Showing 30001 words to 33000 words out of 72611 words

Chapter 11 - farouk Ko haidar complete by one love.pdf

Advertisement

One Love   

23 Mar 2025

5825

yazo mata
Cikin tashin hankali ta kirasu
Kallonsu tayi bayan sun zo tace

Kunsan me kuka aikata kuwa to inaso anjima Idan an kuma zama kada Wanda ya kuma ja da
Mai martaba
Fad'a sosai tayi musu sannan tace Su tafi
Ada yau zasu tafi amma kasancewar wannan abinda Ya faru yasa
Daddy Ya Kira Mamie yace dole su Bari sai gobe.
Ammar yace
Mom ni Wlh hakan ya mini Allah Ya sa a tura shi shida iyayenshi gidan kurkuku
Yayar me martaba Wacce ita bata taba haihuwa ba suna kiranta da hajiya yaya tace
Hmm yaro yaro ne kana gani yaja da me martaba Da zai hukuntashi ai daya hukuntashin Kai
acikin yayanshi da jikoki ban da modibbo akwai me ja da Maganar me martaba ne ya barshi
Shiru sukayi kafin suce Hakane kuma fa
Can ammar yace
To anjima dai zamu ga wane hukunci aka yanke masa.
Karfe sha biyu suka sauka a Kano
Motoci aka turo daga masarautar Kano domin su daukesu
Sai da suka Fara Mik'a gaisuwa sannan suka wuce Garin Sarina Salim ya musu jagora har
kofar gidan
Mutane an firfito ana leke
Kowa da abinda yake cewa
Salim ne ya shiga yayi sallama da baffa Don Sunyi sa'a yana nan
Bayan ya fito suka gaisa kallon su yayi yace
Ku shigo ciki
Daddyn yola yace
Ba zama mukazo yi ba so muke kashiga ka fito da mahaifiyar farouk Sarkin adamawa na
nemanku
Duk da dakiya irin ta baffa amma sai da gabanshi ya fadi
Lafiya dai ko?
Ya tambaya
Murmushi abba yayi yace
Ka dai zo Muje Kaji acan
Shiga yayi babu dadewa ya fito tare da Inna Mari
Mota aka bude musu suka shiga
Mutanen gari sai surutu sukeyi.
Daddy hamma kuwa Garin yake bi da kallo Cikin tsananin tausayawa
Filin jirgi suka wuce Daga nan suka D'aga zuwa adamawa
Dai dai lokacin sallar La'sar suka isa Dan haka masallaci suka shiga kawai sukayi sallah
Suna fitowa suka wuce d'akin iyalai haka suke cewa wajen domin Idan sarki zai Gana da
iyalanshi nan ake zama
Wajen Fa mutane ne zaune
Bayan sarki sai daddyn yola gefe kuma daddy hamma ne
Ata Dayan hannun kuma daddyn Abuja ne sai Gefensa abba ne
Dama dasu hajiya Salma Da hajiya Zainab ne sai hajiya yaya
Matan sarki Fulani sai yafindo Hari sai yafindo karima

Daddy ne sai baffa suna facing d'in su daddyn Abuja
K'asa kuwa Salim sai farouk sai haidar
Gefe kuma amra da ammar sai sumayya da Muhammad.
Kanwar sarki ce ta shigo hajiya delu Waje ta samu itama ta zauna
Abba Ya bude taro da addu'a
Mai martaba ya Kalli baffa da daddy yace
Inaso na sani shin da gaske kune iyayen yaran nan na ainihi?
Shiru sukayi
Daddyn yola yace
Shin ba tambayarku sarki yake yi ba?
Baffa ya

📑farouk Ko haidar 📑


Written by deeja one �

Dedicated to madina m umar 🌹

Kunason typing da yawa amma ku bakuyin comment yadda ya kamata
Zan dau minti goma ko ishirin ina typing amma ku Idan kun tashi Wani ma dakyar zai iya yin
comment da Tnxs Wani kuwa t kawai zai sa
And kuma still kunaso nayi typing da yawa.
To mu taru mu gayra mana inyi typing me tsayi kuma ku tattauna Akan page d'in da nayi type
d'in domin tanan zan gane me nayi kuskure ko badai dai ba.
Duk Wanda a Cikin ku yaga nayi ba daidai ba ka kasa gayawa mini to gaskiya ba masoyina
bane.

Like comment and share pls

Vote comments and follow @13deeja

Comments and forward it to other groups

Much love
Hafsat Hausa novel h²😘
Khaleesat haydar Hausa novel
Kunfi sauran group comments Hakan nasa Ko banyi niyyar typing ba Idan na tuna daku sai Naji
inaso nayi.
Kada kuyi mini wata fassara ku Bari Kuji karshen littafina kada Wacce ta zageni pls. Nasan
zakuce taya uwa zata yardar da yaranta to ku Bari na kai karshe tukunna pls.
24
Baffa yace

Eh ba Wai karya zamu fad'a ba
Dan murmushi daddyn yola yayi yace
To ai kunsan hukuncin Wanda yayi karya Dan haka munaji
Dan numfasawa yayi kafin yace
Shekara ashirin da biyu data wuce wata Ranar alhamis na dawo daga gona ina tafe da fatanya
ta sab'e a kafada.
Wata matace sanye da kaya na alfarma hannunta rike da jariri sallama tayi mini na amsa
Bayan mun gaisa tace
Dan Allah bawan Allah ka taimaka mini da ruwa na bawa yarona kishi yakeji
Kallon yaron nayi sai Naji ya bani tausayi Dan haka na ajiye fatanyata na nufi Wani bingi Ya
Debo ruwa akwanon sha Na kawo mata
Neman Waje tayi ta zauna ta bashi yasha
Kallona tayi tace
Mun gode sosai sai dai motarmu na gaba kadan da Garin nan ko zaka taimaka ka daukar mini
yarona Muje tare
Ganin irin wahalar datasha yasa na amsheshi
Tana gaba ina baya har muka fito wajen motar
Mace daya da maza biyu na gani.
Bindiga Dayan Ya sa mini.
Matar ta juyo tace
Yaron dake hannunka yarona ne amma bana kaunar ganinshi saboda abinda mahaifinsa yayi
mini ka rikeshi ka raineshi ka kuma bashi ilimi na Boko.
kasa magana nayi
babu damuwa Ko Wani fargaba ta bude motar ta shiga
Duka suka rufa mata baya har Sunyi nisa ta Leko ta window tace
Sunanshi FAROUK......
Jan numfashi baffa yayi yace
Wannan shine abinda na san ya faru.
Rumaisa kuwa fashewa tayi da kuka Cikin matsanancin tashin hankali tace
Me marta......
Da sauri Ya D'aga mata hannu yace Bana bukatar kice komai
Daddyn yola ya dubi daddy yace
Kaine ainihin Wanda ya haifi haidar
Girgiza Kai yayi yace a, a
Yadda mal Adamu Ya bada labari kusan hakanne sai dai nawa bayan Na taso wajen aiki ne ta
tsareni Akan na taimaka na rage mata Hanya tausayin data bani yasa na yarda na dauketa
Kawai sai jin bindiga nayi akaina Tabbas abinda ta gayawa Adamu haka ta gaya mini kan cewa
Dan tane Wanda ta Haifa sai dai ta tsaneshi saboda abinda mahaifin shi Ya Mata
Tanaso na bashi ilimi sannan sunanshi HAIDAR .
Daddyn yola ya juya ya Kalli rumaisa Ya nuna ta yace
Waccen ce
Baffa yace duk da shekaru sunja amma Tabbas itace.
Daddy yace

Ni tunjiya da suka fito daga mota tareda ita na ganta na tabbatar itace sai dai da yake bansan
Meye dangantakarku ba yasa nayi shiru.
Kallonta duka yan d'akin keyi
babu abinda ke tashi sai gunjin kuka
Cikin tsananin kuka rumaisa ta durkusa tace
Kuyiwa Allah ku yafe mini wallahi nayi nadama
Daka mata tsawa daddyn yola yayi yace
Ashe bakida hankali har da zaki d'auki ya'yan Cikin ki ki Rabar a duniya
Ansan modibbo yayi miki laifi saiki hukunta wa'inda basu sukayi miki ba.
Daga mishi hannu Mai martaba yayi yace
Ya isa haka
Juyawa yayi Ya Kalli rumaisa yace
Mahaifiyarki ta mutu ta barku na daukeki na rainane ki bayan kin girma na daukeki na aurar
dake ga dana Wanda na fiso bayan kaddara ta gifta kika dauka a laifi yayi miki yana sane na
d'auka ahaka na hukuntashi da hanashi zaman kasarnan gaba d'aya.
Kika bukaci ki koma wajen Yar uwarki a Zaria na yarda kika koma
Kika zo mini a matsayin Kunyi hatsari jikokina sun mutu murus (lol) a wutar data tashi.ko
gawarsu ba'a samu ba
Domin Kauda miki da kewa na aurar dake ga kaninshi domin wanke laifin daya yi miki .kika
kawo mini korafin bakya haihuwa haka nasa yayan mijinki Ya dauki yaranshi har guda biyu ya
baki Ashe duk shirine?
Kukanta ne ya tsananta.
Girgiza Kai Mai martaba yayi yace
Ni bazan hukuntaki ba Akan abinda kika aikata sai dai akwai Abu daya zuwa biyu dazan
gindaya muku keda mijinki.
Juyawa yayi Ya Kalli daddyn baby (haka suke kiranshi dashi kasancewar suna kiran farida da
baby)
Yace inaso ka d'auki matarka ku tafi taraba kada ka sake na k'ara ganin ta tako da sunan tazo
gaisheni ko dubani Idan har Baso kuke na mutu ba sannan ku maidawa da Ahmad yaranshi
danasa ya baku.
Kallonsu duka yayi yace sannan kada Kowa yazo mini da sunan Wai na yafe Mata ni banyi fushi
da ita ba ta nemi yafiyar yaranta gasunan Idan sun yafe Mata shikenan.nidai bana bukatar k'ara
ganinta a gidana.
Juyawa yayi Ya tafi
Wajen tsit yayi sai sautin kukanta daya ke tashi
Hajiya Zainab ta Kalli hajiya Salma ta kashe mata ido daya.
Ganin shirun yayi yawane yasa daddyn yola ya Rufe zaman da addu'a
A hankali mutanen ciki ke fita har sai da ya rage Daga su baffa sai su daddy
Sai rumaisa dake kuka sai daddy hamma daya kasa motsawa idanu kawai ya zuba musu.

A hankali ya mik'e nuni Ya musu dasu taho kowannensu iyayenshi ya kalla
Murmushi sukayi musu Alamar su tafi mana
A sanyaye suka Karasa kusada shi janyosu yayi Ya rungume kuka ya fashe dashi yana fadin

Kuyi hakuri Laifina ne ya shafeku har yasa kuka Kasa samun soyayyar mahaifa.
Hannunsu Ya rike ya juya ya Kalli su daddy yace
Ku shigo daga ciki mana.
Tab ai sai ka shiga gidan wato labari har ya zagaye gida Akan cewa anga yaran daddy hamma
Kowa ina zai sakasu yake
Shidai modibbo yana rike da hannun yaranshi da kyar Ya samu Ya kutsa Tsakanin mutane
bangarenshi Ya nufa dasu
Part ne na alfarma Dan kayan dake ciki daga gani kasan na Wanda yaci Ya tada kaine
A kujera ya zaunar dasu shafa Kansu yayi yace
Yanzu ku gaya mini me kuke so
Farouk ne Wanda bakinshi yayi nauyi da kyar Ya bude baki yace
Inaso nayi wanka
Hannunshi ya rike ya kaishi har bathroom Kamar ya mishi wankan haka yakeji Wai yaranshi
kenan ikon Allah kenan
Zuwa yayi Ya zauna Ya zubawa haidar idanu
Shidai haidar babu eh babu a'a
Ganin shirun yayi yawa yasa daddy hamma yace
FAROUK KO HAIDAR?
Da kyar haidar ya bude baki yace haidar
Kaine ke kaduna kenan
D'aga Kai kawai yayi
Wanda yayi daidai da fitowar farouk kallonshi daddy hamma yayi yace
Ina zuwa haidar kaima shiga kayi wanka
Fita yayi Ya shiga Wani hadadden bedroom Wanda yake blue and white in colour
Kaya ya ciro a hadaddiyar wardrobe d'in d'akin
Dakinshi Ya koma ya tarar da farouk tsaye gaban dressing mirror Mika masa kayan hannunshi
yayi
Warwarewa yayi kayane hadaddu masu tsada da kyau
Bakin Wando ne sai Riga light purple
Yana sakawa hakan ya haska fatarshi
Kallonshi daddy hamma yayi murmushi
Wayarshi Ya ciro domin kiran dayake shigowa wayarshi duk na yan uwa ne da suke masa
Barka da ganin yaran nashi.
Sai abokananshi dayake kira yana gaya musu ganin yaran nashi
Haidar ne ya fito hakan yasa farouk yace
Ga kayan da zaka saka
Amsa kawai yayi Ya saka
Daddy hamma yana ajiye Wayar Wani kiran ya shigo ganin daddyn yola yasa yana dagawa
yace
Afuwan yaya wanka suka shiga yanzu suka fito mun Kusa fitowa
** *** *** ***
Bangaren rumaisa kuwa ganin babu Wanda yabi ta kanta ne yasa tabi ta kofar baya Ya wuce
sasan yafindo Hari ta kwanta Tana Cigaba da kukan ta ahakan har zazzabi ya saukar mata.

Su haidar suka fitowa mutane suka kara taruwa Kowa Na murna
Wasu kuwa yake sukeyi kawai Kamar su hajiya Zainab da hajiya Salma
Su dai su farouk burinsu kawai suga iyayensu haidar ya Kalli Yusra yace
Inasu Mamie suke
Murmushi tayi tace suna bangaren Fulani
Can suka nufa yayinda duk inda suka wuce sai an kallesu domin Kamar da suke Gashi kayan
da suka saka kala d'aya.
Kuyangu kuwa sai Mika gaisuwa sukeyi.
Acan kuwa suka tarar da su Mamie din Waje suka samu suka zauna babu Wanda yayi magana
cikinsu
Dan murmushi Mamie tayi tace
Ikon Allah yau Babyn momma babu shagwaba kenan
Dariya akayi duka dakin
Fulani ta karbe da cewa
Yo yayi shagwaba bayan yasan ya Girma
Inna tace
Me martaba yace Sai jibi zamu koma shi a yadda yakeso ma mu dawo nan da zama to amma
mun fison can din dai
Murmushi farouk yayi yace
Hakan yayi Dan banason zaman mu Anan
Kusan duk Wanda ke Falon beji dadin furucinshi ba
Mamie tace
Amma kasan nanne gidanku ko?
Shagwabe fuska yayi yace
Allah zamana a Cikin mutane da yawa sai sa mini matsala
Dariya haidar yayi yace
Mamie Anan fa busa ke farkar Da mutum daga barci
Dakuwa tayi musu
Dan murmushi farouk yayi yace
Ina Salim
Mama tace Yana wajen garden d'in kusada fada
Mik'ewa sukayi suka tafi domin zuwa wajenshi
Ammar da Faisal ne zaune suke a balcony suna fira
Sai da suka zo kusa da juna sannan ammar yace
Hi brothers
Kallonshi kawai farouk yayi Ya juya ya Cigaba da tafiya
Haidar ne ma yayi k'ok'arin cewa
Sannunku da hutawa
Shima daga haka be k'ara ko A ba ya bi farouk da sauri.

�typing is not easy oh.
Ni daku one love 😘
📑farouk Ko haidar 📑

Written by deeja one love �

Dedicated to madina m umar 🌹
25
Salim yana hangosu ya Fara dariya
Da gudu haidar ya karasa
Shi kuma ganin haidar ya taho shima yasa gudun
Zagaye garden d'in suke yayinda Salim d'in be Dena dariya ba
Su daddyn yola ne suka shigo wajen
Tsayawa sukayi suna kallon ikon Allah
Haidar yana ganinsu yayi saurin Tsayawa ya daure fuska
Gwalo Salim yayi mishi Wanda ya k'ara bashi haushi
Apple dake gaban Wani saurayi yana d'auka Ya jefa masa
Kaucewa yayi yana dariya kara k'uluwa haidar yayi Wanda yasa kadan Ya rage yayi kuka
Zaro idanu daddyn Abuja yayi yace
Meye haka?
Shidai Salim be Dena dariyar ba
Dakuwa daddyn baby yayi mishi kafin ya janyo haidar jikinshi
Kyaleshi kawai
Farouk kuwa kallonsu kawai yayi Ya Kauda fuska
Tashi yayi Ya matsa Kusa da Salim d'an Marin fuskarshi yayi a wasa yace
Shine sai ka gudu ko?
Dariya yayi yace
To me zan tsaya nayi muku tunda mun zama d'aya ai zaku nemeni.
Rumaisa ce tafe ta riko hannun fahad farida kuma na gabanta Daga gani karfin Hali take Dan
ba Lafiya gareta ba
Sallama tayi musu suka amsa
Kallonsu Salim daddyn baby yayi yace
Ku Bamu Waje zamuyi magana.
Dasu da sauran wa'inda ke wajen suka Fara kokarin fita
Farouk ma Ya juya zai fita
Daddyn Abuja ya riko hannunsa yace
Malam ai harda Kai a Maganar
Sai da suka nemi Waje suka zauna sannan daddyn Abuja yace
Ga mahaifiyarku tazo baku hakuri
Rumaisa hawaye na k'ok'arin zubo mata Cikin raunin zuciya irin na Mata tace
Dan Allah kuyi hakuri ku yafe mini nasan na cutar daku amma ina neman yafiyarku.
Farouk Ko kallonta beyi ba
Haidar kuwa Yana jikin daddyn baby yana wasa da links d'in hannunsa
Kamar badasu Take magana ba
Daddyn Abuja yace

Wai ba magana ake muku ba
A hankali farouk yace
Me kace daddy bamuji bane
Tsabar mamaki Kasa cewa komai sukayi wato Dan rainin wayo ma basusan Tana magana ba
kenan.
Links d'in hannun haidar daddyn baby Ya kabar yace
Wai ba magana ake muku ba
Cuno baki haidar yayi yace
Wayyo hannuna.
Kuka rumaisa ta fashe dashi
Daddyn Abuja yace
Mamanku na neman yafiyarku kunji
Kada ku tilasta ma jikokina Akan abinda aka zalince su
Juyawa sukayi da sauri
Mai martaba ne da daddyn yola
Nuni Mai martaba ya musu da su taho
Da sauri suka karasa wajenshi
Shafa Kansu yayi yace
Allah yayi muku albarka
Ameen suka had'a baki suka amsa.
Wai waye farouk waye haidar
dariya sukayi gaba d'aya
Haidar ya nuna kanshi yace
Nine haidar
Murmushi Mai martaba yayi yace
Aliyu gadanga kusar yaki
Hannun farouk ya girgiza yace
Jarumi Mara tsoro umar
Oya kuzo Muje kuga Garin adamawa
Juyawa yayi Ya Kalli daddyn baby yace
Zan Saba maka Idan har na dawo na tarar da wannan a gidan nan.
Tafiya suke yana jan su da fira
Wanda duk Wanda ya gani sai Ya tsaya Yana mamaki amma ganin wa'inda suka fi shekara
ashirin da biyar basa mamaki saboda sun San soyayyar dake Tsakanin sarki da babansu haidar
d'in.
A parking space suka tsaya inda motoci sunfi talatin suke a jere suna jiransu.
Farouk ya Kalli me martaba yace
Bari

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login