Showing 36001 words to 39000 words out of 72611 words
Chapter 13 - farouk Ko haidar complete by one love.pdf
Duka suka fito Shidai ammar binsu kawai yakeyi
Suna fita takaddama ta tashi kan Wanda zaiyi driving
Dariya ammar yayi yace
To ku kawo ni nayi driving d'in
Shikenan ma
Budewa sukayi suka shiga.
Haidar ya dubi farouk yace Nawan shigo mana
Lumshe idanu yayi Ya juya ya bar wajen.
Da mamaki suka bishi da kallo
A sanyaye ammar yace
Kuje ku bashi hakuri Bari na fita
Kallonshi Salim yayi yace
Malam yi zamanka Bari na taho dashi.
Wajenshi Ya karasa
Yace
Wai Kai ka fasa fita ne
Eh
Atakaice Ya fada
Dan Had'e rai yayi yace
Kama isa wallahi sai kaje
A dake yace
Bazanje Idan wancan shi zai yi driving ba.
Salim yace
Wai Kai me Kake nufi ne Yafa baka hakuri Meye Hakane.?
Kallon Salim yayi yace
Amma ai haidar be Rama marinshi ba
Dan zaro idanu yayi yace
Kai Wai saboda wannan ne
Hannunshi yaja ya Cigaba da cewa
Muje malam.
Salim yace
Haidar yi driving d'in kawai
Salim da haidar suke gaba yayinda ammar da farouk ke baya.
Duk shirmen da suke be sa musu baki ba shi kuwa ammar dariya da mamaki suke bashi
Salim yace
Allah Kai ka cika San jiki
Dariya haidar yayi yace
Kaji Wai kura zatace da kare Maye Waya kaika San jiki.
Juyawa Salim ya yi yace
Wai bro Hakane
Ko kallon inda suke be yi ba.
Ammar yace
Ku kuna Abu Kamar yara.
Haidar yace
Ai har yanzu na sa mana pampers.
Ammar yace
Allah Ya baka hakuri
Dariya duka sukayi haidar ya Dora da cewa
Kai Wlh Salim akwai Rashin ji ga shiririta
Harara farouk ya galla mishi
Dan Kauda Kai haidar yayi yace
Nifa kana bani mamaki Idan kana Abu Kamar Mace
Salim ya zaro idanu yace
Ni nake Abu Kamar Mace
Of course yes
Bayan muna makaranta ni nake girki ka zauna ka ci
Har Tana farouk sai da yayi dariya
Ammar ya Kalleshi da mamaki
Cikin dariyar yace
Da kuwa bamuci abinci ba
Salim Cikin tsokana yace
Ko fa Lipton baka iya dafawa ba.
Had'e rai yayi yace
Waye Ya gaya maka haka?
Dan murmushi yayi yace
Mamie mana
Karya Kake kuma ai gwara ni
Ikon Allah kawai ammar yake kallo
Husuma ce ta tashi Kowa na ya iya girki
Farouk yace
Nidai kun dameni da hayaniya ya isa haka.
Da taimakon ammar da Salim suka zagaya Garin adamawa
Suna dawowa suka tarar dasu abba da daddyn baby a bakin get
Daddyn baby yace
Yan biyu Andawo
Gaisheshi sukayi sannan suka wuce
Karfe hudu filin gidan daya decorating Ya Fara cika da yan uwa wa'inda ke tayani daddy hamma
farin ciki ganin yaranshi.
Farouk da haidar shadda dark brown anyi walima me kayatarwa soyayya masu bakin Ciki nayi
masu farincikin nayi.
Washegari da wuri su baffa da daddy da abba suka tafi sai da akayi fama da farouk kan ya
yarda ya zauna
Akan nan da sati Mai zuwa zasu tafi. Farouk tun bayayiwa ammar magana har ya koma yana yi
masa.
Suna zaune suna hutawa ammar suka jero tare da Faisal.
Sai da sukayi musu sallama sannan suka zauna.
Faisal yace
Mummy na tace na gaya muku za'a Fara lectures Next Monday
D'aga Kai farouk yayi kawai
Salim ya Had'e fuska yace
Nidai sai nan da sati biyu zan koma
Kallon baka isaba farouk yayi mishi
Dan Tabe fuska haidar yayi yace
Ai bama a lectures sosai Idan an koma makaranta.
Dariya ya basu duka
Cikin dariya Faisal yace
Wai ma sai kace secondary school
Haidar yace
Da gaske nake
Harararshi Salim ya yi yace
Kalallab'a kawai
Zaro idanu farouk yayi
Ammar Cikin dariya yace
Tab Wai ai ni tsakaninku bansan Wanda yafi Wani son jiki ba
Haidar ya ce
Yafini mana bakaga yadda yakeyi bane
Salim yace
Ai kowa yasan banda son jiki kamarka
Farouk ya harari ammar yace
Kaga ka janyo yanzu zasu damu mutane ko
Shidai dariya kawai sukeyi dashi da Faisal su kuwa su Salim husumar su suka Cigaba
Kiran Wayar farouk ne ya sashi tashi ya bar wajen
Yana dagawa Cikin kuka
Tace
Yaya farouk bazaka dawo bako?
Lumshe idanu kawai yayi yanajin kukan Nata
Can Cikin makoshi yakira sunanta
Humairraaaa.
í ½í³‘farouk Ko haidar í ½í³‘
Written by deeja one love
Dedicated to madina m umar í ¼í¼¹
28
Sheshsheka ta ajiye Alamar zatayi kuka tace
Yaya to kaine kayi zamanka Gashi su umma ma sun dawo Kai kuma ka k'i dawowa
A hankali yace
Kinaso na dawo ne?
D'aga Kai tayi Kamar yana gabanta sannan tace
Eh
To ai zamu koma makaranta ne
Ya bata amsa
Kuka ta Fara yi Tana fadin
Nidai yaya kazo inaso na ganka
Ajiyar zuciya yayi yace
Zanzo Idan Allah Ya yarda
Murmushi tayi Wanda sai da yaji sautin shi
Cikin matukar farin ciki tace
Allah Ya kawo ka Lafiya
Murmushi shima yayi Ya amsa da Ameen
Yau Saura kwana biyu Su koma makaranta
Duk Wani shirye shirye an riga da an Gama
Da yamma farouk ne zaune suna fira da daddy hamma
Kallonshi yayi yana murmushi yace
Amma satinsu d'aya yau Da tafiya Ko me zakaje kayi
Dan marairaice fuska yayi yace
Daddy Wlh inaso naje akwai abinda zai kaini
To shikenan kaje anjima ka gayawa Mai martaba
Bayan sallar magrib Ya wuce turakar Mai martaba
A zaune Yana lazimi Ya sameshi
Da hannu yayi mishi nuni daya matso Kusa dashi.
A hankali ya Matsa ya tsugunna Kusa dashi
Sai da yagama sannan ya shafa kanshi yace
Farouk Ko haidar
Dariya yayi ya juya Kai yace
Farouk ne
Hannunshi Mai martaba ya rike yace
To gaya mini me ya faru
Sunkuyadda Kai yayi yace
Dama inaso gobe na tafi Kano ne
Su kuma su Salim su wuce Zaria Idan yaso Ranar lahadi na dawo
Kallonshi yayi na Wani lokaci yace
Hakan yayi maka
D'aga Kai yayi yace
Eh
To Jeka Allah Ya maka albarka
Washegari Salim na Kwance yana barci
haidar yana gefe yana kallon farouk na hada kaya
Haidar ya ce
Amma wannan wace Kalar tafiya ce Ko humaira ta murza kanbuntane?
Harara ya aika mishi yace
Bansaniba
A waje suka had'u da Faisal da ammar
Da mamaki suke tambayarsa
Lafiya Ya had'a Jaka
Haidar yace
Wai kano zai tafi
Faisal yace
Me zakaje yi
Dariya haidar yayi yace
Tadi
Ammar yace
To Muje mu rakaka
Sai da suka shiga bangaren duka matan Mai martaba
Fulani tace
Shi ina Salim d'in
Farouk yace
Yayi barci
Tace
To basai ku tasheshi ba
Farouk yace
Allah Fulani Idan yasan zan tafi cewa zaiyi sai Ya bini.
Dariya duka dakin sukayi
Yafindo Hari data shigo yanzu tace
Ai Salim sai Kai wallahi
Haidar yana dariya yace
Yafiye rigima ne
Farouk ya zuba masa idanu
Ahankali Ya dauki jakarshi yana fadin
Nidai ka kula dashi kawai
Dan Tsayawa haidar yayi Ya bata rai yace
To ni waye zai kula Dani
Juyowa yayi yace
Faisal mana
Dariya Faisal yayi Wanda ya kular da haidar
Duka ya Kai mishi
Shidai farouk gaba yayi
Haidar ya Kalli yafindo Hari yace
Kinji abinda Nawan yace ko shi yafi damuwa da Salim
Ammar yace
Kana kishi ne
Harararshi yayi yace
Bansaniba Kamar ansaka dakai
Fulani ta Janyoshi tace
Kyalesu Kaji
Salim ne yayi sallama ya shigo
Kallon Dakin yayi yace da haidar
Ina farouk
Ammar yace yanzu ya tafi Kano
Zubawa ammar idanu yayi yace
Ba gaskiya bane
Faisal yace Da gaske yaro
Kwabe fuska yayi Kamar me shirin kuka
Yafindo Hari ta Janyoshi tace
Kwana biyu zai yi Ya dawo.
Tun yana kumbure kumbure har ya sauko suka Cigaba da harkarsu.
Farouk kuwa Yana fita
Wani dogari ya k'araso yace
Ranka Ya dade Mai martaba ya bada umurnin mu kaika har Kano
Wata mota Benz ya bude mishi Ya shiga
Motoci sunkai goma suka tafi rakasu
Goma a Kano tayi musu
Suna fara shiga Garin aka Fara binsu domin ganin irin motocin
Dan murmushi yayi a zuciyarshi yace
Oh yan Garin nan ko sai yaushe zasu waye?
A daidai kofar gidansu motocin sukayi parking
Audu ne ya fito da sauri Dan labari Ya Riga da Ya iso.
Rungume juna sukayi suna farin ciki da ganin juna
Sai da ya Fara ajiye kayanshi a dakin su
Ya sallami wa'inda suka kawo shi sannan ya shiga Cikin gidan
Abin mamaki yau duk sasan Kowa kallonshi yakeyi
Hakama sa-sa na biyu
Da sallama ya shigo
Inna Mari na daka
Indo kuma na wanki
Cak ta tsaya domin batayi tsammanin zuwanshi ba
Sai da ya gaisar da Inna Sannan ya mik'e
Wajenta ya nufo
Sai da ya matso daf da ita yace
Gani nazo ya akayi kike nemana
Sunkuyaddakai tayi Tana wasa da yatsun hannunta
Hannun ya rike
Dayan kuma yasa ya dago fuskarta kallon juna suke ido Cikin ido
Sallamar Inna hadiza ya dakatar dasu
A hankali ya Janye Idanunshi ya Maida kan Inna hadiza
Gaisheta yayi Cikin farin ciki ta amsa
Kan ya juyo Indo har ta gudu Daga wajen Dan murmushi kawai yayi
Bokiti ya d'auka Ya shiga wanka
Yana fitowa Inna Mari ta tareshi da tuwon shinkafa hadadde
Sai da yaci sannan suka tafi wajen baffa
Ahanya farouk yace Da Audu
Har yanzu sani yana zuwa wajen humaira Ko?
Dariya Audu yayi yace
Haba dai farouk kada kace mini Kai matsoraci ne baffa ya hanashi zuwa Dan har iyayenshi ya
turo amma yaki karshe babanshi ya ji haushi ya aura mishi binta Yar gidan habu mahauci
Dan murmushi farouk yayi
Audu ya Dora da cewa
Da munajin haushi meyasa baffa ya hanata sani tunda alamu yanuna Tana sonshi sai kuma
daga baya muka fahimci Ashe danshi yayiwa mata
Kafe shi da idanu yayi
A sanyaye ya ce
Amma humaira taji haushi
Audu yace
Har kuka tayi
Shiru kuma yayi Wanda da alamu sai da yayi Maganar Kuma yayi dana saninta
Kallon farouk yayi sai dai be Ga Alamar canzawa agareshi ba
Hakan yasa ya Dan ji sanyi
A bangaren farouk kuwa Abin ya kona masa rai matuka Wanda ya daure ne kawai
Suna zuwa suka tarar baffan baya nan
Audu ya ce
Kaga mun manta yau alhamis kasuwar Darki yau takeci
Sai dare sannan baffa ya dawo da mamaki yace
Saukar yaushe?
Kuma ai munyi dakai bazaka dawo ba ko
Kanshi a k'asa yace
Baffa banaki bin umarninka bane humaira ce tace sai nazo
Ganin Kowa Ya zubo mata idanu yasata sunkuyadda Kai hawaye na zubo mata
Da sauri
Yasa hannu ya goge mata Hawayen yace
Meye kuma na kuka zo Muje na baki
Tsarabarki
Hannunta Ya rike suka tafi
Baffa yayi murmushi ya Cigaba da cin abincin sa
Wata Leda ya dauko ya miko mata yace
Sumayya tace na kawo miki
Wannan kuma husna da Yusra
Ga ta Salim wannan kuma tawa.
Ajiye duka nasu tayi ta bude tashi
Wata hadaddiyar Riga da wando ne Pakistan sai takalma guda biyu
Murmushi tayi tace
Na gode yaya
Nuna mata sauran yayi yace duba wa'innan mana
Ta Salim ta bude
Su chocolates ne da sweet da chewing gum
Hannu yasa ya miko mata ta sumayya
Dogunayen riguna ne guda hudu sai brezia da pants
Da sauri ta kalleshi ganin ita yake kallo yasa ta kara jin kunya
Dariya ya kunshe ya juyar da Kai
Da sauri ta Maida kasa bude nasu Yusra tayi
Ki bude mana
Dan girgiza Kai tayi
Matsowa yayi yace
Kina tsoron ki bud'e kiga abinda yafi wancan kunya ko
kasa cewa komai tayi
A hankali ya Kai hannu zai d'auka
Cikin sauri ta kwashe tayi Waje da gudu
Dariya ta bashi Wanda sai da ya durkusa
D'akin Inna Mari ta fada Tunawa da tayi zai iya biyota yasa ta fita
Can kuryar dakin Inna hadiza ta shige
Sannan ta bude
Takalma da veil sai kayan kwalliya.
Wata babbar Leda ta ciro
Juyawa tayi ganin bata gane Ko Meye ba yasa ta ajiye
Inna hadiza na zuwa Cikin farin ciki ta nuna mata.
Washegari kin Bari tayi su had'u dashi
Yana sane Dan haka ya kyaleta.
Acan adamawa kuwa ammar yayi musu rakiya har parking space ji yake Kamar kada su rabu
Haidar yace
Kada ka damu kaima fa gobe ne zaku tafi
Murmushi kawai yayi Ya D'aga musu hannu
Wayar Salim ce tayi kara
Ganin wake kiran yasa ya Had'e rai
Haidar yayi dariya yace
rigimamme
Harararshi yayi yace
Ina ruwanka
Wayar haidar yayi Kara
Shima kin dagawa yayi
Murmushi kawai farouk yayi yace
Rigimammu kawai
Faisal ya kira
Bayan sun gaisa yace
Ina Salim d'an bashi Mika masa yayi
Da farko Kamar bazai amsa ba sannan daga baya Ya amsa
Kamar yana gabanshi ya Tabe fuska yace
Shine kayi Wani tafiyarka
Dariya farouk yayi yace
Wai kai bakasan ka girma bane.
Noke kafada yayi yace
Ni mun bata
Murmushi kawai yayi yace
Humaira tace Tana so ta ganni.
Dariya Salim yayi yace
Kace tadi ka tafi
Farouk ya ce
Kanwartawa?
Haidar ya kwace Wayar yace
Wato ni baka nemana ko
Dan murmushi yayi yace
Kai ai jinin jikina ne koda yaushe kana tare Dani.
Dariya haidar yayi yace
Ka gaida umma da Audu kace na kira wayarshi akashe
Eh babu caji ne
Haka suka Cigaba da Wayarsu
Yana kashewa Wani Kira da bakuwar number ta shigo
Koda ya D'aga muryar Mai martaba yaji yana cewa
Haka akeyi aboki sai ka sauka tun jiya babu ko kira
Cikin jin kunya yace
Yi hakuri wallahi na manta ne
Nasiha Ya sake masa sannan sukayi sallama
Number din ammar ya kira
Bayan sun gaisa yace
Turo mini da number din daddy
OK yanzu zan turo maka
Kun tafi kun barni da kewa Ko?
Da sauri hajiya Salma ta kwace Wayar ta kashe Cikin D'aga murya tace
Wallahi ammar ka fita idona kanajina Idan ba haka ba zan Saba maka wawa kawai Meye
hadinka dasu ne?
Shidai Wayar kawai ya amsa ya mike Ya fita yana mamakin halin mahaifiyarshi.
Sai da ya Koma daki sannan ya sami damar tura masa da number din
Farouk yana ganin number din be bata lokaci ba ya kira
Bayan sun gaisa ya bashi hakuri Akan dalilin daya sa be Kira jiya ba
Bakomai ya su ummantaka?
Daddy Ya tambaya
Suna Lpy lau
To ka gaishesu da haka sukayi sallama
Daddyn baby ne tsugunne gaban sarki
Yace
Mai martaba Allah Ya huci zuciyarka amma Dan Allah kayi hakuri ka bari mu dauki yaran nan
wallahi rumaisa tayi nadama baka gani ba Kamar zata mutu
Cikin bacin rai Mai martaba yace ....
í ½í³„farouk ko haidarí ½í³„
Written by deeja one love
Dedicated to madina m umarí ¼í¼¹
29
Ta mutu mana wayayi asara?
Kaga tashi ka bani waje tunkan raina ya baci dakai ,mikewa yayi yace
Allah ya huci zuciyarka
Kiran rumaisa yayi ya gaya mata yadda akayi
Kuka ta fashe dashi tace
Yanzu haka zan zauna ni daya daddyn baby pls do sumting mana.
Sai dare sannan ya sake lallaba daddyn yola sukaje still babu wani canji karshe ma cewa yayi
kada su sake su sake zuwar masa da maganar rumaisa.
Jiki a sanyaye daddyn baby ya koma taraba
Kuka tayi yafi say nawa.
Da dare mama ta kirata
Kara bata hakuri yayi sannan tace
Ga farida ta dameni tun da safe wait ita wajen mommyn ta zata koma.
Yake rumaisa tayi tace
Kada ki damu zasu saba be
Hmm banga alamu ba kema ki sake tura daddyn baby wajen mai martaba mana.
Mama ta fada
Wallahi yaje amma yaki hakura na rasa ya zanyi
Rumaisa ta bata amsa
Haidar dake jikin mama ya tabe bani
Harara mama ta aika mishi sannan tace
To Allah ya kyauta kun koma asibitin ko?
A'a wlh amma may be zuwa Gobe
Farida ta mikawa wayar India suka cigaba