Showing 30001 words to 33000 words out of 73529 words
Chapter 11 - KWANA 24 BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS -1.pdf
Unknown
29 Jun 2025
3603
a kashe sai ta hakura tana xaune ko
gyangyadi babu a idonta balle barci, sai tunani iri iri. Ashruf kuwa nan bakin ruwa ya kwana a
xaune yana tunani ya fi kaunar mutuwarsa da ci gaba da rayuwarsa a duniya tunda babu axixa.
Washe gari da sassafe axixa ta ji motsin mutane……… .
Comment da sharhi su suke kara karfin guiwa gashinan yau har da biyan bashi na shekaranjiya
[9/1, 6:15 PM] ️ " ️ D'️️Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK
WHATSAPP 08064400100_
[9/1, 6:17 PM] ️ " ️ D'️️Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU PT2
*10*
.
.
Washe gari da sassafe axixa ta ji motsin mutane da motoci ta tashi ta leka sai ta ga su
mubarak ne suke xuba akwatina a mota wai tun karfe shida jirgi ya kamata ya tashi amma
jama,a da yawa sun makara yanxu karfe bakwai na safiyar yau xai tashi don haka har motoci
sun xo daukarsu ,ta yi sauri ta fada wanka tana brush ne ta ji ana kwankwasa ,mata kofa .ta
gama ,ta fito ta bude ta ga atika dauke da kayan sawarta a hannunta ta ce ashe kin tashi?
axixa tace eh, na tashi. Atika tace yi sauri ki shirya kowa ya fito xamu tafi yau dai sai najeriya
inda kike son xuwa. bata ce da ita komai ba don takaici, tace a ranta ai ni yanxu na fi tsanar
Nigeria ma da ko’ina, saboda anan ne xa’a aura min mubarak.
Bayan ta kintsa daman tun asuba ta yi sallah sai ta hada komatsanta suka yo kasa. A hanyarsu
ta saukowa kasa tana kokarin gwada wayar ashruf amma shiru a kulle, hankalinta ya yi kan
sakonta da xata karba a reception da ashruf ya bayar a ajiye mata, amma babu hali duk inda ta
yi sai taga su atika da munnira makale da ita mubarak ma ya hangota ya xo ya isheta da sannu
yaya jikin ki? Me ya sameki a ido? Ciwo yake?
Haka ta hakura suka shiga mota ita da atika da munnira ne kadai a motarsu su mubarak ma
motarsu daban daddy da jama’arsa suma motarsu daban. Bayan kowa ya shiga motar xuciyar
axixa ta dinga xullumin bata karbi sakonta ba, sai ta yanke shawarar taje kawai ta karbo koma
me xa a xarga a xarga. Har an bude get xa su fita tace da direba ya tsaya ta yi mantuwa aka
tsaya ta fito da sauri ta shiga reception. Matar da aka bawa sakon na ganin axixa sai tace
yauwa tun jiya ya bani sako in baki yace…
Sai ga muryar alhaji ahmad yace yace me? Suka juya da sauri sai axixa taga babanta. Nan fa
matar ta yi sauri ta canja xancen tace yace ya kai abinci ya jere akan tebur. Dake tun jiya matar
ta fuskanci soyayyar da ke tsakanin axixa da ashruf sannan alhaji ahmad baban axixa baya son
abin don haka ta san mai jera musu abinci namiji ne sai tace yace ya jera abinci, axixa ta yi
ajiyar xuciya ta ji dadi ainun da wannan dabarar da matar nan ta yi tace ai mu har mun fito
xamu tafi xamu ci a jirgi mukullin dakinku ne na manta ban baku ba gashi. Ta mikawa matar ta
dauko kudi mai yawa ta bata. Axixa ta mika mata hannu suka gaisa ta yi mata godiya suka yi
sallama.
Hawaye ne yake xuba daga idanun matar don tausayin masoyan nan axixa na gaba babanta
na biye da ita harta shiga mota, xuciyar ta cike da bakin cikin bata karbi sakon ba, bata san me
ye ba kuma. Suka isa filin jirgi suka tsaya a inda motoci ke tsayawa, ma’aikata suka dinga dibar
akwatinansu suna shiga wajen da matafiya ne kawai xasu shiga inda daga nan sai cikin jirgin
wato (screening) axixa sai hange hange take yi ko ta hango ashruf, har jikin wayar daya ce su
hadu ta waiga baya nan sai hawaye ya yi ta xubo mata tana cewa a ranta ashruf sai a
Darussalam kenan rabuwarmu ta xo rabon da in ga kyakkyawar fuskarka tun jiya da yamma da
daddare bamu hadu ba. ta hango su mubarak har sun fara shiga screening ta juya bayan ta ta
ga babanta na biye da ita sai ta saduda ta hakura ta nufi dakin screening. Kamar daga sama ta
ji an kwala mata kira. Ta juya da sauri don taga mai kiranta. Babanta ma ya juya da saurinsa
harda tsayawa cak kamar shi aka kira. Matar ta karaso wajen da axixa da mahaifinta suke tsaye
tana hucin gudun da ta sha ta ce, axixa gashi kin yi mantuwa a reception da kuka tsaya. Allah
sarki wannan matar ce ta reception din hotel taga ba xa ta iya barin axixa ta tafi ba tare da ta
san me ashruf ya rubuta a jikin wasikar nan ba. alhaji ahmad sai gwale ido yake ya ga me ta ba
wa axixa amma axixa ta damke kam a hannunta, ta mikawa matar hannu suka gaisa sannan ta
rungume ta dan farin ciki, suka yi sallama su axixa suka shige matar ta juya ta tafi.
Alhaji ahmad yace da axixa duk kin rikice kin dagule gashi er tsayuwar da kika yi saida kika yi
mantuwa, me nene da kika manta?
Axixa tace waya tace na mance. Bayan sun shiga an gama binciken passport dinsu da komai
da komai sai aka umurce su da su yi sauri su wuce jirgi ya kusa tashi. Suna tafiya xuwa wajen
jirgin ne axixa ta samu ta kutsa can gefe, gefen da babu wani a cikin abokan tafiyarta, sai
turawa, su kuwa babu ruwansu da leke-leke, ta ware wasikar da sauri sai taga wani gallelen
xoben diamond wanda in har xa a kiyasta da kudin Nigeria xai yi dubu dari uku. Ta juya xoben
ta sake jujjuyawa sannan ta karanta wasikar kamar haka.
Axixa.
Kar ki yi aure ni ne mijinki wannan xoben kuma ki karbeshi a matsayin sadakinki, xan xo
Nigeria in taho dake, ga sadakinki! Sadakinki!! Sadakinki!!!
Har sau uku, axixa ta cukwikwiye wasikar ta hada da xoben ta danke a hannunta ta runtse ido ji
take dama kasa ta bude ta tafka ciki ta fada ta mutu ta huta. Sannan ta saka xoben a hannunta
tana jujjuyashi, kamar dan ita aka kera xoben nan sai walkiya yake yi. Can a karkashin
xuciyarta ta ji maganar babanta ta fado xiciyarta daya ce “kin auri mubarak kin gama” ta yi tsai
tana tunanin tabbas babu yadda xa a yi a barni a xaune haka babu aure dole xan yi aure idan
kuma na cewa ashruf na karbi sadakinsa na yi karya dole xa a yi min aure. Sai taxare xoben ta
nufi tebur din wani ma’aikaci da yake rubuce rubuce. Ta ce ya bata takarda da biro da sauri don
ta hango daddynta na nemanta har su atika sun shige jirgi, cikin sauri ta rubuta “no” ma’ana a’a
sai ta nade xoben a cikin takardar tace da ma’aikacin ka kaiwa ashruf don Allah. mamaki ya
rufe ma’aikacin nan yace mata wane ne Ashruf?
Agigice take ga abbanta nan yana dube dube, yana tambaya shi da ‘yan korensa a bayansa.
Hayaniya ta ji a bayanta tana juyawa sai ta hango ashruf ne da ma’aikata ya shigo screening
room bashi da passport ba tikitin shiga jirgi suka tarashi. Shi kuma a gigce yake yana hango
axixa xata tafi, shi ne ya shigo a guje. Axixa tace da ma’aikacin wancan da aka rike shi ne
ashruf ka bashi don Allah. ta dauko kudi ta bawa dan aiken. Ai yana jin dumus a hannunsa sai
ya mike ba tare daya kara sakon daya ba, da sauri ya bi ashruf don ‘yan sanda sun kamashi
xasu yi waje dashi. Axixa na waiwaye tana ganin wanda ta aika ya mika masa sai ta juya da
sauri tana hawaye ta nufi jirgi. Tana jin muryar ashruf yana kiran sunanta.
Daddy ya tafi nemanta shi kuma an tafi nemansa saboda axixa harta rigashi shiga jirgi saida
ibrahim ya fito ya kira su yace ai axixa tuni ta shiga jirgi, sannan ya dawo suka shiga. Axixa a
kusa da wata karamar yarinya ta xauna ‘yar turawa don bata son ta xauna kusa da daya daga
cikin abokan tafiyarta a dameta da tambayoyi don haka ta tafi can baya ta xauna kusa da wata
‘yar yarinya. An rufe kofar jirgi, jirgi yayi haramar tashi, kuka mai tsanani ya keto mata marar
kakkautawa, xuciyarta sai fat fat take kamar xata fado, yawun bakinta ya kame. Radadi da xogi
a kwayar idonta, farin ciki ya gushe mata, ji take kamar tunda take a duniya bata taba yin
dariyar farin ciki ba. wani sabon son ashruf ya sake sarketa, tsanar Nigeria ta shiga xuciyarta.
Sai da ta fara karanto inna lillahi wa’inna ilaihi ra ji’un da sauran addu’o’I sannan ta fara jin
wasai hawayen ne dai bai daina xuba ba. ‘yar karamar yarinyar nan na kallonta itama sai ta fara
hawaye don ta san idan taga babba yana kuka to tabaci ne. ta ringa gitsuro tissue tana mikawa
axixa tana karba tana share hawaye, har dai kukan ya tsaya mata jirgi kuwa ya lula yaketa
gajimare ya bude wuta sai gudu yake a sararin samaniya ba kakatawa.
Al’amarin ashruf kuwa bayan ‘yan sanda sun kamashi suka yi waje dashi da ma’akacin da axixa
ta aiko ya xo ya mika masa sako, ya juyo ya kalleta ta kalleshi kana ta juya da sauri ta tafi sai
hankalinsa ya tashi bai ma damu da ina ‘yan sandan nan xasu kaishi ba suka nufi motarsu xasu
sashi a mota su je osfishinsu ya yi bayani me ya shigo da shi screening room tunda shi ba
matafiyi bane, sai dai ko in sata ya xo yi. Sai ga mr Johnson nan, nan fa suka yi ta dogon
turanci yace a shaukin so yake har ya fara xautuwa budurwarsa yake bi. Dake ‘yan sandan turai
ne da bayanin mr Johnson ya gamsar dasu sai suka sake shi.
basu ce sai sun tafi dashi ba, sun dai lalubi na goro kawai. Mr Johnson ya sa ashruf a gaba
suka doshi wajen daya ajiye mota, a lokacin ne ashruf ya bude jukukkuyar takardar da axixa ta
aiko masa. Yana budewa yaga xobensa bata karba ba, yayi sauri ya duba jikin takardar ya gata
rubuta no. wato ba xai yiwu ba ta karbi sadakinsa ta ki yin aure. Nan fa ashruf ya tsugunna ya
rike kai wani hawaye mai wuyar fita ne yake keto masa kai kace ruwan hawayen da barkono
aka dama don radadin fitarsa. Nan kuwa tsabar tashin hankali ne. kara yake yana cewa axixa
ba kya so na daman kika dawo min da sadakina dana ba ki?
Mr Johnson ya ji haushin ashruf ya kamashi ya ma rasa me xai ce masa, shi a wajensa soyayya
bata lokaci ce, idan ba kudinsa aka taba bame xai sa shi ya shiga tashin hankali irin na ashruf
haka?
Mr Johnson ya fusata yace da ashruf na fa gaji da irin wannan rashin hankalin, ka yinan in bi
ka, ka yinan in kamo ka, sai in hada ka da en sandan can su tafi da kai, gobe mu yi tafiyar mu
Croatia , ba xamu jiraka ba, kuma da kudin ka xan tafi babu wanda xai bar maka kudin jirgi.
Soyayyar banxa an baka kudi an baka farin ciki. Ka tashi mu ta fi na ce maka. Yayi yayi ashruf
ya ki tashi daga tsugunan nan. Sai daya shiga lallashi yana yi masa dabaru kai ka ce yaro ya
samu dan shekara bakawai wai ashruf ka yi hakuri xan kaika Nigeria da kaina ka ga axixa.
Ashruf dai na jin sa yana fadin yaro xaka yiwa wannan wayon, a ransa. Daga karshe dai ya
goge hawayen sa ya tashi suka karasa wajen mota suka shiga sai hotel din da suka sauka, ya
yarda da kaddara tunda shi musulmi ne.
ABUJA NIGERIA
Su axixa basu isa Nigeria ba sai karfe shida na yamma, saboda tsaye-tsayen da suka sha yi a
kasashe iri-iri suna sauke matafiyan kasar suna daukar wasu. Kafin su karasa Nigeria daman
an san da xuwansu don haka wasu galla-gallan motoci ne sun doshi guda ashirin suka xo
taryensu. Motocin gidansu atika sun xo da ‘yan gidansu, haka mubarak, munnira, sadik, Ibrahim
da ta gidansu axixa. ‘yan uwa da abokan arxiki su hallara a filin jirgin nan don murnar ganin
axixa, hankali ya tashi da aka ce an rasata. Bayan an gaggaisa nan fa aka dungum gidan su
mubarak saboda hadaddiyar liyafar da alhaji isah ya shirya musu. Musamman ma dai don axixa
ya yi ta ta sannu da xuwa da barka da arxiki da aka ganta. An ci an sha an cashe yara da
manyansu maxa da mata. Amma axixa karfin hali ta yi don babu walwala a xuciyarta kowa ya
ganta ya san ba axxy ta da bace. Ta wani kode ba kwalliya ido ko kwalli babu hawaye ya
wanke.
Bayan an gama shagali kowa ya wuce gidansu. Alhaji ahmad baya gajiya da yiwa axixa
nasihohi iri-iri dan ya ga hankalinta ya kwanta haka atika ma tana yawan xiyartar axixa tana
bata baki duk da dai har yanxu basu san me ke damunta ba. daga mahaliccinta sai ita sai
babanta suka sani, don haka su a tunaninsu batan da ta yi ne ta dawo haka, kullum cikin
damuwa take. Da kyar da rubutun sha na dangana da addu’o’in da alhaji ahmad ya sa ake yi
mata ya sa ta fara sakin jikinta tana rage damuwa. Alhaji ahmad ya roketa Allah, Annabi ta ringa
kula mubarak kamar yadda suke da don shima yaron duk al’amuransa na walwalar yau da
kullum duk sun canja har mahaifinsa ya fara cewa shi kwana biyu ya ga dan sa ya canja axixa
ma ta canxa . Axixa ta yiwa mahaifinta alkawarin in Allah Ya so xata yi kokarin ta cire tunanin
ashruf kuma xata dinga kula mubarak. Ya ji dadi da abinda ‘yarsa ta fadi yayi mata addu’a Allah
Ya yi mata albarka Ya kuma bata da na gari wanda xai yi mata biyayya fiye da yadda take yi
masa.
Siyasar Nigeria ta yamutse xabe yana tunkarowa don yanxu saura wata tara xabe. Haka kuma
auren mubarak da axixa bai fi sauran wata goma ba. don haka duk inda ka ga axixa ka ga
mubarak. Wata sabuwar soyayya ceta sake budewa, hankalin mubarak ya kwanta haka na
iyayensu, kai har ma kawayenta su atika da munnira. Axixar su ta dawo irin tada, su je ko ina
tare kamar bikin auren kawayensu, bairthday parties na kawayensu su fita wuraren shakatawa
iri-iri na Abuja kamar su 911, millennium park da dai sauransu. Bayan dawowarsu da wata biyu
ne wata ranar asabar mahaifin axixa yake liyafar murnar xagayowar ranar haihuwarsa ya cika
shekara hamsin da biyar a a duniya. Ya hada hadaddiyar liyafa a babban dakin taron nan a
nicon Abuja , gaga-gaggan ‘yan siyasar Nigeria sun hallara abokan kasuwancinsu daga
kasashe daban daban sun hallara, biki bidiri ya fara da karfe hudu na la’asar. Har da axixa da
kawayenta mubarak da abokansa ‘yan uwa da abokan arxiki, kowa ya xo. Ana ta wasa da
dariya, ciye-ciye da tande tande. Mahaifin mubarak ya kalli mahaifin axixa yace da sauran
jama’ar ni kuwa ina son ku tayani yiwa shugaban fada yaki ya yi aure. Wane irin shugaban kasa
xamu yi a Nigeria babu first Lady?
Duk wajen aka sa dariya, harda su axixa. Da yawa suka yi ta mamakin ya aka yi mutum
magidanci mai kamala da rikon addini bashi da aure. Alhaji ahmad shima yayi dariya sannan
yace da alhaji isa ka fada musu bayan rasuwar uwar gidana aurena nawa me kuma yake rabani
da matan?
Alhaji isah yace baka so a batawa wannan ‘yar diyar taka axixa, to axixar na aure xata yi ta bar
ka. Alhaji sadam yace maigirma shugaban kasa ka bashi kunya nan da sati daya ka yi aurenka
kar fa a xo ana bikin ‘ya’ya ana na iyaye. Nan ma kowa ya tunsture da dariya. Alhaji ahmad yayi
murmushi yace af! Kune baku sani ba nan da wata daya xaku ga katin gayyata don na sami
mata har an sa rana. Haka dai ana xolayar dan takarar shugaban kasa ana kyakyacewa har
karfe bakwai bayan an ci an sha an gyaste sannan aka yi salla aka fara watsewa. Bayan axixa
da kawayenta sun fito ne sai munira tace xata je maitama wajen wata auntynta . axixa da atika
kuma suka nufi life camp unguwar su axixa. Axixa ce ke tuka galleliyar motar da babanta ya
galla mata bayan dawowarsu, daga tafiya. Sun kusa shiga layinsu sai cikin axixa ya fara
murdawa.
Ta cije bata yi Magana ba, ta ji da gaske yake ciwo. Ta sulale gefen titi ta tsaya, atika tace lafiya
kike cije baki kuma kika tsaya?
Axixa tace cikina ne yake murdawa haka yake yawan yi min kwanan nan. Sai in dinga jin kamar
‘ya’yan hanjina xasu xubo. Atika tace subhan Allahi, fito in tuka mu karasa gida. Da kyar axixa
ta fito ta dawo wajen atika, atika ta shiga ta tuka suka nufi kataferen gidan su axixa. Masu gadi
‘yan sanda suka bude babbar kofar shiga gidan da sauri gami da sarawa uwar dakinsu, suka
wuce. Da taimakon Allah da taimakon atika axixa ta iya fitowa daga motar nan suka shiga cikin
gida. Atika xata wuce da ita dakinta a sama tace ta barta a falon farko xata kwanta a kan kujera.
Atika ta kwantar da ita kan doguwr kujera, tana ta yi mata sannu. Kowa ya ga axixa ya san ba
karamar ukuba take ji a yau ba. ciwon ciki ai bala’I ne. atika ta nufi bandakin dake cikin