Showing 12001 words to 15000 words out of 72611 words
Chapter 5 - farouk Ko haidar complete by one love.pdf
Written by
Deeja one love
Dedicated to madina m umar í ¼í¼¹
09
Tashi farouk yayi Ya zuba musu abincin
Yana Lura dashi kawai juya cokali yakeyi
Kamar yadda Salim ya zata
Mamace ta kirashi a Waya tace
Tana bukatar ganinshi
Salim yace
Mama ki Bari sai next week Dan wannan satin ina da ayyuka da yawa
Umarni na baka fa ba shawararka nake nema ba
Kashe Wayar tayi
Kallon farouk yayi sannan ya Mike ya fita
Ya Muhammad Ya Kira a Waya ya gaya mishi abinda Ya faru
Ajiyar zuciya yayi yace
Salim ka bari zan Mata magana amma kasan halinta Ko?
Eh amma ai ni babu Laifina fa a ciki
Salim ya bashi amsa
Suna gama Wayar ya hango haidar na tahowa
Had'e rai yayi
Haidar yayi dariya yace
Dama Sakin ranka kayi Dan ba kyau Kake ba Idan ka daure fuska.
Ai bansan kaima í ½í²£ bomb bane da ban kaika ba
Salim ya fada
Dariya haidar ya kuma yi kafin yace
Haushi suka bani
Salim yace
Amma ka sani Dan uwana í ½íº€ rocket ne
Dariya haidar yayi yace
Tab Allah Ya kyauta
Ya kuka k'are to
Had'e rai yayi
Bayan ka ja mini matsala Kake tambaya ta yanzu ina zakaje
Shafa cikinshi yayi
Dariya Salim yayi yace
Wlh mummy na k'ok'arin Kaifa consumer ne.
Jan hannun shi yayi yace Naji Muje
daga jiya zuwa yau nayi missing girki me dad'i.
Fira suke har suka karasa d'akin yana zaune Yana Karatu suka shigo
Dago Kai yayi Ya amsa sallamar su
Kallon kallo aka koma yi Tsakanin haidar da farouk
Cikeda mamaki haidar yace
Mutumina ka ga abinda na gani Ko aljanine
Dariya Salim yayi yace
Ba ina gaya muku kuna Kama ba kuma karyata ni ai Gashi Nan kun gani da idonku
Shidai farouk be ce komai ba sai idanu da yake binsu dashi
Zuba masa abincin yayi
Shi kuma ya Fara ci
Haidar na gamawa yaceda juya ya Kalli farouk yace
Mutumina Anya kuwa wannan yana magana
Tab'e baki Salim yayi yace
Bro ai yadda kasan ya had'a Jini dana sarauta Ko ni bazan gaya masa miskilancin ba.
Ko kallonsu be yi ba
Tashi Salim yayi Ya fusge littafin dake hannunshi yace
Bro Meye Hakane Wai kanaji ana magana kayi shiru
Kallonshi kawai ya tsaya yi kafin ya kwace littafin
Had'e rai Salim yayi Ya Mike
Da sauri farouk ya rike hannunsa yace
Kai Wlh ka cika rigima to yanzu gaya mini me Kake so nace
Bansani ba
Salim ya fada a zafafe
Murmushi yayi ya juya ya Kalli haidar yace
Barka haidar Ko
Daga Kai yayi Alamar eh
Kaga bro yaji haushi ka saka baki mana
Haidar ya Kalli Salim yace
Haba mutumina ai Ya bada hakuri ya wuce Ko
Harara ya galla mishi yace
Bansan katsalandan malam ina tare ka ganmu
Kallon farouk haidar yayi Ya Tabe fuska
Cikin shagwaba yace
Ka ga na saka baki ya gwasaleni Ko?
Sakin hannun Salim yayi Ya matso kusada haidar yace
To ai kaine ina tare ka ganmu
Zaro idanu yayi yace
Had'e mini Kai zakuyi
Dariya Salim yayi yace
Ai maganinka kenan
Tashi yayi yace
Bazan kuma dawowa d'akin nan ba Dan watarana duka zakuyi mini
Farouk zai bishi Salim yayi saurin riko shi yace
Kyaleshi gobe ma zai dawo
** ** ** ** ***
Haidar ya Kalli Salim daketa had'a kaya yace
Wai Kai sai kace me kwana goma ina kwana biyu kawai zakayi
Farouk yace
Kyaleshi Nawan wannan daka gani ba Karatu yakeso ba
Dariya Salim yayi yace
Ba Muda lectures Ranar Monday da Tuesday fa Shiyasa zan kwana hudu
Kallonshi farouk yayi yace
Yanzu kai sai ka tafi ka barni ni d'aya
To baga haidar nan ba
Salim ya bashi amsa
Shiru yayi yace
Ko nima na tafi Kano ne?
Haidar yace da sauri
A'a ni Kadai zaku Bari kenan
Murmushi farouk yayi yace
To ai kai dama kana da abokin zama
Shiru yayi kafin yace
Gaskiya ban yarda ba
Wai ma a Kano a ina Kake
Salim yayi dariya yace
Kasan Sarina dake wudil local govt
D'aga Kai yayi Alamar eh ya k'ara da cewa
Amma jinta nakeyi
To Dan can ne
Har bakin get suka rakashi kafin su juyo
Mama tace
Yi mini shiru banason jin komai a gabanka za'a ciwa Zainab mutunci ka kyale wai Salim da
bakinka Kake cewa gwara bare da Dan uwanka to Wlh ka kiyayeni bance kada kuyi Abota ba
amma matukar zaka dinga janyo bacin rai na to Tabbas zan datseta
In banda Kai Wani irin mutum ne taya zaka yarda a dinga wulakanta Dan uwansa Haba
Yanzu Gashi aunty halima ta kirani tace nanda end of this month zasu zo Idan kuma Maganar
taje kunnenta Nace Mata me?
Shi dai Salim be ce mata komai ba
Numfasawa tayi kafin ta Cigaba da cewa
To daga yau kada hakan ta kuma faruwa sannan Daga yau Kullum kaje ka gaisheta wannan
umarni na ne
Sunkuyadda Kai yayi yace
To Insha Allah zan dinga zuwa sannan Allah Ya huci zuciyarki kiyi hakuri hakan bazai kuma
sake faruwa ba
Tashi kaje
Mikewa yayi tafi
Haidar yace
Bani labarinka Nawan
Murmushi yayi yace
Me zakayi da labarina
Dariya haidar yayi yace
Let's keep our selves busy mana
Littafi farouk ya janyo Ya Mika masa
Dariya haidar ya kuma yi Ya ce
Nifa labarinka nake so.
Kallonshi farouk yayi yace.
Gidan mu babban gidane a Sarina
Mahaifina manomi ne yanada yara takwas mace d'aya maza bakwai
Nida yayyena da kannena
To Kaji labarina
Ajiyar zuciya haidar yayi yace
OK ni kuma ina a kaduna anguwar rimi
Momma na babbar justice ce high court babana kuma babban likita ne da ake ji dashi a kasar
nan Dan shine likitan dake kula da iyalan governor na kaduna
Mu biyar ne ya'yansa
Maza uku mata biyu
Yaya Abbas shine babba commissioner of police na kaduna
Sai yaya Adnan shi kuma babban lawyer ne
Sai ni dake Karatu yanzu nake karantar medicine/surgery
Sai surayya ita kuma tana karantar mass communication me a Cambridge University England
Sai sumayya ita Ko candy bata yi ba
Kasancewar babu tazara tsakanina da surayya yasa tafi Raina ni
Wannan shine labarina
Murmushi farouk yayi yace
Meyasa ba'a fitar da Kai ba?
Nine Bana so kawai ji nayi nafison nazo nan nayi Karatu
Haidar ya bashi amsa
Gaskiya gidanku gidan yan Boko ne
Farouk ya gaya Yana dariya.
í ½í³‘farouk Ko haidar í ½í³‘
Written by deeja one love
Dedicated to madina m umar í ¼í¼¹
Eh Ni yar Zaria ce da magana ne da kikace ba Muda hankali munji bamada ki gaya mana
kasuwar da kika sayo naki sai muma Muje mu siyo.
Allah yasa mu dace Ameen
Assaburu indal azaa.
10
Haidar ya Kalli farouk yace
Yauwa me zai Hana Muje gidanmu kawai muyi hutunmu
Kallon juna sukayi shida Salim suka fashe da dariya
Salim Yace
Tab Kaji wata magana
Kawai kuyi zamanku a gidanmu next Hutu sai Kowa yaje yayi a gidansu
Allah kamata yayi ace duk Hutu a Kusa mukeyi
Kallonshi haidar yayi yace
Ka isa ma ai Kd awa d'aya zuwa da Rabi zamu je shima babu nisa
Husuma ce ta tashi Tsakaninsu
Cikin fushi Salim yace
To baka isaba sai ka tafi Kai kad'ai Nida bro muyi hutunmu anan
Harararshi haidar yayi yace
Sai dai Kai ka zauna ni da farouk kuma mu tafi kaduna.
Ka isa ai tare ka ganmu
Salim ya gaya a zafafe
Haidar yace
Ai kuma nidashi muke Kama
Shidai kallonsu kawai yakeyi
Ganin bazasu Dena ba yasashi cewa
Ku dakata nifa Kano zani nayi hutuna
Zaro idanu duka sukayi
Cikin fushi duka suka ce
Gurina malam zakayi Hutu
Ajiyar zuciya yayi yace
Ai sai naga Wanda zai jani ta karfi
Dukkansu daukar Waya sukayi suna gayawa mamansu
Shi dariya Abin ya bashi
Amshe Wayar yayi yace
Wai ku baku gajiya da rigima ne
Yanzu yadda za'ayi mu Fara zuwa kaduna muyi sati d'aya sai mu wuce Kano muyi sati d'aya sai
mu dawo Zaria muyi kwana Tara yayi haka ina
Harara Salim ya galla wa haidar yace
Ni nasan kafi sonshi Shiyasa kace a Fara zuwa gidansu.
Ni kabarni gidama zan tafi
Haidar ya maida masa da hararar yace
Dalla rufewa mutane baki bayan yafi sonka jifa Wai kwana Tara
Wlh Nidai nasan yan ubanci kawai ake mini.
Zama farouk yayi Ya dafe Kai
Wayarshi ya d'auka Ya Kira mama.
Ya gaya mata abinda Ya faru
Dariya tayi tace
Ka kyalesu Wlh ka Dena biye musu
To fa mama duka Sunyi fushi
Ya bata amsa
To zan kira Salim d'in.
Kiran mamie yayi itama ya gaya mata
Dariya tayi tace
Kana ma kokari ai farouk ka barni da haidar d'in.
To Ya amsa tareda kashe Wayar
Kusan a tare Wayarsu tayi ringing
Bayan sun Gama amsa Wayar duka suka juyo suka kalleshi suka ce
Taso Mu tafi.
Har suka fito bakin get babu Wanda yace
Komai.
Zaman jiran minti talatin sukayi sannan driver d'in ya iso
Shiga sukayi suka tafi
Ko a hanya babu Wanda yace komai
Farouk duk da ba Wani biye musu shiriritarsu yakeyi ba amma sai da yaji babu dad'i
To amma shi besan yadda zai dawo dasu normal ba Dan haka shima yaja bakinshi yayi shiru
A anguwar rimi
Anguwace ta masu hannu da shuni
Gine ginen farouk ya zubawa idanu Tabbas haidar ba daga gidan kananan mutane ya fito ba
Dai dai bakin Wani makeken gida drivern yayi horn
Gidane haddadde kuma zagaye da securities
Wata farar matace daga gani kasan Hutu da dukiya ga uwa uba ilimi Ya zauna
Cikin sauri Ta k'araso Tana fadin
Oyoyo my baby
Tsayawa tayi ta zuba musu idanu
Fahimtar bata ganesu bane yasa haidar ya nufeta da sauri Ya fada jikin ta.
Salim yayi murmushi a ranshi yace
Wai Dan ma ba kaya kala daya suka saka ba
Dan farouk shaddace ajikinsa ruwan milk
Haidar kuma Wani farin yadine.
Cikin shagwaba yace
Momma I miss you so much
Peck tayi masa a goshi tace
Babyn momma I miss you too.
Su farouk kuwa Sakin baki sukayi suna kallon ikon Allah
Jan tsaki Salim yayi yace
Mutum Ya girma besan ya girma ba
Ai dai yanzu tunda nazo kuma nine k'arami
Duka sai da sukayi dariya
Mamie ta k'arasa Kusa da farouk ta rungumeshi tace
Welcome my son Ya hanya.
Murmushi yayi yace
Lafiya lau Mamie
Wajen Salim ta nufa da sauri Ya noke kafada yace
Ni ban yarda ba sai da kika gama da wancan katon sannan zaki kulani
Rike Haba tayi tace
Ikon Allah haka Salim dama Kake da rigima
Dariya sukayi gaba d'aya
Cuno baki yayi yace
Ai ni wancan kika Fara Tara
Janyoshi Jikinta tayi tace
Yi hakuri zo my son
Shima peck dinsa tayi a goshi
Cikin farin ciki suka shiga Cikin gidan
Ajiyar zuciya farouk yayi Dan gidan Ya had'u karshe
D'akin haidar suka shiga
Mamie tace
Fresh up then sai kuzo Kuci abinci.
Wanka sukayi sannan suka fito
Wajen cin abincin ma haka suka dinga rigima Shidai farouk sai dai kawai yayi murmushi
Mamie ta kalleshi tace
Gaskiya na baka girma Dan kafi cancanta haka suketa shiririta
Murmushi kawai yayi Ya D'aga Wayar dayake kira yayi
Bayan ya amsa sallamar yace
Mama dama cewa nayi Bari na kira na gaya miki mun iso Lafiya
Cikin fara'a tace
Kai Masha Allah ka fisu hankali dama
Murmushi kawai yayi yace
Ga Mamie ku gaisa
Amsar Wayar tayi Kamar sunsan juna haka suka dinga fira
Bayan sun Gama Mamie tace
Bari zan amsa number dinta sai mu dinga gaisawa
To farouk ya bata amsa
Audu ya kira yace
Idan kana gida bawa Inna
Ya kuwa yi sa'a yana gidan Dan haka ya bata
Bayan sun gaisa yace
Dama na kira ne Nace mun iso Lafiya
Ga kuma Mamie ku gaisa
Kan ta amsa Salim yayi sauri Ya kwace
Bayan sun gaisa yace
Inna dama nan da sati d'aya muna nan zuwa
Dariya tayi tace
To Salim Allah Ya kawo ku Lafiya
Yauwa Inna Kalar dambun da kike yiwa Dan uwa nake so
Dariya tayi tace
Oh shi Ya baka labari
Kallonshi yayi kafin yace
Eh
Haidar yayi tsaki ya kwace Wayar ya ce
Inna kada ki damu da wannan k'aton wahalar dake zaiyi.
Cikin fara'a tace
Babu komai ai
To Inna Dan wake ni nakeso
Mamie ce ta fuzge Wayar tace
Kyalesu Dan Allah wai'nnan basuda aikin yi
Dariya Inna tayi tace Kada ki damu ai
Mamie tace
Wlh suka zo sai sun isheki itama fira suka yi kafin tace
To UMMAN farouk na gode
Inna tace
Babu komai Wlh nice da Godiya
Kuma ma dinga gaisawa ta Wayar audun
Mamie tace
Au babu Waya a wajenki
Eh amma munkanyi amfani data yarane.
Cikin mutunci sukayi sallama da juna
Sallama sumayya sukayi suka shigo
Da gudu ta taho Tana Oyoyo yaya
Tsayawa tayi cak Tana kallonsu
Surayya ita ma tana karasowa ta tsaya Tana kallonsu
Kacin ci kancin ci ta fara
Dariya Mamie tayi tace
Ato banbance mini Auta
Kamar me doubting ta karasa ta zauna a jikinsa
Tace an dawo Lafiya
Dama surayya bata da madafa Dan haka kawai ta biye Mata
Shidai amsawa kawai yakeyi
Kallon haidar yayi yaga Ya juyar da Kai
Dariya Salim yayi
Surayya ta kalleshi tace
Kai kuma me ya baka dariya
Cikin dariya yace
Gani nayi lokaci guda kun kasa gane kyakkyawa da katon banza
Harara haidar ya galla mishi yace
Wlh ka fita harkata
Shiru sumayya tayi tace
Me Kake nufi
Had'e rai yayi yace
A, a Babu komai
Itadai Mamie dariya kawai takeyi
Cikeda k'uluwa surayya tace
Ki kyale wannan Ya Salim Din dama Ya haidar yace Mana Ya fiye tsokana
Salim yaceda sumayya
Kinji matso na gaya miki gaskiya
Tasowa tayi daga jikinsa ta matso
A kunnenta Ya rada mata
Kallon haidar tayi Cikin dariya tace
Sisi Wlh Ga yaya haidar d'in nan
Da sauri surayya ta kalleta tace
Da gaske
D'aga Kai tayi
Dariya suka kwashe dashi gaba d'aya .
í ½í³‘farouk Ko haidar í ½í³‘
Written by deeja one love
Dedicated to madina m umar í ¼í¼¹
11
Surayya ta Matsa Kusa dashi tace
Wlh yaya Kai Ko
Hannun sumayya ya rike yace
K'anwata Ya makaranta
Lafiya lau yaya
Sumayya ta bashi amsa
Kumburo baki surayya tayi tace
Ni kuma ai baza a tambayeniba
Eh ai dayake ninace ki dawo dole ki dameni.
Haidar ya bata amsa
Matsawa Kusa da Mamie tayi tace
Mamie kinaji baki ce komai ba
Dariya tayi tace
To ai kun Saba dama gwara ku raba Hali
Washegari suka shirya suka shiga Cikin garin kaduna
Sunyi yawo sosai haka kuma farouk ya ga gari Dan wannan ne zuwanshi na farko
Cikeda santin Garin suka dawo
A dinning suka tarar da abba da Mamie
Abba Ya ce
Ga yaran abba sun dawo
Cikin sauri karasa kusada abba Ya rungumeshi.
Turo baki haidar yayi
Dariya Mamie tayi tace
Tab rigimar zaku Fara ko
Hannunta Salim ya rike yace
Mamie kada ki damu da wancan katon ya girma besan ya girma ba
Abba yace
Lallai ma dai Allah Ya shiryeku
Kallon farouk yayi yace
Kaidai ka huta my son babu ruwanka
Murmushi yayi yace
Ni ai babbane
Sumayya ta Kalli haidar tace
Allah Ya haidar ka cika fitina ka Gama da Sisi ka koma kan yaya Salim