Showing 18001 words to 21000 words out of 72611 words
Chapter 7 - farouk Ko haidar complete by one love.pdf
zufar fuskarshi yayi a hankali
Wani mutum ne daure da sarkoki a jikin wata bishiya me feshin wuta
Wasu irin halittu ne zagaye dashi suna azabtar dashi
Akodayaushe baya ganin fuskar mutumin Wani haske ke zuwa ya Rufe masa idanu
Amma a yau Allah Ya taimakeshi Ya gani fuskar farouk ce
Kusa dashi ya Matsa ya taba shi
Jikin sa Wani irin zafi yayi Kamar garwashi
Arude Ya Fara tashin Salim
Da sauri Salim yace
Meke faruwa
Kuka haidar ya keyi yace
Salim farouk mutuwa zaiyi
Cikin sauri Salim yakai hannu jikin sa
Ba Shiri Ya Janye domin kuwa zafin yayi yawa
Bude kofa yayi Ya shiga kwankwasawa su Audu kofa
Abinda Ya bashi mamaki Shine
Bugawa daya Audu ya bud'e yace
Farouk Ko dama na zaci haka Jeka Bari na kira baffa
Salim komawa dakin yayi yayinda Audu ya tafi taso baffa
Shima dai baffan barcin beyi nisa ba Dan yasan hakan zata faru
Tareda su Inna Mari ya taho
Ruwa a cikin bokiti k'arami aka zubo
Da tsaftataccen tsumma
Inna hadiza ke jikawa Tana shafa masa
A hankali zafin jikin Ya Fara raguwa
Maganin da ta bayar aka siyo mishi tunkan Ya tafi Inna Mari ta dauko aka bashi ya sha
Baffa ya Kalli su haidar yace
To sai da safe ko
Amsawa sukayi jiki a sanyaye
Kowa da abinda yake tunani har gari Ya waye
Alhmdllh lafiyar Allah Ya tashi babu ko ciwon Kai
Sai dai haidar daya tashi da ciwon idanu
Inna hadiza tace
Oh ni dije Daga wannan sai wannan
Su uku suka tafi wudil suka siyo masa magani
Yadai yi sauki
Ganin sun damu yasa yace
Kada ku damu dama nakanyi lokaci zuwa lokaci
Ana gobe zasu tafi
Da yamma suna zaune suna fira Indo tazo wucewa
Hango su da tayi yasa Jikinta har Bari yakeyi tazo ta wuce
Farouk yayi murmushi yace
Ina zuwa
Da sauri Ya bita har ta Kusa zuwa gida
Humaira
Cak ta tsaya
Juyowa tayi
Idanunta har ya kawo ruwa tace
Wlh ban tsaya da Kowa ba yau
Murmushi yayi yace
Ba wannan na tambayeki ba gobe zamu tafi fa
Ajiyar zuciya tayi tace
Allah Ya kaimu
Tare suka karasa gidan
Wanka Ya shiga yayinda ita kuma ta shige dakin Inna Mari
Washegari suka d'auki hanyar babban birnin ilimi Garin autan sambo balaraben sarki
Garin zazzau ci Garin Hausa
Bayan su Inna Mari sun cikasu tsarabar K'auye irinsu kuka da kubewa da dadda.......
Farouk Ko haidar
Nidai Nace farouk
Maryam khamis (one love) tace
Wai haidar
To readers let see wayafi mutane
Idan kana bayana kace ni Idan kuma kana bayan haidar wato My one love ka D'aga hannu.
í ½í³‘farouk Ko haidar í ½í³‘
Written by deeja one love
Dedicated to madina m umar í ¼í¼¹
Yeah munfita mutane Wlh í ½í¸
14
Sun tarar dasu duk suna gida
Kwanciya Salim yayi yana fadin
Wayyo Allah na gaji
Dariya haidar yayi yace
Wlh Kai kacika San jiki
Harara farouk ya galla mishi Ya shige bayi
Salim yace
Kai Wlh ka kiyayeni fa
Hararshi yayi yace
Anki a kiyaya d'in yi Abin da zakayi
Yana fitowa daga wanka Ya shirya
Kallonsu yayi Ya ce
Ku tashi kuyi alwala mana
Sai da sukayi sallah sannan suka Ci abinci
Alhmdllh idanun haidar d'in ya Washe sosai
Da yamma
Haidar na zaune kusada mama
Salim kuma ya kwanta a kujera
Kan shi na Saman kafar farouk
Shi kuma farouk d'in yana danna Waya
Yaya muhammad da yaya Mubarak ne sukayi sallama suka shigo
Cikin matukar farin ciki yaya Muhammad yace
Lallai kace iyayen rigima sun iso gidan.
Salim ya dago ya kalleshi yace
Yaya waye masu rigimar?
Kai da farouk mana
Kallon juna sukayi shida haidar suka kama dariya
Da mamaki yaya Muhammad d'in ya bisu da kallo
Kallon Mubarak yayi yace
Yaya kaga wasu identical twins?
Kallonsu duka yayi yace
Tab Kamar tayi yawa
Salim yayi dariya yace
Yaya bafa yan biyu bane hasali ma d'aya na Kano d'aya na kaduna.
Cikin mamaki suka dinga kallonsu.
Mubarak yace
Ni Wlh akwai Wanda suke mini Kama ma dasu
Mama tace
Nima haka na ke gani
Tashi Salim yayi Ya matsa kusada yaya Mubarak yace
Yaya Ashe ka dawo ina tsarabata
Hararshi yayi yace
Wato tsaraba ita ta dameka Ko to Tana wajen mama.
Da dare suna gama cin abinci Salim yace
Mama har yanzu fa baki bani ba
Yusra tace
Me za'a baka?
Ina ruwanki ne
Ya bata amsa
Mama ta Kalli husna tace
Jeki ki dauko mini jaka Akan besides cabinet
Tafiya tayi
Mama tace
Amma ai nan da bikin yayanku zaku dawo Ko
Cikin farin ciki Salim yace
Ansa ne?
Eh mana nanda three months
Yaya Muhammad yace
Ai gwara yayi Ya wuce nima sai nayi
Dariya sukayi gaba d'aya
Yusra mu kuma sai a had'a namu da naka Ko yaya Salim
Tabe fuska yayi Cikin shagwaba yace
Mama Wai kinji ai ban isa aure ba ko
Dariya suka kuma yi
Haidar yace
Kai Wlh akwai katon banza
Hararshi farouk yayi bece komai ba ya Cigaba da Danna wayarshi
Dariya Salim yayi yace
Kai Wlh ka kasa gane nine na gaban goshin farouk indai kayi mini ba daidai ba sai Ya harareka
Husna data dawo daga Aiken mama ta Mika mata jakar
Haidar yace
Ni ai hakan be dameni ba
Murmushi mama tayi tace
To ai kuwa ka Dena nuna musu Haka Dan su masu tuya da ruwa ballantana sun sami Mai
Abba yace
Nidai zan so naga aurenku
Kallonshi Salim yayi yace
Abba yanzu Kai sai kayi mini aure
Abba yace
Irinka mashirmanciya zan nema na had'aku
Dariya suka kuma yi
Mama ta mik'awa Salim jakar hannunta tace
Gashi
Amsa yayi
Laptop ne apple product sai turarruka da agogo
Haidar ya dauke agogon yace
Wannan Nawane
Tab malam ka isa sai dai ka d'auki laptop d'in Ko turare amma ni agogon nake so
Da sauri farouk yasa earphone a kunnenshi
Ja inja suka Fara wannan na cewa be so wannan ma haka
Su kuwa duk zuba musu idanu suka yi
Ganin abun bazai kareba yasa
Yaya Muhammad yace
Abinda za'a yi shine
Farouk ya dau laptop Kai haidar ka d'auki agogo Salim kuma tunda kaine k'arami ka d'auki
turare
Zunboro baki yayi yace
Dama Kai ai tun ba yau ba nasan Dan adawatane
Yaya Mubarak yace
To Kai haidar ka Bar mishi agogon ka d'auki laptop d'in
Mak'e kafada yayi Alamar a'a
Mama tayi dariya tace
Tab ikon Allah gaskiya farouk na Kokari
Ganin Abin bazai k'are bane yasa farouk cire headphones d'in yace
Dalla kun damu mutane
Wlh mama ki kwace duka Ki hanasu
Salim yace
To ai Ma ni Ya kamata ya barwa tunda nine k'arami
Kallon haidar farouk yayi yace
Kaga ka bashi kawai ka dau turare ko laptop d'in
Had'e rai yayi Ya ajiye yace
Dama nasan shi kafi so ai kuma bayanshi zaka goya banaso duka ma
Girgiza Kai yayi Ya d'auki agogon Ya Matsa Kusa da shi yace
To amsa ka rike
Kin Karba yayi ajiye masa Kusa dashi yayi.
Wajen Salim ya koma yace
Kai ka hada duka dakin laptop din da turaren
Hararshi yayi yace
Sai da ka fifitashi akaina sannan zaka Wani ce na had'a duka biyun to banso ma duka
Ikon Allah
Har suna hada baki wajen fadin hakan
Farouk kuwa kallonsu duka yayi Wai nan Sunyi zuciya
Ajiyar zuciya yayi
Kafin ya d'auki wayarshi Ya bar wajen
Mama ta janyo haidar Jikinta tace
Haba yarona Meye haka Wai
Ka amshi agogon mana
Murmushi yayi yace
To mama
Kallon Salim tayi tace
Kai kuma zo ka dau Wani Abin Anan
Bayan sai da kika rarrasheshi sannan zaki kula Dani
Abba yace
Ni ina ganin maslaha kawai d'aya daga Cikin ku ta dau wannan d'in anjima sai biyu suje su siyo
suma
Salim ya harari haidar yace
Sai ka rike wannan d'in
Shima hararshi yayi yace
Sai dai Kai ka rike
Wata husumar ce ta tashi
Da yaya Muhammad da husna kuwa me zasuyi banda dariya
Abba kuwa k'ok'arin shi d'aya daga Cikin su ya d'auka
Ganin Abin nasu da iskanci
Yasa yaya Mubarak ya daka musu tsawa yace
Dalla malamai Wani ya d'auka Ko na gaggaura muku Mari
Abin kuma sai Ya koma duka Kowa Na k'ok'arin d'auka
Shi kanshi wannan karan yaya Mubarak din sai da yayi dariya
Mama tace
Amma wallahi Allah Ya shiryeku.
Yaya Muhammad yace Kowa Ya dauki Abu daya gobe sai Ya siyo Cikon biyun sannan aka sami
maslaha
Karshe ma dai farouk suka barwa agogon
Dariya husna tayi tace
Mama gwara da yan autanki basu Nan da abin yayi miki yawa
Dariya yaya Mubarak yayi yace
Tab aiko da suna nan sai dai su su hakura
Ko kuma wa'innan katon banza su Dena ba
Yusra tace
Ji Kamar ba yanzu suka Gama fada ba amma har sun Cigaba da firarsu
Farouk ne ya fito daga daki
Kallon Salim yayi yace
Kai inaka sa mini wannan book d'in
Yana Cikin Jakata
Hararshi yayi yace
Kamar Wani karatun yakeyi
Da ido Ya nuna mishi abba
Dariya haidar yayi yace
Mutumina kaga yadda kayi kuwa Kamar Akuya a gaban kura
Dariya sukayi gaba d'aya
Harararsu farouk yayi yace
Dalla ku tashi Muje mu kwanta.
Washegari ma wajen siyayyar haka suka dinga rigima
Yaya Muhammad ganin zasu bata mishi lokaci yasa shi daukar musu da kanshi
Ana gobe zasu koma makaranta
Haidar ne Kwance jikin mama yana barci
Salim da farouk suka shigo gidan
Salim ya daka mishi duka yace
Dagata
Tsaki haidar yaja yace
Allah Ya isa Wlh
Dariya Salim yayi yace
To na fasa gaya maka abin da nayi niya
Mama ta Mike tace
Allah Ya shiryeku wallahi.
Shidai farouk d'aki Ya tafi ya barsu a wajen
í ½í³‘farouk Ko haidar í ½í³‘
Written by deeja one love
Dedicated to madina m umar
15
Suna shiga makaranta suka Fara Dagewa da karatu domin next semester suka shiga
Yanzu har Salim da haidar sun rage shirmensu sai dai lokaci zuwa lokaci
Yau Cikin matukar gajiya
Haidar ya shigo
D'akinsu
Farouk yace
Yadai
Kwantawa yayi a Gadon Salim yace
Na gaji since jiya nake library Yanzun ma wanka zanyi naci abinci sai na tafi ina da lectures
Murmushi farouk yayi yace
Kafa rame kwana biyu
Gefen fuskarshi ya shafa yace
Wlh ji nake Kamar na gudu.
Dariya Salim yayi yace
Rago kawai
Da mamaki suka kalleshi
Wai yau Salim ne ke cewa Wani Rago
Ikon Allah
Jan plate din haidar yayi yace
Yaro banda lokacinka yanzu
Shaf shaf yaci abincin ya wuce block dinsu
Sai four sannan suka tafi
Library
Karatu ne can ma sukayi
Sai six suka fito
Direct school cateen suka nufa
Cake da coke suka siya
Suna zama
Salim ya Kalli farouk yace
Wlh karatu da wuya Dan bakaji idona ba .
Murmushi kawai farouk yayi.
Suna Cikin ci haidar ya karaso zama yayi sannan ya ciro Wayar shi
Yace
Meyasa ka kashe wayarka mama ta kira tanaso tayi magana da Kai
Farouk yace
Wlh nama mantane ban bude ta ba yau gaba d'aya
Tace ma ta Kira ta Salim shima no answer Wai Lafiya Nace Wlh karatu ne ya samu gaba
Haidar ya fada Yana mikowa farouk d'in wayarshi
Bayan sun gaisa tace
Dama Maganar kayan daurin auren yayanku ne za'aje siyowa to shine nakeso Naji
measurements dinku
Murmushi yayi yace
Ai duk kawai Kai d'aya zai yi mana
OK to takalmi fa sannan waincan yan rigimar Kalar agogon da suka fi so
Murmushi ya kuma yi sannan yace
Kada ki damu dasu Mama kawai kala d'aya zaki daukar mana
To shikenan ayi karatu Lafiya
Insha Allah.
Kashe Wayar yayi Ya Mike yace
Kuzo mu tafi.
Yau dai zasu wuce kaduna Su dubo mamie datayi Rashin Lafiya kwana biyu.
Haidar yace
Dan Allah ku Bari sai next week kafin nan na Gama mu tafi tare
Make kafada Salim yayi yace
Tab mun shirya ka tsayar damu
Next zuwa kaje
Farouk ya Dafashi yace
Ka bari nanda next month zamuyi Hutu fa
Sai Muje duka. Kwana daya nefa gobe zamu dawo
To shikenan sai kun dawo.
Har bus stop sai da ya kaisu sannan ya dawo .
*** **** ****
Zaune take Tana shan lemo da waya a hannun ta
Cikin nishadi take
Sallama tayi tace
Ya akayi Zainab kin sallameshi
Madam Zainab tace
Wlh yaya Salma nayi bincike bazai yiwu ba domin yayanshi babban lawyer ne babanshi kuma
babban likitane.
Share zufar dake fuskarta tayi Cikin Tsakanin bacin rai tace
Zainab ki san yadda zakiyi ya bar makarantar kafin muzo bikin su saifullahi.
Kashe Wayar tayi ta Mike tana safa da marwa Tabbas bata shirya barin daular datake ciki ita da
ya'yan ta ba.
Madam Zainab ta Kalli Faisal tace
Ka Nemo mini marasa ji na makarantar nan.
Bayan ya kawosu ta kallesu tace
Aikin zan baku Wani nakeso Kuyiwa dukan tsiya amatsayin fad'a kukayi
Zaro idanu sukayi dayan yace
Tab amma madam ina fatan baki manta Meye hukuncin Wanda aka Kama Sunyi fad'a a
makarantar nan ko
D'aga Kai tayi tace
Kada ku damu zan San yadda zanyi ku dawo
Kun yarda
Ta tambayesu
Eh
Suka bata amsa
Nuna musu hotonshi
Tace da Faisal
Wayarshi Ya Danno hoton
Kallonshi sukayi suka ce
Ai munsan wannan guy d'in
To shi
Angama sai balance dinmu
Kudi Faisal ya ciro Ya Mika musu yace
Ga dubu talatin nan Idan kun Gama aikin naku zan cika muku.
Cikin farin ciki suka amsa suka tafi
Farouk kuwa suna isa suka kirashi suka gaya mishi
Bayan sun Gama Wayar ya wuce cafe
daga can library ya wuce
Sai after eleven sannan ya tafi daki ya kwanta
Washegari kasancewar Sunada tutorial eight yasa da wuri Ya shirya
Kallon Hafiz yayi yace
Zo Muje school cateen na siya Wani Abin naci
Kiran farouk ne ya shigo wayanshi
Da sauri Ya D'aga yace
Yaya kun taho
Eh yanzu dai zamu taho yaya Adnan zai kawo mu
Cikin farin ciki yace to ni yanzu ma tutorial zan tafi
Adawo Lafiya
Allah yasa kuma haka
Hannunshi rike da cake Dayan kuma yoghurt.
Bangajeshi yayi Wanda yasa Abin hannunshi gaba d'aya ya zube
Shi kanshi sai da ya Kusa faduwa
Hafiz da sauri Ya tarboshi
D'agowa yayi Ya kalleshi yace
Haba kana gani ka bige ni ai ko hakuri ka bani
Hannu yasa ya bugeshi a kafada yace
Ko zaka Rama ne?
Cikin fushi haidar ya Kai mishi naushi
Suna daga gefe sukayi saurin tasowa suka rufeshi da duka
Dakyar sauran mutanen suka rabasu
Wasu suna basu Rashin gaskiya wasu kuma suna bawa haidar d'in
Jan hannun Hafiz yayi suka tafi
Ranshi a bace har suka Gama tutorial din
Suna dawowa ya kwanta Akan gado barci ya d'aukeshi
Cikin barci Hafiz yazo yana tashinshi
Bude idanu yayi yace
Ya akayi ne?
Hafiz Cikin kaduwa yace
Yanzu nagani a notice board Wai ana nemanku a admin block office din co-ordinator
Mik'ewa yayi yace
OK Bari nayi sallah naje
A can ya tararda wai'nda sukayi fadan
Tana hakimce Akan kujerarta ya sameta
Murmushin mugunta tayi tace
Amsa
Hannu yasa ya amshi takardar
Takardar expelling from school ce
Ta Dora da cewa
Makaranta ta sallameka saboda fadan da kukayi.
Murmushin gefen baki yayi yace
Well done Ya juya ya fita.
A daki ya sami Hafiz jiki a sanyaye ya tareshi yace Ya akayi ?
Murmushi yayi ya Mika masa takardar
Kallon shi yayi yace
Innalillahi yanzu ya zakayi.
Zan jira yaya Adnan Idan ya kawo su Nawan zanji me zaice.
Kiran farouk ne ya shigo wayanshi yana dagawa yace
Gamu a main get kazo ku gaisa da yaya Adnan
OK Ya amsa
Kallon Hafiz yayi yace
Kada ka damu gasu nan sun iso
Suna tsaye ya samesu
Yaya Adnan ya kalleshi yace
Babyn