Showing 6001 words to 9000 words out of 72611 words
Chapter 3 - farouk Ko haidar complete by one love.pdf
na Kusa rabuwa dashi ai
Kallonshi yayi da sauri yace
Ka gaji danine?
Halinka na gaji dashi
Audu ya bashi amsa
Shiru dai yayi be kuma cewa komai ba
Tab'e baki yayi yace
Ai bazaka Dena ba
To sai nayita zuba surutu babu ma'ana
Dariya Audu yayi yace
Oh surutun da muke shine Mara ma'ana?
Be ce komai ba sai ma wayarshi daya ciro yana dannawa.
Me Hali be fasa halinshi
Still bece masa komai ba
Bayan sun Gama cin abinci farouk yace
Baffa zamu Fara lectures nan da sati biyu
Baffa yace
To ikon Allah yanzu ya za'ayi?
Sauke Kai k'asa yayi yace
Eh nan da kwana goma zan tafi Dan naje na shirya.
To Allah ya kaimu
Farouk ya amsa da
Ameen
Indoce tsaye Tana shanya ya shigo gidan
Amsa sallamar da yayi tayi
Kusa da ita ya tsaya yace
Kina nan kina wanki kin manta da karatu Ko
Sunkuyadda Kai tayi tace
a'a innace ta sani
Tab'e baki yayi yace
Ki mini alfarma d'aya mana
Wasa take da yatsun hannunta
Kinga gobe zan tafi makaranta inaso pls kada ki tsaya da kowanne saurayi
Kallonshi tayi tace
To inasha Allah bazan tsaya da Kowa ba
A sanyaye yace
Har sani fa
D'aga Kai tayi Alamar Eh
Murmushi yayi yace
Gud gal
Washegari da wuri Ya shirya domin tafiya
Kaf gidan Kowa Allah Ya tsare yake masa
Audu da suke tafiya Don su fita titi ya kalleshi yace
Daba Dan kun had'a uba da Indo ba da sai nace Ko ita zaka aura
Murmushi yayi yace
Nidai kawai ka tabbatar da bata saurari Kowa a Garin nan ba
Jinjina Kai yayi yace
OK Babu Matsala
Har Sai da ya sami mota kafin Audu ya koma.
*** **** *** *** ***
Kamal ya Kalli haidar yace
Yanzu duk makarantu kaduna ka rasa makarantar da zaka tafi sai Zaria
Kallonshi haidar yayi yace
Nima haka kawai Naji can nakeso na tafi kuma ai makaranta ce me kyau.
Kamal yace
Hakane
Yanzu dai zo Muje kaci abinci and kada ka manta gobe kazo da wuri Ka kaini.
OK ba matsala
Washegari da wuri suka shirya suka tafi
Farouk na sauka a fly over Ya Kira Salim yazo Ya d'aukeshi
Gidansu Salim d'in suka Fara zuwa
Sai da suka kwana d'aya kafin su wuce
Kan su tafi daddy ya tarasu yace
To Sarkin rawar Kai bance kaje kana shiririta ba Dan zan sa masu duba mini me kukeyi a
makarantar banda shirme Karatu kawai ya kunayi
Sannan ku rike juna Salim ga d'an uwanka nan farouk
Kaima farouk ga Dan uwanka nan Salim ka fishi nutsuwa Dan Allah Idan yayi Abu ba daidai ba
ka tsawatar masa
Sunkuyadda Kai yayi yace
Insha Allah daddy
Tashi kuje Allah Ya muku albarka Ya baku abinda kukaje nema.
Ameen suka amsa duka
Daddy da kallo.ya bisu Tabbas yaron Yanada nutsuwa sosai kuma Yanada saurin shiga rai
Da yamma suka shiga makarantar
Gyara dakin sukayi kafin suyi alwala su tafi sallah
Suna fitowa Salim ya Kalli farouk yace
Yunwa fa nakeji
Daidai lokacin da motorsu haidar tayi parking
Kamal yace
Wazamu tambayane kaga waincan d'in sun juya sun tafi
Ka ajiyeni kawai ka tafi kaga olredy dare yayi
Suna zaune suna cin abinci Wayar farouk tayi k'ara
Kallon Salim yayi yace
Ina zuwa
Waje ya fita domin amsa Wayar
Yana dagawa Audu yace
Farouk kanajina
Eh
Ya amsa
Dama Indo ce tace na kira ka
Bata Wayar yayi
Cikin sauri tace
Yaya kana makarantar yanzu
Eh
Ya bata amsa
Haidar ne ya karaso kusada Salim yace
Pls ina so na tambayeka admin block ne
Jin muryarsa yasa shi saurin d'agowa
Dariya yayi yace
Haba farouk me zakaje yi admin block
Cikin Rashin fahimta haidar yace
Bangane ba nifa tambayarka nazo yi kuma kanaso ka gaya mini wata magana daban
Salim yace
Kai farouk Meye Hakane Wai?
Kai ba sunana farouk ba haidar nake inaji ka sami Matsalar kwakwalwa ne
Wucewa yayi Ya barshi da mamaki.
Farouk ne ya k'araso yace
Ka Gama mu wuce
Cikin mamaki yace
Kai dakata Yanzunan Wani me Kamada Kai Ya barnan
Dariya farouk yayi yace
Me Kamada ni kuma
Cikin maamaki yace
Dama kana dariya?
Kai kabar shirme Dan Allah zo Muje kawai
Cikin sauri yace
Wlh da gaske nake Dan da farko na d'auka kaine ma
To sauke
Farouk ya bashi amsa
Duka ya Kai mishi daga nan suka Cigaba da harkarsu
Yau Dai suka Fara daukar lectures
A gajiye suka dawo
Kwanciya Salim yayi shi kuma farouk daukar bokiti yayi Ya nufi tap Dan d'ibar ruwan wanka
Har ya dawo yana nan yarda ya barshi
Tsaki yaja yace
Mtsew dallah tashi banza kalallab'a kawai
Dariya Salim yayi yace
Wlh buddy bakasan me ba
Ji nake Kamar na gudu
Be ce masa komai ba har ya Gama shiryawa
Hot plate ya jona Ya d'ora musu abinci
Har ya Gama Salim be tashi ba
Zubawa yayi Yace
Ka tashi muci abinci
Mikewa yayi Ya sauko
Dauke abincin farouk yayi yace
Wlh baka isaba kaje Ka wanke hannu
Yana mita ya mik'e Ya wanko hannun yazo Ya saka hannu suka Ci abincin
Salim dai shi kad'ai yake firarsa.
í ½í³‘farouk Ko haidar í ½í³‘
Written by deeja one love
Dedicated to madina m umar í ¼í¼¹
Kuyi hakuri na manta masu kananan Waya number din bazai fito ba amma yanzu na gyara
Sannan ba lallai na dinga muku posting sau biyu ba amma Idan ya samu zan iya muku
Na gode
06
Haidar ne ya fito daga library hannunsa dauke da littafi.
Gefensa Hafiz ne (room mate dinsa)
Wata shegiyar motace taho a rough driving
Cikin sauri Salim da yazo shiga Cikin library yayi saurin Kautar da haidar d'in
Cikin ikon Allah motar tayi gefe
Parking tayi can gefe
Kusan minti uku kafin a bud'e motor a fito
Irin crazy din nan ne sunsha swag
Duka Tsayawa kallonsu sukayi
Kallon up and down yayi musu kafin ya shafi lips dinsa yayi hanyar school cateen
A Fili haidar yace ja tsaki kafin ya juyo Ya Kalli Salim yace
Na gode sosai
Nunashi yayi yace
Kamar na Sanka Ko?
Murmushi Salim yayi yace
Admin block
Dariya haidar yayi yace
Hakane Ashe kanada hankali dai
Harara Salim ya balla masa yace
Da me ka maidani?
Dariya haidar ya kuma yace
To Naji yanzu ina abokinka me Kama Dani.
Sosa Kai Salim yayi yace
Yana d'aki yana barci
Oh I see
Haidar ya gaya
Juyawa yayi Ya kalli Hafiz yace
Ka tuna Wanda nake baka labari akanshi to ka ganshi nan
Dariya Hafiz yayi yace
Ai na tabbatar
To yanzu Bamu number dinka so that sai muna gaisawa
Dariya suka yi duka kafin suyi exchanging numbers
Salim yace
Am sure zaka yarda da maganata one day
Tame fa
Haidar ya tambaya
Ta cewa kuna kama da Dan uwana
Oh Ya fara kenan
Ya gaya Yana jan hannun Hafiz Ya Cigaba da cewa
Salim let's call it a day
Murmushi yayi
Farouk ne ya k'araso yace
Kai buddy ina kaje ne
Dariya yayi yace
A ina ka ganni ne?
D'aga Kai yayi Ya ce
Oh ka Fara hankali gaskiya zan gayawa daddy
Dariya Salim yayi yace
Yanzu muka rabu da. Me Kamada Kai
Murmushi farouk yayi yace
Ka Fara ko
Allah da gaske nake har muryarku iri d'aya sai dai shi yafika fara'a da surutu
Murmushi kawai farouk yayi yace
Muje mu shirya kasan munada lecture
Suna tafe suna fira
Ajiyar zuciya ta sauke sannan tacewa driver
Mu tafi.
A gajiye suka dawo Dan haka farouk wanka kawai yayi Ya kwanta
Salim ya kalleshi yace
Kai buddy ka tashi ka d'ora mana abinci Wlh am hungry
Juyawa yayi yace
Kai ma ai ka iya
Dariya Salim yayi yace
Tab shiririta ma kenan
Farouk na jinsa yayi banza dashi.
Ganin bazai tashi bane ya sashi mik'ewa Ya fito domin siyan Wani Abin da zai ci
Haidar yayi dariya bayan Salim ya bashi labarin yunwa ta fito dashi daga daki
To mu karasa nima ita nakeji
Dariya sukayi gaba daya kafin Salim yace
Kasan Dan uwana akwai kafiya ne
Tunda be so ba bazai Dafa ba
Karar Wayarsa ta katse shi
Ganin me kiran yasa yayi saurin dagawa
To gani nan zuwa kawai ya fad'a
Kallon haidar yayi yace
Ba kana tunanin shirme nake gaya maka akan kuna Kama da Dan uwana ba
To kazo Muje yanzu ka ganshi
Dariya haidar yayi yace
Wannan Dan uwan naka din jinsa yafi ganinsa
Dariya Salim yayi yace
Muje daga nan kaci girkinsa
Kallon d'akin yayi yace
Tab gaskiya ya tsaftatu sai kace da Mace
Dariya kawai Salim yayi
Wayarsa ya ciro Ya Kira farouk
Yana dagawa yace
Bro ina ka shiga ne gamu tareda haidar
Naje submitting assignment ne amma bazan dade ba zan dawo
Farouk ya bashi amsa
Salim yaceda haidar
to Kaji Ya tafi cafe
Daga kafada yayi Alamar babu damuwa
Yace
Yanzu dai zubo mana girkinsa muci
Dariya Salim yayi yace
Wlh da Dad'i
Haidar yace
To Nace babu dad'i ne kawai ka bari bakina zai tantance
Zuba musu abincin yayi suka Fara ci
Haidar dai harda santi
Bayan sun gama yace
To ni zan wuce Dan zanje library yanzu Idan ya dawo ka gaishe dashi.
To zaiji
Rakashi yayi kafin ya dawo ya kwanta
Sallama farouk yayi Ya shigo
Tsaki yaja ganinshi a Kwance yace
Ni Wlh na gode wa daddy da be fitar da Kai kasar Waje Karatu ba
Dariya Salim yayi yace
Eh naji babu komai haidar na gaisheka
Kallo farouk ya bishi dashi kafin yace
Wa kaje ka jajibo mana ne?
Kanaso ka ce mini ka manta da Wanda na ce maka kuna Kama ne.
Tsaki ya kuma ja ya d'auki bokiti ya fita
*** *** *** *** ***
Wani
Makeken gida motor ta shiga
Wata da bazata wuce 32yrs bace ta fito daga motar
Cikin sauri take tafiyar tanayi Tana hadawa da gudu
Falon ta fad'a Ko sallama babu
Bata kula da yaranta dake mata sannu ba
Upstairs kawai ta nufa
Wani hadadden bedroom ta shiga.
Jakarta da mayafi ta jefar Akan gado
Zagaye d'akin ta Fara Cikin sauri
Tace
Bazai yiwu ba
Da sauri ta janyo wayarta ta Danna kira
Ana d'agawa tace
Aunty mun shiga uku sirrinmu dake boye shekara goma sha ashirin ya kusa Ya bayyana
Daga can barin tace
Meya faru?
Yau naga d'aya daga Cikin 'Ya 'yan yaya idris
A gigice tace
Me?
Karyane Wlh bayan boka yace sun mutu ki dai sake bincikawa .
Huci tayi tace
Wlh Ko zanyi yawo tsirara bazan Bari su bayyana ba
Ni ina nan shekara goma sha shida na kasa Haifar yara .
To bazai yiwu kisan yadda zakiyi dashi
Ajiyar zuciya tayi tace
Bakisan Meye tashin hankalin ba
Tareda Salim d'an wajen kareema na ganshi
What ya akayi suka had'u
Wlh ban saniba na dai gansu kawai
Ki san yadda zakiyi ki rabasu ke Idan ta Kama kiyi sanadiyar barinshi makarantar
To.
í ½í³‘farouk Ko haidar í ½í³‘
Story and written by
By deeja
One love
Dedicated to madina m umar í ¼í¼¹
07
Haidar Kalli Salim yace
Wai wannan Dan uwan naka Anya akwaishi kuwa duk lokacin da zan zo baya nan
Harara Salim ya galla mishi yace
Ai koda nake Da surutu nasan me nake fad'a
Dariya haidar yayi yace
Am sorry Kaji friendy yanzu dai zuba mana abinci muci.
Salim yace
Sai dai na zuba maka Dan Ranar nan da mukaci tareda Kai daya zo sai da yayi magana
Murmushi haidar yayi yace
Daga ji MA zai yi kishi
Dariya suka yi gaba d'aya
Abincin ya zuba masa yaci
Yana gamawa yaceda Salim
Kalli zan tafi sbd inada lectures Karfe biyu sai gobe
OK to jirani na raka ka mana
Tare suka jero har Waje
Sai da ya kaishi har bakin room dinsu kafin ya juyo
A bakin kofa Ya taradda farouk
Harararshi yayi yace
Kai Wlh kanada matsala yanzu kuma daga ina Kake
Kallonshi kawai farouk yayi yace
Daga ina Kake?
Dariya Salim yayi yace
Daga library daddy
Murmushi farouk yayi yace
Ai Nike taking responsibility dinshi Anan
D'aga gira d'aya Salim yayi yace
Da gaske?
Kana tambaya ne
Ni Muje Dan Allah
Shiryawa sukayi suka tafi lecture
Sai hudu suka dawo
Tana office dinta Tana nazari Ya shigo Ciki
Babu batun sallama kujera yaja ya zauna
Cikin shagwaba yace
Mummy Don Allah account Dina yayi low kuma daddy tun jiya yace zai mini transfer har yanzu
shiru
Tura masa Jakarta tayi
Yasan me take nufi hakan yasa ya zura hannu ya Debi yadda yakeso ya tashi ya Fita
Clash sukayi da farouk da Salim.
Har ya wuce Ya dawo ya tsaya
Nuna Salim yayi da hannu yace
Kai zo nan
A hankali Salim ya Fara tafiya
Ganin da gaske zuwan zai yi yasa farouk saurin janyoshi baya
Me Kake nufi ne ?
Ko kallonshi be yiba yaja hannun Salim Don su wuce
Tare hanyar yayi yace
Kai bada Kai nake magana ba
Kallon rainin wayo yayi masa yace
Kwakwalwarka bata ja ne ina nufin bazai zo ba.
Zaro idanu yayi yace
Kai kasan koni waye?kasan waye babana?
Kasan waye mamana a makarantar nan.
Kallon Salim yayi a zafafe yace
Kai zo nan
Da sauri yaceda farouk
Bro yi hakuri ka bari naje
Farouk be ce komai ba ganin hakan yasa ya taka yaje har gabansa
Kallonshi yayi sama da k'asa yace
Daure mini igiyar takalmi na
Tsugunawa yayi Ya daure masa
Runtse idanu farouk yayi
Salim ya dago ya kalleshi yace
Na Gama
Lips d'in sa ya shafa yace
Jeka ka dauko min wayata a office din mummyna
A sanyaye ya juya ya tafi
Har ya Kai bakin kofa Ya D'aga murya yace
Sorry boy Gata a jikina
Salim ya Kalli farouk
Watsar da takardun hannunshi yayi Ya juya ya bar wajen da sauri
Dariya yayi yace
Gud boy ina ka samo wannan shi kuma
Faisal wannan abokina ne duk wulakancinka Ya tsaya kaina Kada ka kuskura kaje kanshi.
Salim ya bashi amsa sannan ya tsugunna yafara tattara takardun da farouk ya zubar
Take d'aya Faisal yayi yace
Me kace shin abokinka yafi Dan uwanka ne?
Mikewa Salim yayi yace
Baka San Wani abokin yafi Wani Dan uwanba ballantana a yanda nakejin farouk yafi mini Kai
sau dubu
Tureshi yayi sannan ya tsugunna Ya d'auki paper d'in ya tafiyarshi
A hanya suka had'u da haidar
Dariya yayi yace
Mutumina sai ina
Dan karamin tsaki ya ja kafin yace
Zanje wajen Dan uwanane
Muje to
Duk inda suke tunanin zasu ganshi babu shi
Hankalin Salim ya tashi sosai da sosai
Haidar ya kalleshi yace
Ka kwantar da hankalinka bazai bace ba
Kallonshi yayi
Idanu Sunyi ja yace
Ranshi abace yake kuma be iya fushi ba
Zama sukayi Akan Wani dakali haidar yace
To amma na d'auka bakuyin fad'a ai
Shiru yayi for some seconds
Sannan yace
Bani na bata masa rai ba
To waye?
Haidar ya tambaya
Labari Salim ya bashi
Murmushi Haidar yayi yace
To yanzu dai ka sake kiran wayarshi
Kira yayi no answer
Haidar yace
Kawo number din na kira da