Showing 51001 words to 54000 words out of 72611 words

Chapter 18 - farouk Ko haidar complete by one love.pdf

Advertisement

One Love   

23 Mar 2025

5835


To
A bakin kofar ya tarar da amra
Kallonta yayi yace
Muje
Suna shiga suka fara bincike bincike
Kaf duk Indiana suke tunanin gani sun duba amma basu ganshi ba
Amra ta tsugunna kasan gado ta janyo wani akwati
Cikin sauri ta bude ta ciro kayan ciki
Da sauri suka fice
A garden suka Tarar da faisal zube kayan sukayi
Wannan karamar randar
Ammar ya daga
Yafindo karima ta fito daga bayi
Kallon gadon tayi
Zaro idanu tayi ta dafe kirji
Da sauri ta leka window
Ganin aika aikan da su ammar suke shirin yi yasa ta kwallara kara
Dai dai lokacin dasu mai Martaba suka dawo masallaci
Jin Kara yasa suka nufi garden
Suma dake cikin fada suka fito da gudu
A rikice yafindo karima ta zubo da gudu tana fadin kada ka fasa
Zaro idanu hajiya salma tayi itama tace
Ammar kada ka aikata
Su mai martaba kallonsu kawai sukeyi domin basu fahimci me ake nufi ba
Ammar ya kalli faisal yace
Action
Murmushi yayi ya banka musu wuta
Ammar ya bugata da kasa ta tarwatseee

*📑FAROUK KO HAIDAR* 📑


*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~💫💫💫*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~â„we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our
creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u
np pain~*

written� By Deeja One Love

Bashier sufyein ina gaisuwa sosai duk da kwana biyu naji shiru Allah ya kara hazaka yasa kafi
haka
Ameen
48-49
Gidan gaba daya yayi baki wani bakin hayaki ya fara fita daga cikin fasashshiyar tukunyar
Ihu yafindo karima tayi lokaci guda fuskarta ta koma baka.
Farouk kuwa ji yayi kamar an kwanceshi daga daurin da aka masa
Cikin sauri ya mike ya fito
Ganin harabar gidan babu kowa yasa shi nufar garden
Yana isa wajen yafindo karima tayi ihu ta shaki wuyan hajiya salma tana fadin
Sun lalata mana komai kinga abinda yaranki sukayi mana
Mun shiga uku zamu mutu
Na gaya miki zamu mutu.
Hajiya salma kuwa idanu yayi jajir domin ba karamar shaka tayi Mata ba
Cikin sauri su hajiya zainab suka kwaceta
Ihu ta kumayi ta fara fuzge fuzge
Duk wani kulle kulle da sukeyi sai da ta fada tanayi tana soshe soshe
'Ya'yanta kuwa kuka suka farayi
Mai martaba ya bawa doagarai umarnin da su kamata su kaita cikin turu.
Mai martaba ya dubi mutanen wajen yace
Kowa ya shigo ciki
Bayan kowa ya zauna daddyn yola yace
Salma munaso muji meke faruwa? ko kuma nace mai ya faru?
Kuka ta fashe dashi tace
Dan Allah Ku yafe mini wallahi nayi nadama
Daddyn yola ya daka Mata tsawa yace
Tambayarki fa akayi mai ya faru?
Hawaye ta share tace
A lokacin da mahaifinmu ya rasu muka dawo nan gidan tun lokacin nakeson hamma

Sai dai hankalinshi kwata kwata baya kaina yana kan yar uwata
Ganin hakan yasa na fara kishi da ita
Nayi bakin ciki lokacin da akayi bikina da abbansu ammar
Amma duk da haka ban saduda ba kuma ban Dena son hamma ba
Lokacin da akayi auren rumaisa da hamma naji bakin ciki sosai sai dai babu yadda zanyi
Ana haka watarana mama ta kirani a waya kan ta sami wani malami da zai mini aiki mun dade
muna ja in ja da ita kafin na amince
Farkon aikin daya fara mana shine kashe abbansu ammar
Domin babu yadda za'ayi na auri hamma ba tare da aurena ya mutu ba
Bayan malamin ya tura aljani ya kasheshi sai mukaji labarin rumaisa nada ciki ansha tura Mata
aljani ya sace cikin amma abu ya garara saboda yawan addu'arta
Da hakan bai samu ba sai muka sa aka kwance tayar motarta duk da haka muka bita abaya
nida mama har sai da muka ga konewar motar sannan muka juya muka koma wajen malamin
Aranar ya bani maganin da nasawa hamma har ya fara sona
Abin ya bamu mamaki da mukaji bata mutu ba
Alokacin mama tace mu koma a kasheta sai dai na nuna a'a
Hakadai har tayi convincing dina akan cewa idan fa ban kasheta ba to lallai har yanzu sunada
abinda ya hadasu wato 'ya'ya
Wannan yasa na yarda domin banason abinda zai hada hamma da rumaisa
Wannan yasa muka koma ya bamu magani akan mu sa Mata a abinci hakan zai Kara Mata
kiyayyar hamma kuma zai sa tayi duk abinda muka sata
Sai layar da muka binne Wanda hakan shine zai sa bazata taba cewa mu muka sata ta yar da
yaran nata ba
Haka kuwa akayi muka bawa zainab ta sa Mata a abinci ta kuma ci
Ni na Kira ta a waya tace da ita akan ta cewa halima zata taho
Babu musu tace to
A hanya mama ta tareta suka je kaduna suka fara bayarda haidar sannan suka wuce kano suka
bayar da farouk kuma mu muka tsara abin ya zama kamar hatsari ne.
Duk da haka bamu kyalesu ba mama ta kuma cewa mu koma wajen bokan a samusu ciwon da
zai dinga wahalar dasu
Haka muka koma wajenshi ya bamu amma da sharadin cewa duk ranar da asirin mu ya tonu to
daya daga cikin mu zai haukace
Haka muka yarda dan a tunanin mu asirinmu bazai taba tonuwa ba
Mun so a tura musu aljanune sai dai inda suke akwai kariya sosai wannan yasa hakan bai yiwu
ba
Duk da haka sai akayi amfani da yawan zuciyar farouk aljanun suke shafarshi shi kuma haidar
sai akayi amfani da yawan kallace kallacenshi aka turo wanda suke taba idanunshi
Ta kwashe sauran abinda ya faru ta gaya musu
Tsit wajen yayi
Sunkuyad da kai tayi tace
Dan Allah ina neman yafiyarku Ku yafe mini
Amra ta mike tace
Wallahi bazai taba yiwuwa ba kullum kina yaudarar mu akan mahaifinmu rasuwa yayi

Ashe kasheshi kikayi ashe ba sonmu kike ba
Daddyn yola yace
Ya isa haka amra koma ki zauna
Komawa tayi ta zauna tana Kuka
Kowa shiru yayi yana jiran hukuncin da mai martaba zai yanke
Gyaran murya yayi yace
Alhamdulillahi abubuwa sun faru da yawa a wannan familyn to mu godewa allah da hakan ya
faru domin idan har yana sonka ne sai ya jarabceka
Dan haka komai ya faru zamu dauka a matsayin jarabawa
Ni yanzu bazan yanke muku hukuncin komai ba sai dai zan barku da Allah shi yasan mai. Yafi
dacewa daku
Sannan magana ta karshe shine nidai allah ya gani koda Dan uwana ya mutu ya barku nayi dai
dai iya yanda zanyi Ku sami kyakkyawar tarbiya Allah kuma yana sheda
Don haka tunda hakan ya faru zaki koma bayan gida da zama sannan ki nemi yafiyar wa'inda
Kika yiwa laifi idan sun yafe miki shikenan
Ran da kika kashe shi kuma keda mahaliccinki.
Yana gama fadan hakan ya mike yayi cikin gida
Tashi tayi tana kuka ta dubi daddy hamma da rumaisa tace
Dan Allah Ku yafe mini
Ajiyar zuciya daddy hamma yayi yace
Allah ya yafe mana gaba daya
Ita ma momma abinda ta fada kenan
Su haidar da farouk ta duba tace
Nasan na cutar daku sosai na raba mahaifiyarku da mahaifinku na rabaku da juna na raba Ku
da lafiya amma duk da haka ina neman yafiyarku
Haidar yayi murmushi yace
Komai ya wuce mummy Allah ya yafe mana
Farouk yayi ajiyar zuciya yace..............
*📑FAROUK KO  HAIDAR* 📑

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~💫💫💫*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~â„we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our
creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u
np pain~*

Written�by deeja one love

Dedicated to madina m umar🌹
50-51

A sanyaye farouk yace
"Allah ya yafe mana gaba daya",kowa yaji dadin abinda ya fada.


Sai da aka kai ruwa rana sannan amra da ammar suka yafewa mahaifiyarsu.

Sai da suka koma bangarensu sannan salim yace
"Ashe farouk ya farfado".

Dariya haidar yayi yace
"Baka ganshi ba sai yanzu",Murmushi kawai yayi yace
"Kyaleshi haidar neman magana ne kawai kalar nashi".

Matsowa salim yayi yace
"Wai ya akayi ka Tashi ne?,Shiru farouk yayi.


A ranar cikin farin ciki suka kwana,sai dai da safe aka wayi gari da yafindo karima ta mutu,
Mutuwar da ta sa jikin mutane da yawa yayi sanyi.


Bayan anyi suna hassanar aka sa mata sunan inna Mari wato mariya suna ce Mata
islam,hussaina ita kuma taci sunan mamie wato khadeeja suna ce Mata iman.
Suna yayi yadda ake so sai dai muce Allah ya raya Islam da iman.


Bayan kwana biyu da suna kowa ya fara shirin tafiya ,
Haidar da salim sun tafi kasuwa domin siyayya,farouk kuma yana kwance.

Momma tayi sallama ta shigo kallonshi tayi tace
"Mai yasa bazaku zauna anan ba?

"Saboda can yafi dadin zama"
Ya bata amsa atakaice.

Shiru tayi na Dan lokaci kan tace
"Saboda me kace haka?".

"Saboda can babu hayaniya da yawa "
Ya Kara bata amsa .

Riko hannushi tayi tace

"To farouk mu tafi taraba tare mana"

Murmushi yayi yace
"Momma duk yadda zamuyi bazai yiwu ba saboda su baffa da daddy gani zasuyi kamar ke
muke so mu dawo wajenki;
Jinjina kai tayi alamar ta gamsu
Farouk ya Dora da cewa
"Kidai bari kawai mu dinga kawo miki ziyara amma bazai yiwu ace Dan mun hadu da iyayenmu
ba muce zamu juya musu baya".

Numfasawa tayi tace
You have a point.

Fira suka cigaba da yi har su haidar suka dawo ,
Nan suka dinga shirmensu ,
Farouk dai murmushi kawai yakeyi
Momma ta girgiza kai tace
"Ku wallahi bakwa girma har yanzu kuna abu kamar kananan yara"
Ta mike ta fita.


Washe gari da wuri suka dauki hanya,sai da suka ajiye su farouk a kano sannan suka wuce,ana
zuwa Zaria su salim suma suka wuce gida.


Bayan wata biyu daddy hamma ya fara Gina musu tafatsetsen hospital a cikin garin yola,
daddyn yola yaso ya sama musu aiki amma sukace su basa son na gwamnati abarsu da private
din da daddy ke gina musu.


Yanzu indo anzama yan Mata ta Kara wayewa sosai, Dan lokaci zuwa lokaci takanje Zaria ko
kaduna har taraba ma wajen momma,
Su Islam kuwa watansu uku amma sunyi Wayo sosai da sosai.


Shekara mai zuwa indo zata zana waec da neco hakan yasa farouk ya dage da koya Mata
abubuwan da bata Sani ba.


Farouk ya gama shirin shi na zuwa Zaria
Indo ta shigo dakin daga bakin kofa ta tsaya.
Hade rai tayi kallonta kawai yakeyi yana murmushi.

Hawaye ya gangaro daga idanunta still kallonta kawai yakeyi,ganin yaki cewa komai yasa ta
fara bubbuga kafa a kasa
Kusa da ita ya matso yace
"Humaira tsaya kiji".


Girgiza kai tayi ta turo baki gaba tace
"Nidai kawai yaya farouk kaje dani"


Ajiyar zuciya yayi yace
"To jeki shirya kayanki".


Tsallen murna tayi da sauri ta juya ta tafi,girgiza kai yayi yace
"Humaira rigima ".


Cikin lokaci kankani ta gama shirinta cikin tsokana yace
"Wai ni na rasa mai kike zuwa yi Zaria kodai kinyi saurayi acan ne?,
Rufe fuskarta tayi tana dariya.


Sai karfe biyu suka shiga zaria a gidan hajiya zainab suka fara yada zango,
Cikin murna faisal yace
"Ah lallai wannan Karon anyi abin kai "
Murmushi kawai farouk yayi .


Sai da suka ci abinci suka huta,sannan faisal ya kwashesu a mota suka tafi gidansu salim,
a bakin get ya ajiye su sannan ya wuce wajen aiki.


Suna shiga ya samu husna da yusra suna ta dambe akan hijab,
Sun cika gidan da hayaniya,
Yanayin sallama kowacce ta natsu.


Yace
"Ina mama?
Da sauri sukace
"Ta tafi kasuwa amma bazata dade ba zata dawo",

"Ina salim"
Ya Kara tambayarsu,
"Yana bangarensu"


Be ce komai ba ya mike ya tafi har ya wuce ya dawo yace
"Ku cigaba da damun mutane tunda Ku bakusan me yake muku ciwo ba"
Sunkuyad da kai sukayi
"Oya bani hijab din"
Da sauri yusra ta mika mishi,
Amsa yayi kawai ya wuce.


Yana tafiya husna ta bata rai tace
"Wannan fa yazo kenan wallahi"
Humaira tayi dariya tace
"Ko na kirashi ne?
Cikeda kuluwa yusra ta harareta tace
"Kirashin mana",
Cikin tsokana humaira ta fara kwala mishi Kira,
Husna ta dau filo ta bita dashi humaira ta haye sama tana dariya.


Farouk kuwa yana zuwa ya sami salim sai sharar barci yakeyi ,
Ajiye jakarshi yayi ya shiga bathroom yayi wanka ,
Sai da ya gama shiryawa sannan ya tasheshi.


Da mamaki salim yace

"Yaushe kazo?
Harararshi farouk yayi yace
"Taya zaka San nazo kato da kai kazo ka kwanta kana shakar barci".


Dariya salim yayi yace
"Wallahi nagaji ne "
Farouk yace
"Wai ka gaji to me kayi daka gaji?
Salim yace
"Kai dai bazaka gane bane kawai"

Girgiza kai farouk yayi yace
"Shiyasa ai kaji dadi da har yanzu ba'a fara aiki ba ko",
Dariya salim yayi kawai.


Da yamma mama ta dawo ta tarar dasu farouk
Da farin ciki tace
"Maraba da mutanen kano, ai dama tunda naji gidan shiru babu hayaniyar wa'inann marasa jin
nasan kazo"'
Murmushi kawai yayi.

Bayan sun gaisa ne tace
"Zakuje amsa kiran mai martaba ne?,daga kai kawai yayi.

Washe gari da wuri suka wuce kaduna,sun tarar da haidar yana hospital din su daddy.


Salim yayi dariya yace
"Kaga namiji jarumi",harara haidar ya galla mishi yace" kafa fita idona kallaba kawai",farouk ya
harari haidar ya kauda kai.


Indo kuwa sai murna take domin kuwa tareda su husna suka taho,tunda tazo ko farouk ma bata
nema ba,shima kuma haka be nemeta ba.


Da safe yaya adnan ya kwashe su sukaje gidan amare,bayan sun fito ne suka wuce companyn
motoci kowa ya zabi wadda yake so,da farouk da salim kala daya suka dauka baka range rover
sai haidar daya dauki camry new model 2008 ash in colour(ruwan toka).


Cikin farin ciki suka dawo gida,kowa ya tayasu murna,yaya adnan kuwa yasha
godiya,murmushi kawai yayi yace"komai nayi muku ban fadi ba kannena".


Daddy yana dawowa suka bashi labari shima ya tayasu murna sosai.

Washe gari suka wuce adamawa kowa da motarshi,farouk ya dauki indo,salim kuma surayya da
husna,haidar kuma sumayya da yusra.


Sun iso ana kiran sallar magrib wai a hakan ma sunyi sauri sosai(kun San dai yadda mutum
yake idan aka bashi sabon abu especially abinda ya shafi ride�).

Masallaci suka fara wucewa sai da sukayi sallah sannan suka shiga gidan,shidai farouk
bangarensu ya wuce,da haidar da salim kuma bangaren fulani suka wuce.


Sai da yayi wanka sannan yaje ya samesu,shirmen da suka saba shi suke tayi dai,fulani nayi
musu dariya.


Tsaki farouk yaja yace"wallahi kudai baku girma ,anan suka ci abinci sannan suka wuce
bangarensu,wajen wankan ma sai da suka Kara raba hali sanana sukayi.


Ana idar da isha suka biya suka gaida sarki,cikin farin ciki ya tare su har yana Jan su da wasa.

Washe gari da safe bayan sun karya,wani dogare yazo ya tsuguna yace"ranku ya dade mai
martaba na nemanku a falonshi"
Salim ya amsa da "kace muna zuwa"

Dogari yace"yace Ku taho da kannenku"
Salim ya kuma bashi amsa da to.

Sai da suka biya bangaren Mata na gidan suka dauki su sumayya sannan suka wuce,a zaune
suka sameshi bangarenshi na dama fulani bangaren hagu kuma yafindo hari,sai faisal da
ammar akasa,suma kasan suka nemi waje suka zauna.

Mai martaba yayi gyaran murya yace
Alhamdulillahi abinda yasa na kiraku shine kunsan dai cewa yanzu kune akan layi.

Haidar ya dago yace "layin me?,mai martaba yace"aure,dariya abin ya basu.

Da mamaki mai martaba yace"meye na dariya?ya isa haka kai ammar ga yar uwarka nan
yusra,farouk ga humaira nan,haidar ga surayya nan,faisal ga husna nan,salim kaida sumayya.
*📑FAROUK KO HAIDAR* 📑


*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~💫💫💫*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~â„we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our

creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u
np pain~*


written� By Deeja One Love


Bashier matafiya uku munji shiru fa ya kamata a duba mu. í ½í¹í ¼í¿»


52-53


Shiru sukayi domin basuda ta cewa,mai martaba yace"bakuce komai ba".


A sanyaye ammar"mun gode Allah ya saka da alkhairi.

Haidar zai yi magana faisal ya take masa kafa,dagowa yayi ya kalleshi shi kuma ya galla masa
harara.

Murmushi mai martaba yayi yace"masha Allah naji dadi Allah ya muku albarka,da sauri suka
Amsa da ameen.

Suna fita haidar yace"gaskiya banji dadi ba a rasa wacce za'a bani sai wacce muke sa'a,salim
dariya ya dinga yi,cikin jin haushi ya bishi da gudu,ganin ya taho shima yasa gudu.

Faisal yace"ai wallahi za'ayi kallon shirme,shidai farouk bece komai ba.

Mai martaba kuwa daddyn yola ya Kira yace ya kira members na family nanda three weeks
bikin su farouk,duk wanda aka Kira sai yayi murna idan yaji cewa tare da bikin bude asibitin za

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login