Showing 48001 words to 51000 words out of 72611 words

Chapter 17 - farouk Ko haidar complete by one love.pdf

Advertisement

One Love   

23 Mar 2025

5813

mugunta tayi tace
Kai mama shiyasa nakeji da ke wallahi yanzu dai komai yana tafiya yadda ya kamata
Jinjina kai yafindo karima tayi tace
Komai yana tafiya dai dai saidai kudi yayi kasa
Hajiya salma tace
Indai kudine kada ki damu zan turo miki
Cikin farinciki tace
To nagode 'yata
Sai bayan awa biyu wani likitan ya fito
Da sauri suka bishi
Tsayar dasu yayi yace
Kuyi hakuri ina zuwa amma za'a kara masa jini leda biyu Dan haka idan kunada Wanda zai
bada sai Ku kirashi idan kuma babu sai dai asiya.
Salim cikin sauri yace
Nawa 0± ne zan iya bashi muje kawai adeba
Likitan yace
To kaje lab za'ayi gwaje gwaje sannan sai a diba amma duk da haka ya kamata a nemo wani
domin a debi left dayan
Salim yace
Likita babu lokaci muje a debi biyun kawai
Baffa yace
A'a salim leda biyu yayi yawa ka bari a nemo wani kada hakan ya shafi lafiyarka
Salim yace

Baffa pls ka bari a deba ni be dameniba indai shi zai tashi shikenan
Baffa yace
Haba salim ya za'ayi abata biyu daya bata gyaruba
Salim cikin lallami yace
Leda biyu bazai bani matsala ba
Baffa yace
Duk da haka dai
Ajiyar zuciya salim yayi yace
Okay
Lab yaje inda aka gwada jinin
Kallonshi yayi yace
Leda biyu zaka diba
Amsawa yayi
Sai da ya Dan kwanta for some minutes sannan tashi
Sai da suka tace sannan suka sa mishi
Likitan yace dasu baffa
Ku kwantar da hankalinku an shawo kan Matsalar stress Ya tarawa kanshi sannan gaskiya Idan
zan gaya muku ita to ciwonshi ba na asibiti bane ya kamata ku dinga hada mishi dana
musulunci
Jinjina Kai baffa yayi yace
Insha Allah
Daddy hamma da ammar ne suka shigo hankali a tashe
Sai da likitan ya kwantar musu da hankali sannan ya gaya musu yadda ya gayawa su Salim.
Shiru daddy hamma yayi yana tunani
Ammar a zuciyarshi yace
Mum Anya babu hannunki a Matsalar nan kuwa?
Haidar kuwa Yana farkawa yayi wanka sannan ya fito a zaune ya tarar da Mamie Tana karatun
Al Qur'ni
Kusada ita ya zauna  yace
Mamie ina wayata
Dan Jim tayi tace
Me zakayi da ita?
Zan kira Nawan ne.
Ya bata amsa
Mamie ta numfasa tace
Haidar  daddynka dazu yake amsa
Turo baki yayi yace
To Ara mini taki
A takaice tace
Na Barta a office
Zuba mata idanu yayi
Zai yi magana ta katse shi ta hanyar cewa
Jeka kaci abinci

Shiru yayi
D'agowa tayi tace
Ba magana nake maka ba
Jiki a sanyaye ya Mike ya hau dinning
Washegari da safe Mamie tace
Shirya muje unguwa
D'aga Kai kawai yayi domin tun jiya har yau be dawo dai dai ba
Wanka yayi kawai ya shirya ya fito
Ganin harda daddy abin ya bashi mamaki Amma beyi magana ba
Yaya adnan shi yake driving sai daddy da mamie da haidar suna baya
Ganin sun dauki hanyar kano yasa gabanshi faduwa
Cikin sauri ya kalli mamie batace masa komai ba
Suna isa suka hadu dasu daddyn baby
Tare suka shiga asibitin
Sun tarar da mai martaba shima yazo
Momma ta karasa kusa dashi
Idan ba numfashi dayake ba sai kace gawa ce
Fashewa da kuka tayi
Daddyn baby ya riketa yace
Amma kin mini alkawarin bazaki yi kuka ba ko?
Girgiza kai tayi tace
Ji halin dayake ciki
Ajiyar zuciya mai martaba yayi yace
Yanzu wane hali yake ciki
Daddy hamma yace
Likitan yace
At any time zai iya farkawa
Shiru dakin yayi
Salim ne ya turo kofa ya shigo
Kallon daddy hamma yayi yace
Daddy likita nasan ganinka
Har ya mike sai kuma ya koma ya zauna ya kalli baffa yace
Kaje kai
Murmushi baffa yayi yace
Babu komai kaje kai
Tashi yayi ya tafi
Bayan ya dawo yace
Likitan yace
Akwai wani babban doctor da zai zo daga India ranar laraba zai duba shi amma suna sa ran ko
zuwa anjima ya farfado
Shiru dai har zuwa yamma
Daddy ya kalli mamie yace
Tashi mu wuce kada dare yayi

Kallonshi mamie tayi tace
To
Haidar hade rai yayi
Murmushi daddy yayi yace
Dama bazance kazo muje ba ai ka wani hade rai
Sai da ya bawa kowa dariya
Washegari da safe da salim da haidar suka tafi sarina
Sun hado komai sannan suka taho da inna Mari da inna hadiza sai indo
Audu kuwa sai gobe idan baffa ya koma
Suna zuwa suka tarar da mai martaba sunzo domin gidan sarkin kano suka je da safe
Anan suka zauna har zuwa yamma babu wani labari
Washegari laraba suka likitan yazo
Bayan ya gama bincikensa yace
A gaskiya kwakwalwarsa lafiya lau take haka gangar jikinsa
Bashuda internal injuries haka ma external to mai yahanashi farkawa?
Mai martaba yace
Inajin zamu wuce dashi can adamawa  idan har abin. Yaci tura
Likitan yace
Eh to amma bazaku sami wani bayani sama da wannan ba
Girgiza kai kawai mai martaba yayi
Bayan bakon likitan ya tafi
Suka zauna sukayi shiru
Daddy hamma yace
Mai martaba kozan tafi dashi can India ko Allah zai sa adace
Girgiza kai mai martaba yayi yace
Kada ka damu za ayi masa na musulunci anan
Washegari daddy hamma da ammar suka koma India
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION


❄We beare's of soo golden a pen,We writer's assiduously percieven No pain,so Magical Our
creative golden pen,Be hold our worlds,A product of our pen savour Our worlds for it will cause
u no pain

farouk ko haidar

         Written by deeja one love�

Dedicated to madina m umar

44-45

Mai martaba kuma sai washe gari,Da safe Abba da mama suka iso kowa yaga halin da ya ke
ciki sai ya tausaya masa Humaira kuwa kullum batada aiki sai na kuka
Su salim kuwa saida daddy ya tsaya ya nuna musu bacin ranshi sosai sannan suka koma wajen
service dinsu Amma fa koda yaushe hankalinsu na kanshi Kwananshi goma sha biyar daddy
yace Akwai wani malami abokonshi a kaduna mai zai hana  a koma dashi can Haidar yaji dadin
hakan sosai da sosai Yau suka gama services dinsu kowa na murna amma su nasu da sauki
Salim kuwa a ranar suka tafi kaduna shida haidar
Akan nanda two weeks zasu dawo domin graduation.
Saukar hajiya salma daga flight ta Kira mai martaba aka tura mata dogarai da driver suka
daukota
Fada ta fara wucewa tayi gaisuwa sannan ta shiga wajen fulani
Bayan sun gaisa fulani tace Sai kukaji abu Mara dadi Hajiya salma ta marairaice fuska tace
Uhum wallahi abu babu dadin ji kwata kwata allah ya kyauta gaba
Fulani tace
Ameen dai
Haka ma data shiga wajen yafindo hari
Itama sai da tayi Mata jaje
Sannan ta karasa wajen uwar gijiyarta
Da murna ta karasa
Rungume juna sukayi cikin farin ciki
Bayan tayi wanka taci abinci ta kwanta barci sai bayan la'asar ta farka
Hajiya salma ta kalli yafindo karima tace
Wai mama ya akayi hakane?
Yafindo karima tayi dariyar mugunta tace
Zo ki Gani
Bedroom suka shiga
Wata karamar tukunyar kasa ta bude tasa hannu ta ciro wani abu kamar kwallo kuma
transparent
Da mamaki hajiya salma tace
Wannan menene?
Yafindo karima tace
Wannan shine rayuwar farouk matukar tana cikin nan to bazai taba Tashi ba
Dariya hajiya salma tayi tace
Kai mama malam ne ya baki ko kuwa?
Yafindo karima tace
Wane malam wani na sake
Tafawa sukayi da hajiya salma tace
Kice mama wannan gama aikine
Yafindo karima tace
Kamar kinsani yar uwa amma fa da sharadi
Hajiya salma tace

Meye sharadin?
Yafindo karima tace
Zaki kai kanki wajensa ma'ana zaki bashi kanki()
Murmushi tayi tace
Babu matsala allah ya kaimu gobe
Ai ni indai bukata zata biya to ko meye zan aikata
Jira nake agama da wannan ma sai mu koma kan wancan idan yaso daga baya naji da ubansu
shi fa atunanunshi son yaranshi nakeyi
Dariya suka Kara shekewa dashi  suka tafa kamar wasu kawaye(allah ka sa mufi karfin
zuciyarmu ameen)
Washegari suka tafi wajen malam din
Babu laifi yanada tsafta watakila ko dan yana cikin garine oho
Yafindo karima a waje ta tsaya ita kuma ta shiga ciki
Wajen awa uku sannan ta fito a hargitse
Da mamaki yafindo karima ta kalleta
Cikin matukar galabaita tace
Mama muje gida kawai
Tun a hanya  tafara barci Dan haka suna komawa ta kwanta bata farka ba sai bayan magrib.
Tana cin abinci tace da yafindo karima
Gobe zan je Zaria daga nan zan shiga kano a matsayin zan duba wancan Dan iskan yaron.
Dariya yafindo karima tayi tace
Hmm aike kam naga kinfi tsanarshi ne da sauri tace eh mana.
Firarsu suka cigaba.
Washegari da wuri ta shirya ta tafi
Amra kuwa sai murna take yau mamanta zatazo
Yaya muhammad ya kalleta ya tabe baki sai daf da isha tazo
Amra ta shirya komai sai murna take kamar me
Sun sha fira sosai sannan ya muhammad ya dauketa ya kaita wajen mama kasancewar basuda
nisa da juna
Acan ta kwana
Washegari Abba yace dama suma sunaso su koma Dan haka su mama suma suka shirya
Suna isa kano asibitin murtala suka wuce Domin can akayi transfer dinshi
Gaskiya duk Wanda yaga halin dayake ciki sai ya tausaya mishi
Domin idan ka ganshi zakace barci yakeyi sai dai fa rama dayayi.
Cikin tausayawa mama tace
Allah ya yaye maka
Hajiya salma tace
Ameen.
Suna zaune su salim suka shigo
Da kallo mama ta bisu su kansu duka sun rame kadama salim yaji labari Dan shi dama bai iya
sa abu araiba.
Gaishe dasu sukayi sannan mama ta Kara musu nasiha akan su Kara hakuri cuta ba mutuwa
bace

Haidar yayi ajiyar zuciya yace
Nanda next week ma zamu wuce adamawa ai
Ok allah ya kaimu but dan allah Ku Kara hakuri kunji Allah zai bashi lafiya
Jinjina kai sukayi
Haidar ya kaisu sarina domin sure gaisa da sure baffa
Hajiya salma dai ruwa batasha agarin ba ta tattara ta tafi
Ita kuma mama sai da akayi magrib sannan suka tafi.
Haidar kuwa a sarina zai kwana tunda yanzu shifting sukeyi idan haidar ya kwana yau gobe
salim jibi audu
Sai dai wajen juyashi da goge masa jiki shine sai da safe idan wani yazo acikin su sai su hadu
su biyu suyi.

Bayan sati daya mai martaba ya zo aka shirya aka maida su adamawa
Koda aka maidashi adamawa abubuwa sunyi sauki tunda yanzu sukan hadu suyi jinyarshi da
yawa
Faisal kam tuni ya fara aiki amma su haidar mai martaba babu fadan da be musu ba amma
sunce su bazasuyi aiki ba tareda farouk ba
Bayan an kwana biyu ya sake tarasu ya Nuna musu yanzu sun girma fa ya kamata susan da
hakan
Duk yadda ya bullo musu abu ya gagara karshe harya fusata yace
Kamar baku yarda da kaddara ba yanzu kuma idan mutuwa yayi fa ?
Kuka salim ya fara mishi yana fadin bazai mutu ba
Haidar kam tabe fuska yayi
Ganin abin Nasu da gaske sukeyi yasa ya tattara ya zuba musu idanu
Sun je aiken da mai martaba yayi musu sun dawo
Haidar ya ajiye maganin akan bedside table ya shiga wanka
Salim kuma ya kwanta
Kamar a mafarki yaga idanun farouk na neman budewa
Cikin farinciki ya fara kwalawa haidar Kira
Ba shiri haidar ya daura towel ya fito.
farouk ko haidar




https://www.facebook.com/groups/156937
*FAROUK KO HAIDAR*


*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~❄we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our
creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u
np pain~*

written� By Deeja One Love

Written by deeja one love�


Dedicated to madina m umar

46-47
A hankali ya bude idanunshi
Maidawa yayi ya lumshe idanun domin haske yayi mishi yawa
Da sauri salim ya tafi sanar da su mai martaba.
Cikin farin ciki suka taho
Kowa so yake yayi mishi magana amma abu ya gagara domin koya bude baki da nufin yin
magana sai abu ya gagara
Hamdala mai martaba yayi yace
Da alamu sauki ya fara samuwa
Kan lokaci kankani har labari ya bazu a family haidar ya bude idanu.
Kowa murna yakeyi domin sauki ya fara zuwa
Momma kuwa tanaji har hawayen farin ciki sai da tayi
Daddyn baby ya na ta tsokanarta
Murmushi tayi tace
Ni dai idan allah ya kaimu gobe zamuje ko?
Kallonta yayi yace
Da wannan cikin naki zakije a'a gaskiya sai kin haihu
Shiru tayi bata kuma cewa komai ba
Daddare tana zaune Tana tsefewa baby kai.
Mararta taji ta murda Mata cikin dabara ta zame kan baby ta mike
A bedroom ta sami daddy yana aiki da laptop
Kallonta yayi Cikin kulawa yace
Ya dai ko da matsala ne?
Girgiza kai tayi
Kan ta yunkura juwa ta kwasheta
Da sauri daddy ya tarota
Daukarta yayi cak ya nufi parking lot da ita.
Koda suka isa hospital da sauri aka amsheta
50mins ta haifo yaranta guda biyu duka Mata
Bakin daddyn baby ya kasa rufuwa
Sai buga waya yakeyi

Salim na zaune yana Danna waya kiran daddyn baby ya shigo
Kallon haidar yayi dayaketa shakar barcinshi
Daga wayar yayi
Cikin farin ciki yace
Mamanku ta haihu
Ihun murna salim yayi.
Cikin sauri salim ya bude ido yana mazurai
Kallon salim yayi ya dalla mishi harara
Yace
Kai dai wallahi akwai banza Muna barci kawani tasheni
Kafin salim yace wani abu an bude kofar an shigo
Yafindo hari
Cikin sauri salim ya rungumeta
Da haidar da farouk zuba musu idanu
Da mamaki salim yace
Wai mai ya faru ne?
Salim ya washe baki yace
Momma ta haihu
Da gudu haidar yazo ya rungume salim
Murna kam ba'a magana
Farouk kuwa da idanu yake binsu.
Ga abin murna amma babu dama
Murmushi yayi
Haidar yace
Lah! Ji nawan yana murmushi
Ranar dai Kwanan farin ciki familyn sukayi
Washe gari da wuri yafindo karima da yafindo hari suka tafi taraba
Ana sallamota daga hospital suka wuce da ita adamawa.
Suna isowa suka sami gida ya cika da yan uwa
Kowa na kokarin daukar yaran
Hannun haidar ta rike tace
Ina dan uwanka
Murmushi daddyn baby yayi yace
Muje ki huta sai kije anjima mana
Daga kai tayi badan ranta yaso ba
Bangaren fulani ya kaita
Ruwa mai sadi tayi wanka dashi
Kafin ta fito an ajiye mata tuwon dawa da miyar kubewa yaji man shanu
Sai da taci ta koshi sannan ta kwanta
Daddyn baby da yafindo hari suka shigo da babies a hannunsu
Ajiyesu sukayi
Yafindo hari ta juya ta fita
Kallon daddyn tace

In taso muje ka kaini wajen farouk din?
Murmushi yayi yace
Ina zuwa
Bai dade ba suka dawo tareda fulani
Yace
Fulani ga yaran nan zamuje ta dubo farouk
Fulani tace
Kekam ki bari ki huta mana
Daddyn baby yace
Fulani Barta muje kawai idan ba haka ba yau bazata barni na huta ba
Murmushi fulani tayi tace
Adawo lafiya
Har bangaren mazan ya kaita
Salim yana kwance yana barci
Haidar kuma yana wanka
Da idanu ta bishi yayi haske sai dai ya rame
Murmushi yayi Mata
Hannunshi ta rike tace
Ya jikin
Lumshe idanu yayi ya bude
Haidar daya fito daga bayi yace
Momma har kinzo ganin jikinshi
Daga kai tayi alamar eh
Ya Dora da cewa
Ai ma ya sami sauki
Kallon salim yayi ya daka.mishi duka yace
Tashi kallallaba
Harararshi farouk yayi ya kauda kai
Momma tayi dariya tace
Ah lallai jiki da sauki tunda an iya harara
Duka sukayi Dariya
Yafindo karima ta kira hajiya salma tace
Kinji rumaisa ta haihu
Hmm naji mana jiya.mijinta ya kira hamma ya gaya mishi.
Ta gaya cikin takaici
Yafindo karima tace
To yaushe zakuzo
Nisawa tayi tace
Sai ranar laraba
Allah ya kaimu dole idan kinzo mu koma wajen malam din nan
Ana Jibi suna su ammar da mutanen kano sukazo
Yan zaria da yan kaduna suma sunzo
Gida ya cika masha Allah

Ammar ya kalli amra yace
Ki bari anjima idan aka tafi sallar magrib sai mu duba
Jinjina kai tayi alamar to
Da yamma yafindo karima tace
Bari zuwa anjima mu karasa shi
Su kuma yaran gobe idan an gama taron suna
Murmushi hajiya salma tayi tace
Ai gwara ayi ta ta Kare kawai
Ana kiran sallah kowa yana haramar shiga masallaci
Amra ta Kira ammar tace
Bro yafindo karima ta shiga toilet kayi sauri
Yana ajiye wayar cikin sauri ya kalli faisal yace
Ka tanaji ashana kazo wajen garden
Da sauri yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login