Showing 72001 words to 73529 words out of 73529 words
Chapter 25 - KWANA 24 BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS -1.pdf
Unknown
29 Jun 2025
3594
wajen tsiburin nan da suka bata
gob su Mar. Johnso su taho su same su a can. Haka kuwa aka yi suka shiga dan karamin jirgi
Ashruf na tukawa Aziza na gefensa da jakar kayayyakinsu da zasu bukata suka tafi. Su Atika na
daga musu hannu har suka yi nisa. Basu isa wajen ba sai da yamma. Da fitilar hunnu mai haske
Ashruf ya haska cikin dakin yaga tastas dakin kamar masu dakin basu dade da tafiya ba. Don
ga tokar itace nan a cikin murhu. Suka kade gadonsu suka shinfida sabon zanin gado da
filulluka suka yi sallah suka ci abincin da suka yi guziri a jakarsu. Suna rungume da juna har
barci ya dauke su.
Da sassafe ko farkawa daga barci basu yi ba su ka ji odar (horn) din jirgin ruwa su Mr. Johnson
sun karaso, suka fito daga dakin don suga masu yin horn sai suka ga su din ne kuwa. Atika da
Munnira cikin murna suka zo suka ringune Aziza Munnira ta ce “Kai amma Aziza garin nan na
ku ya yi min kyau”. Ta dinga zagayawa da su ta ce “Nanne muke yin abu kaza nan muke yin
kaza”. Ta kaisu har cikin dakinsu suka sha dariya suka ce “Lallai kunsha wuya har kwana
ashirin da hudu a haka cafdijiam dole ki saduda Aziza”. Dukkansu suka nuna su ma suna da
shaa’awar zama anan, Ashruf ya yi wa Mr. Johnson bayani akan suna so suyi KWANA
ASHIRIN DA HUDU anan don haka suna so ya sa ma’aikatansu su buga musa tanfol (‘yan
runfuna) guda uku amanya manya daya zai zama dain Munnira da Rislan, daya na Atika da
Mahmud day kuma na Aziza da Ashruf. Sai su Mr. Johnsun su tafi Italy su jirasu ranar da suka
cika KWANA ASHIRIN DA HUDU da sassafe su zo su daukesu. Haka kuwa aka yi ma’aiaktan
Mr. Johnson suka buga ‘yan runfuna aka shinfida dardumai a ciki aka dora katifu runfuna
bibbiyu da zannuwan gado da bargo kowanne da jakar kayansu. Wannan dakin itaccn nasu
Aziza na da ya zama bandakinsu anan zasu ringa wanka har ‘yar shadda injiniyoyin nan suka
hada musu da dubaru irin nasu. Dr. Rislan ya karbi kayan aiki a wajen likitoci, kayan kicin da
kayan abinci duk Aziza ta sa an jifge musu yadda zai ishesu har KWANA ASHIRIN DA HUDU.
Da har su Atika sunce a bar musu kuku daya don dafa abinci da sauran aikace aikace Aziza ta
ce a bar shi meye amfaninsu in har ba za su iya dafawa mazansu abinci ba. Yawanci ma duk
abinci gwangwani ne da lemon kwalaye da gwangwanaye ba wani giriki zasu dinga yi ba sosai.
Mr. Johnson ya yi musu sallama suka tafi suka bar su anan. Sunji dadin wanan waje sosai waje
ne kuma na hutu musaamman ga masoya, ga ruwa cikin tekun nan yana busowa abin gwanin
ba sha’awa anan ma su dr. rislan sunsha dariyar aziza da ashruf suna gwada yadda suka yi.
Amma maimakon marin da yake taska mata yanzu idan ya zo gwadawa sai ya shafa mata
fuskar ya rungumeta ya rada mata a kunne tayi hakuri kuskure ne yar sa ya mareta a da. Aziza
kuwa tama dai na kiransa da ashruf sai master take ce masa shi kuma ya ce matamai girma
aziza. Atika tana da shegen tsoro tana jin dadin wajen da rana saboda yaddasuke watayawa
suci su shag a rundumemiyar riloda wani lockaci asa kida. Ba wasanni kala kala kowacce da
mijinta har was an ‘yan goye goye suke amma ita matsalarta tsoro take ji da daddare. Da kyar
take iya yin barci sai ta kankamemahmud wani lokaci har kuka take fashe masa wai ita tsoro
take ji. Munnira kuma saboda sanyi da daddare idanuwata suka kukkumbura, said a dr. rislan
ya tsikara mata allura gashi tsoron allura tae don ta sami sakin kumburin. Ranar da suka yi
kwana goma suka tubure suka ce sufa wajen nan ya isheshu su tafi. Aziza da ashruf suka ce su
kuma alkawari suka yi sai sunyi KWANA ASHIRIN DA HUDU sannan zasu tafi. Daga karshe dai
suka tsayaar da shawarar a yiwa mr. Johnson waya ya zo ya kwashesu su bar aziza da ahruf
kawai in ya so idan suka cika KWANA ASHIRIN DA HUDU azo a daukesu su samesu a wana
hotel din na Italy da suka sauk da. Haka kuwa aka yi an yiwa mr . johson waya sunzo sun dauki
su atika da mazajensu zuwa Italy. Aziza da ashruf dinta kadai suka rage sunma fi sakewa yanzu
su kadai, soyayya ce take gudana tsakanin masoyannan biyu a kungurmin dajin nana kamar su
hadiye junansu. Su ci abinci tare, su yi wanka tare, su yi barci tare a kullum wayewar garin allah
kara son junansu suke yi. Aziza tana burge ashruf matuka saboda irin yadda take yi masa abin
yana bashi mamaki duk inda mace ta gari take aziza ta kai hart a wuce ta. Bata barinsa ya
dauke tsinkekomai yi masataketa bashi abinci a baki ruwa ma haka wankansa ka kayansa,
shafa mansa. Kalamanta suna kwanta mas da hankali kallon da take yi masa sukan kasha
jijiyiyin jikinsu. Tafiyarta tana burge shi har baya kaunar ya sake kallon wata mace ba ita ba. Ga
uwa uba ladabi da biyayyar da take yi mas kamar zata kwanta masa dan ladabi. Aziza ma tana
son ashruf kmar yadda yake son tad a yawa. A bangarnta itama tana alfahari da godiya ga allah
ya bata miji nurusttse wanda baya so yaga b acin ranta wanda yake riritata kamar kwai, kamar
wata yar jaririya a hannun uwarta. Kamar ya lasheta don son da yake nuna mata. Alhamdulillahi
kiyayya ta zamo soyayya, soyayya mai karfi kuwa.
Haka suka kansance cikin jin dadi basu so KWANA ASHIRIN DA HUDU bat a cika. Ranar da
kwanakinsu suka cika da sassafe suka yi wanka suka kinkintsa kayansu suka zuba a
jakunkunansu suka taho bakin ruwa suka tsaya suna jiran jirgi. Ashruf ya rike dan yatsanta inda
ya saka zoben nan day ya bata na azurfa a ranar da aka zo aka tafi da su. Ya ce ‘’allah sarki
komai mai wucewa ne kin tuna ranar da na saka miki zoben nan kina kuka ina kuka zamu rabu?
Yanzu gashi iyayenki da kansu suka dauko ki suka dankamin ke kacikan dinki kyauta. The poor
also laugh’’. Ta kayalkayle da dariya t ce ‘’ the rich also cry inji wata nurse da ta ganni ina kuka a
asibiti t ace ‘oh the rich also cry tana yanzu ka ce the poor also laugh’’. Yace ‘’haka ne mana
aziza tun ina dan shekara bakwai nafara ganin wahala dab akin ciki a rayuwa. Sai wannan
shekarar allah ya yassare mana lokaci guda. Allahu akbar allah mai girma bau abinda ya gagari
ubangiji’’. Ya ce ‘’zo mu yi alwala mu yi salla raka’a biyu nafila don kawai mu godewa allah’’.
Haka kuwa suka yi. Suna idarwa mr. johson suka dira a gabansu, ma’aikata suka debo
kayyaakinsu suka zuba a cikin jirgi suka shiga sai kasar Italy. A wannan hotel din suka iske su
atika. Aziza na shiga reception din hotel din taga wannan matar da ta kai mata sakon ashruf
itama matar kallo daaya tayiwa aziza ta ganeta. Murna ta kamasu suka rungume juna, matar
tayi mamaki da taji cewar ashruf ne mijinta ta yi musu fatan alheri ta tayasu murna.
Kwanan su aziza uku a hotel din nan. Miss katrine sunnan matar da take aiki a reception ta
zama kawar aziza sosai. Da zasu tafi taji babu dadi sun saba kuma zasu rabu, sun mata kyartar
kusi mai yawa wanda tayi mamaki kwarai da gaske. Danganan suka yi sallama das u mr. johson
ma kuka bashi kudaden jirginsa. Fillin jirgi suka nufa don auwa france. Kamar yadda suka yi
alkawari kasashe ASHIRIN DA HUDU zasu zazzagaya yandu daai sunje amerika. Sunje crotia,
Malaysia, indonusia, india, Pakistan, Italy duk ta hanyar jirgin sama zasu bi su ci gaba da
zagaye kasashhe yanzu sun tafi france daga can zasu je iran da irak. Tunusia, sauth Africa,
Canada da sauran kasashe, idan suka je saudia suka yi umra sais u wuce Germany don kallon
kwallon world cup. Ball din da za a yi kasar Germany daga can sai suka yo gida. Anwaye da amre sun yo tsarabar kaya. Ko ni nan ma marubuciya akwati na daban ta tsarba
abin ma sai wanda ya gani. Wata akwati daban suka ciko suka cein raba ku makaranta na duk
mai son tsaraba yazo ya karba inji aziza da ashruf. Nayi murna da tsarabar da suka kawo min
amma naïf murna da biro da littafin da suka kawo mi don in samu in rubuto muku wasu
littatafaina.v sannan kumakowacce ta cikin yayi wata tara aziza ta haifi mace Fatima, Atika,
Munnira, Ummar Ashruf da Anti Sharifa duk maza suka Haifa. Allah ya raya Amin!! KARSHE
Ina fatan zaku cigabada kara. Ni a kullum burina in koyar da darusa, mosjadamtarwa da kuma
deve muku kewa.
Taku Jamila Umar Tanko Grmel.
Inde littafin yaburgeku kubiyoni da comment ya kukaji dadinsa
Kuma littafin gaba shine Adon dawa na jamila umar Tanko
Amma kuma to.
KARSHE
ALHAMDULILLAHI