Showing 72001 words to 72611 words out of 72611 words

Chapter 25 - farouk Ko haidar complete by one love.pdf

Advertisement

One Love   

23 Mar 2025

5838

farouk tayi Kara ganin kiran momma ne yasa yayi saurin dagawa,gaishe ta yayi kafin
tace"farouk Ku zo Ku dauki Dan Ku Dan ya ishe mu,farouk yayi murmushi yace"zan yiwa audu
waya zai zo ya dauke shi Dan mu aiki ya mana yawa,daga haka ya kashe wayar.



BAYAN SHEKARA TARA

Wata mota ce Ferrari fara ta tsaya a bakin harabar gidan,yarane guda uku suka bude motar
suka fito da gudu.
Bayan su wani Dan saurayi ne sai farouk daya riko mishi hannu.


Da sallama suka shiga gidan,a zaune suka sami humaira hannun ta rike da wata kyakkyawar
yarinya,su kuma wa'inda suka shigo suna kasa kowa na kokawa da leda.


Farouk yace"mama na kawo na bude Mimi,cikin sauri karamar yarinyar ta mike ta nufi wajen
shi.

Sallama salim yayi bayan shi sumayya ce sai yara guda biyar da suka biyo bayan su,da sauri
humaira ta mike tana cewa"oyoyo takwara ta,"harararta sumayya tayi tace"to ban zo da ita ba.


Cikin sauri tace"saboda?",saboda kin fi son ta akai na,dariya suka yi duka kafin salim yace"ke
kuma jealousy ko?.


Wasu yaran ne suka kuma shigo wa bayan su surayya ce,yau dai ziyara aka kawo mana kenan
ko?dariya a kayi gaba daya.


Salim yayi sallama ya shigo,bayan sun zauna suka cigaba da hada-hada,wata yarinya ce ta
shigo wacce ba zata wuce shekara goma sha hudu ba,ganin gidan a cike ta hade rai.


Farouk yayi murmushi yace"taho nan kinky,mikewa tayi a hankali taje. wajen shi,hannun shi ta
rike tayi murmushi tace"FAROUK KO HAIDAR?"

Sakin baki suka yi sumayya cikin zafin rai tace"uban ki ne,dariya suka yi suka ce"ai baki yi karya
ba,hannu ya mika mata suka tafa.


Murmushi haidar yayi yace"kuzo muyi selfie.
Duka matsawa sukayi.


Gefe na koma ina kallon ikon allah daga me tabe baki sai mai kwalalo idanu.


Dariya nayi nace"allah ya bar Ku tare masoya har abada.


Tammat bi hamdullahi.


Anan na kawo karshen littafi na mai suna
FAROUK KO HAIDAR.


Abin da nayi kuskure allah ka yafe mini.

Jinjina gare Ku kungiya daya tamkar da million GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION kun

cancanci yabo daga gareni baku kyamar bako haka baku wulakanta karamin marubuci Allah ka
Kara hade kanmu ameen

Jarumin admin din mu umar dalhat lallai ka cancanci yabo domin kana jajircewa wajen ganin
typing din mu ya tafi yadda ya ka mata
Allah ya baka mata ta gari da 'ya'ya wainda zasu ji tausayin ka yasa ka gama da iyayen ka
lafiya.ameen


Sister nabeela ubangiji allah ya baki lafiya yasa kaffara ne,group din sai yayi babu dadi da babu
ke a ciki yini daya kawai gaskiya muna missing dinki,fatan mu allah ya tashi kafadun ki.



Sardaunan gauraye kai ma ina godiya a gare ka bashier sufyein(lazy writer)kawai.



Godiya gareku
Aeeshat Adam(daughter)
Marakisiyya mustapha.
Amatul manan
Shamsiyya m magaji
Khadeeja duhu
Aisha yunusa
Maryam khamis
Fatima hussein
Dijency

Members of

Sardauna myth
Aunty fati hausa novels
Dandalin littattafan jarumai and hausa novels
Hausa novels a yau
Hafsat hausa h² novels

Da sauran wainda ban samu damar ambatar su ba duka ku sani one love na sanku kamar
yadda kuke sonta.


Ku kuma star boy umar da abubakar Ahmad na kusa aurar daku na huta ehe!

❤❤❤one love ❤❤for you guys and babs❤❤






Ramadan mufeeda in advance to all Muslim ummah all over d world.

Sai mun hadu bayan sallah idan muna da rai da lafiya.


*bye for now*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login