Showing 6001 words to 9000 words out of 73529 words
Chapter 3 - KWANA 24 BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS -1.pdf
Unknown
29 Jun 2025
3583
ya sharo mata wannan
danyen kifin a jikinta don ta bangaje shi, shi kuma daro a kafadarda da kifi. Axixa ta tsuke fuska
tace da ashruf da kifin xa ka xubo min aka? Ashruf ya ce a’a ke kika bangaje ni daron ya kusa
subuce min sai na rike da sauri dan kar ya xube. Ya yunkura xai wuce sai ya ga ta tari gabansa
ya sake bin ta gefe xai wuce sai ta sake tarar gabansa sai ya tsaya cak yana kallonta, tace mr
ashruf kake ko waye? Kana jiyo sautin kida kuwa daga nan dakin?
Ashruf yace, eh inaji. Ta ce yauwa yanxu abinda nake so ka sauke daron kifinka ka taka min
rawa in gani. Ya ji wani takaici ya lullube shi yace a ransa yarinayar nan ta dauke ni wani
sakarai marar mutunci wanda ma bai san abinda yake yi ba, talauci ba hauka bane ai kudi ma
ba hauka ba ne.
Axixa tace, kana bata min lokaci ka yi min rawa nace. Ashruf yace da ita rawa bata cikin aikin
da aka dauke ni na dinga yi. Ana biyana kamun kifi ne aiki na manya ko kanana da dai kifi ne
idan na kamo manyan kika ce kanana kike so xan kamo kananan kuma suma idan basu yi miki
ba sai kice kwan kifi kike so tunda aikina ne xan nemo miki, amma ba rawa ba. talaka yana da
abin yi, baya rasa aikin yi ya xauna yana rawa don haka matsa min in wuce. Ya wuce abinsa
har ya shige kicin axixa na tsaye tana kallonsa. Ta nisa tace, ashruf baka san halina ba sai ka
gwammace baka bani irin wannan amsar ba. ba xan fadawa mr Johnson ba don kawai shi
sallamarka xai yi amma da aikin naka farin ciki ya gagari xuciyarka yaro axixa kake ji baka santa
ba. dan attajiri ma baya gangancin gaya min Magana balle dan matsiyaci, matalauci kamar ka.
Axixa ta wuce cikin dakin da suke rakashewarsu.
A ranar da daddare axixa ta sawa ashruf dokoki ir-iri tace, idan suna cin abinci ya xo ya tsaya
har sai sun kare don bata so ko tana da korafi akan wani abu sai ta sha wahalar dannan
karrarawa. Duk dai wani abun da ta san xai Konawa ashruf xai kuma wahalar dashi shi ta sa a
cikin dokokinta. Kwanci tashi satinsu biyu a hanya sun kuma tsaya Italy sun yi kwana biyu sun wuce. A da a
kowace rana sau daya ashruf yake kamo kifi wata ranar ma baya komawa in wanda ya kamo na
wannan ranar masu yawa ne yakan isa a ci yau a ci gobe. Amma a wannan tafiya saboda axixa
wani lokacin ma har sau uku yake kamo kifi iri-iri daban daban ya kamo wannan tace ba irinsa
ba, ya koma ya kamo wani tace bashi ba, sai yayi sau uku, ko biyu daga karshe ma tace ita yau
ta ma fasa cin kifin kaji xa ta ci aje a bawa masu ci. Ashruf ya kule ga jigata ko barci bai cika
samu ba balle wai ya xauna a xaune da rana yana hutawa ai sai dai idan su axixa sun fita ne a
karamin jirgi, amma muddin axixa tana nan ashruf shi da kishingida bissalam.
Don haka duk wanda yasan ashruf da idan ya ganshi yanxu ba xai ganeshi ba, don ya rame
kullum a cikin bacin rai babu walwala a tare dashi. Mr Johnson ya lura cewa gaskiya axixa har
da don ta musgunawa ashruf take sashi wannan aiki iri-iri. To babu yadda xai yi da ita tunda
xuciyarsa ta kone a wajen son kudinta, sai dai yakan kira ashruf yana ta bashi baki akan yayi
hakuri da duk abinda axixa xata yi masa dan lokaci ne xa su rabu, amma shi kam da wannan
hakuri na mr Johnson ai gara babu ya kyaleshi ya ci gaba da fuskantar wulakanci da
kaskantarwar da axixa take masa, ashruf yakan daga hannu ya roki gafara a wajen Ubangijinsa
yace gwanda ya dauki ransa a cikin wannan hali da yake ciki baya so ya karasa wannan
masifaffiyar yarinya don cin mutuncinta ya isa. Abokansa kukun nan guda uku suma har sun
gaji da lallashin ashruf idan sun xo kwanciya barci don duk juyin da xasu yi cikin dare saisu ga
idaonsa biyu yana tunani kawai wani lokaci ma yana hawaye duk don axixa.
Ranara da suka cika kwanaki ashririn, ashirin ga watan febarairu kenan axixa ta cika shekaru
ashirin da hudu a duniya. A yau kuma ta hada kayataccen (birthday) a cikin wannan jirgin ta sa
aka huhhura balo ko ina aka saka abin kyale kyale, an rubuta HAPPY BIRTHDAY AXXY BEST.
Anan farfajiyar aka harhada kujeru na alfarma, ga wani kek mai hawa hudu shima an caba
masa ado wanda xata yanka, da misalin karfe takwas na dare aka haifeta don haka saida karfe
takwas din aka fara shagalin wannan bikin xagayowar ranar haihuwar axixa. Ta kuwa caba ado
da wata dandatsetsiyar doguwar riga irin ta turawa daga kanta har kafarta gwala gwalai ne
kanta babu dankwali ta saki gashinta har gadon bayanta, ashruf na can kurya yana labe yana
kallon kudi a gidansu ya kurawa axixa ido yana kallon halittar Allah.
Ya ce a ransa wannan yarinyar kin yi dace da kyau dama ace kin yi dace da hali me kyau da
kin ji dadi duniya da lahira. Ya ga gashi mai sunan gashi ga tsawo ga yawa ga tsantsi sai ka ce
ba bakar fata ba, idanuwanta dara dara masu kyau ga wani hanci dodar har baka, baki dan
karami a wannan kewayayyar fuskarta tata, haka ya dinga kallon kirar kyakkyawar halittar da
Allah Ya mata, wanda ya ga cewa duk a banxa suke, domin babu hali ko daya.
Ashruf yana ta kallon axixa yana xano halitunta can ya nisa, yace a ransa wai yau kwana na
nawa da axixa ace ban taba lura da wadannan halittu ba sai a yau? Ya ce ko da yake sai a yau
naji raina ya dan washe don ita ma wacce take sani damuwar naganta yau a cikin farin ciki shi
yasa ma kyanta ya fito sosai har na lura, don idan ta kular da ni kyakkyawar fuskarnan tata
kamar ta bakin kumurci nake gani. Ashruf ya ci gaba da kallonsu. Mubarak ma ya fito sanye da
wata tsadaddiyar bakar coat (suite) a jikinsa. Ashruf yace a ransa lallai Mubarak ka yi rawar jiki
a kanta don na tabbata ba don kaima kana da kudi ba ne axixa ba xa ta kula ka ba, wani baki
kirin dashi babu kyaw babu fasali. Ana ta daukar hotuna iri-iri dana bidiyo, ga fitulu kala kala,
haske tar wajen kai ka ce ranace. Su mr Johnson dasu kuku da likitoci da sauran matuka jirgi
da masu tukin kananan jirgi duk sun hallara a wajen wannan shagali, amma ban da ashruf shi
dai yana wani dan lungu a boye. Yana jin mr Johnson yana nemansa ya ki ya je, yace ni kare na
je wajen partyn uwargijiyata, ai sai in dinga shinshina mata kek din ta, in haramta mata shi.
Atika da munira duk sun yi kyau sun caba ado da samarinsu su Ibrahim da sadik, an kuwa
warware disco mai ratsa jiki ana kurba lemo ana taka rawa a hankali kowacce da nata abun
kaunar. Bayan an taka rawa sai aka umarci shugabar taro wato axixa ta yanka wannan katon
kek din mai hawa hudu ta yanka a kasa tafi raf raf. Duk ana ta dauka a hoto ana dauka a bidiyo
caset. Axixa ta xo gefe tana gwada waya ko da sabis tana so ta kira babanta don shima ya san
yau ranar xagayowar haihuwarta ne ya san duk ida take yau tana gudanra da bikin xagayowar
haihuwarta yana so yayi mata congratulations yana ta kokarin nemanta sai ta yi kamar xata
shiga sai ta tsinke, itama axixa tunda safe take gwada neman babanta a waya ta kasa samu.
Wayar turaya ce (new modern) wacce ko a ciki sahara kake xaka iya yi da ita amma yau gashi
sabis yana yankewa. Axixa ta ji haushi kamar xata fashe da kuka tana juyawa gefenta sai ta
hango ashruf a loko a sakule yana kallonta. Ta dan ji tausayinsa kamar tace masa ya xo cikinsu
sai wani girman kai da isa taga fa dan talakawa ne shi in yana so mai xai hana ya shigo cikinsu.
Sai ta wucewarta ta rabu dashi. Haka dai suka kai kusan sha biyun dare suna cashewa da kida
iri iri da ciye ciye da tande tande da lemuna kala kala ashruf na xaune yana kallo suka yi suka
gama kowa ya watse ya nufi makwancinsa sai ya ga axixa ta tunkaro shi ta xo ta tsaya a
gabansa tana kallonsa, ta yi murmushi tace guldo mun gama da sauran kasusuwa a wajen ka je
ka tande ka gyara wajen kafin da safe mu fito. Ta wuce tana karairaya kamar xata gurde kugu.
Ashruf ya bita da kallo harta wuce ta sauka kasa ya buga hannunsa da kansa yace oh God.
Takaici ya lullube shi ya yi awa daya a xaune ya ma rasa mai xai yi, sai ya mike ya doshi wajen
gyaggyarwa yaya xai yi? Ranar da suka cika kwana ashririn da hudu ga watan febirairu, da
la’asar likip gamin magariba kamar karfe biyar da rabi na yamma, ga hadri ya kidimo garin ya yi
kitif kamar ruwa xai kece. Ashruf da wasu matuka karamin jirgi su biyu suna xaune a farfajiyar
jirgin suna gyare gyaren inji. Sai suka ji ana hayowa daga kasa ana tafiya a matattakala su dai a
sanin su babu kowa a matafiyan nan da wadansu ma’aikata kamar mr Johnson da captain
james dasu Mubarak, atika, munira, sadik, Ibrahim duk sun tafi can wata kasuwar bakin ruwa
don kallon wani katon kifi da aka kamo a wani teku. Mr jihnson yace musu kifin yayi girman gini
wato (shark) sunan kifin yana kuma iya hadiye mutum cancak. Munira tace shark xai iya kifar da
jirgi fa! Mr Johnson yace ai ba a ruwan nan aka kamo shi ba nan dai aka xo aka jifgeshi, tiawa
masu bincike daga kasashe suna nan suna bincike a kansa ana daukarsa a hotuna yace ai shi
wannan ruwan saida aka fiffitar dasu tas da ireiren su sannan jiragen ruwa suka fara bi ta cikin
sa.
Shine tun karfe biyu na rana suka shirya ita kuwa axixa tana ta sharar bacci sunyi sunyi da ita
ta taso su tafi kallon kifin amma tace su kyale ta ita ba xata je kallon wani abu kifi ba kamar
wata marar aikin yi. Don haka suka cika kananan jirage guda biyu da masu tukasu suka tafi, ita
kuma axixa sai yanxu ta farka, bayan ta yi wanka ta yi sallah tayi brush da sauransu. Ta shiga
sauran dakunan bata gan su atika ba ta shiga falo nan ma basanan, wajen cin abinci nan ma
basa nan, to shine sai tayi xaton ko sun fito farfajiyar ne suna shan iska tunda dama da yamma
anan suka saba xama suna shakatawa. Tana fitowa taga saisu ashruf ne kawai a farfajiyar. Duk
suka xuba mata ido suna mamakin ganinta don sun xata da ita aka tafi. Ta xaro gilas wanda
yake sakale a jikin rigarta ta saka tace, ina ‘yan uwana suke? Daya daga cikinsu yace, ai tun da
rana suka tafi wani waje da ake kira curbe xasu kalli wani katon kifi. Ta ce koma dai me suka je
gani ina son daya ya dauko jirgi yanxu nan ya kaini, wannan ya kalli wannan, wannan ya kalli
wancan saboda sun san wajen nan yana da bala’in nisa kuma ko babu hadari a garin to fa
tabbas kafin su kai dare yayi, kafin su dawo kuwa sai tsakar dare. Kuma da daddare babu ma
wanda xasu samu a wajen, suma su mr Johnson a duk inda suke yanxu suna hanyar dawowa.
Daya ya mike xai je ya dauko jirgin su tafi tace dashi, banda kai koma ka xauna. Dayan ma ya
mike tace, koma ka xauna ,guldo maxa a dauko jirgi a taho ko?
Ashruf ya rasa abinda xaice shi dai tuki ba aikin sa ba ne yace. Mai girma axixa shawarar da
xan baki shine ki bari sai gobe, dare yayi yanxu kuma da hadari a garin, bayan haka kuma
wurin yana da bala’in nisa ba xai yiyu mu kai wurin yanxu ba in ba can cikin dare ba kuma ko
munje babu wanda xamu iske. Ta ce shawarata gare ka shine karka kara sakon ashirin da hudu
kaje ka dauko jirgi ka xo mu tafi.
Ashruf ya mike ya tafi karkashin jirgi inda kananan jirage suke ya dauko jirgi yaxo yahada yace
to a shigo mutafi sauran suka daga musu hannu cike da tausayin su, irin wahalar da xasu sha
ga jirgin a bude yake tik babu rumfar da xata kare musu ruwa, gashi daga ganin hadarin ba
karamin ruwa xa’ayi ba, yau ana iya kwana ana ruwannan.
Ashruf ya bude wuta yana ta sharar gudu a cikin ruwa, bayan tafiyarsu da kamar minti ashirin
da hudu sai gasu mr Johnson da ‘yan uwan axixa sun dawo, su kuma ta wani bangaren bata
bangaren dasu axixa suka bi ba. suna ta saukowa suna hawowa babban jirgi ta wata
matattakala. Bayan sun hawo gabadayansu hannayensu rike da ledoji sun yo sayayya, sai
mutanen nan na xaune masu gyaran jirgi suka ce kunyi sabani yanxu ashruf da axixa suka biku
mr Johnson yace, kai yanxu da daddaren nan xasu nufi wannan hanya, shi ashruf din bashi da
hankali ba xai gaya mata nisan wajen ba?
dayan yace babu abinda bai fada mata ba amma tace lallai ya dauko jirgi su tafi. Hankalin
sauran ya tashi musamman Mubarak suka rasa yadda xa su yi. Mubarak yace, lallai a dauko
jirgi a bisu a kira su. Wasu daga cikin su suka ce a kyale su ida suka ga ruwa xasu dawo don
yanxu an fara yayyafi.
Ashruf shi dai tafiya yake yi kawai yayyafin yana jijjika su. Can suna tafiya sai jirgin ya mutu inji
ya daina aiki. Ashruf ya mike tsaye yaja belt din da ake tayarwa ya yi ta tayar da injin amma
jirgin nan ya ki ya tashi. Axixa ta daka masa tsawa tace, malam ka tada injin nan In xaka tayar
dama ka san injin bashi da kyau ka dauko mana wannan jirgin ko babu gas da yawa ne? ga
ruwa nan duk ya fara jika ni, ashruf dai baice da ita komai ba yaci gaba da tayar da injin yayi
yayi injin nan yaki tashi har ya gaji ya xauna, ruwa sai sake tsugewa yake. Ashe ahsruf dama
yayi shirin ruwa sai ya dauko rigar ruwa ta leda ya saka ya juyawa axixa baya yayi xamansa,
sanyi da jikewa suka gallabi axixa ga yar karamar rigar da ta saka sak duk ta soma jikewa.
Axixa tace, nifa sanyi nakeji, wato dama da niyya ka dauko jirgi marar kyau kaxo tsakiyar ruwa
ka ajiye ni ko, to sai ka raina kanka. Ka tashi jirgin nan ka mayar da ni na fasa xuwa. Ashruf
fuskarsa cike da murmushin dadi baice komai ba ya luf a cikin rigarsa. Can axixa ta hango wata
rigarsa wadda yake kamun kifi da a! ita kot ce ta jawo ta kade ta yaba ta a jikinta sai ta xabura
ta warar da ita gefe tace karni sannan tayi tsaki. Ashruf ya juyo ya dubeta yace rigar
matsiyacinda baya so ya huta sai bautar banxa kuma baiyi kudi ba sai kamun kifi kin san dole
tayi karni. Axixa ta fusata tace ka tashi jirgin nan ka juya da ni kafin ranka yabaci, dabba kawai.
Ashruf ya ce yau kashe ki xanyi, dan a cikin ruwan nan xan jepa ki kipaye suyi bandar ki sai
naga iya ji da kai din naki, ni kuma daga nan kasar mu xan koma .... Lol.
.
Ga littapi dai iya littapi, dadi ba'a magana amma sai naga kamar en gidan nan basu shirya ba
dan bana ganin comments kaman ruwa, sai da na tambaya lokacin da aka shirya amma aka ce
jiya, da son ganin jama'a a daure ana comments,
Idan kuma littapin ne baiyi ba sai kuyi magana.
Dboy
[8/28, 9:44 PM] ️ " ️ D'️️Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK
WHATSAPP 08064400100_
[8/28, 9:46 PM] ️ " ️ D'️️Y: .KWANA ASHIRIN DA HUDU.
*3*
.
.Can axixa ta hango wata rigarsa wadda yake kamun kifi da a! ita kot ce ta jawo ta kade ta yaba
ta a jikinta sai ta xabura ta warar da ita gefe tace karni sannan tayi tsaki. Ashruf ya juyo ya
dubeta yace rigar matsiyacinda baya so ya huta sai bautar banxa kuma baiyi kudi ba sai kamun
kifi kin san dole tayi karni. Axixa ta fusata tace ka tashi jirgin nan ka juya da ni kafin ranka
yabaci, dabba kawai.
Ashruf ya ce da kenan axixa,
axixa ta ji yau ya kira sunanta gatsai kuma har kamar yana yi mata musu. Ta ce wato da biyu ka
kawo ni nan ko?
Ashruf yace ni ban daure ki ba na jawoki, ke kika tilasta min na taho ashe don a koya miki
darasi ne kika ce mu taho, yace Allah sarki talaka shi ba mutum bane, dan bashi da kudi sai ya
yini a ruwa kema yau sai ki dandanan ruwa kiji yadda yake ji, anan xamu kwanan. Axixa ta ji
wani takaici da kunci don a rayuwarta yau ne rana ta farko da ta taba haduwa da kunci da
wahala irin ta yau.
Ta yi shiru can dai taga sanyin nan da gaske yake xai illata ta sai ta jawo rigar nan mai karni ta
saka tana sauraron taga yadda Allah xai yi da