Showing 27001 words to 30000 words out of 72611 words
Chapter 10 - farouk Ko haidar complete by one love.pdf
Kallon juna sukayi sukayi murmushi
Murmushin Mamie tayi kan tace ai basa ji ma.
Da mamaki tace
Amma duk Wanda ya ganku yaga Fulani
Sallama Salim yayi yashigo
Wajen Mamie ya Fara zuwa Cikin murna yace
Barka da zuwa Mamie
Had'e rai haidar yayi
Kallon farouk Salim yayi yace
Barka da zuwa Dan uwa
Sumayya tace
Ai fa yaya Salim ga yaya farouk d'in nan
Kallonta ya yi yace
Waye Ya gaya miki haka ai ni duk inda naga mummuna ina ganeshi
Duka haidar ya Kai mishi yace
Wlh zan koma inda na fito yanzu.
Yana dariya yace
Sai ka dawo.
Mikewa sukayi Salim ya kira Khairat Wanda take Yar uwarsu ce
Yace Mata.
Kinga su mama suna wajen kamu ga Mamie nan Idan su mama sun dawo ki hadasu mu zamu
fitane.
D'aga Kai tayi tace
To
Wani Bangare na gidan suka nufa Wanda yake can gefe
Wani kofar suka bud'e suka shiga
Garden ne me kyau ta gefenshi suka bi
Wani wajene Kai kace haddadden hotel ne
Suna bud'e kofar suka shiga
Lifter
Hawa na biyar suka tsaya
Dakine reras gasunan Wani daki ya bude Wanda ya hadu sosai komai na d'akin milk and brown
ne.
Salim yace
Wannan shine d'akina
Haidar ya tambayeshi
Bangane ba
Dan murmushi yayi yace
Duk Wani family na gidan nan to Yanada d'aki Anan
Bangaren mata kuma yana ta gefen fada
Koda Kai ba mazaunin Garin bane Ko kasar amma sai an maka naka d'akin
Murmushi farouk kawai yayi yace
Nuna mini bayi nayi wanka
Yana fitowa haidar ya shiga
Wasu kananan kaya ya saka
Bakar Riga da Blue Jeans haka ma haidar.
Salim kuwa Manyan kayane ajikinsa wato shadda Riga da Wanda sky blue.
Masallacin fadar suka shiga sukayi sallah
Suna fitowa daidai lokacin da motoci ke parking gasunan bila adadin
Cikin mamaki haidar yace
Wannan family tab kiyashi kenan
Hararshi yayi yace
Mune kiyashin?
Dariya yayi kawai
Farouk kuwa Dan karamin tsaki ya ja kafin yace
Ai ni wannan ko hayaniyar su ciwon Kai zata sani
Haidar yace
Muje Ko
D'akin Salim d'in suka koma sunata fira
Washegari da safe busa ta tada su
Tsaki farouk ya ja yace
Kai Wlh dama banzo ba
Cikin gida kuwa
Mamie na zaune suna fira wata mata ta shigo
Da fara'a ta k'arasa kusada mama tace
Halima an tashi Lpy
Itama Cikin fara'a tace
Lafiya lau rumaisa kin iso muna can muna Kamu
Murmushi tayi tace
Wlh matsala aka samu amma da tun shekaranjiya zamu iso
Kallon Mamie tayi tace
Sannu baiwar Allah
Gaisawa sukayi Kamar sunsan juna kafin tace
Su farida basu farka ba tun jiya suke damuna da tambayarki
Dariya kawai mama tayi .
Karfe biyu fadar ta cika taf Kamar zata tsage saboda mutane
Hada hada akayi
Farouk ne zaune a d'aki
Salim ya harareshi yace
Wlh ka tashi Muje Ko kuma na gayawa yaya Mubarak baka je daurin aurenshi ba
Banza yayi dasu hakan yasa haidar yayi dariya yace
Ashe dai kuna fada
Harara ya galla mishi kafin ya mik'e Ya Kalli Salim yace Muje Ko
A lifter suka had'u da Faisal da ammar da yaya Muhammad
Gaishe da yaya Muhammad sukayi Cikin murna
Yace
Yan biyun Mamie saukar yaushe
Dariya Salim yayi yace
Jiya fa suka zo
Faisal da ammar kuwa haushi kamar ya kashe su ganin Ko su nuna sun San dasu.
í ½í³‘farouk Ko haidar í ½í³‘
Written by deeja one love
Dedicated to madina m umar í ¼í¼¹
22
Daurin aure ne akayi sun Kai guda bakwai
Kai wannan family da girma yake
Farouk ganin kanshi na neman Ya fara ciwo yasa shi barin wajen
Wajen wasu bishiyoyi yaje ya zauna
Sun Kai su shida suka jero
Tundaga nesa amra ta ce
Waye wancan ne?
Yusra tace
D'aya daga Ciki tace
Wake nan
Da hannu amra ta nuna shi
Ganin wa aka nuna yasa Yusra yin murmushi tace
Abokin yaya Salim ne
Da mamaki tace
A haka daya juya Kamar daddy hamma
Murmushi Yusra tayi tace
Zo Muje ki tabbatar bashi bane
Jan hannunta tayi yayinda sauran suka wuce
Suna karasawa Yusra da murmushi tace
Yaya FAROUK Ko yaya HAIDAR
Da sauri Ya juyo ganin Yusra ce yasa yayi tsaki yace
Ke bakida hankali Ko haka ake Idan aka zo Waje babu sallama babu komai sai surutu
Sunkuyadda Kai tayi tace
Yi hakuri na manta ne
Ina sumayya
Ya tambayeta
Tana tareda husna
Amra kuwa Sakin baki da hanci tayi Tana Kallonshi Tabbas wannan shine Wanda ya dace ta
aura
Gyaran murya tayi Wanda yayi daidai da karasowar su haidar
Salim yace
Barka da hutawa aunty na
Dan murmushi Tayi kawai ta Kauda Kai gefe
Dariya haidar yayi yace
Tsiyar ka zamo yaro kenan Ko Wacce karamar yarinya ka dinga ce mata aunty.
Had'e rai yayi Ya ce
Oya kaima gaida ita
Dan kallon gefen ido yayi mata yace
Tab Allah Ya kyauta wannan yarinyar.
Amra kuwa mamaki ne ya cikata sai ta Kalli haidar sai ta Kalli farouk
Wa'innan identical twins d'in irin haka
Magana take shirin yi su Faisal suka karaso
Kallon up and down yayi musu kafin yace
Ammar kasan talaka be iya samun wajeba.
Dan murmushi ammar yayi yace
Kuda kuma wajen kwadayi yake mutuwa.
Cikin zafin rai haidar yace
Kai Kama kanka wallahi nafi karfin nazo kwadayi ku kanku kun sani
Dariyar mugunta Faisal yayi yace
A hakan Ban gani akasa ba
Amra da sai yanzu tayi magana tace
Kai brother Wai Meye Hakane
Farouk kuwa yadda kasan ba'a halliccesu Awajen ba .
Banza Ya bawa ajiyarsu.
Haniya wajen ya tashi dashi Wanda takai ga ammar ya D'aga hannu ya Mari haidar
Cikin bacin rai farouk shima Ya wankeshi da tafi Wanda yayi daidai da isowar sarki Al'ameen
tareda modibbo sai abba da karamin su daddyn Abuja.
Kowa Tsayawa yayi.
Abba Ya ce
Meye haka
Daga hannu sarki yayi yace
Gobe Idan Allah Ya kaimu ina bukatarsa ganinku gaba daya a fada Naji me yasa kuke fad'a a
Ranar da aka daurawa yan uwanku aure har takai ga Mari.
Wucewa sukayi Wanda jikin su gaba d'aya yayi sanyi
Faisal yace
Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun yanzu Mai martaba yasan ni na Fara hada wannan fadan ai da
matsala.
Ammar yace
Kai Allah Ya kyauta da nasan Hakane da bangaren Fulani na wuce Ko yafindo Hari
Kowa watsewa yayi
A lifter Salim ya kallesu ganin Kowa harkarshi yakeyi babu Wanda ya damu yasa yace
Ku bakusan me kuke bako?
Cikin halin ko in kula haidar yace da akayi me?
Jinjina Kai kawai yayi Ya Cigaba da harkarshi.
Da yamma aka Fara tafiya hall d'in da za'ayi dinner
Salim ya kira mama a Waya
Tace
Yaya kun taho Gamu tareda mamien taku
Cikin jin haushi yace
Mama Wai farouk ne bazai zo ba
Jim tayi kafin tace
Lafiyarsa kalau kuwa
Eh mama
Ya bata amsa
Tace
To Kai Idan zaka zo ka taho mana.
Yana kashe Wayar ko kallonshi be yi ba ya juya ya fita.
Haidar na fitowa daga bathroom Cikin sauri Ya Fara shirinshi
Kallon farouk yayi yace
Kai Nawan ina Salim
Kamar bazai yi magana ba sai kuma yace
Ya tafi
Tsayawa yayi yana kallonshi
Can ya dau wayarshi Ya Kira Salim d'in
Koda ya D'aga masifa Ya Fara yi mishi
Salim yace
To Idan ka Gama sai ka taho ai
Harara yayi Kamar yana ganinshi yace
Waye zai kawoni
Akwai wa'inda basu Gama tahowa ba ai.
OK
Ya gaya Yana kashe Wayar
Agogonshi yake daurawa yana tafiya
Jirani mu tafi
Juyowa yayi Ya Kalli shi yace
Oh dama zakaje
Be yi mishi magana ba har ya Gama shiryawa
Ankon dinner ne ajikinsu yadi ne Kamar silk me Kalar blue and sky blue.
Bakin harabar gidan mutane ne tsiraru wa'inda basu Gama tafiya ba
Tunawa yayi da key d'in motor da suka zo da ita Dan haka
Juyawa yayi domin yaje ya dauko
Yana tsaye har ya dawo
Bude motor yayi suka shiga
Har ya ja zai tada ta k'araso da sauri
Glass d'in ta kwankwasa
Zugewa yayi
Koda suka had'a idanu sai da gabansu Ya fadi
Farouk dai wayarshi kawai yake dannawa
Ganin shirun yayi yawa yasa yace
Ba wajen dinner zakije ba
Sai a lokacin Ta sami damar D'aga Kai Alamar eh
To shigo
Suna gaba Tana baya
Sai dai duk da haka gabanta be daina faduwa ba
Motor shiru sai haidar lokaci zuwa lokaci dayake magana
Abinda ta Lura dashi Na gefen surutu be dameshi ba
Juyowa haidar yayi Ya ce
Ko kinsan hanyar
Eh na sani
Kallon farouk yayi yace
Nawan koma baya ko?
Sai da yayi Jim sannan ya bude ya fita
Kallonshi take Wanda ya hassada mata sake rudewa
Sai da ta zauna sannan tayi Ajiyar zuciya
Bata sake tabbatar wa ba sai da ta kuma kallonsu
Ya ilahi
Ita ke nuna hanyar har suka iso
A bakin harabar hall d'in
Haj salma da haj Zainab ne tsaye suna
Magana
Dayan gefen kuma abbane da daddy sai daddy hamma suma suna magana
Motor na Tsayawa duka kallo ya koma kanta
Fitowarsu yayi daidai da bugawar zuciyar yawancinsu.
Daddy hamma a ranshi fadi yake
Meye hadin rumaisa da wa'innan yaran
Haj Zainab kuwa da haj Salma zufa ce ke zubo musu
Cikin tashin hankali haj Salma tace
Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun na shiga uku ni Salma
Me zan gani
Cikin rudewa haj Zainab tace
Kiyi hakuri Wlh bansan zasu zo
Ba
Sudai ciki suka shiga
Neman Salim sukayi dakyar suka ganoshi Cikin sauri Ya juyar da Kai
Haidar yace
Dalla ni da ka tafi Ka barni banji haushi ba sai kai
Hararar farouk yayi yace
Da wannan nake fa
Au Wai Dani Kake
Banza Salim yayi dashi
í ½í³‘farouk Ko haidar í ½í³‘
Written by deeja one love
Dedicated to madina m umar í ¼í¼¹
23
Sai wajen Karfe sha d'aya sannan aka tashi
Suna isowa gida kwanciya kawai sukayi
Bangaren rumaisa kuwa bangaren yafindo Hari ta nufa
Wata matace da bazata wuce shekaru Hamsin da biyar ba
Zaune hannunta rike da casbaha Tana ja
Cikin sauri ta fad'a jikin ta Tana fadin
Yafindo yau na gansu
A kidime yafindo Hari tace
A ina kika gansu kuma su waye
'Ya'yana yafindo kuma a wajen dinner
Dan murmushi tayi tace
Watakila yaran da suka zo ta bangaren halima kike magana
Wai'nnan ma ai ba yan biyu bane kawai kamace da suke.
Kallon mamaki take binta dashi kafin tace
Dama kin gansu
D'aga Kai tayi tace
Kwarai kuwa jiya suka zo
Jinjina Kai tayi tace
To yafindo wai'nnan 'Ya'yana ne jikina ya bani
Kallo kawai ta bita dashi domin Abin Nata sai da addu'a Shiyasa batason abinda zai kawota
najeriya domin duk zuwanta sai ta rakito ya'yan wasu tace natane
Nisawa yafindo Hari tayi kafin tace
To yanzu Jeki kwanta Idan Allah Ya kaimu gobe ayi Maganar.
Mik'ewa tayi ta tafi
Da kallon tausayi yafindo ta bita.
Daddy hamma ne bayan sun Gama fira dasu abba Kamar bazai yi magana ba sai kuma yace
Ahmad su waye wa'inda suka kawo rumaisa d'azu
Dan murmushi yayi yace
Hamma abokan Salim ne kaga baban daya daga Ciki
Ya nuna daddy
Shi kuma Dayan fa ?
Ya kuma tambaya
Yana Kano
Ya bashi amsa
Be kuma cewa komai ba
Hajiya Salma tace
Na shiga uku wallahi duk Wanda ya Kalli wai'nnan yaran yasan jinin modibbo ne Idan me
Martaba ya gane haka na shiga uku
Dan murmushi hajiya Zainab tayi tace
Kin manta dama mun shirya zuwan wannan Ranar Kedai ki kwantar da hankalinki da bakinta
zakiji ta amsa ita ta yardar da yaranta
Share zufa tayi tayi Murmushin mugunta tace
Hakane fa Kin fini saurin gane Abu
A Ranar mutane dayawa awannan familyn basuyi barci ba
Ciki kuwa harda Salim
Ganin yawan motsin da yake yasa
Haidar yace Lafiya kuwa
Dan karamin tsaki ya ja kafin yace
Ina tunanin hukuncin da me martaba zai yanke mana Gobe ne Idan Faisal ya nuna cewa nafi
sonku sama dashi.
Shiru na Dan Wani lokaci sukayi kafin haidar yace
Tab wato dai halin Fulani yana nan
Salim yace
Ai Al Adar Nan ba'a auren bare
Dan murmushi yayi yace
Kace kaima auren zumunci zakayi
Tsaki ya ja kafin yace
Auren soyayya dai.
Suna fira a haka har barci ya d'aukesu
Washegari da safe
Bayan sunyi breakfast Kowa Ya tafi fada
Anan suka Ga ainihin yawan familyn su Salim Wai ma a hakan wasu sun wuce tun jiya
Shidai haidar gaba d'aya kanshi ma Juyawa yakeyi.
Daddyn yola(wanda shine d'an sarki na farko )
Ya bude taron da addu'a
Kallon ammar yayi yace
Kaine babba meya had'aku
Labari Ya bayar na karya da gaskiya
Jinjina Kai me martaba yayi
Daddyn yola ya dubi Salim yace Saura Kai
Tashi ya yi Ya bada labarin abinda Ya sani
Shima Jinjina Kai yayi
Faisal shine Wanda ya bada labarin abinda Ya faru a karshe
Daddyn yola Ya dubi su haidar yace
Waye zai yi magana a Cikin ku
Daddyn Abuja Ya Mike yace
Amma hamma jabiru kasan dai bakine ba yan family bane
Me martaba yace
Halliru zauna
Dole tasa yabi umarnin mahaifinsa
Mik'ewa haidar yayi Ya bada nashi labarin
Me martaba ya Kalli haj Zainab ya girgiza Kai
Daddyn yola yace
Amma meyasa Kai zaka fifita baki Akan yan uwanka
Sunkuyadda Kai Salim yayi
Daddyn yola yace
Yanzu za'a hukunta Wanda ya Mari ammar a Cikin ku.
Mik'ewa farouk yayi yace
Ina da magana
Da idanu me martaba ya bishi
Wajen tsayin minti uku kafin yace
Anbaka dama
Kallon me martaba yayi yace
Hukuncinku babu adalci a ciki
Kowa taso mishi yayi
Da sauri me martaba ya D'aga musu hannu hakan yasa sukayi shiru
Kallon farouk yayi yace
Me yasa kace haka
Babu tsoro Ko fargaba yace
Saboda ai ni baku tsaya kunji nawa labarin ba sannan kuma kun tambayi shedun dake wajen
kafin na mareshi me yafaru Ai sumayy na wajen da ita da wata yarinya.
Dan mu Bamu a family naku sai ku mana zalinci
Dan murmushi me martaba yayi yace
To me yayi maka ka mareshi
Basu labarin abinda Ya faru yayi sannan ya Dora da cewa
Ai da shedu domin mahaifinsa shine Ya tura sojoji suka kamani Akan danshi ya mareni
Me martaba ya juya ya Kalli modibbo
Shi kuma sunkuyadda Kai yayi kawai
Juyowa yayi yace
Cigaba
Farouk ya Dora da cewa
Sannan a labarin da Dan uwana ya bada ai madam zainab tasa an koreshi Daga makaranta
saboda kawai ta zageshi ya mata magana.
Ko duk wai'nnan ba laifi bane?
Dan murmushi me martaba ya kuma yi kafin yace
To Kai Marin da kayi mishi fa?
Saboda ya mareni a Zaria ne bansami damar ramawa ba.
Jinjina sarki yayi mishi yace
An gaida namiji inaso naga iyayenka.
Farouk yace
Me zakayi musu
Mik'ewa me martaba yayi yace
Zan shiga daga ciki zuwa anjima da yamma za'a kuma zama sai dai inaso zaman yafi wannan
zama na sirri abinda Ya shafi iyalai ne na jiki
Juyawa yayi Ya Kalli daddyn yola yace
Jabir kazo mini da iyayen su duka Su biyun.
D'aga Kai yayi yace
Angama Allah Ya ja kwananka.
Dan murmushi yayi ya shige Ciki
Yana tafiya daddyn yola ya Kalli abba yace
Kaji abinda me martaba yace
Dan haka ina iyayensu suke?
Abba yace
Iyayen Haidar suna nan Cikin gida Dan sunzo biki
Sai dai iyayen farouk suna Kano su.
Daddyn yola yace
To zamu booking flight mu tafi sai mu taho dasu.
Modibbo ya Mike yace
Nima ina neman alfarmar binku Idan yaso sai nayi magana akawo mini jet Dina.
Jinjina Kai daddyn yola yayi yace
An baka dama
daga haka daddyn Abuja ya Rufe taro da addu'a sannan Kowa Ya Mike
Magan gani kanana suka Fara tashi kan cewa yaro k'arami yaja da me martaba
Mamie na zaune labari