Showing 60001 words to 63000 words out of 73529 words
Chapter 21 - KWANA 24 BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS -1.pdf
Unknown
29 Jun 2025
3602
ace ‘’har ya did dr. rislan naki haba aziza doctor fa’’.
Aziza t ace ‘’gaskiya tislan ma dan gida na ne ya za ayi kenan?”
Munnira ta zo gaban aziza dake zaune a gefen gado ta zauna ta rike hannuta t ace ‘’kince
barista hayat yana da matukar kirki, ga tausayi yana burgeki kuma d azan kulashi da na kyauta
miki ko?”
Aziza ta yi murmushi ta ce ‘’haka nace saboda yana da nutsuwa gashi handsome mai kyau da
zan kulashi da shi amma fa ba ruwan karki cewa dr. rislan nina sa ki kula shi’’. Munnira t ace
‘’atika kece shaida kina jin wannan yabon barista da aziza ke yi ko? To barista hayat tun ranar
da akayi miki tiyata ya sami labara ya zo gidanmu ya sameni ya ce inyi miki sannu, idan kin
warke in isar masa da sakonsa yana matukar sonki, kina burgeshi kina da matukar kiriki gaki da
tausayi gaki very beautiful mai kyau dake’’. Su duka suka tuntsire da dariya har anti sharifa da
take kan abin salla tana jan carbi tana kallonsu said a munnira ta bata dariya.
Aziza t ace ‘’tukashi ashe barista zai sha magiya har makogoransa ya tsage. Baya iya surutu ba
irin nasu na lauyoyi to sai y gaji da rokona don har abada b azan soshi ba’’.
Munnira Ta ce ‘’haba aziza meye laifinsa bayan ke kika yabe shi yanzun nan. A kotu ya hadu da
ni dazu n ace karfe biyu yazo nan gidan mu hadu gaki gashi gani kuma. Na bashi lambar waya
ta n ace ya kirani idan ya zo Danni tunda ya bani sakon na kasa gaya miki gara ya zo kotu
hadu’’. Anty sharifa ta ce ‘’aziza tashi kema ki shirya ki fita gunsa ba a haka ke baa bin kunya ba ne
ace babbe dake baki iya tsayawa saurayi, kalli kawayenki yada suke yiwa samarinsu kwalliya”.
Atika da munnira suka kyalkyale dariya aziza ta cika tayi fum kamar zata fashe ta suri gyale ta
fita atika da munnira suna biye da ita har fargajiyar gidan. Dr. rislan d barista hayat sun hadu a
jikin motar barista hayat sunna gaisuwa dake sun san juna sukan hadu daman annan gidan a
lockacin case din nan na aziza Mahmud sa’ad shi da bai sansu ba yana zaune a motarsa yana
jin kida a rediyo. Fitowar ‘yan matan nan guda uku shi ne ya haske musu ido, kamshi ya daki
hacinsu su dukkansu suka dago kowanne indanuwansa ya dira akan wacce yake muradi. Sai
murmushi n bata mayar masa ba. Bayan aziza ta gaisa dad r. rislan da tsaye tayi dan murmushi
dakyar, sannan ta gaisheshi. Atika da munnira suka ha samarinsu izuwa cikin katafaren labun
da yeke daga bayan gidan don karawa hirar soyayyarsu armahi. Saman sun gayawa masu aiki
s kaiwa bakinsu lemuna da kayan marmari. Masu aiki ne suke wucewa da farnatai an yayyanka
a barba, mangoro, lemon bawo, gwanda, kankana, tufa {apple} kayan marmari dai kala kala.
Aziza ta bisu da kallo babu abinda take tunowa a ziciyarta sai dama ace ashruf yana nan suma
su wuce da masayansu. Lambun nan ya dau sanyi zaiyi dadin zama saboda kwalla ranar da
ake yau garin zafi kau.
Barista hayat ne ya katse mata tunaniunta ya ce ‘’malama aziza naji dadin ganinki na godewa
allah na godewa munnira da ta isar min da sokona izuwa wajen wata wacce tayi fintinkau bazan
iya isar da sakon da kaina ba’’. Ta yatsune fuska kadan sannan ta nisa t ace ‘’barista hayat
moh’d munnira ta isar da sakonka gareni naji dadi na gode kace kana sona amma kayi hakuri
soyayya bata gabana bawai dakai bane bazan yiba a a ita kanta soyayyar ce bana so da kowa
ma saboda wasu dalilai da suke surri ne a zuciyata. Kayi hakuri barista kayimin halacci a
rayuwata bazan manta da kokarin da ka yi mana ba a wahen shari’ar da muka yi nagode sai
anjima’’.
Barista hayat ya ji wata mummunar faduwar gaba da jin kalaman aziza nana da nan ya gigice
ya hau dogo turanci akan ta tsaya ya yi mata bayani ta ce ya yi hakuri ba zata iya tsayawa ba
taji wani bayaninsa ta wuce zuwa cikin gida yayi tsaye yena kallonta kuka ne kawai bai rusa ba
saboda ya samu ba. Alhaji ahmed yana tsaye a wundon dakinsa yana kallonsu ya sauko da
sauri ya tari azziza gashi bai kallonsu ya sauko da sauri ya tari azziza a babban falo tana
tambayarta. Ya ce ‘’ azziza barista hayat na gano a waje kuna tsaye meke faruwa?”
Ta ce ‘’daddy babbu komai zuwa ya yi ya mun ya jiki”.
Alhaji ahmed ya ce “a ‘a aziza a fusace naga kin juyo yana binki yana rokarki gaya min
gaskiya”.
Ya ce “ke kuma baki sonsa ko? Bakya son mai sonki aziza haka ake rayuwa? Ina tsaye a
window naga rislan da munnira naga atika da wani yaro duk sun zabi kamillalu suna can sunna
far’a amma ke kin shawa naki kamilallen kunu kina yi masa fada. Aziza komai ya wuce yanzu
lokaci ne daya kamata ki nutsu [9/12, 5:32 PM] ️ " ️ D'️️Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK
WHATSAPP 08064400100_
[9/12, 5:33 PM] ️ " ️ D'️️Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU PT4
*28*
Ashruf ma kince kin daina sonsa ba za ki aure shi ba, Barista Hayat ma kince bakya sonsa mai
yasa zaki kishi?”
Aziza ta yi narai narai da ido kamar zata fashe da kuka ta ce “Dady ciki fa nayi wazai aure ni da
daraja?” Ta fashe da kuka. Alhaji Ahmed ya daga kanta ya ce” Daina kuka Aziza ya isa ciki
kaddara ce daga Allah (S.W.T) ki daina damuwa saurayi yake auren bazawara ma ai babbar
sunna ce balle ke baki yi auren fari ba ma. Don haka nafi son ki auri Ashruf tunda yafi kowa
sanin ya ya aka yi”. Ya yi mamaki da yaga Aziza tana da murmushi ya ce “Aziza ko ba haka
ba?” Ta dinga murtsike ido kamar mai goge hawaye kamar mai jin kunya. Ya ci gaba da cewa
“Kefa da kanki kika fadamin a Italy yanzu Ashruf kike so harma kuka yi shirin guduwa yanzu
kuma kika ce mana kin fasa”.
Aziza ta ce “Dady Ashruf fa ya tafi ba dawowa zai yi ba”.
Ya ce “Waye ya fada maiki? Ko dazu munyi magana da shi da zarar ya sami biza zaizo saboda
iyayensa ma ba za mu barsu su koma Jamaika ba sunzo gida kenan kinga Asharuf dole zai zo”.
Da yariya ta kyalkyale don dadi, dadi ya rufe mahaifinta yayi dariya ya ce “Ja’ira ashe kina
sonsa kika ce kin fasa aurensa”. Ta tashi aguje ta hau bene tana dariya.
A ranar da daddare Aziza kwana suka yi da Anty Sharifa suna hirar rayuwa Anti Sharifa ta bawa
Aziza kwana suka yi da Anty Sarifa gwagwarmayar rayuwarta kakaf. Ta ce “Tayi digiri a Gemany
tayi Doctoring Degree a India tana koyarwa a wata jami’a kake babban birnin India. Da
maigidanta ya rasu sai ta daina ta tafi Saudia ta zauna. Tana fada tana hawaye. Aziza ta
zaiyane mata itama nata labain Anti sharifa tace “Allah ya nuna min kina cikin wani hali a
mafarkai na hakan ne ma ya taso dani na taho inzo in ganki”. Anti Sharifa tace Sati uku zata yi
anan ta tafi Guru garinsu tayi wata biyu ta wuce Maiduguri garin mijinta tayi wata saita koma
Saudia don ba ba za ta iya zama a Nigeria ba. Aziza tace ai kuwa ba za ta bar Anty Sharifa ta
koma Saudia ba taza kenan kafarta kafarta zata rakata Guru da Maiduguri suje su dawo. Anti
Sharifa a gidansu zata zauna.
Anti Sharifa tayi dariya tace “Yarinta ce take damunki Aziza yaushe zanzo in zauna anan gidan
bayan ‘yar uwata bata nan kuma kema aure zaki yi ki tafi ki barni. Daga karshe Anti Sharifa ta
bata shawarar akan tayi hakuri ta auri Ashruf. Ita tafi yi mata sha’awar sa, suka yi addu’ar Allah
ya zabar musu mafi alheri. A daren ne kuma jikin Hajiya Fatima mahaifyar Ashruf ya rikice. Tana ta surutai tana kokarin fita
da gudu an bata maganin tasha amma taki yin barci. Ashruf ma a lokacin ya bugo waya yaji
muryar mahaifiyarsa sai ya fashe da kuka kawai yaji kuma hankalinsa ya jiyo Nigeria yazo ya
ganta. Ba shiri Alhaij Ahmed ya buga waya wani asibitin mahaukata mai zaman kansa dake nan
Abuja a kazo da mota aka saka ta, mijinta ya so a tafi da shi don ya yi zaman jinyrarta aka ce
ba a zaman jinya a asibiti. Asibitin akwai kwararrun likitoci na kwakwalwa daga kasashen
turawa daban daban aka daukosu sai dai akwai kudi. Wannan ba wata mtsala ba ce a wajen
Alhaji Ahmed Abdulfathi ya biya kudin komai da zasu bukata har da saura, daga karshe yaba
mijinta hakuri kada ya damu suci gaba da yi mata addu’ar Allah ubangiji ya bata sauki.
Bayan an kwana biyu da yin haka Maman Atika cikin sirri ba tare da kowa yasan abinda yke
tsakaninta da Aziza ba game da Ashruf ta nemo lambar wayar Ashruf a wayar maigidanta. Sai
da ta tabbatar babu kowa a gidan sannan ta rufe kanta a daki ta bugawa Ashruf waya da
misalin karfe takwas na dare. Bata sha wuya sosai ba wayar ta shiga. Ashruf a zaune yake a
bakin wata kwata a kofar gidansu. Yana kallon samari rungume da ‘yan matansu zasu fita
shakatawa gidajen rawa ko hotels, ko wasu parties da ake hada casu su sha giya ayi shakiyanci
kasancewar rikakkun arna sunfi yawa a kasar Jamaika babu ruwansu da shari’ar musulunci. Ya
ji wayarsa ta yi kara ba tare da ya duba lambar ba ya tsinke wayar saboda baya so ya amsa a
tunaninsa Mariah ce wata budurwa data ganshi a filin jirgi take ta binsa wai tana sonsa. Ya sha
mamakin yadda akayi ta sami lambar wayarsa, kullum sai ta kirashi shi kuwa tinani da takaici ya
dame shi iri iri. Ga mahaifiyarsa a asibiti a Nigeria gashi ya kasa zuwa Nigeria saboda fargabar
yaga Aziza kuma ba damar ya aureta. Babansa ya fara fada masa irin shawarar da su Alhaji
Ahamed suka yanke masa cewar yayi zamansa da iyalinsa a Nigeria kawai. To amma Ashruf
baice komai ba dai tukunna a zuciyarsa dai yasan ba zai yiwu ba ne kawai saboda shi ba zai iya
zama a Nigeira ba yaga masoyiyarsa Aziza tana auren wani ba shi ba, kuma ba zai iya rabuwa
da iyayensa ba da sai suyi yamansu a nigeria shi kuma ya zabi wata kasar ya darje yaje ya
zauna. Wayar ta sake shigowa a fusace Ashruf ya cirota daga aljihunsa ya kalli lambar sai yaga
wata bakuwar lamba amma code din Nigeria ce. Ba tare da ya kara sakon daya ba sai ya
danna. Muryar wata kamilar mata yaji tayi masa sallama ya amsa cikin ladabi babu wacce
zuciyarsa ta kawo dama itace sai Azizarsa ya ce a ransa “Yau da ace Aziza ce ta kirani da
kwana zanyi sallah ina godiya ga Allah, amma kash yaji ba muryarta ba ce. Ta ce “Ashraf ne”.
yace “Nine wacece ke magana”.
Ta ce “Hajiya Rabi’a ce Maman Atika Sadam daga Nigeria”.
Bai san sanda ya zabura ya mike tsaye ba don mamaki ya duka duk da a waya ne ya gaisheta.
Ta amsa ta kuma yi masa congratulation akan shari’ar da aka fafata da mahaifinsa kuma ya ci
galaba sannan tayiwa mahaifiyarsa kuma ya ci galaba sannan tayiwa mahaifiyarsa fatan Allah
ya bata lafiya a can asibiti. Ta kuma ce masa ya kwantar da hankalinsa sunje dazu sun dubota
tana ta bacci jikin yana sauki. Ashruf ya yi dariya ya yi godiya ya nuna farin cikinsa kwarai da
gaske. Ta ce “Daman na bugo maka ne inji lafiya ba ka zo ba ance biza ka rasa amma ni nasan
ba biza bace ta hana ka zuwa har yau, ba wani ya fadamin ba sai ni nayi tunanin haka saboda
ina wajen a lokacin da kuka yi waya da Aziza cikin fushi tace idan ka tafi karka dawo ina fatan
ba za ka boye min ba wannan shine dalilika ko? Tsakaninka da Allah kuma zaka fadamin”.
Ashruf yayi dan murmushin dadi yace “Mama wannan n dalilina”. Tace “Nifa nasan shi ne dalilin,
abinda nake so in gaya maka shine ka kwantar da hankalinka kazo Nigeria idan ka gamu da
Aziza ku gaisa kada kayi dar ko ka nuna mata wani abu ya taba faruwa a tsakaninku kaji ko? Ni
zan tsaya maka zan kuma shawo maka kanta kafinka karaso haba Ashruf soyayya fa kake.
Fargaba do tsoro ba naka bane. Kaine fa namiji faduwar gaba a wajen yai ba taka bace balle
yakin neman aure”. Asharuf ya yi dariya sake kyalkyalewa da dariyar dadi yace “Nagode
madalla Mama, wallahi jiya na sami biza harna je filin jirgi na fasa tafiyar saboda fargabar kada
inzo Nigeria ga Aziza amma ta gagareni. In Allah ya yarda jibi zanbi jirgin da zaije Amerika daga
nan Jamika. Gata Jirgi daga Amerika zai je Nigeria a takaice dai nan da kwana hudu zan iso
Nigeria insha Allah. Ya kara godiya gami da shi albarka iri iri suka yi sallama ta kashe waya.
Maman Atika taji dadi sosai Ashruf ya linkata jin dadi nan da nan ya fada cikin gida ya hau
shirye shiryen tafiya. Babu wanda Maman Atika ta fadawa cewar sunyi waya da Ashruf yace
zaizo nan da kwana hudu tafi so a ganshi kwatsam don tayi surprising din Aziza.
Bayan yin wayarsu da kwana uku Aziza ta kawowa Maman Atika Anti Sharifa su gaisa da gaisa
yadda ta fara kaita gidansu Munnaira suka gaisa da Ummar Munnira, Anti Sharifa tayi musu
godiya bisa kulawa da suke yiwa ‘yar marainiyar ‘yarta Aziza suka ce babu komai Aziza ai
‘yarsu ce. Kafin su Aziza su baro gidan su Atika sai kusn goma na dare Aziza tasa Maman Atika
a gaba tana ta yi mata Zancen Ashruf a hankali ba tare da Anti sharifa da su Atika ba sun ji me
suke cewa. Maman Atika ta ce da Aziza kada ta damu insha Allahu komai zaiyi dai dai Ashruf
kuma ba zai ki zuwa ba dole zaizo duk daren dadewa. Washegari da misalin bakwai da rabi na
dare Aziza na kwance akan cinyar Anti sharifa tana daukar darasai game da yadda ake rikita
miji yadda zaka ga miji y8ana son matarasa har wasu suyi tunanin ko asiri tayi masa nan kuwa
tsabar kulawar da take yi masa taga maman Atike ce ta matsa da sauri ta ce “Hello Mamain
yimi”
Mama ta ce “Lafiya Azizav zo kiga kawarki Atike tana wani abu da ya bani mamaki” Aziza ta
zabura ta tashi zaune tace “Mama me take yi Atikar” Tace “ ki zo dai ki gani da kanki ki tayani
dariya ki fadawa dady in nake kiranki kar yaga kin fitra da daddare” Aziza ta mike da sauri ta
zari mukullin mota tace da Anti sahrifa “ anty maman atika na nemana ki gayawa dady idan ya
fito suna falo shi ‘yan siyaasa suna meetin nasan zasu dade basu fito ba “anty sharifa ta ce “To
rungumeta ta su nbace ta a kumatu suka kyalkyale da dariya su duka. Aziza ta fita kai tsaye
cikin motarta ta shia ta figa sai maitama lake chad street inguwar su Atika. Bata tsaya a ko ina
ba sai a cikin farfajiyar gidan. Ta fito daga mota ta shiga ciki a babban falo ta iske Tanim kanin
Atika ta ce “Tanim ina Atika” Ya ce “ Anty ati ta fita unguwa” Tace “Mama fa ?” yace tana falonta
“ Aziza ta wuce kai tsaye cikin falon.
Wai! Wai!! Wai!!! Wata farar fuska ta gani mai kyan gaske ga kwarjin da wasu kayatattun
idanuwa dara dara suka dago da sauri ksuka kalleta. Ashruf Elmustapha ne zaune a falon shi
kadai ga jakar kayansa a kusa da shi daga gani yanzu ya shigo kasar. Ta tsaya cak tan kallonsa
sai dai wannan karon kallon da suke fuskarsu cike da murmushi dukaninsu. Ta shigo a sanyaye
kan ta a sunkuye a kasa gami da yin sallama a gareshi, ya amsa mata cikin tattausar murya. Ta
wuce daki. Ta iske Maman Atuika a kan abin sah tana lazumi suna hada ido sai dukkaninsu
suka kece da dariya.
Aziza taje ta fada jikinta cikin sahgwaba ta ce “mama me yasa kika ce min Atika zan gani babi
cemin Ashruf ba me ?”
Ta yi murmushi ta ce “ Au to bari ince ya juya jamaika”Aziza ta riketa tana cewa “Naji dadi
amma ni kunyarsa nake mama zo ki rakani” Ta ce” Ashe ba za ga Ashruf din ba kenan kinga ba
ni waje inje in shiryawa nagona abici kafin ya dawo” Aziza ta yi dariyas tace “Mama kece
amaryar kenan” Tace “ Amarya ce Mana soyayya bata tsufa Aziza zo ki wuce wajensa ki bashi
ruwa da abincei yanzu ya shigo , in kinga fita ta na barki da shi “ Mama ta fita Aziza ta mta ido.
Yayi ajiyar zuciya ya ce “ Aziza yaya? Kuna nana Ashruf” ya ce “ Na rame, nayi baki sabada
raashinki ke fa?” su duka suka yi dariya tace “ ya ka ganin? Dukka yadda ka ganin haka akayi”
Yace “Naga kin trame kinyui fari amma kin kara kyau”
Te ce “ to haka akayi” suna hira wasa da dariya can ta yunkara zata jie ta dauko masa ruwa da
abince ya dafe hannaunta ya ce “ Tayi zamanta shi ya koshui babu kishirwaba yunwa gainta ne
ya kosar da shi. Ta yi masa congratullation bia samun nasarar shri’ar da suka yi da kuma fatan
Allah ya bawa mahaifiyar sa lafiya . shi kuma ya mata godiya wahalar da suke yi da iyeyensa.
Daga karshe suka dunguma zuwa wajen mota don su tafi gida.
Kwatsam Alhaji Ahmed da Elmustapha da