Showing 3001 words to 6000 words out of 72611 words
Chapter 2 - farouk Ko haidar complete by one love.pdf
sauri ta k'araso Kusa dashi
Yau ma kin d'auki tallan?
Hawaye ne ya zubo mata tace
Eh amma Wlh ban kulashi ba
Kallonta yayi Kamar na minti biyu har ta cire Ran bazai yi magana ba
D'aga Kai yayi Alamar yaji
Sannan yace
Jeki zubo mini abinci
Audu dai na tsaye Yana kallon ikon Allah
Dariya yayi yace
Wlh matarka ta shiga uku da mulki
Be ce komai ba
Domin yasan dama bazai yi magana
Indo ce ta k'araso da abinci a hannunta
Mik'a masa tayi
Amsa yayi Ya Kalli Audu yace
Bismilla
Kad'a Kai yayi Ya saka hannu suka Fara cin abinci
Da yamma suna zaune a Dandalin yamma
Sani yazo Ya zauna
Ya Kalli farouk yace
Haba umaru Ya haka Dan Nace inason k'anwarka sai kuma ka hanata?
Kamar bazaiyi magana ba sannan yace
Kanwata ce ina to zata auri Wanda na zab'a mata ne
Baki bud'e Audu yake kallonshi
Sani be ce masa komai ba
Ya mik'e yace
Ina dai a matsayin wa Kake kawai amma Kake wannan tsarin Kamar ubanta to zaka gani
kuwa
Murmushi farouk yayi yace
OK zaka gani
Yana tafiya Audu ya kalleshi yace
Meye Hakane Wai?
Kasan dai watarana aure zata yi Ko to kuma kana korar mata masoya.
Tashi yayi Ya bar wajen.
Da dare suna zaune suna cin abinci Inna hadiza ta Kalli farouk daya fito wanka tace
Ka kyauta Wai wane irin yaro ne Kai ka hanata Tsayawa da samari ni wannan wane irin Abu
ne?
Kallonta yayi yace
Ita ta gaya miki haka?
Bansaniba
Murmushi yayi yace
Nifa cewa nayi kawai ni zan zab'a mata mijin aure
Dukansu bud'e baki sukayi suna maamaki.
K'asimu yace
Cab Abin naka har yakai nan kuma
Shidai be kuma cewa komai ba ya shige d'akin Inna Mari
Indo kuwa matso hawaye take Dan tasan da wuya yau be daketa ba
Suna gamawa ya kalleta yace Muje muyi Karatu
Babu inda zataje
Inna hadiza ta gaya Tana mik'o masa Leda
Amsa yayi Ya duba
Maganinsa ne a ciki Kallonta yayi yace
To Inna yau kuma rigima kike ji.
Had'e rai tayi tace
Aika rainani dole ka gaya mini haka
Shiru yayi Ya zauna kawai
Baffa yayi murmushi kawai ya mik'e
Bayan wata biyu sakamakon su ya fito yaci nine credit.
ABU Zaria Ya samu admission
Yana gayawa baffa yace
Anya farouku Zaria beyi nisa ba
Shafa Kai yayi yace
Dama ai d'aki zan Kama
To Allah ya taimaka
Ameen
Ya amsa
Yana gayawa Inna Mari ma haka tace
Inna hadiza kuwa cewa
Tayi
To dayaake Abin da zamani amma duk fad'in Kano ka rasa inda zakaje makaranta sai Zaria
Murmushi yayi yace
Zan dinga dawowa Hutu ai
To Allah ya taimaka
Ameen
Haka sauran 'yan uwansa suma suka ce
Bayan kwana biyu yana zaune a Dandalin yamma
Abu tazo wajen
Sanin halinta yasa Audu be mata magana ba
Ganin Idan ba ita tayi mishi magana ba bazai kulata ba yasa tace
Umaru yanzu Zaria zaka tafi bazan kuma ganinka ba
Dukda yadda bayasonta amma sai da ta bashi tausayi
Cikin sanyin jiki yace
Ai zan dinga zuwa Hutu.
Dariya tayi tace
To amma yau Naji dad'i kayi mini magana me dad'i
Kallonta yayi yace
Kinga Abu nifa burina nayi Karatu ba yanzu zanyi aure ba
To ai zan jiraka
Kina ganin gidanku za'a barki?
Shiru tayi Dan tasan baza a tab'a barinta ba.
Tashi yayi Ya tafi gida
Kamar yadda ya zata kuwa
Tallan da be k'auna ake kasawa Indo
Ko Kallon inda suke beyiba Ya Debi ruwa a rijiya ya shiga wanka.
Audu ya shigo gidan
Ganin Inna hadiza yasa ya tambaye ta
Ina farouk?
Ya shiga sana'artasa
Zama yayi yana jiran fitowarsa
Kallon Indo yayi mata alamu da tazo
Tsugunawa tayi gabansa.
A hankali yace
Kinason sani?
Daga Kai tayi Alamar Eh
To kada ki damu zan shawo miki kanshi
Farouk daya fito yana jinsu ,banza yayi dasu Kamar be jisu ba.
Yan mata uku ne tafe zasu je d'iban ruwa
Suna tafe suna fira
Dayar tace
Nifa Idan nice ke bazan iya jure wulakanci da umaru ke miki
Dagowa tayi tace
Wlh binta inasonshi ne bazan iya rabuwa dashi ba
Dayar ta kalleta tace
Au to magaji fa?
Bana sonshi gaskiya
Girgiza Kai tayi
Suna mamakin irin son da take masa
Suna isa suka tarar da farouk ya rako Indo d'ibar ruwa
Binta ta taba Abu ta nuna mata
Murmushi tayi ta nufi wajen su
Sallama tayi musu
Yana tsugunne yana d'ibar mata ruwan
Indoce ta amsa
Dagowa yayi yace
Abu kema d'ibar ruwan kikazo.
Dariya tayi tace
Eh
Mik'awa Indo Nata tulun yayi yace
Kawo naki
Wayyo Kamar ansaka a aljanna
Da sauri mik'a masa
Yana amsa daidai isowar magaji da sani da idi
Da sauri sani Ya nunawa magaji yace Kalli can
Cikin zafin zuciya ya nufi wajen
Cikin fushi yace
Kai umaru Meye Haka dama Wai amanata kuke ci Ko?
Ko kallo be isheshi ba
Hakan ya k'ara kular dashi
Sani yace
Sannu me zab'awa k'anwarshi mata to nima k'anwata mijin dana zab'a mata shi zata aura
Kallon Abu yayi yace
To kinji me yayanki yace
Dan haka kibi zabinshi
Cikin sauri tace
Amma ni Kai nake so
Murmushi yayi mata
Ya mik'a hannu ya amsa tulun hannun Indo yace Mata Muje
Cikin kuka Abu ke kiranshi.
Tsabar haushi dukanta sani Ya Fara
Da kyar su magaji suka kwaceta
Yau farouk ke shirya kayansa domin ya wuce Zaria registration
Kudin dake hannun baffa Ya amsa
Yace
Baffa Idan na samu yadda nakeso yau gobe zan dawo Idan kuma ba haka ba to sai jibi
Daga Kai baffa yayi yace
To Allah ya Tsare
Ameen Ya amsa
A kafa Ya zo har darki kafin ya sami motor da zata kawoshi Kano wajen obasanjo bridge
Anan ya sami mota direct har Zaria
Tunda ya shiga motor Gabanshi ke faduwa Dan wannan ne tafiyarshi ta farko da zai bar Cikin
Kano.
A motor Ya hadu da wani me Dan banzan surutu.
Tun yana shareshi har ya saki
Kallonshi yayi yace
Kai Dan Zaria ne?
Eh Kaifa?
Registration zanje
Dariya yayi yace
Kanada Wanda zai nuna maka abubuwa ne
A'a
Dariya ya kumayi yace
To Idan munje na raka ka
Ka gannin nan suna na Salim haifaffen Zaria ne
Yanzu haka kan na taho akaje aka mini registration a pharmacy
Murmushi yayi yace
Nima haka.
Wai ya sunanka ne?
Umar farouk.
Farouk ya bashi amsa
Suna zuwa aka sauke su
Motor samaru suka nema
Sai da suka shiga ABU Zaria suka Gama komai
Farouk dai Sakin baki yayi yana kallon makarantar Tabbas ta hadu sosai fiyeda yadda Kake
tunani
Salim yace
Zan nema mana accommodation sai mu zauna daki daya
Daga Kai yayi kawai
Yanzu Muje gidanmu ka kwana
Kallonshi farouk yayi yace
A'a kaje dai zan nemi wajen kwana
Dariya Salim yayi yace
Tab Ai kafata kafarka
Ganin bazai kyaleshi bane yasa ya bishi.
í ½í³‘farouk Ko haidar í ½í³‘
Written by deeja
Love
Dedicated to Madina m umar í ¼í¼¹
0⃣4⃣
Gidan babu laifi Dan gidane na alfarma
Bayan sun gaisa da mamarshi suka wuce d'akinsa.
Gadone makeke komai a d'akin Masha Allah
Salim yace
Farouk nan ne gidanmu ga d'akina
Murmushi yayi yace
Na gode wannan d'aki haka Kamar Wani me mata
Abin ya bashi mamaki sosai Dan be tab'a tunanin farouk d'in ya iya tsokana ba.
Hmm kasan me?
Girgiza Kai yayi Alamar a'a
Muje mu ci abinci in Kai ka kaga gari
To yanzu dai Fara nuna mini bayi inyi wanka
Nuna masa Salim yayi shi kuma ya shiga.
Bayan yayi wankan ya fito ya shirya sannan suka fito
Mama na nan a inda suka Barta
Salim yace
Mama Kinata hutawa abinki
Harara ta aika mishi dashi tace
Ai ka dawo dole ka dameni
Wasu 'yan mata ne guda biyu suka shigo gidan da gudu.
Dayar taje bayan mama ta boye.
Ihu suke suna zagaye falon
Daka musu tsawa Salim yayi yace
Dallacan matsa ku bani Waje.
Cikin Zunboro baki Kowacce ta Kama hanyar d'akinsu
Suna gama cin abincin suka fita
Yawo sukayi sosai yana nuna mishi Cikin garin Zaria.
Duk da Garin ba Wani kyau gareshi sosai ba amma Yanayin tsarin Garin ya birgesshi sosai.
Sai bayan isha'i sannan suka dawo.
Yanzu dai harda wa'inda be gani d'azu ba yanzu duk sun dawo.
Duka kallonshi sukeyi
Mama ta Kalli Salim tace
Talkative aika gabatar wa da 'yan uwanka abokin naka Ko?
Kai mama!
Yanzu Daman zan aikata.
Brothers and sisters wannan shine abokina umar da muka had'u a mota d'azu dana dawo daga
Kano.
Dariya Abin ya basu.
Had'e rai yayi yace
Meye kuma na dariya?
Babban ciki yace
Kai ai Garin kwashe kwashenka sai ka kwaso Wanda zai siyar damu
Mama ya kalla ganin batace komai ba yasashi cewa farouk
Buddy tashi mu tafi
Dayar da suka shigo d'azu tace
Yi hakuri yaya
Harara ya galla mata yace
Matsa kafin na mareki.
Suna shiga d'akinsa Ya Kalli farouk yace
Kada ka damu da abin da suka fad'a haka suke dama.
Murmushi farouk yayi Ya zauna bakin gado.
Tab'e baki Salim yayi shima Ya zauna
Mu bakwai ne a wajen daddynmu ainihin mu 'yan adamawa ne aiki Ya kawo mu nan .
Wanda yayi magana shine d'a na biyu a wajen daddyn mu sunanshi Muhammad babban kuma
sunanshi Mubarak yana UK ne yana Karatu.
Shi kuma Muhammad yana Cairo ne ya dawo Hutu ne
Sai ni Salim Wanda zan shiga yanzu makaranta.
Murmushi farouk yayi yace
Kai baza'a fitar dakai bane
Dariya yayi yace
Tab daddy ya fitar Dani ai yasan me yayi.
Sai wa'innan 'yan matan daka gani su 'yan biyu ne d'aya yusra d'ayar husna
Sai wa'inda ke binsu suma 'yan biyu ne fahad da farida su suna wajen wan daddynmu ne a
South Africa.
Acan yake zaune?
Farouk ya tambaya.
A'a yaje check up ne
To Kai bani labarinka.
Kwanciya yayi yace
Yanzu na gaji gaskiya sai dai zuwa anjima.
Dariya Salim yayi yace
Zo Muje mu sayo abinci
Farouk yace
Saboda me bazamu ci Anan ba?
Shiiiiiii Salim yasa hannunsa abakinsa alamun yayi shiru
To Bari nayi wanka
Da kallo Salim ya bishi yace
Wai Kai kana gajiya da wanka kuwa
Bece masa komai ba har ya shige.
A jere suka fito
Yanzu Basu a zaune a falo suna kan dinning
Ganin suna k'ok'arin fitane yasa
Muhammad cewa
Ku kuma ina zuwa?
Husna ta bashi amsa da
Siyan abinci zamuje
Ta fad'a Tana Had'e rai
Irin yadda yakeyi Idan an bashi haushi
Dariya sukayi gaba daya kafin mama tace
Kaga farouk kyaleshi kazo ka zauna kaci abincinka.
Da sauri Salim ya kalleta yace
Mama me hakan ke nufi.
Ta canza d'a
Yusra ta bashi amsa
Harara ya aika Mata yace
Nayi magana dake ne
Dariya suka kuma yi
Muhammad Ya mik'e Ya matso Kusa da su ya kama hannun farouk yace
Muje kaci abinci ka manta da wannan rigimammen.
Binshi farouk yayi
Hakan yasa suka kuma dariya
Buga k'afa ya Fara yi k'ara dariya suka kuma yi.
Mama tace Kaji kyalesu autan mama
Dariya yayi yace
Yauwa mamana
Muhammad yace
Jishi k'ato dashi Wai auta
Kallon farouk yayi yace
Kannensa hud'u fa
Murmushi farouk yayi yacigaba da cin abincin sa.
Har suka Gama cin abincin Kowa da drama da yake yi
Abin birge farouk yayi
Washegari tun da wuri farouk ya shirya.
Babu yadda basuyi Akan ya hak'ura zuwa anjima sai Ya tafi
K'in yarda yayi hakan yasa suka kyaleshi
Sun masa Sha Tara ta Arziki
Salim yace
Kome ke tafiya zaka dinga ji ta wajena yanzu Bani number dinka.
Ai ni banada Waya
Farouk ya fad'a
Mama tace
To aikuwa bazai yiwu ka tafi ba'aji daga gareka.
Kiran Muhammad tayi tace
Ka biya ta sahad ka siyo mini waya.
Samsung Galaxy S5 ya siyo
Bashi tayi tace
Ya rike Dan su dinga ji daga gareshi
Haka ya tafi Yana mamakin mutuncin mutanen.
Yana isa Garin darki ya sami me mashin ya d'aukesa har Cikin garin Sarina.
Be tarar da Kowa a gidan ba Kamar yadda ya zata
Wanka kawai yayi Ya shirya ya tafi gona.
Suna ta aiki yaje ya samesu.
Bello yace
Ga 'yan makaranta sun dawo
Murmushi farouk yayi yace
Ina Audu
Bello yace
Yana wajen baffa suna girbi
Murmushi yayi yace
Bari naje wajensu.
Da baffa da k'asimu ne a tsaye suna magana yayinda Audu da ibro suke girbin.
Cikin fara'a suka tareshi suna tambayarsa Ya makarantar.
Labari ya basu gaba daya sannan ya ciro Wayar ya nuna musu.
Cikin farin ciki Audu ya amsa yace
Tab Kai ka fara wannan Yar dangwalen kaf Garin Sarina.
Shima cire Riga yayi Ya duk'a suka Cigaba tare
Indoce zaune da faranti a gabanta
Abu ta k'araso ita da harira
Abu tace
Naji ance yayanki ya dawo Ko
D'agowa tayi ta kalleta tace
Wlh ban saniba Kinga tun dazu Na baro gidan ban koma ba
To shikenan inaji k'aryane
Abu ta gaya Tana k'ok'arin mik'ewa
Indo tace
Wai ke Abu baki hak'ura da yaya umar ba kiga dukan da sani Ya miki
Juyowa tayi tace
Tab Ko kasheni zaiyi bazan so magaji ba.
To Allah ya taimaka
Ameen
Indo na dawowa ta sami farouk na wanke takalmi
Da sauri ta k'araso Tana dariya tace
Yaya harka dawo.
D'aga mata Kai yayi yace
Eh kin tafi talla Ko?
Daga masa Kai itama tayi
Murmushi yayi yace
Da kyau,Kin had'u da sani ko?
Girgiza Kai tayi
Shigowarsu Inna Mari yasashi yin shiru.
Da fara'a suka k'araso suna fad'in
Barka da yan makaranta.
Murmushi kawai yake yi be ce komai ba.
í ½í³‘farouk Ko haidar í ½í³‘
Written by
Deeja one love
Dedicated to madina m umar í ¼í¼¹
Wayyo 'yan Zaria zasu cinye ni Wai Nace garinsu babu kyau to ai nima 'Yar nan ne.
Yanzu dai sai kuyi hakuri bazan kuma ba
Umar farouk hauwa'u da Aisha salisu ku Janye Allah Ya isanku kunji Zaria tafi Abuja kyau lols
0⃣5⃣
Gaishesu yayi kafin ya basu labarin abinda Ya faru.
Sunyi farinciki sosai da sosai
Salim yasha addu'a har mamaki Ya dinga yi
Yau dai Cikin farin ciki ya tashi Dan jiya Sunyi Waya da Salim Akan sun sami accommodation
sannan kuma lectures zai Fara nan da sati biyu.
Kowa Ya fahimci yana Cikin farin ciki sosai
Tafiya suke tareda Audu zasuje wajen
Da suka Saba zama
Magaji ne da sani suka tsayar dasu
Magaji ya nuna farouk yace
Kai baka jin Magana Ko?
Nace maka ka rabu da Abu kak'i Ko to Wlh ni ba sa'an wasanka bane bar ganin kana zuwa
makaranta Cikin birni dukan ban mamaki zan maka.
Murmushi farouk yayi yace
Kaje ka tambayi Abun Idan na tab'a cewa ina sonta da kazo kana wannan haukar.
Audu yace
Haba magaji Meye Hakane na tareshi kana wai'nnan magan ganun
Shiru yayi Shidai bai kuma cewa komai ba
Ganin abin na neman Ya zaman musu fad'a yasashi Janye audun domin su tafi
Masifa audun yaketa yi
Shidai be kulashi har suka isa wajen
Zama sukayi sannan Audu ya harareshi yace
Ka wani tsaya miskilanci Kamar Wani d'an sarki
Murmushi yayi ya juya ya Kalli gefe
Tsaki Audu yaja yace
Wannan shegen miskilancin naka