Showing 9001 words to 12000 words out of 72611 words

Chapter 4 - farouk Ko haidar complete by one love.pdf

Advertisement

One Love   

23 Mar 2025

5827

wayata
Kira yayi still be D'aga ba
Ajiyar zuciya haidar yayi yace
To yanzu abinda za'ayi shine
Muje room dinku mu zauna may be zuwa anjima Ya dawo
Tsayin one hour be dawo ba
Haidar yace
Friend zan tafi gaskiya Dan inaso naje Wani waje.anjima.
D'aga masa Kai kawai yayi
Yana fita Salim ya koma ya kwanta
Tunani yakeyi Wai shi farouk wane Kalar mutum ne
A haka har barci ya d'aukeshi
Motsin bude kofa Ya sashi farkawa
Kallonshi yayi kafin yace Wani Abu farouk yace
Ka tashi kayi sallah kazo muci abinci
Kallo kawai Salim ya bishi dashi
Be kuma cewa komai ba
Sai ma wajen zama daya nema Ya zauna yana karanatawa Waya a kunne

Daga yanayin yadda yake Wayar ya gane da Indo yakeyi
Cire Wayar yayi yace
Malam Kaifa nake jira
Tashi Salim yayi yaje yayi sallar
Har ya dawo Wayar yakeyi
A sanyaye yace
Za muci abinci yanzu sai anjima
Da sauri Salim ya amshe Wayar ya Kara a kunne
Sallama yayi Ta amsa
Kai waye ?
Ta tambaya
Kai baki sanniba ni sunana yaya Salim
Farouk najinsu suna shirmensu be ce komai ba har su Inna Mari sai da yasa ta basu suka gaisa
Shidai farouk abuncinsa Ya Cigaba da ci
Sai da kud'in ciki ya k'are sannan suka hak'ura
Farouk na gamawa ya d'auki Wayarsa da papers d'in d'azu Ya fita
D'aga kafada Salim yayi Ya Cigaba da cin abincin sa
Sallama sukayi suka shigo
Dariya haidar yayi yace
Kana nan zaune ya dawo Ko?
Daga Kai yayi kawai
Hannu haidar yasa acikin abincin
Kallon Hafiz yayi yace
Bismillah sunaci
Suna fira har suka Gama
Dariya Salim yayi yace
Wato Hafiz abokinka yacika kwadayi
Dariya Haifz yayi yace
Eh mana
Hada fuska haidar yayi yace
Dan ma ina taimaka muku
Kana taimakawa cikinka dai
Tashi yayi yace
Tunda Hakane bazan kuma cin abincin ku ba .
Fita yayi
Hafiz yayi dariya yace
Kofa ruwan Lipton be iya dafawa ba
Dariya Salim yayi yace
Allah sarki Kamar ni kenan
Farouk ne ya shigo kallonsu sau daya yayi Ya Kauda fuskarsa
Hafiz yace
Ya ka dawo kuma har Ka je ka canza kaya gaskiya kayi sauri
Farouk dai da idanu ya bishi

Can yace
Kai bro ina ka samo wannan kuma?
Dariya Salim yayi yace
Hafiz ga Dan uwana da nake baka Labari
Sakin baki yayi yace
Wlh na d'auka wasa Kake Ashe da gaskene ikon Allah Wlh da zance haidar ne
Murmushi Salim yayi yace
Bro ga friend d'in Wanda nake baka labarin kuna Kama haidar ka tuna shi
📑farouk Ko haidar 📑

Story and written by
Deeja one love �

Dedicated to madina m umar 🌹

Dafatan anyi zabe Lafiya Allah Ya k'ara Had'e kanmu baki d'aya Ameen
08
Murmushi yayi yace
Wai Kai wane iri ne haka?
Ji ka yarda Wai muna Kama?
Hafiz yace
Wlh bakuda banbanci Kamar Ku d'aya
Dafa kanshi yayi yace
To Kai ma Ya saka maka virous d'in kenan
Dariya Hafiz yayi
Had'e fuska Salim yayi yace
Wane virous gareni
Daukar bokiti yayi Ya fita
Dariya Hafiz Ya kuma yi Wanda ta kular dashi
Daukar pillow yayi Ya bishi da gudu
Sai da ya kaishi block dinsu sannan ya kyaleshi
Wayarshi ce tayi k'ara
Ganin mamanshi yasa shi dagawa
Cikin bashi umarni tace
Kaje office din Hajiya zainab
Kan yace komai ta kashe Wayar
Iska ya furzar Ya nufi hanyar admin
Sallama yayi
Sai da aka bashi izinin shiga sannan ya shiga
Tana zaune Kan two seater shi kuma d'an mulkin yana kan Kujerar ta ta aiki
Wayarsa yake daddannawa
Yafi minti talatin a tsaye kamar basu San dashi ba
Jikin dakiya ya kuma cewa

Aunty gani
Ai na san da Kai tunda ina gani
Ta gaya Tana d'agowa ta kalleshi
Tafi minti biyar har ya Fara tsarguwa sannan tace
Kaje ka Kira abokin naka Wanda yafi Dan uwanka
Murmushin takaici yayi
Ya juya ya fita
Tabbas da matsala na kira farouk muzo nan
Ya fad'a to yanzu yaya zanyi
Wata dabara ce ta fado masa arai
Da sauri Ya nufi block dinsu
Suna zaune suna fira ya samesu
Zama yayi a gefe
Haidar ya juyar da Kai
Hafiz yayi dariya
Harara Salim ya galla mishi
Ya juya ya Kalli haidar yace
Kai mutumina zo Muje Kaji
Babu inda zan je
Haidar ya gaya Yana mik'ewa
Hannunsa ya rike yace
Haba aboki kada kayi mini haka mana
Kazo Kaji
Haidar yace
Ka kyaleni malam babu abinda zan ji
Sakin hannunsa yayi yace
Ina Idan aboki yana Cikin matsala aboki na taimaka masa amma Ashe ba haka bane
Kenan gaskiya ta fada
Da sauri haidar yace
Wacece?
No babu damuwa kawai
Juyawa yayi Ya fita
Da sauri haidar ya bishi
A hankali ya Dafa kafadarshi yace gaya mini gaskiya me ya faru?
Ajiyar zuciya yayi yace
Muje wajen da yakeda sirri
Garden suka je
Salim ya Kalli haidar yace
Ka tab'a jin ana masarautar modibbo
Dariya yayi yace
Waye besan da zamanta ba kace mini masarautar adamawa
Murmushi yayi yace
Sarki Al'ameen idris abdussamad

Sarki na talatin da uku
Sarki ne me adalci sosai ya haifi yara guda goma sha bakwai a ciki akwai mata akwai maza
Babana shine d'a na hud'u yana da yaya Wanda yake bi Al'ameen suna kiransa da modibbo
Yana India acan yake da zama bayan Wani Abu ya faru
Cikin kannen kakanmu akwai Wanda ya haifi Hajiya Zainab
Kallonshi haidar yayi yace
Kana nufin Hajiya Zainab dana sani Ta nan makarantar
D'aga Kai yayi yace
Bata da mutunci da babana da ita full cousin ne
To Tana da Ya Wacce ke auren wannan wan babana dana gaya maka
Ta fita Rashin mutunci sosai
Da mamana da hajiya zainab babansu d'aya kuma Yarta ita ta raineta wato Hajiya Salma
Mamana macece me ha'kuri dalilin dayasa take danne wasu abubuwan dake faruwa kenan
Ita duk Wani Abu daya shafi Hajiya Salma to girmamashi take
Hakan yasa muke taka tsantsan da bacin ran Wanda ya danganceta
Jiya na baka labarin me ya faru tsakaninmu da Dan hajiya Zainab Wanda kanwa take ga hajiya
Salma
To yanzu ta kira mamana tace naje
Naje d'in tace sai naje da farouk
Jinjina Kai haidar yayi yace
To yanzu meyasa ka bani labarin nan ?
Na baka ne saboda inaso kaje a matsayin kaine farouk Dan zuwa da farouk akwai matsala
Salim ya bashi amsa
Na fahimta
Haidar ya fada
Yauwa nasan kafi farouk sanyin zuciya Dan Allah Idan mukaje suka nemi da ka bada hakuri ka
bayar Kaji
Salim yace da haidar.
D'aga Kai yayi Alamar yaji
Yadda ya barsu haka ya dawo ya samesu
Kallon haidar tayi
Har saida ya Fara gajiya da kallon
Ta bagaren ta kuwa gaban ke faduwa Tabbas wannan jinin modibbo ne
Ya ilahi
Ta fada a hankali Tana dafe Kai
Dan karamin tsaki haidar ya ja
Cikin zafin rai Faisal yace
Kai karamin Dan Iska mummyna Kake Jawa tsaki
Gefe ya kalla bece komai ba
Kallon Salim tayi tace
Nima ya fini a wajenka Ko?
Girgiza Kai yayi Alamar a'a
Ba Abin mamaki bane Dan hakan ya faru tunda tarbiyar da halima ta baka kenan.

Runtse idanu Salim yayi Dan zafin daya Keji
Haidar kam Abin mamaki yake bashi
Kallon haidar tayi tace
Kai kuma a gida haka aka baka tarbiyar girmama na gaba da Kai
Kallon gefen ido yayi Mata yace
Point of correction
Ai ni tarbiyar da aka bani shine na girmama Wanda ya girmama kanshi amma Idan har mutum
be rike girmanshi ba to koshi Ya yankewa k'asa cibiya nakan bi takai na taka ne
Mari Faisal ya Kai mishi yace
How dare you talk to my mum like dis
Murmushin takaici yayi yace
Oh Kai kadai Kake da uwa mu tamu ba haifar mu tayi ba sannan mu Bama kishin iyayenmu sai
Kai
Matsowa Kusa dashi yayi yace
Wannan kaci alfarmar zuwa nayi har Cikin office din mahaifiyarka amma ka kuma Marina to zai
zama babban Kuskuren da zaka aikata a rayuwarka
Jan hannun Salim yayi Ya matsar har gabanta yace
Madam zainab ki sani Salim shine kadai Dan uwanki amma ba farouk ba Idan har kuskure yasa
kika kuma kirana Akan dis nonesense things zan gwada miki ni wanene
Aikin banza kawai
To ko club grade by grade ne.
Murmushin gefen baki yayi mata Ya juya ya fita
Office d'in shiru yayi kafin ta daga Kai ta Kalli Salim tace
Uwarka ka tsaya yi
Da sauri Ya fita
A admin block d'in ya had'u da farouk d'in
Cikin tashin hankali yace
Kai bro ina ka shiga tun d'azu naketa nemanka ?
Jan hannunshi kawai Salim yayi suka tafi
Suna zuwa d'aki Ya zaunar dashi
A sanyaye yace
Mamane ta aikeni wajen Yar uwarta.
Girgiza Kai yayi yace
OK
📑farouk Ko haidar 📑


Written by
Deeja one love �

Dedicated to madina m umar 🌹
09
Tashi farouk yayi Ya zuba musu abincin

Yana Lura dashi kawai juya cokali yakeyi
Kamar yadda Salim ya zata
Mamace ta kirashi a Waya tace
Tana bukatar ganinshi
Salim yace
Mama ki Bari sai next week Dan wannan satin ina da ayyuka da yawa
Umarni na baka fa ba shawararka nake nema ba
Kashe Wayar tayi
Kallon farouk yayi sannan ya Mike ya fita
Ya Muhammad Ya Kira a Waya ya gaya mishi abinda Ya faru
Ajiyar zuciya yayi yace
Salim ka bari zan Mata magana amma kasan halinta Ko?
Eh amma ai ni babu Laifina fa a ciki
Salim ya bashi amsa
Suna gama Wayar ya hango haidar na tahowa
Had'e rai yayi
Haidar yayi dariya yace
Dama Sakin ranka kayi Dan ba kyau Kake ba Idan ka daure fuska.
Ai bansan kaima 💣 bomb bane da ban kaika ba
Salim ya fada
Dariya haidar ya kuma yi kafin yace
Haushi suka bani
Salim yace
Amma ka sani Dan uwana 🚀 rocket ne
Dariya haidar yayi yace
Tab Allah Ya kyauta
Ya kuka k'are to
Had'e rai yayi
Bayan ka ja mini matsala Kake tambaya ta yanzu ina zakaje
Shafa cikinshi yayi
Dariya Salim yayi yace
Wlh mummy na k'ok'arin Kaifa consumer ne.
Jan hannun shi yayi yace Naji Muje
daga jiya zuwa yau nayi missing girki me dad'i.
Fira suke har suka karasa d'akin yana zaune Yana Karatu suka shigo
Dago Kai yayi Ya amsa sallamar su
Kallon kallo aka koma yi Tsakanin haidar da farouk
Cikeda mamaki haidar yace
Mutumina ka ga abinda na gani Ko aljanine
Dariya Salim yayi yace
Ba ina gaya muku kuna Kama ba kuma karyata ni ai Gashi Nan kun gani da idonku
Shidai farouk be ce komai ba sai idanu da yake binsu dashi
Zuba masa abincin yayi

Shi kuma ya Fara ci
Haidar na gamawa yaceda juya ya Kalli farouk yace
Mutumina Anya kuwa wannan yana magana
Tab'e baki Salim yayi yace
Bro ai yadda kasan ya had'a Jini dana sarauta Ko ni bazan gaya masa miskilancin ba.
Ko kallonsu be yi ba
Tashi Salim yayi Ya fusge littafin dake hannunshi yace
Bro Meye Hakane Wai kanaji ana magana kayi shiru
Kallonshi kawai ya tsaya yi kafin ya kwace littafin
Had'e rai Salim yayi Ya Mike
Da sauri farouk ya rike hannunsa yace
Kai Wlh ka cika rigima to yanzu gaya mini me Kake so nace
Bansani ba
Salim ya fada a zafafe
Murmushi yayi ya juya ya Kalli haidar yace
Barka haidar Ko
Daga Kai yayi Alamar eh
Kaga bro yaji haushi ka saka baki mana
Haidar ya Kalli Salim yace
Haba mutumina ai Ya bada hakuri ya wuce Ko
Harara ya galla mishi yace
Bansan katsalandan malam ina tare ka ganmu
Kallon farouk haidar yayi Ya Tabe fuska
Cikin shagwaba yace
Ka ga na saka baki ya gwasaleni Ko?
Sakin hannun Salim yayi Ya matso kusada haidar yace
To ai kaine ina tare ka ganmu
Zaro idanu yayi yace
Had'e mini Kai zakuyi
Dariya Salim yayi yace
Ai maganinka kenan
Tashi yayi yace
Bazan kuma dawowa d'akin nan ba Dan watarana duka zakuyi mini
Farouk zai bishi Salim yayi saurin riko shi yace
Kyaleshi gobe ma zai dawo
** ** ** ** ***
Haidar ya Kalli Salim daketa had'a kaya yace
Wai Kai sai kace me kwana goma ina kwana biyu kawai zakayi
Farouk yace
Kyaleshi Nawan wannan daka gani ba Karatu yakeso ba
Dariya Salim yayi yace
Ba Muda lectures Ranar Monday da Tuesday fa Shiyasa zan kwana hudu
Kallonshi farouk yayi yace

Yanzu kai sai ka tafi ka barni ni d'aya
To baga haidar nan ba
Salim ya bashi amsa
Shiru yayi yace
Ko nima na tafi Kano ne?
Haidar yace da sauri
A'a ni Kadai zaku Bari kenan
Murmushi farouk yayi yace
To ai kai dama kana da abokin zama
Shiru yayi kafin yace
Gaskiya ban yarda ba
Wai ma a Kano a ina Kake
Salim yayi dariya yace
Kasan Sarina dake wudil local govt
D'aga Kai yayi Alamar eh ya k'ara da cewa
Amma jinta nakeyi
To Dan can ne
Har bakin get suka rakashi kafin su juyo
Mama tace
Yi mini shiru banason jin komai a gabanka za'a ciwa Zainab mutunci ka kyale wai Salim da
bakinka Kake cewa gwara bare da Dan uwanka to Wlh ka kiyayeni bance kada kuyi Abota ba
amma matukar zaka dinga janyo bacin rai na to Tabbas zan datseta
In banda Kai Wani irin mutum ne taya zaka yarda a dinga wulakanta Dan uwansa Haba
Yanzu Gashi aunty halima ta kirani tace nanda end of this month zasu zo Idan kuma Maganar
taje kunnenta Nace Mata me?
Shi dai Salim be ce mata komai ba
Numfasawa tayi kafin ta Cigaba da cewa
To daga yau kada hakan ta kuma faruwa sannan Daga yau Kullum kaje ka gaisheta wannan
umarni na ne
Sunkuyadda Kai yayi yace
To Insha Allah zan dinga zuwa sannan Allah Ya huci zuciyarki kiyi hakuri hakan bazai kuma
sake faruwa ba
Tashi kaje
Mikewa yayi tafi
Haidar yace
Bani labarinka Nawan
Murmushi yayi yace
Me zakayi da labarina
Dariya haidar yayi yace
Let's keep our selves busy mana
Littafi farouk ya janyo Ya Mika masa
Dariya haidar ya kuma yi Ya ce
Nifa labarinka nake so.

Kallonshi farouk yayi yace.
Gidan mu babban gidane a Sarina
Mahaifina manomi ne yanada yara takwas mace d'aya maza bakwai
Nida yayyena da kannena
To Kaji labarina
Ajiyar zuciya haidar yayi yace
OK ni kuma ina a kaduna anguwar rimi
Momma na babbar justice ce high court babana kuma babban likita ne da ake ji dashi a kasar
nan Dan shine likitan dake kula da iyalan governor na kaduna
Mu biyar ne ya'yansa
Maza uku mata biyu
Yaya Abbas shine babba commissioner of police na kaduna
Sai yaya Adnan shi kuma babban lawyer ne
Sai ni dake Karatu yanzu nake karantar medicine/surgery
Sai surayya ita kuma tana karantar mass communication me a Cambridge University England
Sai sumayya ita Ko candy bata yi ba
Kasancewar babu tazara tsakanina da surayya yasa tafi Raina ni
Wannan shine labarina
Murmushi farouk yayi yace
Meyasa ba'a fitar da Kai ba?
Nine Bana so kawai ji nayi nafison nazo nan nayi Karatu
Haidar ya bashi amsa
Gaskiya gidanku gidan yan Boko ne
Farouk ya gaya Yana dariya.
📑farouk Ko haidar 📑

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login