kuma babu Rashin Lafiya
Eh mana
Audu yace
Kawai zuciya ce tayi mishi yawa
Dariya Salim yayi yace
Tab kasan me na tuna
Girgiza Kai sukayi Alamar a'a
Dariya ya kuma yi sannan yace
Lokacin da aka watsawa Audu ruwa
Dariya suka yi dukan su
Hakadai har dare yayi suka bar wajen
Washegari sai wajen Tara sannan ya farka
Da addu'a a bakinshi
Duka idanu suka zuba masa suna kallonshi
Shima dai su yake kallo
Shiru sukayi for some minutes sannan haidar yace
Sannu Nawan ya jikin
D'aga Kai yayi Alamar yaji
Da hannu ya nuna mishi Alamar ya D'aga shi
Cikin sasan su ya nufa sai da yayi wanka sannan ya dauro alwala dakin Inna Mari ya shiga ya
Rama sallolin da ake Binsa
Gaishe da Inna yayi kallonshi tayi tace
Akawo maka abinci
Girgiza Kai yayi Alamar a'a
Indoce tayi sallama ta shigo
Ganin farouk a zaune yasata
Fita da sauri
Inna hadiza ta shigo
Tana fadin
Ina farouk d'in Indo tace
Ya farka
Eh Gashinan a zaune
Inna Mari ta bata amsa
Sauran yan uwansa ne suka dinga shigowa suna mishi sannu
Har zuwa dare bai samu yaci komai ba
Dan ji yake Kamar ana hura wuta a jikinsa
Da zasu kwanta ruwan addu'a baffa ya bashi ya sha ya shafa a jiki sannan ya kwanta
Cikin dare haidar ya farka da salati a bakinshi

Kallon farouk yayi
Tabbas yasha yin wannan mafarkin to amma me
Be tab'a ganin fuskar mutumin ba sai yau
Share

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login