Showing 63001 words to 66000 words out of 72611 words
Chapter 22 - farouk Ko haidar complete by one love.pdf
worlds for it cause u
np pain~*
written By Deeja One Love
Dedicated to madeena m umar
Barka da gama littafinki namesy allah ya Kara hazaka da zakin hannu.
Jinjina gare Ku kungiyar golden pen writers allah ya Kara hade kanmu ameen.
60-61
Hall din ya cika sosai da sosai kasancewar biki ake na 'ya'yan gata.
Duk Inda ka duba mutane ne,cikin annashuwa da farin ciki.
Babu abinda yake tashi sai busa da tashin algaitu.
Motarsu a jere tayi parking...a hankali suke fitowa,ammar da yusra,faisal da husna,farouk da
humaira,haidar da surayya sannan salim da sumayya.
zagaye su akayi sannan suka fara shiga,kowanne rike da hannun amaryarshi,salim ya dubi
haidar ganin duka sun dauke kai abin ya bashi Dariya.
Cikin sauri ya janyo hannunshi ya hada da nata,harara haidar ya galla mishi Sannan ya juya ya
kalleta,ko kallonshi bata yi ba,hakan yasa yaja tsaki kasa-kasa.
Wajen zaman da aka tanada domin zaman suka je suka zauna.
Ana kiran Amare da angwaye su fito suyi rawa Wajen ya dau tafi,cikin nutsuwa kowa ya mike
tare da tashi matar,akan dandalin aka fara cashewa,shidai farouk kallon su kawai yake yi domin
be iya rawa ba.
Babu abinda kake gani a sama sai kudi,momma ta fito tayi bajinta sosai Dan sun sha ruwan
kudi.
Bayan kowa ya natsu aka fara ci da sha,daya ke serve yourself ne.
Can naga A'eeshat da marakisiyya ana dambe akan abinci,ikon allah.
Shamsiya kuwa hannu baka hannu kwarya,kamar yau ta fara cin abinci kodan wannan special
ne oho!.
Members na Hafsat hausa novels kuwa suna kan dandali suna cashewa,nace"Ku kuma nan
kuka fi auki.
Ina zagowa muka hadu da amatu ana ta Jan kaji,ba'aje daurin aure ba an iya zuwa dinner.
Hayaniya muka jiyo daga bakin hall,can suka fara shigowa,wa'innan ai members na hausa
novels by ask,tab Ku kuma sai da aka kusa gamawa kuka zo.
Dinner ta kayatar yadda ya kamata sosai,an ci ansha an deba an zuba a jaka(da namesy da
star boy umar ba).
Ana dawowa aka fara shirye-shiryen kai amarye,duka za'a fara ajiye su a adamawa kafin wani
lokaci sai kowa ya dauki Tashi matar.
Humaira kam kankame inna mari tayi da kyar aka Raba su,kuka take kamar zata shide.
Yan kai amarya suna kaisu suka juya,humaira duk tsoro ya kamata,bakin kids ta fito ta
tsaya,tana wajen motar shi ta shigo harabar gidan.
Farouk kuwa yana fitowa ya hango kamar duhun mutum,cikin natsuwa ya fara Tasia,sai da ya
matsa kusa da ita sannan ya game ta.
Hannunta ya rike kawai ya jata zuwa cikin gidan.
A falo ya zaunar da ita,shikuma ya shiga ciki.
Humaira dai sai zare idanu takeyi,Jim kadan ya fito sanye da wasu kayan daban which means
wanka ya sake.
Kitchen ya shiga komai a gyare yake tsaf-tsaf dashi,plate ya dauko sannan ya fito.
Kazar daya shigo da ita ya bude ya zuba a plate din,ita dai humaira da idanu take binshi.
Hannunta ya rike ya zaunar da ita,bece Mata komai ba ya fara bata a baki.
A sanyaye ta bude bakin ya fara bata,sai da taci ta koshi sannan shima yaci.
Suna gamawa yaja hannun ta ya kaita Dakin shi,kallonta yayi yace"ki shiga kiyi alwala kinji.
Sai da ta fara yin wanka sannan tayi alwalar,kayan jikinta ta maida,shiru yayi be ce Mata komai
ba.
Wardrobe ya bude ya dauko Mata wasu kayan,har kusa da ita ya karaso,hannunta ya rike yana
murzawa a hankali.
Da sauri ta dago suka hada idanu,kallon juna suke ido cikin ido,ⁿ
Sauke idanunta tayi a hankali ta karbi kayan.
Bathroom ta shiga sannan ta saka,farouk kuwa murmushi yayi kawai,shima kayan ya dauka ya
saka.
Humaira ta dade a cikin bayin tana kallon kanta a madubi,a zuciyar ta tace"wai yaya farouk
yana nufin a haka zan fita ko me?,sai ta murda kofar sai ta maida ta rufe.
Farouk kuwa ganin taki fitowa yasa shi biyota,yana bude kofar numfashin shi ya tsaya
cak,domin kayan yayi Mata kyau sosai.
Humaira kuwa runtse idanu tayi gaban ta na faruwa,da kyar ya tattaro ragowar jarumtar shi ya
karasa kusa da ita hannunta ya riko ya fito da ita waje.
Hijab da darduma ya miko Mata,kanta a sauke ta amsa.
Salloli raka'a biyu suka yi sannan ya kama kanta yayi Mata addu'a yana gamawa ya Mata
tambayoyi akan addinin ta,kusan duka ta amsa mishi.
Mikewa yayi yaje ya kwanta,da idanu humaira ta bishi.
Ganin bata taho ba yasa ya juya yana kallon ta,da ido ya Mata alama da lafiya,cuno baki tayi ta
fara mitsitsika idanu,hannu ya bude Mata alamar ta taho.
Noke kafada tayi,cikin sauri ya mike ya taho,gabanta ya fadi,hawaye ya zubo Mata.
Harshe yasa ya fara dauke hawayen,cikin sanyin murya yace"zo muje babu abinda zan miki.
Kallonshi tayi tace"promise?da ido ya bata amsa,hannunta ya rike sannan suka kwanta.
Kanta na kirjin shi,yayin da ta zagaye hannayenta har zuwa bayanshi,a hankali yake shafa
bayan ta har barci ya dauke ta.
Sam fa barci yaki zuwar wa farouk,kallon kawai yake yi,ganin abin ba mai karewa bane yasa ya
mike ya daura nafila.
Cikin dare humaira ta farka,jin babu alamun mutum yasa ta tsorata,zaune ta mike ta bare baki
zatayi kuka.
Farouk ya taso da sauri ya koma wajen ta,sai da ta koma ta kwanta yadda take sannan barcin
yazo.
Murmushi yayi wato ita tana barcin ta shi kuma barcin ya gagareshi,a haka yana tunane-tunane
har barci ya dauke shi.
Sai da yayi alwala da asuba sannan ya matsa kusa da ita,a hankali yake shafa fuskar ta.
Mika tayi sannan ta bude idanu,murmushi yayi yace"tashi kiyi sallah.
Cuno baki tayi,Hannu yasa ya rike bakin.zafin da taji yasa hawaye ya zubo mata.
Daure fuska yayi yace"oya Tashi maza kinsan bansan wasa da sallah.
Yana fita ta murguda baki sannan ta mike tayi alwalar.
Tana idar da sallar ta dauko alqur'ani,farouk yana dawowa tun daga palour ya fara jiyo sautin
karatun ta.
Yana shiga ta dago ta kalleshi shi,murmushi suka yiwa juna sannan tace"ina kwana,shafa kai
yayi yace"ya bakunta,sunkuyar da kai kawai tayi.
Kusa da ita ya zauna yace"oya bude muyi musaffah.
❤❤❤❤
❤❤❤❤
One love ce
❤❤❤❤❤
❤❤❤❤❤
❤❤❤❤❤
*FAROUK KO HAIDAR*
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~❄we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our
creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u
np pain~*
written By Deeja One Love
Dedicated to madina m umar
63-64
Sai da gari yayi haske sannan suka rufe alqur'anin,komawa suka yi suka kwanta.
Humaira kuwa karfe takwas ta farka,falo ta fara kakkabewa Sannan ta shiga kitchen,tab gaskiya
an kashe kudi da yawa.
Falo ta dawo ta zauna,door bell aka Danna,da sauri ta mike taje ta bude,wani dogari ta gani,sai
da ya tsuguna ya gaisheta sannan ya miko Mata basket,Amsa tayi sannan ya juya ya tafi.
Akan dinning ta jera sannan ta tafi dakinta,wanka ta shiga tayi tana fitowa ta fara kwalliya
simple makeup tayi,wata atamfa ta dauko mai ruwan hoda ta saka.
Tayi kyau sosai da sosai,tana tsaye tana gyara Dan kwalin ta farouk yayi sallama ya shigo.
Ta mirror suke kallon juna,murmushi suka yiwa juna sannan ya karaso kusa da ita.
Hannun ta ya rike a kunne ya rada mata"kin yi kyau,sassayyan murmushi tayi tace"na gode kai
ma kayi kyau.
Kallon kan shi yayi wani yadi ne dark blue a jikinshi dinkin mu hadu a abuja.
Murmushi yayi har hakoranshi suka bayyana kafin yace"nima na gode,muje mu ci abinci.
A nutse suka fito har falo,humaira tayi serving din su.
A plate daya suka ci cikin farin ciki.
Yau sati biyu da bikin su,idan kaga farouk da humaira kuwa sun Kara haske da kyau,sai dai har
lokacin babu abinda ya shiga tsakanin su.
Humaira ita tsoro take ji shi kuma farouk haha so ya takura mata.
Humaira kwance kan kujera tana chatting dasu surayya suna fira suna dariya,farouk yayi
sallama ya shigo.
Da idanu ya bita wato ita duniyar dadi take Mata bayan shi kullum dare a wahalce yake.
Humaira kuwa mikewa tayi ta mishi sannu da zuwa.
Murmushi yayi Mata kafin yace"gobe zamu fara aiki a hospital din mu.
Cikin farin ciki ta taya shi murna,kallon ta yayi yace"amma ni kadai ne zan fara zuwa,da mamaki
tace"saboda me?,
"Eh saboda su haidar zasu tafi honey moon" ya bata amsa.
Shiru tayi kafin tace"saboda me mu baza muje ba,da mamaki yake kallon ta kafin yace"me
zamu je yi bayan baza ki iya bani hakkina ba?.
Kasa tayi da kai,mike wa yayi Sannan yace"ki shirya anjima zamu je gida domin gaisuwa.
Shiru tayi,kallon ta yayi yace"baki ce komai ba",daga kai kawai tayi.
Sai da yayi wanka sannan suka yi lunch,yana gamawa ya wuce bedroom dinshi.
A sanyaye humaira ta bishi Dakin a kwance ta same shi,cikin sauri itama ta Hau bed
din,idanunshi a rufe yace"please humaira sauka i wanna sleep.
Zaro idanu tayi to kodai an bata mishi rai ne a waje,tuna wa tayi da yanayin Zaciyar shi,cikin
sauri ta mike ta fita.
Dakin ta ta koma ta kwanta hawaye ne suka fara zubo mata,waya ta dauka kamar zata kira
surayya sai kuma ta fasa tunda ta San anjima zasu hadu.
Da yamma tayi wanka ta saka swiss lace ruwan hanta da ratsin ruwan madara,mayafi Kalar
milk da jaka da abin hannu,tayi Kyau sosai.
Falo ta fito ta zauna kamar ta shiga sai dai tana tsoron shi,tunda tasan yanayin fushin shi,sai ta
je Kofar sai ta kasa shiga.
Farouk kuwa wanka yayi ya shirya cikin shadda kalar ruwan madara yayi kyau sosai,sauri-sauri
yake yi domin baya so humaira tayi ta jiran shi.
Yana bude kofa ya ganta tsaye a bakin kofar,tausayi ta bashi domin yasan tsoro take ta shiga.
Murmushi yayi Mata yace"ya dai yan mata,ajiyar zuciya tayi kafin tace"dama ina so nace maka
ne na shirya".
Hannun ta ya janyo ta fado jikin shi,tsam ya rungumeta cikin wata kalar murya yace"kin yi kyau
kamar kada mu fita gaskiya ina kishin wani yaga wannan kwalliyar.
Murmushi tayi a Zuciyar ta tace"ina fa zan yarda wani a fasa fita Dan ina so naga aunty yusra
yau.
Jan hannun ta yayi suka koma dakinta,its dai kallon ikon Allah take,hijab ya ciro Mata milk
colour yace"ki saka wannan Dan gaskiya bazan yadda ki fita da wannan shigar ba.
Amsa tayi babu musu ta saka,hannun ya rike sannan suka fita.
Sai da ya tada.motar sannan ya Kira salim yace"gamu mun fito".
Motocinsu a Jere suka fice daga unguwar,suna shiga fada aka fara guda,farouk kuwa hannun
humaira ya ja yayi tsaki kasa kasa.
Fada suka fara shiga sukayi gaisuwa sannan suka shiga cikin gida,bangaren yafindo hari suka
gaisheta ta.
Suna fitowa suka yi hanyar bayan gida da mamaki ammar yace"farouk pls,kallonshi kawai
farouk yayi ya cigaba da tafiya.
Juyawa yayi niyar yi amma haidar dake bayan shi yace"baka isa ba dole kaje ammar.
Kallon yusra yayi ta marairaice fuska tace"haba zuma na muje mana,hanging ta ya rike suka bi
su farouk.
Hasbunallah!ammar kuka ya fashe da shi domin gaba daya wajen wari yake yi,ga wasu
tsutsotsi da suke fitowa ta kasanta.
Kasa cewa komai tayi sai dai hawaye da yake bin idanun ta,a sanyaye suka bar waje,bangaren
fulani suka wuce.
Su farouk kuwa can suka bar matan su kuma suka fita suka nufi section na maza.
Yusra tayi dariya tace"ai wallahi soyayyar Ku humaira akwai burgewa ni na kalla kun fi kowa
kyau ne,dariya aka kwashe dashi.
Kallon su tayi tace"nifa da matsala,cikin sauri suka ce"meye matsalar?,nan ta kwashe komai ta
basu labari.
Shiru suka yi kafin sumayya tace"amma kin bani mamaki wallahi yaushe ake haka sai kace
zamanin da kinfa yi makarantar boko bare ace gidadanci ke Damon ki,husna ta amshe da
cewa"ki zauna wasa wallahi zaki ga wasa duk zurfin cikin yaya farouk har ya iya fitowa ya gaya
miki amma ki kasa ganewa bari ya miki kshiya naga ta tsiya.
Yusra tace"to bude kunnuwan ki kiji wallahi kodai ki gyara ko a gyareki tab su fa maza sun fi so
suga mace wayayyiya amma kin zauna kauyenci,ita dai surayya bata ce komai ba.
Fada suka yi Mata sosai da sosai sannan suka koma labarin honey moon,yusra tace"wai kuna
ta shirye-shirye ko?.
Husna tace"Sosai ma gobe zamuje passport,yusra ta dubi surayya tace"ke wai me Zaku je
yi?,banza surayya tayi da ita.
Sumayya kam harara ta gallawa humaira kafin tace"ga wannan vanzar da taja mana nan,wai
my choco idan yaya farouk baza suje ba muma haka,dariya akayi gaba daya.
Humaira tace"aikuwa kun lashe,marairaicewa sumayya tayi tace"Dan allah ki taimaka ki lallaba
Mijin ki yayi mishi magana muje tunda Ku ba zuwa Zaku yi.
Meye tukuici na"humaira tace,sumayya tace"wallahi a ranar da zamu bar kasar nan zan baki",to
shikenan.
*FAROUK KO HAIDAR*
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~❄we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our
creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u
np pain~*
written By Deeja One Love
Dedicated to madeena m umar
Sister feenerh ina tayaki murnar gama littafinki mai suna auren soja allah ya Kara hade kanmu
ameen
Wannan page din sadaukarwa ne ga duk mai suna umar farouk.
Sannan wajen numbering ina mistake kuyi hakuri,
bubuwa ne sun fara mini yawa abinka da mai Iyali lols,
Sorry for my mistakes.
65-66
Sai da sukayi isha sannan kowa ya zo ya dauki matar shi.
Suna komawa farouk wanka kawai yayi ya kwanta,humaira kuwa ta dade tana tunanin
magan-ganun dasu yusra suka gaya Mata.
A sanyaye ta shigo dakin ganin ya kwanta ya sata ajiyar zuciya,wanka tayi ta canja kaya
sannan ta kwanta.
A hankali take bin fuskarshi da kallo maganar yusra ke dawo mata inda take cewa"ko be neme
ki ba ke ki neme shi,jinjia kai kawai tayi yama za'ayi ta iya wannan ai rashin kunya ne.
Hannu tasa ta shafa daga kan hancin shi har wajen bakin shi,cikin shagwaba tace"my icy i love
you to amma taya wai zan kawo maka kaina bayan kai baka nema ba,rufe idanu tayi wai ita taji
kunya.
Light kiss tayi mishi a goshi sannan ta kwanta akan kirjin shi a haka har barci ya dauketa.
Farouk ya shafi inda tayi kissing dinshi cikin tsananin murna yace"love you too my teddy",
Cikin shauki yau suka kwana.
Yau dai masu honey moon suka daga zuwa kasar oman,washe gari kuma farouk ya fara aiki a
hospital din su.
Farouk ya shigo gida a gajiye,cikin sauri humaira ta tarbe shi,orange juice mai sanyi ta tare shi
da shi.
Kallon shi tayi tace"yaya farouk wanka,a gajiye yace"teddy kiyi hakuri na gaji",cuno baki tayi.
A hankali ya mike ya shiga wankan,kayan shan iska ta ciro mishi,white three quarter da light
pink armless.
Murmushi yayi domin tana wajen kula dashi humaira bata wasa sai dai kuma ta kasa biya mishi
bukata har yanzu.
A kan dinning ya sameta,abinci yaci sosai domin kuwa cous cous tayi daya ji vegetables.
Bayan kwana biyu,humaira ta fito a zaune ta sami farouk yana waya da salim,kan kafar shi ta
zauna,lumshe idanu yayi yace"da gaske".
Bata ji me salim din yace ba,farouk cikin farin ciki yace"to yaushe zaku wuce india?,nan ma
bata ji me salim yace ba,farouk ya kuma cewa"ok allah ya kaimu,zan sa ran ganin Ku nan da
sati biyu idan kuka wuce ko,to kada ka nufo adamawa kaji na gaya maka,dariya yayi sannan ya
kashe wayar.
Sakala hannun ta tayi ta wuyan shi tace"me yaya salim yake gaya maka",Kara janta jikin shi
yayi yace"sumayya is three weeks pregnant,dariya humaira tayi tace alhamdulillahi kai amma
naji dadi wallahi.
Shinshina wuyanta yayi yace"ke yaushe zaki bani baby,murmushi kawai tayi.
Hancin su ya goga yace"ki shirya mana kaya gobe zamu wuce taraba",cikin murna tace Allah ya
kaimu.
Washe gari da safe humaira ta Kira