Showing 24001 words to 27000 words out of 72611 words
Chapter 9 - farouk Ko haidar complete by one love.pdf
ya dawo amma shiru mun
kira wayarshi akashe mun kira ta haidar itama haka itama Ta Salim a kashe
Shine na kira Mamie tace Wai basu zo ba to shine muka kira mun san sunanan
Mama tayi Ajiyar zuciya tace
Abdallah (Dan haka take ce mishi)
Kai da waye a wajen ?
Ni kadai ne
Ya bata amsa
Bashi labarin meyafaru tayi
Audu banda innalillahi wa'inna ilaihirrajiun babu abinda yake cewa
Abba ne ya amsa Wayar ya kwantar masa da hankali sannan yace kada Ya gayawa Kowa
Amsawa yayi da to
Yana kashe Wayar Wani kiran ya shigo
Ganin Mamie Daga kaduna yasa ta D'aga
Bayan sun gaisa tace
Yanzu Dan uwan farouk ya kira yana tambayar Lafiya?
Hmm Mamie Kedai Bari nan ta kwashe labarin ta bata
Salati tayi sannan tace
Ai be kamata ku zauna bakuyi informing kowaba ya kamata har iyayenshi ki gayawa saboda
kada a sami matsala fa
Jinjina Kai tayi tace Insha Allah zan gaya musu yanzu ya za'ayi
Nisawa Mamie tayi tace
Gaskiya Kinga nima haidar wallahi tunda ya dawo bayada Lafiya Dan Ranar ko barci bamuyi
ba jiyane ma Allah Ya Fara kawo mishi sauki
Abinda yasa ma ban gaya.musu ba kenan saboda kada hankalinsu ya tashi
Ayya Allah Ya bashi Lafiya Ko zuwa gobe zamu shigo mu duba shi.
Mama ta fad'a
Amsar Wayar Salim yayi yace
Mamie ina haidar
Cikin lallashi tace
Yayi barci amma zuwa anjima Idan ya farka I promise zan hadaku
Sannan pls kada ka sawa kanka damuwa Kaji gobe Idan Allah Ya kaimu zaku taho nan Kaji
kuma haidar ba Lafiya gareshi Ko kanaso kazo ya ganka a damuwa shima Ya shiga Cikin Ta?
Girgiza Kai yayi kafin yace
A, a
Yauwa to Naji mama tace ka rame to kayita cin abinci kafin gobe ka maidar kibarka.
Still dai D'aga Kai yayi yace
To
Yauwa to me zan dafa maka
Danbun Dawa?
Dariya yayi Ya Rufe bakinshi da sauri
Yauwa my boy sai kun zo
Cuno baki yayi yace
Bakince zaki hadani da haidar ba
Eh zan had'aku Idan ka kwantar da hankalinka kada kuma ka gaya mishi komai
To Ya bata amsa
Yauwa my boy take care of yourself bye
Kashe Wayar yayi sannan ya mik'awa mama
Murmushi yayi daya tuna Wai
"Dambun Dawa "
Mikewa yayi yayinda mama da abba suka bishi da kallo rabon da sukaga farincikinsa haka har
sun manta ma
Lallai haduwarshi dasu farouk akwai alkhairi.
Mama ta kira Audu ta gaya mishi Akan ya gayawa su mamanshi
Koda ya gaya musu hankalinsu tashi yayi
Karshe sai da baffa yasa ya kira abba Ya kwantar musu da hankali Akan gobe zasu je kaduna
suji yadda za'ayi
Baffa yace
Nima idan Allah yaso zamu taho gobe
Yaso ya hanashi sai kuma ya ga gwara ya barshi
Suna gama Wayar ya Kalli matanshi yace
D'aya sai ta shirya gobe mu tafi
Duka suka amsa da to
Kallon juna sukayi Wanda yasa Inna Mari saurin sunkuyadda Kai
Murmushi baffa yayi yace
Yau soyayyar d'anki tasa kin kasa kawaici Ko
Girgiza Kai tayi tace
A'a taje kawai ai duk dayane
Amma duk da haka addu'a take Allah yasa Inna hadiza tace taje kawai
Cikin ikon Allah kuwa tace
Babu komai yaya kije kawai
Sai ku tafi da Audu
Eh hakane Allah Ya kaimu goben
Ameen suka amsa gaba d'aya.
Washegari suka shirya suka d'auki hanyar zazzau
Suna isa fly over Audu ya kira Salim ya gaya mishi
Mukullin mota Ya d'auka Ya tafi domin daukosu
Suna kan hanya kawai yayi murmushi
Audu dayake yana gaba Ya kalleshi yace
Ya akayi ne
Tunawa nayi da ana gobe za'a d'auki farouk muke fira Nace mishi
Na kosa abba Ya bani mota
Dariya yayi tareda hawaye yace
Kasan me yace
A'a Audu ya bashi amsa
Cewa yayi
Kuma waye zai hau mota kajashi
Nace mishi shida haidar
Hawayen Ya share yace
Cewa yayi Wai basu shirya mutuwa ba
Sai Gashi baya nan yau an bani na dauko ku inama yana nan ya gani
Dafa shi Audu yayi yace
Kada ka damu zai dawo sai ka bashi labari
Murmushi yayi yace
Aikuwa zanso Naji amsar da zai bani
Had'e rai yayi yace
Kai a shiriritar ka ka tuka mini iyaye.
Yanayi yana kwaikwayan muryarshi
Dariya duka sukayi su baffa kuwa tsananin tausayin shi ne ya kamasu
Suna isa gida suka tarar da mama da abba sun shirya
Cin abinci sukayi sannan suka D'auki hanya
Salim ke driving Audu na gefenshi
A tsakiya kuma abba da baffane
Sai husna
Can karshe kuma mama da Inna Mari ne da Yusra
Tafiya suke Kowa da tunaninshi
Yusra dai da husna murna sukeyi yau zasu had'u da sumayya da suke yawan Waya da ita
Sai a lokacin suka tuna
Kallon juna sukayi Ta madubi sukayi murmushi
Husna tace
Baffa Wai meyasa baka taho mana da Indo bane
Murmushi mama tayi tace
Humaira zaku ce ko Aisha
Dariya baffa yayi yace
Har kuka tayi zata biyo mu Nace a'a
Abba yace
Kayya daka sani ka taho da ita
Baffa yace
Rigima zata zo tayi ta mana
Bakin get din sukayi horn
Me gadi yazo Ya bude
Suna shiga Cikin gidan Salim ya fada jikin Mamie yace
Ni Wlh na gaji
Dan bubbuga bayanshi tayi tace
Me yafaru ka gaji
Cuno baki yayi yace
Ba abba bane ya sani driving
Dariya tayi tace
Au kace tare kuke amshi Mukullin parlourn baki ka kaisu can
Kallon su mama tayi tace
Sannunku ku zauna na barku a tsaye
Mama tace
Babu komai
Dan murmushi tayi tace
Wlh ya'yan Nawane akwai rigima
Mama ta Kama baki tace
Ba 'a magana
Inna Mari tace
Aikuwa dai Allah Ya kyauta
Gaisawa sukayi sannan sukayi mata ya Mai jiki
Jiki Da sauki
Salim ya dawo jikin Mamie kawai ya nufa
Mama tace
Ikon Allah kai baka girma ne
Mamie tace
Ai fad'a suke Akan zaman jikina.
Dariya duka sukayi
Mamie tace masa
Jeka ka Kira haidar d'in mana yana d'aki Yadai shiga wanka amma nasan yanzu ya fito
Dariya yayi kafin ya Mike ya tafi
Husna tace
Mamie ina sumayya ne
Tana makaranta dakyar na korata yau Dan cewa tayi bazata jeba
Tunda na ce zakuzo shikenan sai jiya zuwa yau firarku akeyi
Tare da Salim da haidar suka fito
Bayan sun gaisa suka masa Ya jiki
Mamie ce ta Kama hannun husna da yusra tace kuzo ku rakani Mu kwaso abinci
Lafiyayyen tuwon shinkafa da Miyar agushi ne sai jallop d'in couscous Wanda ya wadatu ta
vegetables
Sai kayan cin cin da su cake
Gefe kuma farfesun kifi ne dana kayan ciki
Su haidar suka kaiwa su baffa yayinda su kuma su mama suka ci nasu Anan
Sai da akayi sallar azahar sannan daddy Ya dawo
Bayan sun yi sallah sannan suka had'u domin asan yadda za'ayi
í ½í³‘farouk Ko haidar í ½í³‘
Written by deeja one love
Dedicated to madina m umar í ¼í¼¹
Dan Allah ku tayani da addu'a kwana biyu nan da ciwon Kai nake wuni me tsanani Wlh sannan
Allah Ya biya mini bukatuna na alkhairi
Ameen.
Ya Allah ka bawa khadija haihuwa Tana tsananin bukatar addu'ar ku tace na roka mata.
Nima Nace Allah Ya baki my sisto í ½í¸˜
20
A dinning suka tarar da Mamie
Abinci yaci sosai kafin ya sha maganinsa
Daddy yace
Jeka ka kwanta
Barci yayi har magrib sannan ya farka
Alhmdllh jikin da sauki
Da kyar baffa ya yarda su kwana da aranar yaso su tafi
Su mama dai a Ranar suka tafi tareda Salim.
Washegari da wuri suka tafi
Sai dai kafin su tafi daddy sai da ya kara dubashi.
Suna isa Kano suka sami motar Sarina
Su k'asimu duk suna gida
Jajantawa aka yi tayi.
Farouk kuwa gaba daya jikinshi tsami yayi mishi Don haka bokiti ya d'auka domin wanka.
Inna hadiza tace
Ga ruwa can me dumi kayi amfani dashi
Indo ce ta amsa ta sirka mishi Ta Kai mishi bayi.
Makota da abokan arziki.haka suka yita zuwa
Kasancewar labari A K'auye beda Wuyar yaduwa.
Da safe bayan ya karya ya Kalli Audu yace
Audu ya kamata nadan taka
Baffa yace
Ka bari sai da yamma saboda yanzu Rana zaka ga ta D'aga
Kaga kan nan ma Ya dawo daga kasuwa
(kasancewar Idan rani yayi sukan koma kasuwa ne)
Hakan ne ya faru bayan ya dawo
Suka Fita
Inda suka Saba zama suka nufa sai dai Yau wajen babu laifi a cike yake
Sani Ya Kalli magaji yace
Duba can ka gani
Dariya magaji yayi yace
A'a kaga yan Boko an dawo kenan.
Ko kallonshi farouk beyiba.
Magaji ya kuma cewa
Allah Ya kyauta gaba
Abu ce ta k'araso Tana dariya
Kallon farouk tayi tace
Umar Andawo ahe abinda Ya faru Kenan
D'aga Kai yayi Alamar eh
To Allah ya Kyauta gaba.
Ameen Ya furta Wanda kawai lebenshine Ya motsa.
Murmushi tayi tace
Wlh hankalina ya tashi sosai
Magaji yace
Ke Meye haka wuce ki Bamu Waje
Harararshi tayi
Sani Ya Mike Cikin zare idanu yace
Zaki bar nan ko sai na makeki.
Cikin sauri ta juya
Farouk kuwa Kauda kanshi yayi
Ganin zaman bazai masa bane yasa yace
Su Mike su zagaya gari.
** *** *** *** **
Cikin huci Faisal yace
Wlh bazai yiwu ba
Ammar ya zuba masa idanu yace
Ka zauna ka kashe kanka Akan wata yarinya k'arama.
Harara Faisal ya galla masa yace
Eh ai gwara ni ma tasan ina sonta bayan Kai har yanzu ka kasa gayawa Yusra kana sonta
Murmushi ammar yayi kawai.
Faisal ya zuki taba yace
Wai kasan waccar matar muna fika ce har ta tura d'an ta.
Kallonshi kawai ammar yayi be ce komai ba
Harara Faisal ya galla mishi yace
Kai Wlh wannan izzar taka naga inda zai kaika.
Dariya ammar yayi yace
Ba wannan yafi bani haushi ba shine Sakin wancan yaron da Abban Zaria yasa akayi
Tabe baki Faisal yayi yace
Dama wa'innan son ya'yansa ai Ya mishi yawa
Ammar yace
Na rasa meyasa Wlh be sona.
Oho matsalarshi ce wannan
K'ara zukar tabar yayi yace
Yaushe zamu tafi adamawa
Ammar yace
Nan da two weeks
Kallon rainin wayo yayi masa yace
Kama isa Wlh ban yarda ba
Ammar yace
To zan biya wajen abbana kafin na wuce
Aikuwa sai dai ka biyo ni Dan ni nan da one week zan tafi.
Ammar yace
Kai bikin fa sai nan da three weeks
D'aga Kai yayi yace
Nasani amma bazan yarda wancan ya kayar Dani ba
Dafa kafadarshi yayi yace
Kada ka damu Dan uwa amra zan baka
Dariya yayi yace
To daddy hamma (Al'ameen modibbo kenan)
Hakadai suka Cigaba da firarsu.
Haj Zainab tace
Kada ki damu yaya Idan kin zo zamu koma wajensa domin ya kadasu su shiga duniya
Haj halima tace
Bari sai nazo din amma kada ki Bari su zo adamawa
Dariya Hajiya Zainab tayi tace
Me zai kawosu adamawa Ki kwantar da hankalinki
To sai nazo d'in ki gaida baban Faisal d'in.
Insha Allah zai ji.
Dakyar ammar yayi convincing Faisal ya yarda suka kai sati biyu
Abuja suka wuce Don suyi sati daya
Bangaren Salim ma yau suke ta shirye shiryen tafiya
Harda angon
Salim ke Waya da haidar suna shirya yadda tafiyar tasu zata kama
Haidar yace
Kada ka damu zamu taho on Wednesday
Tabe baki yayi yace
Haba wane Kalar Ranar laraba kafin nan ai ankusa Gama events d'in
Murmushi haidar yayi yace
Amma kasan dole na jira su Mamie ko da Nawan Dan kasan tanan zamu wuce Ko
Hade rai Salim yayi yace
Gaskiya jibi zaku taho
Dariya yayi yace
To ubana bani umarni ne.
Tun Ranar litinin har laraba Salim Waya yake babu sauki
Ganin Abin nashi bazai k'are bane yasa ya hadashi da Mamie
Kwantar Mai da hankali tayi tace
Ranar alhamis zasu biya su d'auki farouk sai su wuce
Haka ya hakura amma duk Wani Abu dayake faruwa sai Ya sanar dasu
Idan kuma na d'auka ne yakan d'auka Ya tura musu su gani.
Yau alhamis Ranar da su haidar zasu wuce adamawa.
Salim ne ke Waya da haidar
Haidar yayi dariya yace
Gamu nan yanzu zamu taho and kada ka kuma kira pls Dan ni zanyi driving.
Dariya Salim yayi yace
Yara duk na rigaku
Murmushi kawai haidar yayi yace
Sai mun iso
Salim yace
To Allah ya kawo ku yanzu muma zamu tafi taro Wani uncle dinmu ne dake South Africa yanzu
zasu sauka
To
Kashe Wayar yayi
Mamie da sumayya ne zasu tafi
Dan surayya Tana makaranta su kuma yaya Adnan da yaya Abbas da daddy zasu zo daurin
aure Ranar Jumu'a
Jan kunnenshi daddy yayi Akan ya tafi dasu a hankali kasancewar yau ne zai Fara driving me
nisa .
í ½í³‘farouk Ko haidar í ½í³‘
Written by deeja one love
Dedicated to madina m umar í ¼í¼¹
21
Sai wajen azahar suka isa.
Duk da Garin k'auye ne amma yanayin Garin ya birge su Mamie
Haidar yayi mata jagora har Cikin gidan
Yayinda daddy Ya tsaya a waje
Inna hadiza ke alwala
Da murna take musu sannu da zuwa har dakin Inna Mari ta kaisu ita kuma ta Riga ta tada
sallah
Haidar yace
Inna ina farouk ne
Ya tafi masallaci
Inna hadiza ta bashi amsa
To muma Bari Muje Masallacin
Indoce ta shigo da ruwa akwanon sha.
Zama tayi ta gaishesu
Mamie tayi murmushi tace
Ashe ma humaira d'in ba babbace
Hannu tasa ta Rufe fuskarta
Sumayya ta jata suna ta fira
Inna Mari Tana idar da sallah suka gaisa
D'an wake ne yaji Mai da yaji me dadi ga salad da tumatir
Sallama su haidar sukayi suka shigo
Tabbas Idan suka jero ba lallai Ka ganesu ba saboda Kamar da sukeyi
Farouk ya Matsa Kusa da Mamie yace
Mamie anzo Lafiya
Shafa kanshi tayi tace
Lafiya lau my son Ya jikin
Yayi sauki
Ya bata amsa
Kallon haidar tayi tace
Da gaskiyarka Babyn momma kamata yayi Akoma cewa d'an wake d'an filawa(í ½í¹ŠMamie tayi
santi)
Dariya akayi gaba daya
Haidar ya Tabe fuska yace
Haba Mamie agaban yaran nan aisai su rainani
Dariya akayi gabadaya
Sumayya tace
Yaya farouk kaga mamie itama tayi santi Ko
Inna Mari tace
Farouk ka tashi ka shirya domin da tafiya agabanku.
Kallon Indo yayi yace
Zubo mana abinci muci tukunna Dan nasan halin wannan.
Dariya aka kuma yi
Farouk kuwa Kauda Kai yayi Kamar bashi ya fad'a ba
Sai da sukaci suka koshi sannan ya mik'e Ya tafi wanka
Indo tace
Aunty sumayya zo Muje kiga gari kafin su shirya
Inna hadiza tace
Daga nan ku biya Dandali ku kira baffanku kice bakin sun iso
Ita kanta sumayya yanayin Garin yayi mata dad'i
Baffan ma Ya rigasu isowa gida Dan sai da suka biya ta bingi.
Suna isowa ma har sun fito
Sumayya ta Kalli farouk da haidar tace
Haba yaya meyasa kuka saka kaya kala d'aya.
Haidar yace
Ke Matsa ki bawa mutane Waje
Farouk yayi murmushi yace
Bama so a ganemu ne.
Haidar yace
To ai ko ita bazata ganemu ba.
Turo baki tayi tace
Mamie Wai bazan gane su ba
Mamie tace
Kyaleshi kawai auta Ko nima ba ganesu zanyi ba
Duka akayi dariya
Gefen me zaman banza haidar ya bude ya shiga
Farouk shi ke driving kasancewar zamansu a kaduna Anan suka koya dukansu.
Sai bayan isha sannan suka shiga Garin adamawa ahakan ma Sunyi gudu
Haidar ya kira Salim
Da haka yana musu kwantance har suka iso
Tab rigiji gabji
Duk iya tunaninka gidan sarautar ya wuce haka
Babu Kowa saboda sun tafi Kamu
Wani yaro ne yayi musu jagora har Cikin gidan
Wata dattijuwace zaune ga kuyangu suna kaikawo.
Cikin fara'a ta tarbesu
Abin ci kala Kala aka kawo musu
Kallonsu farouk tayi ta musu filatanci