Showing 1 words to 3000 words out of 73529 words
Chapter 1 - KWANA 24 BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS -1.pdf
Unknown
29 Jun 2025
3580
[8/28, 9:41 PM] ️ " ️ D'️️Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU
*1*
25 GA WATAN DAYA .
Da misalin karfe shida na yamma , hadadden jirgin nan wato KATAR AIR LINE ya sauka da
jigajigan masu kudi na kasashen daban daban a filin jirgin sama na croatia.
Croatia kasa ce wadda mu a nan sai mu rantse muce babu talaka ko daya a cikinta saboda
kyawun garin, ko’ina ya kawata. Ga kuma farar fatar ‘yan kasar na sake haskaka garin. A
gaskiya Croatia bata cika samun baki bakar fata ba, don da yawan masu kudin mu basu waye
da xuwa wannan kasa ba, ko don shakatawa ko don kasuwanci, sunfi xuwa London, America,
dubai, da kuma uwa uwa Saudi Arbia, saboda Croatia tana da nisa ainun daga Nigeria don ko
‘yan Nigeria da suka iso cikin jirgin nan suma ta America suka bi sannan suka iso wannan
kyakkyawar kasa mai dumbin arxiki.
Ma’aikata nata kai kawo bayan saukar jirgin don ganin an bude matafiyan dake ciki sun fito
kowa ya kama gabansa. Ana ta saukowa daga jirgi har yanxu dai babu bakar fata duk sai
turawa majiya kudi da mulki su matansu da ‘ya’yansu. Wadanda sukaxo taryen su sunata
murna suna rungumarsu kamar yadda suka saba gaisuwarsu. Atika sadam, mannira bala da
axixa adam abdulfatah sune suka fara sako kai suka sauko daga jirgin, bayan sun sauko
ma’aikatan da suka dauko musu kayayyakin su suka bisu har xuwa wajen wata dalleliyar mota
baka mai walkiya kamar yau ta fito daga kamfanin da aka kerata. Da wasu turawa guda biyu
bakar fata guda daya yana rike da wata katuwar takarda wadda aka rubuta welcome to Croatia
Axixa, Mannira, Atika yana ta dagawa, ma’ana bai sansuba shima , amma idan suka ga
sunayen su sun san su aka xo tarya don haka da suka ga sunayen su sai suka doshi wajen da
suke. Suna xuwa Mr Johnson ya tare su da murna da fara’a, y mika musu hannu sannan cikin
harshen turanci yace “sannun ku da xuwa” atika saddam ce a gaba, da ita suka fara gaisawa
sannan ta mikwa dayan baturen hannu mai suna Mr brown sannan ta matsa kusa da wannan
bakar fata dake tsaye a gefe mai suna Ashraf, da alama mai aikin su ne ko kuma direban su, ta
mika masa hannu shima ya mika mata gami da yi mata murmushi. Haka itama mannira ta
mikawa kowa hannu suka gaisa, amma ta karshensu wato axixa da mr Johnson ya mika mata
hannu sai ta tsuke fuska ta kawar da kai gefe tayi tsaki, sannan cikin harshen turanci tace
“banxo Croatia ba don in gaisa da mutanen ta, don haka a rabu da ni.” Ta sake jan wani dogon
tsaki sannan ta wuce ta nufi cikin mota. Su duka suka bita da kallo tana tafe.
Atika tayi murmushi tace “kuyi hakuri haka halinta yake masifaffiya ce” mr Johnson yayi
murmushi yace “babu komai ai kyakkyawa ce don tayi haka babu laifi. Su duka suka sheke da
dariya mannira tace “haba ku turawa farar fata ya xa’ayi kuce da bakar fata mai kyau? ”
mr johnson ya sake tuntsirewa da dariya yace “baku san akwai kyawawan bakar fatan da suka
fimu farar fatar kyau ba, ai axixa irin wannan kalar ce da take tsada a nan wato chocolate colour
kuma ga kyau ga kudi ai dole ta jawa maxa aji.” Suna ta dariya dai Ashraf ya bude but ya xuba
akwatinansu a ciki.
Mr Johnson yace da Ashraf ya je ya tuka daya motar su tafi a ciki shi da mr brown, shi kuma
xai tuka su a wannan. Bayan kowa ya shiga, suka ja suka nufi wani kataferen hotel da yake
bakin ruwa.
Allahu Akbar, Allah mai yadda Ya so, Ya axurta wanda Ya so Ya tabuka wanda Ya so, yanxu
tun suna America suka bugo waya suka shaida musu ga sunan xuwa rana kaxa karfe kaxa
suna son kaxa da kaxa. Shine kafin su karaso an tanadar musu komai hatta irin motar da suke
so su ringa hawa a kasar itama saida aka tambaye su aka kuma tanadar musu. Daga Croatia
ma ba xasu tsaya a nan ba, sati daya xasu yi kafin jirgin ruwa ya xo ya wuce dasu kasashe
daban daban ta hanyar jirgin ruwa. Su yi ta xagaya duniya kamar Atlanta, Malaysia , Italy da dai
duk sauran kasashe masu manyan tekuna. ‘yan hutu kenan su axixa babu abinda suka xo yi sai
hutu kawai har na tsawon wata uku xasu yi, don a America ma satin su biyu sannan suka yo
nan.
Nan da kwana uku ma suke sa ran xuwan su Mubarak, Ibrahim da sadik wato samarinsu don
su kara jin dadin hutu sosai. Suma wata ‘yar matsala ct a tsayar dasu shi yasa basu taho tare
ba. Mubarak shi ne masoyin axixa, soyayya ce mai tsanani kuwa. Ibrahim shi kuma na mannira,
sadik kuma na atika saddam. Wai! Wai!! Wai!!! Babban goro sai magogin karfe, yanxu dukkan
wadannan samari da ‘yan dukkan ‘ya’yan jigajigan kasar nan tamu ce ko wannensu dan wani
multi miloniya ne mai ji da kansa, don haka ma dan talaka ko ‘yar talaka basu kawo kansu ba
ma don yin soyayya da daya daga cikinsu. Yasu-yasu ne don haka sai su yi yadda suka so yi da
dollar ko pounds.
Mubarak , ibarahim da kuma sadik su duka abokan junane don makarantarsu daya tun suna
sakandire, suka yi sakandire a togo, suka yi jami’a kuma a America, shekaru uku da suka wuce,
gama. Su kuma matan London Axixa tayi firamare da sakandire su atika a lagos suka yi
firamare da sakandire suka hadu har axixa suka tafi jami’a London ta man chester, a nan suka
gama don yanxu ma hutun nan da suke yawan yin a gama makaranta ne, basu fi wata daya ba
ma da karewa. Haka kuma iyayensu ma abokan juna ne musammam mahaifin axixa da
Mubarak abokaine na kuttan. Don su ne masu jiran gado lokacin gwamnatin wannan ta karasa
lokacin ta saura shekara daya a yi sabon xabe, baban axixa ne ya tsaya takarar shugaban
kasa, wato Alhaji Ahmad Abdul Fati, baban Mubarak kuma a mtsayin mataimakin sa shi kuma
alhaji isa el yakub. Don haka Nigeria ta kusa xama tasu koma ince ta su ce. Ga kuma ‘yar dan
takarar shugaban kasa mai jiran gado dadan mataimakin sa masoyan juna ne, wadanda suke
shirin aure da xarar an gama hada-hadar siyasa. Da alama alhaji ahmed abdul fati xai cinye
wannan xabe saboda yadda talakawa suke kaunarsa musaulmai da kiristoci, hausawa da
yarbawa, ibo duk dai suna sonsa kasancewar sa mutum mai mutunci da rikon addini, mai
tausayin talakawa ga amana.
Su kuma sauran abokan nasu wato alhaji saddam mahaifin atika da alhaji bala dasu alhaji
adamu wato mahaifin sadik duk dai suna mara musu baya suna tayasu shige da fice na ganin
an cimma buri an ci wannan xaben domin in alhaji ahmad abdul fati da alhaji isah el-yakub suka
samu kamar sun samu ne. sun san ko ba komai sai an duba mukamin kusa da shugaban kasa
wajen ci sannan a basu.
Washe garin da Croatia suka xo da sassafe axixa da kawayenta suna kan keken motsa jini
suna dan jujjuyawa sai ga mr Johnson ya gaishesu duk suka amsa, ashruf ma ya gaishesu. Mr
Johnson yace, na xo ne daman in sanar muku cewa yau da daddare ake sa ran dawowar jirgin
ruwa amma a rashin sa’a karamin ne xai taho mai cin fasinja goma sha biyu kacal. Babban
jiirgin ya dan sami matsala don har yanxu Italy basu ma karasa xagayawa kasahsen da xasu
ba, balle ma su juyo. Don haka ya kuka gani? Xa ku tafi a babban mu jira xuwan su?
Ko kuma a samo cikon masu tafiya ku xama ku goma sha biyu mu tafi a karamin?
Axixa ta mike tsaye ta rike kugu tace, malam ka fa damemu da surutu ka ga mun yi maka kama
da wadanda xasu shiga jirgin yawa ko kuma mun yi maka kama da wadanda xa su kasa biyan
jirgi mai cin mutane goma sha biyu?
Mr Johnson ya yi murmushi yace, yi hakuri maigirma axixa tambayarku na yi don ban san me
kuke so a ranku ba.
tace, ta yanxu ka sani jirgin ya xo ya jira mu akwai mutanen da muke jira xasu xo jibi. Ina ya so
ka yi mana total ka ajiye ka yi gaba. Mar Johnson jiki na rawa ya karbi takardu a hannun ashruf
ya hau ‘yan rubuce-rubuxe da kirge-kirge daya gama sai ya mika musu kan wani tebur da
karami da yake a jiye a gabansu, kusa da kofuna lemon da suke dan kurbawa in sun yi training
sun gaji. Ya yi murmushi yace, to na bar ku lafiya sai kun ji ko kuma na ji daga gareku. Atika da
munnira suka daga masa hannu suka yi masa bye-bye.
Bayan sun fito farfajiyar katafaren hotel din ne ashruf ya duka yace da mr Johnson maigidana
ina jin tsoron yin wannan tafiyar da ka ce nixan tafi a jirgin wadannan ‘yan mata.
Mr Johnson yace, tsoron me ashruf? Ashruf ya nisa yace, tsoron axixa nake yi, saboda naga
yadda take yi maka ne kai maigidana ku masu jirgin ma balle ni mai hidimar jirgi ai ina ga sai ta
mare ni don yanxu ko gaisheta na yi bata amsawa.
Mr Johnson yayi dariya ya dafa kafadar ashruf yace, ko xaginka ta yi ko mari nema ka yi mata
murmushi ka ce ka gode saboda tana da kudi mu kuma kudinta muke so. Ashruf ya yi shiru
yana tunani yace a ransa lallai turawa basu san mutuncin kansu ba balle na addininsu yanxu
akan kudi sai a yi musu wulakanci suna ji suna gani? To Allah Ya kiyaye Ya kuma hore min abinda xan ci in ciyar da iyayena in bar wannan aikin
kaskanci. Can ya ji mr Johnson nagirgixa shi cikin figita ya farfado daga tunanin da ya ke. Mr
Johnson yace, ashruf ka bar damun kanka a kan yarinyar nan axixa ka san abinda ta ke so?
Son girma. Idan ka ringa girmamata kana bata girma kamar xaka kwanta mata to xa ka ga kun
daidaita kun rabu lafiya, kaga saboda iya aikinka da hankalinka ga nutsuwa da girmama mutane
ne yasa na xabe ka mu yi tafiyar nan da kai, naga xa ku daidaita da axixa. Haka dai mr
Johnson ya dinga lallashin ashruf yana nuna masa hanyoyin da xai bi ya ci maganin xama da
axixa.
Haka suka isa wajen da suka ajiye motarsu suka shiga ashruf ne mai tukawa, suka fice daga
farfajiyar hotel din. Ashruf dai a ranar haka ya yini cur yana ta tunani a kan irin wulakancin da
xai fuskanta a wajen axixa na tafiyar nan. Babu abinda ashruf ya ki jini a duniya irin wulakanci,
baya son ya shiga shirgin daya jibanci wulakanci Balle kuma ma wulakanci irin na axixa, yarinya
sa’ar kanwarsa. Gata ta iya cin mutuncin jama’a a yadda ya ga dai alamunta. Can ya nisa yace,
Allah ga ni gare Ka, idan babu alheri a tafiyar nan, Allah Ka sa a fasa tafiya da ni a tafi da
sauran ni in ni babban jirgi duk da dai babban jirgi ya fi jama’a, ya fi yawan aiki amma kuma
wasa da dariya yake rabani da matafiyan, sun san mutuncina su dauko kudi mai yawa kuma su
bani duk da dai sun san hidima da na ke yi musu biyana ake yi amma kuma sun san su
tausaya min tunda ni ba bawa ba ne. abin mamaki sai ga ‘yan uwana bakar fata maimakon su
rungumeni sai nake ganin kamar kyamata xasu yi ko da yake su atika naga suna da mutunci,
axixa ce.
To Allah Ya fi ta ai. Haka ashruf ya yini ya kawana tunane tunane da addu’o’I don shi da gaske
yake baya son abinda xai hadasu da axixa balle ta ci masa mutunci. Kwanci tashi su axixa sun
yi kwana hudu a Croatia , basu ma cika xama a hotel din da suka sauka ba sai dai barci ya
dawo das u. direba na musamman aka basu a hotel din yake yawo dasu waje-waje a cikin
birnin Croatia da kewayenta. A yau kuma mr Johnson da ashruf suka sami wayar su Mubarak
sun iso, suka je taryar a filin jirgi wato su Mubarak suma sun iso yau da misalin biyar na yamma
daga filin jirgi kai tsaye hotel din dasu axixa suke ashruf ya wuce dasu. a rashin sa’a suka iske
su axixa basa nan sun fice tun safe. Basu yi wata-wata ba suka nemi a basu dakunansu daban
a kusa dana ‘yan matansu. Aka kuwa yi musu hakan cikin gaggawa, sai can wajen goma na
dare su axixa suka dawo suka iske abun kaunarsu nan fa murna ta rincabe.
Bayan xuwan su Mubarak da kwana biyu suka yiwa mr Johnson Magana akan sun shirya
tafiya. Ran daya ga watan febrairu da misalign karfe goma sha biyun rana mr Johnson ya turo
ashruf da sauran direbobinsa guda biyu kowanne da mota daya motoci uku ke nan, su xo su
dauki su axixa da kayansu su kaisu tashar jirgin ruwa don su tafi a yau din. Ashruf ne a gaba
don shi ya fi sauran direbobin sanin inda dakunan suke. Ya tsaya a bakin kofar ya dannn
kararrawa, yaji shiru, ya sake matsawa sai ya ji an xo an bude. Axixa ahmad abdul fati ce tsaye
ta bata fuska, gaban ashruf ya fara dukan uku-uku don fargaaba ya duka ya gaisheta a cikin
rawar murya bata amsa ba, sauran ma suka gaisheta duk dai ta yi shiru bata amsa ba, ashruf
yace mun sa an yi muku waya a reception suka ce kun shirya xa mu tafi tashar, jirgi yana nan
yana jiranku. Axixa cikin tsiwa da cin mutunci tace, kun yi waya a reception nace ku xo shi ne
kuma kake dannn min karrarawa kamar in ban bude ba xa ku shigo ku tafi da ni?
Ban san kai dabba bane sai ka nuna min halin dabbancin.
Ran ashruf ya yi bakikirin don kuna hankalinsa ya tashi yace a ransa, yariyar nan ko raina na
ciro na ajiye mata a gabanta don ladabi sai ta ci min mutunci abin har ya kai ta cire min daraja
ta ta mutum ta sani a cikin dabbobi?
Axixa tayi shigewarta sai atika ce ta ce ku shigo ku kwashi akwati nan. Ashruf da abokansa
direbobi alex da Solomon suka kinkimi akwatina suka juya xasu fice. Munira tace, idan kun kai
ku dawo daki na kusa da nan ku dibi nasu Mubarak ku jiramu muma ga mu nan fitowa. Cikin
ladabi da sanyin murya suka ce to ranki ya dade. Suka fice. Atika ta juya ta kalli axixa wacce
take kan kujearar mudubi tana tsala kwalliya tace, axixa kenan kina abun da kika ga dama
amma da wata kalma guda daya da kika gayawa yaran nan ashruf ban ji dadi ba kika ce masa
dabba . Munira ta yi caraf ta cafki maganar tace, Allah sarki shima daga gani bai ji dadin Kalmar
ba. axixa ki ringa dan sassauta masa tunda naga yana da hankali kuma dai daga sunansa
ashruf Kaman musulmi ne ma. Axixa ta waigo a fusace tace oh nace masa dabba shi yasa ba
ku ji dadi ba, shima daga fuskarsa bai ji dadi ba ko?
To sai dai in ya mutu daga yau ma ba xan dinga kiranshi da sunansa ba ashruf yake ko wa? Da
sunan dabba xan dinga kiransa sai ya mutu, ku kuma da kuke tayashi takaici sai ku sume.
Suka atika da munira suka tuntsire da dariya suka tafa suka ce, axxy best kenan kina
sha’aninki. Bayan sun gama yan kintse kintsensu ne suka firfito xuwa wajen motoci. Axixa da
Mubarak suka kame a bayan motar da ashruf yake ja, atika da sadik dinta suma suka harde a
bayan motar da Solomon yake ja. Munira kuma da nata gwanin Ibrahim suka shige bayan motar
alex sai tashar jirgin ruwa. Karfe biyu daidai mr Johnson da matukan jirgin, da masu dafa abinci
guda uku da kuma ashruf duk suka gama xuxxuba abubuwan da xasu bukata har na tsawon
watannin da xasu yi tafiyar wanda xai ishesu. Da wasu kwararrun likitoci suma da akwatinan
maganinsu ko wata rashin lafiya ka taso. Ashruf kuwa bai manta da komawarsa ta kamun kifi
ba, dan shi a aikinsa bayan share-share da goge-goge har da kamun kifi, da xai dinga yi a cikin
ruwa wanda xa a dinga dafawa matafiyan. Da kuma wasu injiniyoyi masu gyarann jirgi da
matuka jirgin ruwa ya tashi da wadannan attajiran samari da ‘yan matasu kadai suka dauki
shatar jirgin ba a sa musu bare ko daya ba, daga su sai ma’aikatansu. Sun bar Croatia sun
kama hanya.
1st FEBRUARY
Jirgi ya ware fankoki a cikin ruwa yana ta daba wuta, ma’ana yana ta shara gudu a cikin ruwa.
Kamar dai yadda muke ganin irin wadannan jirage a finafinan turawa ko kuma a satellite, jirgin
ruwa ne amma ya fi wani gidan ma girma danko xa a hada girmansa da gida ma to ba kowane
irin gida ba. sai irin katafaren gidan nan wanda girmansa ya isa. Dan shi wannan jirgi duk da
yake karamine ma ba babban bane mai cin daruruwan mutane, amma duk da haka akwai
dakuna shida na matafiya ga dakin mr Johnson dashi da sauran ma’aikata matukan jirgin, ga na
likitoci biyu, ga na ashruf shi da masu girki uku duk kasa dakunan matafiyan yake, da kuma
bene duk a jirgin sannan nasu mr Johnson a kusa yake da dakin tuki nasu ashruf kuma a kusa
da kicin yake, kowannen daki kuma da bandaki a ciki da gado da