Showing 69001 words to 72000 words out of 73529 words

Chapter 24 - KWANA 24 BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS -1.pdf

Advertisement

Unknown   

29 Jun 2025

3591

mike ya karasa inda take suka dau kusan mint biyu suma kallon junansu.
Yasa hannu shafa gashin kanta a hankali tayi sauri ta sake ja da baya. Yayi murmushi cikin
sanyayyar murya mai’ kasha jiki yace “Aziza kina gudu na ne?” ya jawo ta kirjinsa ya rungumeta

ta fashe da kuka, kuka mai tsanani. Wannan kuka na Aziza ya tayarwa da Ashruf hankali sosai,
ciki rudani yace “Aziza mai nayi miki kike kuka?” cikin sheshekar kula tace “Ashruf naji na tsni
kaina kuma na tsani wannani rana” yace “me yasa Aziza?” tace “kowacce mace tana alfahari da
wannan dare in mijinta ya same ta cikakkiyar Budurwa, amma ni mai zancewa mijina a yau?” ta
sake rushewa da kuka, yayin da ta fisge jikinta dage kan kijinsa. Yayi sauri ya jawo ta gam ya
rike ta yace “Aziza ya kike magana kamar wata yarinya waye mijin naki in ba ni ba. Wane
bayani kuma zakiyi min bayan na sana mai ya faru? Haba Aziza kar ma ki sake damun kanki,
tun ba yau ba na sanan ke kimalalliya ce, kin kuma tsare mum kanki na gode, Allah yayi miki
albarka. Ya rungumeta, yana goge mata hawaye yasa harshensa yana lasar gefen wuyanta,
tayi dan murmushi tace “ni sake ni zanje in shafa mai Ashruf yace “to muje in shafa miki man”
Ta dan haraeshi cilin shagwaba tace “na fasa” cimak taji ya dauke ta tamkar wata jaririya ya
kaita kan katafaren gadon dake dakin, yasa hannu ya kashe fitila.
Washe gari Ashruf na kwance akan doguwar kujera kansa a kan cinyar Aziza tana shafar
gashin kansa suna hira suna kallon AIT news kwatsam aka nuno Alhaji Isa Elyakubu a kotu.
Kotu ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai har yanzu bai sadam da Alhaji Elmustapha babu
abinda yake, har da alkali da ministocin Nigeira da duk ‘yan Najeriyar ma luka musu ashar
y’a’’ke ‘kamar tababbe. ‘Yan sanda suka tura kcyarsa cikin mota aka tafi da shi a kiri aka
kulleshi. Dadi ya lullbe su Aziza dai dai lokacin Atika ta bugo musu waya’ zata basu labari suka
ce sun gani suma, Munnira ta bugo waya suka taya su murna yau anyi musu maganin
azzalumin nan.
Bayan biki da wata guda Alhji Elmustapha ya kira Ashruf ya ce ya shirya shi da matarsa suje
Libya da Katsina suka dangi, dangi ma su gansu. Haka kuwa aka yi, Liya suka fara zuwa wajien
dangin Hajiya Fatima mahaifyar Ashruf. Ansha murna da koke ko a mafarki basu taba zaton
zasu ganta ba abce musu ta haukace wasu kuma sunce ance ta rasu an turasu a rami duk sun
rasu. Taji birane da kauyuka wajen danginta suka ganta da mijinta da danta da surikarta,
satinsu uku a Libya suka wuce Katsina. Wai! ansha mamaki nan ma da aka ga Alhaji
Elmustapha don su a yadda labari ya kai musu shine ya dade da mutuwa. Wasu kuma suka ce
ance y zama gurgu yana bara amma sai suka ganshi shar da shi Kada daga cikin masu ilimi
masu karanta jaridu suka ce sun ganshi a jarida ana shari’a da Alhaji Isa Elyakub. An taryesu
hannu bibbiyu musamman da aka gansu da ‘yar shugaban kasa kamar a hadiyesu basu baro
Katsina ba sai da aka danaasawa Alhaji E;mustapha sarata dan Isa Katsina aka sha bikin nadin
sarata daga karshe suka yi kwanakinsu suka juyo zuwa Abuja.
Bayan sun dawo ne Munnira da Dr. Rislan suka gaiyaci Aziza da angonta, Atika ma da nata
angon zuwa cin abincin dare a gidans. An harhada abinci lafiyayyu akan dining table a nan suka
hadu su shida suka zazzauna kowacce a kusa da angonta suna cin abinci suna hira. Aziza ta
ce “Tasya in baku wani labari amma fa gulma ce zan yi muku kuma ku yi gum da bakinku kar inji
a gari. Amana zan baku ta bakin yara’’. Suka tuntsire da dariya dukkansu suka ce ‘’mun yarda’’.
Ta ce ‘’jiya naje gida na iske anti shariga tana ta kwara amai dady ya yi dagaje yana rike da ita
wai ciki ne da ita’’. Suka kylkyale da dariya suka ce ‘’amman wanna gulma da dadi take’’.
Atika ta ce ‘’wai! wa ya ga aziza da kani ko kanwa?’’ ta yi dariya ta ce ‘’waya ga dady da sabon
da dai zaki ce, shekara ashirin da biyar fa ba kara yi masa haihuwa ba itama anti shariga
shekararta goma sha tara da aure bata taba haihuwa ba’’. Ashruf ya yi murmushi ya ce ‘’dan
shekara ashirin da biyar, to nima bari in tsegunta muku ummata shekara kararta talatin da wani

abu rabonta da haihuwa to itama dai dan karamin ciki gareta’’. Suka sake tuntsirewa da dariya
dukanu’’. Wayar ahruf ce tayi kara ya daga ya duba lambar ya ce ‘’ban san lambar ba bata
kasar nan ba ce bama’’. Sannan ya matsa kamar daga sama ya ji muryar mr. johson ya ce
ashruf ango, ka yar da mai gidan ko ‘’. Ya ce ‘’kamar mr. johnson’’, ya ce ‘’ni ne mana’’. Nan
murna ta hargetic tsakanin ashruf ya ce ‘’da mamaki, ina ka samu lambata?” ya ce ‘’ a wata
mujala (obession) na ga bikin da lambobin waya’’. Ya tayashi murna kwarai da gaske, Aziza ma
ta karba suka gaisa ta yi masa ya ya jiki? Ya ce ya wartsake ras sai dai dan dingishi yake yi
yanzu. Atiku da munnira sun karbi wayar sun gaisa daga karshe Aziza ta karbi wayar ta ce
farkon shekara zasu zo ya tanadar musu jirgin ruwa mai kyau zasu fitop yawon shakatawa da
mazansu, ya ji dadi kwarai don yasan shekarar cikinsu tazo. Suka yi sallama ta kashe waya,
sannan suka ci kcyarsa cikin mota aka tadi da shi a kiri kiri aka kulleshi. Dadi ya lullebe su Aziza
dai dai lokacin atika ta bugo musu waya zata basu labari suka ce sun gani suma, Munnira ta
buho waya suka yiwa juna murna suka bugaea iyayensu waya suka taya su murna yau anyi
musu maganin azzalumin nan.
Bayan biki da wata guda alhaji elmustapha ya kira ashruf ya ce shirya shi da matarsa suje libya
da katsina suga dangi, dangi ma su gansu. Haka kuwa aka yi, libya suka fara zuwa wajen
dangin hajiya fatima mahaifiyar ashruf. Ansha murna da koke koke ko a mfarki basu taba zaton
zasu gant ba ance ta rasu an turasu a rami duk sun rasu. Taje birane da kauyuka wajen
danginta suka ganta da mijinta da danta da surikita, satinsu uku a libya suka wuce katsina. Wai!
ansha mamaki nan ma da aka ga alhaji elmustapha don su a yadda labari ya kai musu shine ya
dade da mutuwa. Wasu kuma suka ce ance ya zama gurgu yana bara amma sai suka ganshi
shar da shi. Kadan daga cikin masu ilimi masu alhaji isa elyakub. An taryesu hannu bibbiyu
musamman da aka gansu da ‘yar shugaban kasa kamar a hakiyesu basu baro katsina ba sai
dandasawa alhaji elmustapha sarauta dan isan katsina aka sha bikin nadin sarata daga karshe
suka yi kwanankisu suka juyo zuwa Abuja.
Bayan sun dawo ne munnir da Dr. rislan sukaa gaiyaci aziza d angonta, atika ma da nata angon
zuwa cin abincin dare a gidansu. An hahada abinci lafiyayau kowacce a kus da angonta suna
cin abinci suna hira. Aziza ta ce ‘’tsaya in aku wani labarii amma ce zan yi muku
Gaba da tsara yadda zasu yi tafiye tafiyensu kasasahe daban daban har ASHIRIN DA HUDU
zasu zagaya don sai sun shafe watanni shida a can.
DAYA GA WATANDAYA (JANUARY)
Su Aziza sun shirya tafiya tauka yiwa iyayensu sallama suka ce zasu fita hutawa kasashe
daban daban. Iyayensu sunyi mu su fatan alheri allah ya kiyaye sunyi musu fada akan su rike
junansu bisa amana, su zamana masu tsoron allah. Sannan amare da angwaye suka shiga jirgi
suka fara ashirin da hudu anan. Ranar ashidrinm tsari ta ce “su yi kwana ashirin da hudu anan.
Ranar ashirin da biyar ga watan daya suka dira a croatia saboda haka suka yi waccan shekarar
an waccan tafiyar su su mr. johnson suka zo filin jirgi suka taresu sai da aziza ta tuna ranar da
suka fara zuwa croatia suka hadu da ashruf. Hotel din da aka saukesu da suka ce a sauke su
anan daman daman jirgin ruwansu da aka tanadar musu yana nan yana jiransu.
Ashruf da aziza suka kira mr. johnson suka debi makudan kudi suka bashi suka rurrubuta masa
wasu kayayyaki kamar katifa guda uku, barguna uku, zanin gadajc uku filulluka shida electric
stove (risho) da sauran karikicc dai. Sauran sunyi matukar mamakin su aziza da suka sa a sayo
musu wadannan kaya suka tambayesu me zasu yi da katifu da su risho sai Aziza ta basu amsa

da cewa su zuba ido kawai idan lokaci ya yi zasu gani.
DAYA GA WATANBIYU (FEBRUARY)
Ranar daya ga watan biyu da misalin karfe goma sha biyu na rana amare da angwayensu suka
fito daga hotel din da suka sauka a croatin zuwa filin jirgin ruwa da kayansu don tafiya yawan
shakatawa a jirgin ruwa. Wannan karonma su kadai suka dauki shatar jirgi gaba daya. Daga su
sai ma’aikatansu kuku guda uku, masu shara da goge daban, mai shiga ruwa ya kamo kifi
shima daban, akwai injiniyoyi masu gyaran jirgi koda zai iya samun matsala, likitoci da kayan
aikinsu koda wani zai iya samun rashin lafiya. Matuka jirgi shugababan su kakaf Mr. Johnson
(Chief in charge) Wannan karan komai ya banbanta jirgin komai sabo ne na zamani aka sake a
cikin jirgin nan. Da kuma da samrinsu suka taho amma yanzu da mazansu na aure suke tafe,
don haka tafiyar tafi armashi. Kowacce ta kama daki daya da nata angon suka zuzzuba
kayansu a ciki. Abokan Ashruf masu dafa abinci da masu share share sai suka hau mamaki
ganin Ashruf ya auri Aziza. Azizar da ta takura masa ta tsaneshi ta rainashi fiye da kowanne
dan aikii yau ga Ashruf tya fi kowa matsayi a wajen Aziza. Suka ga Ashruf ya yi shar da shi
kamar ba shi ba ya yaga musu yanzu shi ne ogansu sune masu yi masa hidima. Amma Ashruf
bai yar da abokantakarsu ba yaje wajensu suka zauna suna ta hirar yaushe gamo kamar yadda
suka saba hira da.
Jirgi ya ware fanya ya saki tayoyi a ruwa ya bude wuta yana gudu a kan ruwa amare da
angwayensu sun shiga yawon duniya don shakatawa. A ranar mahaifin Ashruf ya bugo masa
waya ya ce shi da mahaifiyarsa suna Amerika, ya samar masa admission a wata jami’a dake
cikin babban burnin Amerika Washington. Don haka ya turo adireshin email don zasu ringa turo
masa darussan da sukeyi ta internate. Ma’ana ba sai Ashruf ya je Amerika ba ya shiga aji ya
dauki darasi a duk inda yake malaman zasu dinga turo masa abubuwan da suke koyarwa a aji
yana karantawa da ga kasar da yake sai dai lokacin jarabawa ne kawai zaije can ya zana
jarabawa shi ke nan a cikin shekaru biyu zai kammala digiri dinsa. Daman mahaifinsa babu
abinda ya tsaya masa a rai sai rashin cigaba da karatun wannan dan nsasa kawalli daya
Ashruf. Yanzu Allah ya basu yadda zasu yi. Ashruf ma ya ji dadin wannan labarin da mahaifinsa
ya bashi cikin rawar jiki ya turawa mahaifinsa adireshin na internet sai dai kawai ya dinga
budewa yana karanta darussan da ake koya musu.
Washegari da sassafe Ashruf ya fito falo shi kadai don dukkaninsu basu tashi ba ya bude
internate dake falon don karanto dokokin sabuwar makarantarsa. Har karfe goma na safe
sannan ya ji muryar Aziza da su Atika sun tattashi sun fara surutansu da suka saba suna
kyalkyala dariya a dakin Aziza suka hadu. Mahmud Sa’ad ya shigo cikin falon suka gaisa ya zo
ya zauna kusa da Ashruf yana tayashi karanta email. Dr. Rislan ne ya y sallama ya shigo ya ce
Shi tun karfe bakwai ya shiga dakin wasa jini ya hau kan keken was jini. Ya ci gaba da yi musu
bayanai irin na likitoci yana basu shawara kamata ya yi su dinga yawan wasa jininsu saboda
maiko zai sami wajen zama a jikinsu idan basa wasa jini suna tsinka shi zai sasu yi kiba. Ashruf
ya ce “Doctor munji”. Suka tuntsire da dariya dukansu. Aziza ta ci kwalliya ta yi kyau sosai da
wata riga da siket din jeans a jikinta ta shigo cikin falon taje ta dafa Ashruf ta baya ta sumbaci
kumatunsa sannan ta rada masa a kunne ya zo dining table suci abinci an fara jera musu break
fast. Ya yi murmushi ya ce taje gashi nan zuwa. Ta juya ta killi Doctor Rislan da Mahmud Sa’ad
ta ce “Good morning guys your food is ready”. Mahmud ya yatsune fuska ya ce “Munki wayon ai
ba haka kika gayawa Ashruf ba nima kira min Atika tazo ta rada min a kunne”. Suka yi dariya su

duka, Aziza ta fice daga falon. Ashruf ya ce suje su fara ci yana so ya gama karanta sakonni ne
da aka turo masa. Mahmud da Doctor Rialsn suak nufi dinning room wajen da matan suke
jiransu. Ashruf na zaune ya ga daya daga cikin ‘yan aikin rike da wani kwanon tangaran ya
doshi dining room. Ashruf ya kirashi ya ce “Mene a a ciki” Ya ce “farfesun kifine Aziza ta ce a
dafa mata”.
Saboda Aziza tana son kifi farfesu, Ashruf ya ce “Ajiye z kai mata”. Ya ajiye akan teburin dake
gafen Ashruf ya tafi.
Ashruf ya mike ya tattare kafar wandonsa da hannayen rigarsa ya dauki kwanan kifin nan ya
nufi dining room inda su Aziza suke. Dr. Rislan ne ya fara hango Ashruf sai ya tabo Mahmud ya
nuna masa Ashruf mamaki ya kamasu ganin Ashruf dauke da kwano ya nade kafar wando da
hannu, ya karaso gaban Aziza ya ajiye kwanan kifi cikin ladabi ya koma da baya ya tsaya kek
kamar yadda yake yi mata da. Ta dago ta kalleshi sai ta tsuntsire da dariya, Atika da Munnirma
suka fashe da dariya suma sun tuna da. Dr. Rislan da Mahmud basu gane wannan dramar da
ake yi ba. Aziza ta bude kwanan kifin ta sa cokali ta gutsira sai ta hau kokarin amai su tika suka
rirriketa ta tofa a shara sai dariya suke tuntsirewa dukkanin su har Ashruf din. Ta yatsune fuska
ta ce “Wannan kifin ya rube aje a canjo min wani”. Ashruf na dariya ya kinkimi kwanan kifi ya
nufi kicin Atika dariya har fau take yi. Mahmud ya ce “Wai dan Allah meye haka mu kun samu a
duhu”.
Mannira ta ce “Au ashe ku bakusan san da aka sha tattaburza Ashruf da Aziza ba ko? To bari in
baku labarin yadda aka yi. Ta gyara zama ta fara fesa musu labari dalla-dalla, suka sha dariya.
Dr. R islan ya ce “Shi ne ake gwadawa yanzu?” Yana rufe bakinsa sai ga Mr. Johnson ya nufo
su Ashruf dauke da kwano yana biye da shi. Suka karaso wajen Aziza ta sha kunu kamar da
gaske Mr. Johson ya karbi kwanon dake hannun Ashruf ribaban kifi ya kawo miki yi hakuri gashi
a cikin sakon ashirin da hudu an dafa miki wani. Mu daku muke alfahari muna sonku amma
munfi son kudinku”. Suka kyalkyale da dariya su duka, Aziza ta ce “Bude kwanon in gani”. Ya
budewa ta kawar da kai gege ta toshe hanci ta ce “Mr. Johnson kwar min da kifin nan daga
gabana na gane irin na dazu ne. To in har ba za ku iya ciyar da ni ba zan fita kasuwar bakin
ruwa in suyo abincina”.
Ya yai sauri ya katseta ya ce “Haba mai girma Aziza ko daya daga cikinmu kike so kici ba’a dafa
miki ba balle kifi fadi ya kike so ayi”.
Dr. Rislan ya fashe da dariya ya ce “Amma Aziza kin musu tsiya ashe”.
Ta ce “Irin wadannan kifin ne ba na so kannana nake so yanzu ya shiga ruwa ya kamomin
kanan”. Suka sake tuntsirewa da dariya. Mr. Johnson ya ce “Ashruf ka ji abinda take so don
haka maza ka shiga ruwa ka kamo mata kifin inda ba haka ba zan koreka daga aiki”> Suka
tuntsire da dariya Aziza ta ce “A’a Mr. Johnson baka ce zaka koreshi da aiki ba”. “Ah, ba wasn
kwaikwayo ba ne? ai kinsan akan kakkara. Ashruf ya marairaice ya ce “To shugaban tafi.” Ya
juya yana tafiyar abin tausayi. Aziza ta mike da sauri ta rukoshi suka rungume juna. Mr.
Johnson ya ciro kyamarar dauke holo ya dauke su a haka. Aziza ta gyaggyarawa Ashruf
kafafuwan wandon sa da rigarsa ta jawo hannunsa suka zo suka zauna adan kujera suka fara
cin abinci suna hira ana tuntsira dariya. Mr. Johnson yana kashe musu fim din kyamara. Dr.
Rislan ya ce “Amma wannan dramar tauo luai oma fatam dao zali ci gaba da yi mana’a duk inda
wani abu ya faru don tuna baya. Ashruf ya ce “Zaku sha kallon darama kuwa yanzu aka fara”.
Haka kuma ranar ashirin ga watan biyu shine ranar da Aziza ta cika shekara ashirin da biyar, da

misalin karfe takwas na dareaka haifeta don haka karfe takwas na da aka fara gudanar da bikin
cikin shkarunta kamar yadda waccan shekarar a jirgin nan ta gudanar da birthday party. Sai dai
wannan karon an kawata wahen fiye da na da birthday party ma ya yi kyau ya yi dadi sosai fifiye
dn da anan ma ashruf da aziza sai da suka gwada abubuwan da kuka faru. Ashruf ya je ya
shige wannan dan saukurutun lungun ya labe yana kallonsu kamar yadda ya yi a waccen sherar
sai da aziza ta zo kamar za ta yi waya sai ta kamo hanunsa sauka fito ana ta dariya. Anci
anshya an cashe an dauki hotuma da bidio cassete abin ba sha’awa. Suna nan har sai da suka
yi KWANA ASHIRIN DA HUDU a cikin wannan jirgi ranar Aziza da Ashruf suka yi shigar
manyan riguna na kayan sanyi suka ce suifa zasu fita zuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login