Showing 69001 words to 72000 words out of 72611 words
Chapter 24 - farouk Ko haidar complete by one love.pdf
Yau su baffa suka tafi saudia domin sauke faralli,haka a lokacin allah yayi wa hajiya salma
rasuwa,abin gwanin ban tausayi,domin yaran ta sun shiga tashin hankali har gwara ammar
yakan danne ya nuna babu komai amma uwa uwace ko yaya take.
Bayan anyi bakwai kowa ya koma inda yake,a lokacin humaira ta fara jarabawa,tun daga
lokacin farouk ya dauke Mata aiki indai ba Tana da interval ba.
Koda yaushe tayi magana sai yace"humaira tun kina karama nake da burin kiyi karatu yanzu
dama ta zo Dan haka kiyi amfani da ita kan ta wuce (damar da yawancin matan hausawa ke
wasa da ita kenan,mijin ki ya barki karatu kiyi ta shiririta,duk da yanzu naga babu laifi ana
gyarawa allah ya Kara fahimtar damu ameen.)
Suna gama jarabawa ya dauke ta suka tafi fada,bayan sun gaida mai martaba suka wuce
taraba kwana biyu kawai suka yi suka wuce kaduna,sai da suka yi sati daya sannan suka dawo.
Bayan kwana biyu ya kaita gidan salim,sun yi farin cikin ganin juna,sumayya anyi nauyi haihuwa
yau ko gobe.
Sumayya tayi murmushi tace"humaira dan allah kiyi wa yaya farouk magana yayi mishi magana
ina so ya kai ni kaduna na haihu acan,murmushi humaira tayi tace "haba kada ki damu kinji
consider it done",Cikin farin ciki suka rabu da juna.
Da dare suna kwance humaira tace"yauwa peach sumayya ta bani sako tace Dan allah kasa
baki,shiru yayi bece komai ba,cuno baki tayi tace"peach ina magana fa",still bece komai ba.
Mutsikka idanu ta fara yi alamar zata yi kuka da idanu ya bita kafin ya janyo ta jikin shi hannu ya
kai ya dauko wayar shi dake ajiye a bed side cabinet.
Number din salim ya nemo ringing daya ya daga,cikin sauri yace"lafiya Dan uwa",murmushi yayi
yace"kabar sumayya taje kaduna ta haihu acan mana,"shiru yayi kafin yace"to shikenan bro zan
kai ta gobe in allah ya yarda",suna kashe wayar ya janyo humaira jikin shi yace"shikenan ai
ko?,daga kai tayi.
Washe gari ya dauke ta ya kaita aka Mata passport,a kwana biyu da yake da kudi aka sama
musu visa.
Salim ya kai su airport,suka wuce italy.
Kwanan su hudu a can sumayya ta haihu,murna kamar humaira tayi tsuntsuwa ta dawo,kullum
ita kenan video call ana nuna Mata yarinyar ta.
Haka ranar suna through out tana online suna video call tana ganin yadda abubuwa ke tafiya.
Satin su biyu a can suka wuce Dubai sosai kasar ta burge humaira,soyayya kawai suke sha
abin su.
Yana shigowa ya samu tana waya jan ta jikin shi yayi ya fara shinshinar wuyan ta,cikin sauri tayi
sallama ta kashe wayar,bata fuska tayi tace"peach waya fa nake",bece Mata komai ba ya
cigaba da abinda yake yi.
Hannun shi ta rike tace"kasan me da surayya muka yi waya tace wai taji kai ka yiwa salim
magana ya bar ta taje kaduna ta haihu shine take so ka yiwa yaya haidar magana itama ya bar
ta.
Shiru yayi kafin yace"humaira salim da haidar da bambanci,amma zan gwada na gani.
Wayar shi ya dauka ya Kira haidar din ringing daya ya dauka bayan sun gaisa yace"haidar me
zai Hana itama ka taimaka ka barta ta je kaduna ta haihu mana",haidar yace'saboda me?,kai
kana can kana honeymoon ni kuma ka barni gauro bazai yiwu ba",kafin farouk yace wani abu
haidar ya kashe wayar.
Kallon humaira yayi yace"ki bata hakuri tayi zaman ta kinji?,a sanyaye tace"to.
Yau saura kwana biyu su wuce India,kwance humaira take tana barci,farouk ya shigo kusa da
ita ya kwanta,bude idanu tayi tace"ka dawo?,Kara shigewa jikin ta yayi.
Tudun da yaji cikin ta yayi ne yasa shi kallon ta,cikin sauri ya yaye blanket din data Rufa,bude
idanun ta tabe fuska tayi tace"haba peach barci fa nake yi.
Da sauri yace"teddy when last kika ga period din ki?,shiru tayi tana tunani can tace"to ai kamar
tun muna second semester wajen four month kenan,cikin farin ciki ya rungume ta yace"me yasa
ban fahimci kina da ciki ba sai yanzu,saurin kallon shi tayi tace"peach ciki kuma?",daga Mata
kai yayi yace"eh mana.
Washe gari suka tafi india a can ya kai ta hospital nan aka tabbatar mishi da tana da ciki har ma
four month likitan yayi ta mamaki jin cewa farouk din shima likita ne amma wai be fahimta ba,sai
da yace mishi"ita fa bata laulayi haka bega wani symptoms na pregnant ba sai jiya duk da dai
ya kan lura da wani lokacin tana yawan barci.
Ai suna dawowa ya Kira salim cikin murna yace"salim humaira nada ciki har wata hudu",zaro
idanu yayi yace"da gaske amma dama ranar da kuka zo ban gaya maka kamar tana da ciki ba
ka musan ta,ai kuwa yanzu Labari zai bazu,suna ajiye waya salim ya fara yayadawa humaira
nada ciki.
Kafin dare humaira gajiya tayi da daga wayar masu yi musu barka,sai farouk ne ya cigaba da
dagawa,momma na Kira tace"amma nan zaka dawo da ita ta haihu ko,"shiru yayi,momma ta
kuma cewa"farouk da kai nake fa,"farouk yace"momma kin ga ana strike ka Mata yayi ace
yanzu ne muka mori hutun mu kan a koma.
Murmushi momma tayi tace"farouk kuka yi me,"da sauri ya kashe wayar.
Washe gari sai ga waya surayya da husna sun haihu,murna ba'a magana,duka maza suka
haifa,ranar suna haka humaira taji kamar ta dawo.
Daddy hamma ya dinga Mata dariya,kuka ta sawa farouk akan ita ta gaji gida ta ke son
dawowa,momma kuwa koda yaushe cikin kiran shi take kan ya dawo da ita.
Watan su biyu sannan cikin humaira wata shida suka wuce umara Dan su baffa tuni sun yi aikin
hajjin su sun koma.
Humaira tayi farin ciki da ziyartar gari mai daraja garin madina,makka kuwa gata ga ka'aba
abinda bata taba kawowa a ranta ba,ibada tayi ta sosai da sosai.
Sai da su kayi wata daya wai sai taga gari,karshe dai momma data gaji ta Kira salim ta gaya
mishi.
Dawowar su daga da'if kenan wayar salim ta shigo,bayan sun gaisa salim yace"bro Dan allah
Ku dawo haka wallahi nayi missing din ka sa yawa sannan momma tana ta kira na a waya wai
na maka magana".
Farouk yayi murmushi yace"on friday jibi kenan zamu taho insha allah amma kada ka gayawa
kowa,"cikin murna yace"babu wanda zan gayawa.
Washe gari ya kwashe ta suka je suka yi siyayya mai uban yawa,ranar friday jirgin su ya daga
zuwa naija.....
Daga alkamin
One love
*í ½í³‘FAROUK KO HAIDAR* í ½í³‘
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~í ½í²«í ½í²«í ½í²«*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~â„we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our
creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u
np pain~*
written By Deeja One Love
Dedicated to madina m umarí ¼í¼¹
Sis nabeela allah ya baki lafiya yasa kaffara ne ameen.
73-74
Karfe biyu da rabi jirgin yayi landing a adamawa,salim ya Kira yace yazo ya dauke sure,sai da
suka biya suka gaishe da mai martaba sannan suka wuce gida.
Haidar ya Kira a waya ya gaya mishi sun sauka,sauran dangi kuwa salim ne ya Kira su ya gaya
musu.
Ita kam humaira a gajiya take,tun da tayi wanka ta kwanta bata Farka ba sai bayan la'asar,tana
tashi ta rama sallolin da ake binta tukunna sannan ta fara neman abinci,a dinning taga babban
leda tana budewa taga take away,murmushi tayi wato ya dawo kenan,tana gama ci ta koma
komawa barcin ta.
Farouk na shigowa da mamaki ya ke kallon ta yace"wannan bata gajiya da barci ne.
Sai washe gari sannan su sumayya duka suka zo Mata sannu da zuwa,yusra tace"allah ke
wannan irin kyau haka",amsar yarinyar dake hannun ta tayi tace"Kairat tayi girma(sunan hajiya
salma aka sawa yarinyar),husna tace"ai yarinyar Kamar ana Jan ta,dariya suka yi gaba d'aya.
Amsar ta hannun sumayya tayi tace"my takwara kin hadu,"dariya suka kwashe dashi haka suka
cigaba da firar su har su haidar suka dawo daga wajen aiki.
Sai da aka kawo musu abinci,salim yace"bro amma kai ka girka ko?"murmushi yayi ya daga
kai,haidar yace"shi yasa nace muku auren babbar mace yafi",faisal yace"wallahi yar shila
tafi",haidar yace"ba wani yar shila ga mai hankalin da zata kula da kai",salim yace"to matan
namu kenan su basu da hankali",nan fa husuma ta Tashi.
Farouk ya gallawa haidar harara yace"wai Ku baza Ku taba girma bane,anji kunya da yara da
komai amma har yanzu kuna kuruciya".
Faisal yayi dariya yace"wallahi Ku gyara Dan zaku haifo yara yan wrestling,su dinga kwasan
yan kallo.
Haka suka cigaba da firar su har suka kai bayan isha sannan kowanne ya dau matar shi suka
wuce gida.
A yanzu haka cikin humaira ya shiga wata Tara,
Yau suka shirya zasu kaiwa momma ziyara
,kowa a motar shi zai dauki matar shi,farouk na gaba sai haidar sai salim.
Suna isa momma ta rin ka farin ciki haka ma inna Mari da inna hadiza domin sun same su acan.
Sai da suka gaishe da su sannan suka fita,ita dai humaira barci ta kwanta.
Da yamma duka suna falo,mazajen suka shigo,shirmen dai su haidar suke yi wanda baya kare
musu.
Kusa da momma haidar yaje ya zauna,farouk kuwa humaira kawai ya nufi wajen ta,haka salim.
Sai da suka zauna suka huta sannan farouk yace"Ku tashi mu tafi kada dare yayi
mana",momma tace"ban gane ba ina zaku farin?",salim yace"adamawa mana momma,"tace"to
allah ya kiyaye hanya amma babu inda humaira za taje.
Da sauri farouk ya Kalle ta yace"haba momma ba muyi shirin barin ta ba fa",haidar yace"haba
kai kuwa idan mun tafi da ita zata wahala sosai",farouk yace"gaskiya bazan iya barin ta ba
haidar ta taso mu tafi kawai.
Inna hadiza da inna Mari babu wanda yace komai,
Momma ta numfasa tace"shikenan allah ta kiyaye hanya,har ta dauko hijab dinta,salim yace",ka
bar ta mana kaji".
Kallon ta yayi yace"shikenan koma ki zauna na rinka zuwa",kowa sai da yayi mamaki,momma
cikin dariya tace"gaskiya na kusa na fara kishi da kai salim,jifa nayi-nayi ya barta amma yaki,kai
kana magana ya kyaleta,dariya akayi duka.
Haidar ya tabe baki yace"ai ni da nayi magana momma nima bai saurare ni ba",farouk yace"ai
nima dana roke ka ka bar matar ka taje kaduna ta haihu kin barin ta kayi,salim kuwa ko
tambaya ta dalili beyi ba ya bar ta",juyawa yayi ya kalli momma yace"kinga laifi na Dan nafi jin
maganar salim?",girgiza kai tayi wato halin shi na riko yana nan.
Dariya salim yayi,haidar ya harare shi ya wuce ya ja matar shi ya fita,murmushi farouk yayi
sannan suka yi sallama suka wuce.
Da dare ciwo ya tashi humaira daga barci,cikin tsananin azaba ta fara tashin momma da yake
anan tare suka kwana.
Rudewa momma tayi ta fita da sauri ta taso daddy haka suka dauke ta sai hospital,daf da asuba
ta haihu,sai a lokacin hankalin momma ya kwanta sannan ta Kira su inna Mari ta gaya musu.
Kiran salim tayi tace"ka gawa dan uwan ka matar shi ta haihu namiji,ai da murna ya daga
sumayya cak yana juyi da ita.
Nan ya Kira farouk ya gaya mishi murna kam ba'a magana,kan kice me maganar humaira ta
haihu ya zaga ko'Ina a fadin adamawa harda kano da kaduna,kowa yaji sai yayi murna.
A ranar farouk ya juya shi da salim,haidar sai Washe gari sai suje shida faisal da ammar.
Suna isa garin suka Tarar da gidan cike kowa na kokarin daukar yaron,ganin anki miko musu
yasa ya takawa salim kafa.
Salim yace"momma a miko mana yaron mana,harara ta galla mishi tace"da yake kai ne Mara
kunya ko shi bazai iya magana ba shiyasa ya wakiltaka sannan duk nan ni ka raina shiyasa ni
kace na miko muku to bana da hannu.
Inna hadiza tace"a'a maman baby ya za kice haka mana duk wanda ya mika yaron ai bai yi laifi
ba",momma tace"amma me yasa bece umman su ba ko ke sai ni",dariya suka yi gaba
daya,sannan inna hadiza ta dauki yaron ta mika musu.
Da sauri duka suka mika hannu,farouk ya juya ya kalli momma ganin shi take kallo yasa yayi
saurin saukar da kan shi ya janye hannun shi,salim yasa hannu ya amsa.
Masha allah kawai ya furta domin yaron kyakkyawa dashi kamar farouk yayi kaki ya tofar,hudu
ba yayi mishi sannan ya mikawa farouk.
Amsa yayi jiki a sanyaye,idanu ya tsura mishi,gaskiya yaron kyakkyawa ne,murmushi yayi yana
dagowa suka hada ido da momma yayi saurin mikawa salim yaron yace "mai dashi mu tafi" .
Har sun mike inna hadiza tace"meye haka tun yanzu,salim ya tabe fuska yace"inna Dan allah
ba dole mu tafi ba tun dazu momma ke wa Dan uwa wani kallo wanda yasa duk ya tsargu ni
gani nake kamar laifi muka yi Mata ma kice tayi hakuri mun tafi.
Sai kuma jikin su duka yayi sanyi momma a ranta tace"wato yana sane kenan,wannan wane
kalan so ne suke wa juna.
Inna hadiza tace"a'a babu abinda kuka Mata Ku koma Ku zauna ko ganawa da matar ka baka yi
ba sannan kace ka tafi gashi ma baka gaya mana sunan yaron ba".
Juyawa yayi ya kalli salim yace"ai ban San wane suna salim yasa musu ba",salim yace"sunan
baffa ne fa wato adam",kowa yaji dadi shi kan shi farouk sunan daya ke so yasa wa yaron
kenan.
Humaira kuwa fitowar ta daga wanka kenan,duka fita su kayi suka bar ta da mijin ta,rungume ta
yayi yace"na gode teddy da wannan babyn da kika bani ban San me zan ce miki ba.
Murmushi tayi tace"nice da godiya kuma ni ya ka mata nayi farin ciki da samun ka a matsayin
miji na.
Sai yamma sannan suka bar taraba,Washe gari su haidar suka zo suma suka ga baby.
Sai ana gobe suna sannan farouk ya sami damar komawa domin har tana kayan da zasu saka
salim ya aika musu dashi akwati guda,da yaji labari murmushi kawai yayi.
Suma su sumayya ana gobe suna suka sami damar zuwa,yusra ta dauki yaron tace"masha
allah ya sunan shi ne?",humaira tace"sunan baffa aka saka",sumayya tayi saurin amshewa
tace"sai a rinka ce masa irfan",humaira tace"to.
*í ½í³‘FAROUK KO HAIDAR* í ½í³‘
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~í ½í²«í ½í²«í ½í²«*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~â„we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our
creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u
np pain~*
written By Deeja One Love
Dedicated to madeena m umarí ¼í¼¹
75-76
*Last page*
Ranar suna gidan cike yake da jama'a,ana ta hada hada.
Mai jigo kuwa ta hade cikin wata dakakkiyar shadda ruwan golden tayi mata masifar kyau,haka
uban gayya shima wankan shadda yayi sai da tashi sky blue ne(aradu ina so naga namiji yasa
sky blue).
Humaira ta shiga wannan ta fita wancan domin kaya dai ta gansu Dan daddy hamma akwati
biyu ya aiko mata da shi daya nata daya na baby haka ma mai martaba,daddyn yola da daddyn
kaduna ma duka sun taka rawar gani.
Suna dai masha allah komai waja-waja domin duk wani abu na ci dana bukata an samar dashi
wadatacce kowa yaci ya sha masha allah.
Satin ta biyu da haihuwa suka koma strike,wanda dole tasa ta komawa adamawa,amma
momma sai da ta hada ta da wata yarinya mai kula da irfan.
Watan irfan takwas amma sai kace Wanda yafi shekara yayi bulbul dashi,karatu kuma yanzu
babu kama hannu yaro domin tana samin kulawa sosai wajen farouk.
Shekarar irfan daya da wata bakwai humaira ta yaye shi,tana yaye shi farouk ya dauke shi ya
kai shi taraba,itama humairan hakan yafi Mata domin tana bukatar hutawa.
Farouk ya shigo ya Tarar da ita sai barci take kwasa,murmushi yayi domin ganin project take yi
amma barci ya dauke ta,dauke laptop din yayi ya karasa Mata.
Shida na yamma ya tashe ta,a gajiye ta tashi,sallah tayi kawai ta kwanta,shidai farouk be ce
Mata komai ba.
Yau allah da ikon shi humaira da sumayya an zama cikakkun gynecology,alhamdulillahi sun
fito da second class upper,duka har mutanen Zaria sun zo.
Dama aiki a hospital din su farouk za suyi.
Yau watan su daya da fara aiki,farouk ya bude kofa ya shiga office din humaira,tsabar aiki
humaira bata dago ba,kujera ya ja ya zauna sai da ta gama sannan ta dago ta kalle shi
tace"yadai meke damun ka,"ya mutsa fuska yayi yace"soyayyar ki mana.
Tashi tayi tazo ta zauna akan cinyar shi,hannun ta ta makalo ta wuyan shi ta fara aika mishi da
kiss.
Bude kofar akayi aka shigo,da sauri suka waiga,haidar yace"amma Ku akwai yan duniya kun
bar patients a waje kun zo kuna shan love ko?.
Dariya sukayi humaira tace"kai ma fa babu Wanda ya hanaka yin love din nan,".
Girgiza kai kawai yayi ya ajiye file din hannun shi yace"idan kin gama gashi sai Ki duba.
Wayar