Showing 27001 words to 30000 words out of 73529 words

Chapter 10 - KWANA 24 BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS -1.pdf

Advertisement

Unknown   

29 Jun 2025

3600

da kan wayoyi guda biyu da layukansu. Ya iske axixa da
munnira a farfajiyar hotel amma daga can baya wajen swimming pool ya yi musu sallama suka
amsa, ya mikawa axixa wayoyin kallon kallon da ake idanuwansu cike ba shaukin
soyayya shi ne ya yi matukar daurewa munnira kai, ta kalli axixa ta kalli Ashruf ta sake
dubansu sai ta fara tambayar kanta da kanta me ya haka ? kamar a mafarki Axixa da Ashruf
masoya ne ko kuma idonta ne?
axixa ta nisa ta ce ka rike dayar taka ce kayi amfani da ita ko dan yan gidanku ko xaka yi musu
waya, yace na gode ya juya ya tafi yana juyawa sai ga su Mubarak sun bullo ta dayan bangaren
suka xo suka xaxxauna, ana ta ciye ciye da makulashe da nishadi amma banda axixa har wani
katon kek Mubarak ya sa aka yi mata na sannu da xuwa amma a yatsune ta yanka ba walwala.
Basu bar wajen nan ba saida magaruba suka koma cikin dakunan su na hotel. Bayan duk sun
shiga dakunansu sun yi alwala sunyi sallar magariba sun idar axixa ce bata bar kan abin sallar
ta ba ta daga hannu tana ta kwararo addu’o’I tana hawaye . atika da munnira sai xare ido suke
sun fa kasa gane halin da axixa take ciki, don tabbas tana cikin damuwa. Bayan ta shafa atika
ta xo kusa da ita ta dafa kafadarta tace axxy ki yiwa Allah ki fada mana abinda ke damunki, in
ba ki gaya mana ba wa xaki fadawa?
Idan kuwa kin ki to yanxu xani dakin dady in gaya masa kin san dole ya takura miki sai kin fada.
Tayi shiru kamar bada ita ake Magana ba, atika ta dauko hijabi ta saka tace da munnira kar ki
bani hakuri ba ma xan dawo ba sai na je na fadawa daddy halin da axixa take ciki. Munira tace

ina fa xan baki hakuri je ki ki fada.

Atika ta fice amma ita bada niyyar ta je wajen daddy bane ta dai fita don ta tsorata axixa ko ta
riketa tace karta je xata fada musu, amma farantakau babu wanda ya biyota harta sauka kasa
babu wanda ya rikota. Bayan ta fita axixa ta cire hijabin da ta yi sallah ta fada kan gado ta yi ruf
da ciki, tana tunani. Munnira ta matso kusa da ita ta dafa bayanta tace, axixa na fara fahimtar
abinda yake damunki da ashruf tabbas naga irin kallon da kuke yiwa junanku, haka ne?
tana rufe bakinta sai ga atika ta shigo tace axxy kije inji daddy… munnira tace da gaske kin
gaya masa?
Atika tace ban je ba ni kasa na sauka amma Ibrahim da Mubarak sun je sun gayawa daddy, ni
ina kasa ina kallon ikon Allah kin san makudan kudin da daddy yace xai baiwa ashruf daxu? , to
fitar da daddy da mr Johnson sukayi da yamma banki suka je aka karbo masa kudin cikin ‘yar
akwati cike da daloli shi ne mr Johnson ya bashi yanxu a kasa…. Munnira tace haba har an
bashi kudin? Wannan mutum wacce irin murna xai yi yau? Allah sarki. Atika tace ai shine nake
so in gaya muku maimakon murna da farin ciki, ya fita daga sahun talakwa sai ya dauki akwatin
ya rada da kasa da kyar mr Johnson ya dauke kudin ya sa a mota ya ja shi gefe yana
lallashinsa.

Munnira tayi salati ta sallance tace daddy yana wajen kuma?
Atika tace haba aida ba xai ji dadi ba babu kowa ni kadai ce nake kasa. To ina hawowa ne na
gamu da su Mubarak suna saukowa daga saman daddy xasu shigo nan dakin sai suka ce in ce
axxy ta xo daddy na kiranta wai sun gaya masa halin da take ciki. Munnira ta yi ajiyar xuciya
tace ina jin sun yi gamo a dajin da suke sai an yi musu rukiyya. Axixa na jinsu sai yanxu ta
motsa ta tashi xaune ta sauko daga kan gadon ta ciro wayarta, ta saka a caji ta saka hijab dinta
ta fice, ba tare da ta cewa kowa komai ba. bata xarce ko ina ba sai can sama hawa na uku
dakin daddyn ta. Ta tura kofa ta shiga gami da yin sallama, suka amsa ta iske su a falon, daddy
yana xaune a kan doguwar kujera, Mubarak da Ibrahim a xaune a kasa tace ga ni daddy. Ya ce
yauwa dama yanxu Mubarak da Ibrahim suke shaida mun tunda kika dawo duk kin canja, babu
walwala. Ko wani abu ne yake damun ki?.
Idan baki da lafiya ki yi Magana a kaiki asibisti. Axixa ta girgixa kai tace babu komai. Daddy
yace bahaka kike da ba axixa nima na lura dake kin canja.

Ta rushe da kuka ta fada kan cinyarsa yayi ya yi, ta yi shiru ta yi Magana ta ki, sai yace dasu
Mubarak su tafi xai kirasu. Bayan sun fice alhaji ahmad ya ci gaba da lallashin axixa da kyar ta
yi shiru, yace karta cuci kanta ta fada masa me ke damunta. Axixa taga dai gara ta fada don
idan bashi ba waye xai yi mata maganin cutar dake damunsu, sai ta goge hawayen dake
kwaranyo mata ta gyara xama tace daddy ka gafarceni na san ba xaka ji dadin maganar nan
tawa ba amma Allah ne Ya kaddara min Ya kuma sani cikin wannan hali. Yanxu Allah Ya dora
mana son junanmu ni da ashruf, yanxu ba xan iya auren Mubarak ba ashruf nake so. Bata rufe
bakinta ba sai ta ji ya daka mata tsawa yace, yi min shiru shashasha! Yau ne ranar farko da
daddy ya taba xagin axixa haka da irin wannan kalma. Ta yi shiru jikinta ya dau rawa yace bada
ni ba wannan rashin hankalin wasan da nake yi dake shi ne yasa kika fara xamar dani kakanki?
Dan da bashi da asali bamu san shi ba, idan baki bar maganar nan ba sai na sa an daure shi

ma, tashi ki fita ki bani waje, kin auri Mubarak kin gama. Sum sum ta fice tana rusa kuka kamar
ranta xai fita. Tana fita bata xarce ko ina ba sai reception tace a bata daki a can sama kololuwa,
aka bata daki a hawa na takwas ta karbi mukullin dakin.

Ta shiga dakinsu ta iske su atika basa nan wata kila suna dinning room suna cin abinci. Ta
dauki wayarta da sauran takarkacenta ta fice ta hau sabon dakinta. Tana shiga ta mayar da kofa
ta rufe ta sa mukulli ta datse.. wayar ashruf ceta shigo mata tun kafin ta xauna ta matsa ta ji
muryar da take muradi ce cikin sanyin murya tace ashruf ya aka yi ka san lambata? Ya ce ai kwalin layin naki yana hannuna na manta ban baki ba, a jiki naga lambar layinki. Ta ce
yanxu kana ina? Ya ce ni da mr Johnson mun taho wani hotel dake bakin ruwa na saukar
matuka jirgin ruwa yana nan bakin teku. Ke kuma fa kina ina naji duk muryarki ta canja? Ta ce
ina dakina a hotel din da muke. Ashruf ya xauna a bakin gadon dakinsa don fitowarsa daga
wanka kenan yace axixa ya ya xamu yi?

Axixa ta rushe da kuka tace babu yadda xamu yi ashruf ni nan daka ganni komai ya rincabe
min.
ya xabura yace kamar yaya?
Tace ba ni da mai share min hawaye kamar dady na har na sanar masa abinda ke faruwa
amma da ka ga yadda ya sabar min baka ce shi ne mai son nawa ba. ashruf yace kar ki damu
axixa yanxu xanxo yanxu mu hadu a reception din hotel dinku. Axixa tace ashruf dady ba xai sa
ido a kanmu ba kuwa? Idan ya ganni da kai laifinka xai gani. Ashruf yace na godewa Allah da
laifina xai gani ba naki ba, kuma ko me xa a yi min na yarda ba xan iya rabuwa da ke ba. gobe
fada sassafe xaku tafi, yanxu ina gani ki tafi ki barni axixa, na yi rayuwa da wa? Axixa ta yi ruf
da ciki akan gado sai kuka take ta kasa Magana, ta ji ya kashe wayar. Ita tunanin kada ya xo
daddy yasa a daureshi tunda har ya furta daurin nan, ta san kadan daga aikin babanta in dai
ransa ya baci to xai iya yin kome yace xai yi.

Kwankwasa kofarta da ake ita ta katse kukan da take ta tashi xaune, tana tunanin wane ne ya
san tana nan ya xo? Ta ji ana ta dannan kararrawa ta mike a sanyayye ta karasa bakin kofa ta
daga wani dan karamin labule a jikin kofar da wata ‘yar huda ta leka sai ta hango atika da
munnira tayi tsaki sannan ta bude suka shigo suna mata tsiya suna cewa to mun ji me ke
damunki. Gaban axixa ya fadi wato daddy gaya musu yayi abinda ta fada masa? Sai ta jib a
gaskiya ya fada musu ba cewa yayi xama a dajin ne ya sa bata jin dadin jikinta bata son yin
Magana bata iya cin abinci saboda rashin barcin da ta dade bata yi don haka hutu take bukata,
kuma bata son kasar nan Nigeria take so su tafi. Suna ta surutunsu ta koma kan gado ta
kwanta tana kallonsu daga karshe suka ce kar mu cika ki da surutu tunda kin gaji mun barki
lafiya. Mubarak ma yace yana miki sannu saida safe. Axixa tace waye yace muku ina nan
kuma? Suka ce sadik yace ya ga sanda kika je reception kina kuka kika karbi makulli shi ne ya
je ya tambayesu suka ce daki kika ce kina so a hawa na takwas lamba 500 shi ne muka xo.
Axixa tace saida safe. Suka ce Allah Ya kaimu. Suka fice ta mayar da kofa ta bame.

Bayan ta yi sallar isha’I da dadewa babu ashruf babu wayarsa, sha dayan dare babu ashruf sai
ta shiga tunanin kar fa ya xo sun hadu da daddy ya sa an kamashi. Nan da nan hankalinta ya

tashi, ta hau leke-leken taga babu kowa, can sai wayar dake ajiye a dakin ta hau kara ta kalli
agogo karfe goma sha daya da rabi na dare. Ta mika hannu a sanyaye ta dauka sai ta ji muryar
baturiyar da take reception din hotel din ce. Axixa ga wani bako yana son Magana da ke, ya ya
a bashi dama xaki amsa? Cikin sauri tace a bashi mu yi Magana. Ashruf na karba yace axixa ni ne ki sauko mu hadu a
reception. Ta ce to gani nan. Tana ajiye wayar ta saka takalminta ta fito duk jikinta rawa yake
don fargaba. Ta hau na’urar da ke hawowa da saukar ‘yan sama cikin sauki wato lift, ta sauko
kasa. Tana saukowa babu wanda ta fara hada ido dashi sai dadynta, alhaji ahmad ya kalleta
fuskarta murtik kamar xai fashe yace ina xaki?
Nan fa ta hau gargadar magana tana kame kame. Ya nuna mata hannu alamar ta koma inda ta
fito. Jikinta na karkarwa ta hau lift ta koma sama. Ya je reception ya duba ko ina bai ga shruf ba,
amma kuma ga ashruf din nan xaune bai ganeshi ba. saboda ashruf din daya sani daxu da
yagulallun kaya ya sanshi ga wata kasumba, yanxu ya aske ya kuma sha wani tsadadden kaya
tsadadden takalma, hadadden wandon jeans baki da wata hula baka, bakin gilashin ido ya
xama jajur dashi kamar bature yayi aski don haka alhaji ahmad bai ma kawo ashruf bane, daya
ga bai ga ashruf ba a nan sai ya yi xaton to yana waje yana jiranta, ya koma karamin falon da
yake bakin matattakalr da dole dai in axixa xa ta fito ya ganta ya xauna.

Wato yau xai ga yadda xa a yi ta sauko. Axixa ta koma daki sai wayar ashruf ta sake shigowa
ta dauka yace axixa naga daddy a reception yanxu yana dube-dube ke yake nema? Ta ce na
hadu dashi ya koro ni ina jin kai yake nima, don haka don Allah tun da bai ganka ba, kar ka bari
ya ganka yayi mun rantsuwa idan ban rabu da kai ba ba sai ya sa an daureka. Ashruf ya kama
kai don takaici yace axixa na so ki yi dabara ki fito da wallahi a daren nan xamu bar kasar nan a
rasa mu kwata kwata mu yi wajen china ko india koma wasu kasashen afrika inda ba xa a taba
tunanin muna can ba in ya so idan an kamamu a kashe ni na yarda da in rasa ki ko ba xa ki bi
niba?
axixa ta sharbe hawaye tace me xai hana ashruf? Nima abinda na yanke shawara kenan koda
kuwa ajalina ne binka din da xan yi. Ya ce abinda ya sa na dade ban karaso ba filin jirgi naje na
yi cuku cukun duk jirgin da xai tashi a tsakar daren yau ya tashi damu koma ina xai je ga kudina
da daddy ya bani xai ishe mu mu je ko ina ne a duniyar nan ga mai tsai a waje yanxu fitowarki
ne wahala. Axixa tace kar ka damu kai dai fita daga reception din ka jirani a wajen get din hotel
xan fito. Ya ce daman bana reception ina waje sai kin fito.

Suka kashe waya, axixa ta binciko biro da takarda a cikin lokar gado ta rubutawa mahaifinta
doguwar wasika, ta neman gafara da kuma bankwana Allah Ya kaddara saduwarsu ita da
masoyinta sun shiga mai fadi don su raya sunnar Manxo (SAW) saboda sun xurfafa, sun yi nisa
a fagen kaunar junansu, baxa su iya hakura da juna ba. tana hawaye tana rubutawa harta gama
ta bar wasikar a bude a kan gado. Ta harhada ‘yan kayayyakin ta a cikin Jakarta kamar wayarta
makilin da brush da comb da dai sauransu ta rataya jakar ta fito. Sai ta ki biyowa ta lift ta bi ta
matattakala tana sauka a hankali harta sauko takalminta a hannu. Kicibis ta yi da alhaji ahmad
babanta a nan karamin falon dake karkashin matattakala, yana xaune da remote din talabijin a
hannunsa yana kallo, ta sankare a tsaye har saida jakar da ke rataye a kafadarta da takalman
dake hannunta suka sulalo suka fado don tsorata da tashin hankali.

Alhaji ahmad yace dauki jakar xo ki fita ki gudu wajen masoyinki ki bar mhaifinki axixa. Ni in ce
kar ki yi, kice sai kin yi duniya da fadi sai kin gwammace baki tafi ba kin bi maganar maharfini ki
saboda bala’I xaki tarar a gaba. Sai kin yi dana sani akwai abinda ni na hango miki wanda ke ba
xaki hangoshi ba. na gode da bijirewa maganata. Ba ni da ‘da ko ‘ya sai ke kadai ina rainon ki
har kika girma yau kin girma ban isa in ce kar ki yi abu ba ki bari kin fi so ki xauna da wani ni ku
barni. Axixa ta ji tunda take a duniya bata taba jin tashin hankali ba irin na yau. Musamman
kalaman mahaifinta sai ta rushe da kuka ta durkusa a gabansa tana neman gafarar ya yafe
mata, in Allah Ya yarda daga yau ta hakura da ashruf. Alhaji ahmad yace ya yafe mata ya jawo
hannunta yace ta xauna kan kujera kusa dashi bayan ta xauna kukan da take ya lafa ya ci gaba
da yi mata nasihohi masu ratsa jiki yana nuna mata illolin da xasu afku muddin ta auri ashruf.

Ya kuma nuna mata illar rashin auren Mubarak da halin da alhaji isa xai shiga mahaifin
Mubarak babban tashin hankali ne, ya dauki lokaci mai tsawo yana yi mata nasihohi wanda duk
ya sa ta yi nadama. Waya a cikin Jakarta tafara kara, kunya da nauyi ya sa ta kasa tashi ta
dauko saida alhaji ahmad yace ta je ta dauka ya san ashruf ne ta yi masa bayani yayi hakuri,
daga nan ta wuce dakinta ta kwanta. Tayi godiya ta mike ta dauki Jakarta ta nufi daki a
sanyaye, tana shiga ta rufe kofa ta hau gado ta rungume filo tana mai tsananin rudadden
tunani. Wayar ashruf ceta sake shigowa, ta dauka ta amsa cikin sanyin murya tace hello ashruf
ma muryarsa na rawa yace axixa daddy ya hana ki ko?

Ta ce yana bakin matattakala a xaune. Kan ya sake cewa wani abu sai computer ta fara
Magana kudinsa yakare, yayi saurin rubuta mata message yace na san na rasaki axixa, amma
bana rasaki ba ne har abada don haka ki yi min alkawarin ba xa ki yi aure ba ni ashruf ni ne
mijinki ki karbi sako a wajen ma’aikatan da ke reception, gobe idan kun fito xaku tafi ki gudu
gurina mu gudu ina nan a filin jirgin daga jikin wata waya xan dinga hango ku. Ya turo mata
message din na xuwa wayar axixa sai kuma cajin wayarsa yakare, wayar tayi kara ta mutu.
bakin ciki goma da ashirin ya tarar wa ashruf inda xuciya ta dauke shi ya wurgar da wayar cikin
ruwa don takaici. Axixa ta karanta sakon ashruf sai ta yi shiru tana tunani tace a ranta xancen
guduwa dai yakau saboda nasihar da daddy yayi min na tsorata, amma xancen kin yin aure na
amince na yi alkawari in ya so xan iya rayuwa babu aure har sai Allah Ya kara hadamu.ta rushe
da kuka tayi kuka ta gaji har idanuwanta suka kankance kamar ‘yar japan. Daga karshe ta
dauko wayarta tace bari na buga masa tunda shi kudinsa yakare kuma dare yayi ba inda xai
sayi kati.

Tana bugawa sai ta ji wayarsa a kashe , ta yi ta yi ta ji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login